Showing 33001 words to 36000 words out of 84387 words

Chapter 12 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28144

kin San cewa aiki na wahala a wanna zamanin yanzu ko? Karki yi wasa da aikin ki fa"



Cikin sauri tace "wallahi Anty bintu madam bata gida, tayi tafiya kuma bata fadi ranar dawowar ta ba, dan Allah Adda muje zan biki, ai kwana biyu zaki yi, har mu dawo ma nasan bata dawo ba" Indo ta fada cikin marairaicewa ba tare da tunanin cewa akwai wanda yake matukar bukatar kulawar ta a yanzu ba, saboda zumudin ganin su Inna da twins din ta....





Ban wani yi editing sosai ba, idan kun ga typing error kuyi =?O?



*ko ina madam gloria ta je Readers?*
Muje zuwa...




Share fisabilillah

Comment for more typing




NoorEemaan
07082281566




Thursday, 3 March
7:36pm




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/12, 10:19 AM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM

*First edition*


*WATTPAD*
@NoorEemaan


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



Chapter 37-38


Ganin tarin damuwa da hawayen da suka cika idanun ta yasa Anty Bintu ta sauke ajiyar zuciya hadi da cewa "toh ya isa, zamu tafi tare, amma Karki manta kwana biyu kacal zamu yi, kar mu tashi dawowa ki ce min baki San zance ba" anty bintu ta karasa tana mata hararan wasa.




Ihun murna Aysha tayi ta rungumi Anty Bintu kana cikin farinciki da wani kwarin guiwa ta mike da gudu hadi da fadin cewa "anty Bintu ki jirani bari na dauko kudi muje kasuwar tare"




Murmushi hadi da girgiza kai Anty bintu tayi tana bin bayan ta da kallo.


Aysha tana shiga dakin kuwa ta d'auko kudin albashin ta, rabawa tayi biyu duk da bata San ko nawa bane, kana ta zuro hijab dinta ta kara saukowa da gudu, anty Bintu ta Mike ganin ta taho , da haka suka nufi kasuwa inda a motar gidan da Bintu ke aiki suka tafi, hakan kuma umarni ne daga hajiyar gidan....



******

Sosai Aysha tayi siyaya, ta siyi kayan sawa wa su Anwar kala uku masu saukin kudi kuma iri daya, ta siyawa Inna atamfa da hijab hadi da takalmi flat, sai kayan Abinci hadi man shafawa na yara, da nata da na Innah duk ta Siya, sai man goge baki(toothpaste) da sabulu, har da spices sa veges ta siya wanda tace zata musu had'add'en girki da zaran ta isa gombe kamar yadda tayi wa Innah Alkawari, anty Bintu dai sai dariya take mata domin zallan zumudi yasa Aysha ke siyan ko me ta gani, sai da kudin hannuna ta suka dawo saura dubu uku sannan idanunta suka washe ta hakura hakan nan...




Kallon Anty Bintu tayi cikin marairaicewa tace "Anty Kinga Wai kudin hannuna har sun k'are, ni dana ce zan siya mana kananun wayoyi ni da Inna ta" ta fada, ta na zumburo baki kamar wani ne ya sata siyayyar dole.



Dariya Anty Bintu ta saki, "ho ho hoo Indo ba dai sakalci da yarinta ba, yanzu nawa kudin ki suka rage?"


Dan d'aga kanta sama tayi hadi da juya manyan fararren idanunta alamun tunani sannan tace "ina ji kamar dubu talatin ne, domin nayi siyayyar dubu talatin da bakwai"


"Na gane yanzu,? a takaice dai kudin hannun ki saura 33 thousand ko?"? anty Bintu ta fada.


"33! Menene 33 anty Bintu?"

Murmushi Bintu tayi tace " Toh dubu talatin da uku nake nufi"



"oho! Eh haka suka rage" Aysha ta amsa mata .


