Showing 63001 words to 66000 words out of 84387 words

Chapter 22 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28152

din hadi da zazzage ta a kasa, abin ciki ya fado kasa...


Kamar mai tsoron taba wani abu ha?a ya mika hannu ya Wauka, gabansa na tsananta bugawa Saboda ganin hoton album din sa, tabbas baya mantawa farkon zuwan su Kaduna ya nemi hoton album din nan bai gani ba, har Madam GLORIA tana cewa kila garin
kwashe kaya ne suka manta a Imo State.


Shafin Farko ya buWe ya fara tozali da hoton sa, cikin sauri sauri ya cigaba da buWe hoto album din yana kallo, fadin tashin hankali da mamakin daya shiga bazai fadu ba.


Mayar da kallon sa ga Aysha dake kwance idanun ta a lumshe yayi, sai da ya Wan daidaita nutsuwar sa, sannan yace "?mammmm!" Ya kira ta Cikin murya dake bayyana halin tashin hankali da yake ciki.


A hankali ta bude kumburarun idanunta ta kalle shi, idanun ta na sake yin raurau kamar mai shirin kuka...
(Kamar yadda kuka sani dama Abraham da turanci yake magana, ina saka Hausa ne domin sauk'ak'awa makaranta na) cikin Yaren Ingilishi yace "wannan album din ma a tare kika gan su tare da sarkan nan dake wuyan ki?"


Cikin rawar murya tace "eh! Yana tare cikin jakar da Matar ta bari a banWakin gidan mu"


"Oh God!"
Ya fada yana hargitsa gashin kansa, daf da Aysha ya matso sosai har yana juyo bugun zuciyar ta yace "You no what? First thing tomorrow morning we are living to Gombe, i just need to finalize some issues, am so confused ?mammmm, am confused" Yana gama fadin haka ya bar daki kamar zai tashi sama.

(Kin san me? Abu na farko gobe zamu je Gombe, ina so na tabbatar da wasu abubuwan, na rude rayuwata, ina cikin rudu)



Jinjina kai Aysha tayi, tana kallon shi ya bar dakin, ta sani cewa yana bukatar kaWaici, sam bata ga laifin sa ba, lumshe ido tayi wasu hawaye Masu dumi suka zubo mata.



Idanunta ta kai kan photo album din, tun da ta dauko a dakin baffa bata taSa budewa ba, a hankali ta sa hannu ta janyo shi daga gefen gado inda ya bar shi, dan mikewa zaune tayi tana cije lips dinta saboda kanta dake barazanar fashewa, majina ta ja sannan ta bude shafin Farko, zuciyar ta ne ya bada dam! Tsoro, firgice, hadi da dimbin al'ajabi ne suka kama ta Saboda hoton Abraham da ta gani, duk da a kananun shekaru aka yi hoton, amma still kamanin sa basu sauya ba.



Toh Meye haWin sa da matar nan da ta bar su Anwar ta gudu? Ya akayi photo album din sa yaje har Gombe, kuma a lokacin basu san juna da Abraham ba, infact Bama ta yi mafarkin fara aiki a gidan nan ba...

Maganganun da suke ta yawo a ?wa?walwar ta kenan, sosai zazzaSi mai zafin gaske ya kara rufe ta, saboda damuwa da tashin hankali, har kad'awa hakoranta ke yi dana juna.

A takaice dai haka kowane su ya kwanta ba tare da bacci ya dauke su ba cikin damuwa, firgice, hadi zullumin abinda zasu tarar gobe...



Karfe shida na safe sun Wauki hanyar Gombe, inda Abraham ke tuka su, Aysha na zaune a gefe shiru, duk wanda ya kalli su biyun a lokacin sai ka tausaya musu, domin sai ka rasa waya fi wani tashin hankali a cikin su.




***********


Bayan wasu awannin suka isa garin Gombe, sannan suka dauki hanyar unguwar su Aysha, duk da ya gaji da tukin, Amma still Abraham Bai huta ba, burin shi kawai su isa gidan, hakan yasa ma ya kara gudun Motar.

Tun daga nesa yake danna horn ga wata mata dake tsaye a tsakiyar titin, inda Wannan matar tafi kama da mai tabin hankali, saboda yanayin shigar ta da kuma yanda kamanin ta suka sauya...
Kamar kurma haka matar nan ta tsaya, wasu mutane dake gefen titin har ihu suka dinga mata domin ta matsa amma inna, hakan bai yu ba domin bata tare da tunanin ta, ga gudun da Abraham ya keyi ya ma kasa taka birki, yana daf da buge ta Allah ya bashi nasara ya taka wani uban birki, amma duk da hakan sai daya buge matar a kafa, Allah ya takaita bai yi sama da ita ba, inda anan ne hankalin matar ya dawo jikin ta...


Ta kwala ihu saboda zafin da ta ji ya ratsa kafar ta, cikin sauri Abraham yace

"ya Allah!"

Sannan ya Salle murfin motar ya fito cikin sauri, Aysha ma ta fito, cikin kulawa