"toh bari na ara miki dubu tara anan, sai ki kara da dubu uku ki siya muku wayar ko yar dubu shida-shida ce, idan munje gida sai ki bani ko"? anty Bintu ta karasa tana dafa shoulder dinta.





"yawwa Addah Nagode sosai"

Aysha tace cikin farinciki daya gagara buya a saman k'yak'yawar? fuskar ta.



Da suka je wajen masu waya aka fito musu da kala uku, daya kirar techno, daya airtel, daya kuma bontel, aka fada musu price din, akwai ta 5,500 sai ta 7000 har da na 10k ma, anty bintu tace a basu airtel din dan 5,500 guda biyu,? inda a nan suka siyi simcard a wani shagon register'n layi dake kusa da shagon wayar, sai da komai ya yi normal suka bar kasuwar Aysha sai murna take tayi keypad...




*****

Bayan sun iso Gate din gidan Aysha ta sauka, inda kayan da suka siya yake booth ba kuma za a fito dasu ba, tunda a ciki zasu tafi gombe, wanda hajiyar gidan ta ce a kai Anty Bintu a motar gidan ba sai taje tasha ba, hak'ik'a karamci da mutumcin hajiyar ya wuce misali.





Tunda suka dawo Aysha ta yi sallah ta sauka kitchen da wuri, inda ta dafa wa Abraham indomie da ya sha veges, hadi da kwai domin shi zai yi saurin dahuwa, ita gabadaya ta manta bai ci komai ba tun karin safe, Bayan ta gama ta zuba a plate ta rufe saman da wani plate din ta hau sama tana fatan kada yayi fushi duk da ba magana yake ba, har tana tunani a ranta cewa ko dai wanna cutar da yayi ya sa muryar sa samun matsala ne, domin Abin da? matukar mamaki ace mutum kusan watanin Kenan baya ko gyaran murya bare ya kai ga furta wata kalma...




Zaro idanunta tayi sak'amak'on abinda ta gani, zaune yake kan gado ya jingina bayan sa bed din, a yanda yake zaune ba wanda zai taba tunanin cewa bazai iya tsaye kan kafafun sa ba, inda tunanin ta yafi bata cewa kila mai gadi ko wani daga cikin ma'aikatan gidan ne ya dora shi kan gadon...



Hada idanu suka yi tayi saurin yin kasa da kanta gabanta na tsananta bugu, saboda mugun jaa da kwayar idanun sa suka yi, ga jijiyoyin kansa da suka fito rudu-rudu.



A sanyaye da yanayi irin na tsoro ta ajiye abinci a gefen gadon, a hankali ta ciri murfin da ya rufe abinci inda k'amshin mai dadin gaske ya daki hancin sa, a hankali ya lumshe idanun sa, fork Aysha ta saka kan abinci ba tare da ta kalleshi ba tace "ga Abinci" duk da tasan cewa ba jin abinda tace yayi ba, amma bata da wani zabi daya fi tayi masa magana .


Sai dai ko motsi bai yi ba kusan mintuna biyar, a dame ta dago da idanunta masu kyalli ruwan hawaye ta kafe masa, a hankali ta kamo k'arfaffan hannayen sa a kokarin ta na bashi fork din, ya janye hannunsa da karfi, har hannun ta na buga fork din.




Mamaki tayi sosai, "me yasa yanayin sa ya sanja a yau, ko dan ban bashi abinci kan lokaci bane yasa shi fushi?" ta fada a ranta tana fashewa da kuka.



A fili tace "Dan Allah kayi......"

Katse ta ya yi ta hanyar daga mata hannu hadi da yi mata alamun ta fita ba tare da ya ko bude idanunsa ba...



Kamar Wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta fice tana share hawaye.


Kan bed dinta ta fada tana kuka, daga nan ta fada duniyar tunani.





*ABRAHAM*

Sosai zuciyar sa ke suya, abubuwa da Dama sun cushe masa zuciya, yau kwana kusan uku bai ga Mummy ba, Matar da ke matukar bashi kulawa right from time amma Ashe fuska biyu ce da ita, Kenan maganganun daya ji tana fada rannan kafin hankalin sa ya gushe gaskiya ce, mummy tana so ya mutu, ya bar duniyar kan dalilin ta da bai sani ba, me yasa abubuwa suka taran masa lokaci daya haka, Aysha da yake jin motsin ta a kusa dashi amma yau tun safe bai sake ganin ta ba, ga kukan da ta fita tana yi yana taba sa matuka, Sam bai kamata yayi treating dinta haka ba, bai kamata dan zuciyar sa na zafi ya huce a kanta ta ba, ita din karamar yarinya ce mai tsananin kulawa da sanin ya kamata, basu hada dangi ba, basu hada addini, basu hada komai ba amma still tana kokarin kula dashi da dukkanin iyawar ta, "why did I make her cry" ya fada daga ta ciki yana cije lips dinsa, a hankali ya kai idanunsa kan noodles din, sannan ya kara kawar da? kansa hadi da rufe rikitattun idanunsa, zallan damuwa, hadi da tsananin kewa ne suka yiwa zuciyar sa rubdugu...






_7:45pm_

AYSHA
A nutse ta iddar ta sallah isha kana ta Mike cikin sauri domin dauko Abinci ta bashi, saboda Sam bata so ya kara jin yunwa irin na dazu bare ya yi fushi da ita, domin tafi tunanin cewa barin sa da yunwa da ta yi ne yasa yake fushi da ita, Bayan ta isa kitchen ta dauko warmer mai dauke French fries hadi da chips sai wani had'add'en lemon k'wak'wa da madara da yayi Sanyi a jug kasancewar daga chest freezer ta jiro shi...



Bakinta dauke da sallama ta shiga dakin sa kamar yadda ta saba, gabanta na fad'uwa tana zullumin yanda zasu kwashe ta ajiye tray din kan gadon, inda idanunta suka sauka kan indomie daya sand'are, cikin rashin jin dadin ganin bai ci ko da loma daya ba, dauke indomie tayi daga kan gadon ta ajiye shi a kasan tiles.



"Ga...abin...cin...ka" ta fada cikin cracking voice da amon sa ke bayyana kukan dake son kwace mata...



Shiru babu Amsa bai kuma Bude idanun sa ba, a hankali ta sa dan knife ta yanki French fries din ta tura masa a bakin har yatsun ta na gogan miyau sa, a hankali ya shiga taunar French fries din

farinciki ya cika zuciyar Aysha, ware idaunsa da suka Dan fad'a ciki yayi ya watsa mata su, alama tayi masa da ido kan ga Abincin sa yaci, yayinda take langwabe kanta ba tare da San tana hakan ba.



Kamar karamin yaro mai jiran umarni ya dauki fork da knife ya shiga ci da sauri-sauri alamun ya jigata da yunwa, aysha kuwa zara-zaran yatsun ta masu dauke da ragowar Jan lalle a Farcen ta ta hade cikin na juna tana kallon sa da burgewa...




Yaci da yawa kana ya ajiye, lemon Aysha ta siyaya a tumbler ta mika Masa ya sha sosai???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? har yana lashe baki, ajiyar zuciya mai tattare da farinciki ta saki ganin yaci Abincin.


Bayan ya gama tattara wajen tayi ta fita da kwanukan, ya bi bayanta da kallo kana ya Lumshe idanun sa...



Aysha kuwa ta cinye ragowar Abincin a kitchen ta wanke warmers din da plate hadi da jug ta mayar da komai a muhallin sa, har ta nufi kofar barin kitchen din ta tsaya cak! Saboda tunanin daya ziyarci k'wak'walwarta...

"tabbas ya kamata na yi masa wani abun kafin na tafi kafa yaji yunwa, domin ba lallai madam ta dawo da wuri ba" ta fada a sanyaye, tana ji kamar karta tafi saboda ta bashi kulawa, amma idan ta tuno twins dinta da Inna sai taji ba zata iya fasa tafiyar ba...




Ingredients din yin cake duk ta fito dasu, kasancewar zaynab akindele ta koya mata wasu abubuwan daya danganci baking, k'waba cake din tayi cikin kasa da 30min, sannan ta zuba a pan mai dan girma ta saka a oven, bayan mintuna arba'in kamshi ya gauraya kitchen din, fito da cake din tayi bayan ta saka hankici (handkerchief) wurin fito dashi, sinken sakace ta cak'a a ciki ta ga bai manne a jikin sinken ba, gyara kitchen din tayi sosai ya dawo hayyacin sa


Bayan ta gama ta dauko wani tray mai oval shape ta kife cake din a kai, sannan ta yanyanka madaidaita sannan ta rufe da wani tray din, wanke cake pan tayi shima ta mayar domin bata son barin ko da cokali mai datti ne, domin anty Bintu tace mata 6:00am daidai ta fito...




***
A matukar gajiye take taka matatak'alar bene hannun ta rike da cake din, burinta yanzu ta samu tayi wanka ta kwanta, a hankali ta tura dakin sa ta shiga.



Yana kwance flat kan gado, numfashin sa na sauka a hankali da alamun ya samu bacci, gajiyayyun idanun ta ta zuba masa tana kallon sa, yayi mata kyau fiye da yanda yake yin kyau idan idanunsa a Bude suke.... Sai kuma tayi saurin d'auke kanta tana gargadin kanta da yawan kallon shi da take yi....




Kan wani center table na zallan glass ta ajiye cake din, daidai yanda ta san hannun sa zai isa, sannan ta dauko lemon 5alive guda hudu na kwali, ta daukar masa Swan water guda biyu sai cup, komai ta jere kan table din, har ta kai kofa sai kuma ta tsaya saboda tuno cewa bai San zata yi tafiya ba.




"Gashi ni ba jin turanci, shi ba hausa, bare na tashe shi"
ta fada tana shagwabe fuska, da tunanin bai kyautu ta tafi hakan nan bai sani ba...




"ya ilaihi! Ya zanyi yanzu?"
ta dora hannun ta a kugu cikin nazari, can kawai ta nufi wajen bed side, ta dauko wani memo da biro da ta gani tayi rubutu a kai kana ta yagi daidai inda tayi rubutun, duk da ta San ba iya karanta wa zai yi domin mutumin da bai iya hausa ba tayaya zai iya karantawa, amma zuciyar ta tafi aminta data bar masa wasikan da haka ta fita, tana zuwa dakin ta ta fada kan gado sai bacci saboda tsananin gajiya ko wanka bata samu ta yi ba, ko mintuna goma bata yi ba bacci mai cike da gajiya ya dauke ta...




Washegari

Saura kiris ta mak'ara sallah'n asuba a kagauce tayi wanka hadi da brush, ta saka kaya hadi da tada sallah, Bayan ta iddar ne ta yi karatu kadan saboda karancin lokaci, ita da take cewa zata masa breakfast kafin shida tayi gashi ta makara...

Abubuwan amfanin ta- ta dauka daidai na kwana biyun ta sauko da sauri ganin shida har da mintuna biyar, duk da taso leka Abraham amma gani take da zaran ta kara bata wasu mintuna Anty Bintu zata tafi ta barta...


Tana fitowa mai gadi yace "ah! ah!! Ayshatu ina zuwa haka"


"barka da asuba, zan je gida ne amma kwana biyu kadai zanyi, anty Bintu na jirana sai na dawo"


Ta fada tana fita da gudu-gudu sauri-sauri...

"ai kuwa naji horn a waje, toh a dawo lafiya Allah ya tsare" mai gadi ya fada ba tare da ya samu amsa ba, domin Aysha ta riga ta fada mota, har driver ya ja motar suka harba kan kwalta....





*_mu hade a next page mah people, banyi editing ba, may be akwai typing error, bacci sosai nake ji shiyasa.. wallahi da k'yar na gama wanna episode din._*



Share fisabilillah

Comment




NoorEemaan>؋?
07082281566



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/12, 9:01 PM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM

*First edition*


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



*WATTPAD*
@NoorEemaan




Chapter 39-40

(Not Edited)




Farinciki ya cika zuciyar Aysha, burin ta kawai ta ganta a garin su tayi tozali da twins hadi da Innar ta, ita gani take ma driver baya sauri saboda zumudi.


&&&

Da misalin karfe daya na rana suka isa kauyen su, inda ta kofar gidan su Aysha aka fara zuwa, cikin sauri ta balle murfin Motar ta fita, Anty bintu har ma da mai gadi suka fara dariya, cikin muryar dariya Anty bintu tace "Tsaya Indo! A ciro kayan nan, domin ni wucewa zanyi sai da yamma zan zo mu gaisa da Inna"




Ba dan taso ba ta tsaya tana shagwab'e fuska, driver ne ya fito ya fara fito da kayan Aysha yayinda Anty bintu ke fada masa kayan dake na iya Aysha, kafin kace me yaran layin har sun zagaye motar tare da fara dauk'ar kayan suna shigar wa shi cikin gidan, gabadaya hayaniyar su ta cika wajen
"Indon baffa liman ce ta zo" ...


Sai da Aysha ta ga an shigar da kayan ciki duka kana ta mara musu baya, tozali ta fara yi da Inna dake tsaye rike hab'a ganin yara nata shigo da kaya, murmushi mai taushi Aysha ta sakar wa Inna kana ta mayar da kallon ta ga yaran, dubu daya ta bawa babban cikin su tace "harisu gashi ku raba dari biyu-biyu" ta fadi hakan ne kasancewar dama su biyar ne.



Ihu na zallan murna yaran suka fara yi kana suka bar gidan a guje, da gudu ita ma Aysha ta fada jikin Inna da fuskar ta ke bayyana farinciki ganin tilon yarta a lokacin da bata zata ba, ita ma Inna hannu tasa ta rungume yarta "Inna ta nayi...." kasa karasa maganar tayi saboda hango twins da ta yi sun tsaya hadi da zuba mata ido, duk da cewa sun shaida ta, amma rashin ganinta na watanin biyun da basu? yi ba yasa suke jin wani yanayi kamar bakunta a tare da su.




"y'ay'a na!" ta fada cikin zakin murya tana ware musu hannuwan ta, fuskar ta dauke da murmurshi tana yaba yanda suka girma a ranta, ai kuwa kamar jira suke suka nufe ta, hadi da Kiran "Ammuh!" dire guiwarta tayi a kasa tana jiran isowar su gareta, hannayenta ta rufe a lokacin da suka shiga jikin ta...


Aysha ta Lumshe idanun ta a lokacin data ji dumin su a jikinta, dago fuskar su tayi tace "nayi kewar ku yan biyu na sosai, ku fa kunyi kewar Ammuh?"


washe bakunan su yaran suka yi suna kallon ta, domin ba wai sun iya magana bane sosai.





"toh tashi ku zauna kan tabarma ko mai y'ay'a" Inna ta fada tana kallon su da burgewa.



Dariya Aysha tayi ta Mike, yayin da yaran suka mara mata baya, kowannen su ya kama rigarta ta gefe da gefe har suka zauna, domin a ganin su zata kara tafiya ta barsu ne.






Sai kallon su Aysha take, ta tallafi fuskar su hagu da dama tana kallon su, masha Allah kuma sunyi kyau Abin su kuma fess suke alamun Inna na matukar basu kulawa, fadin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login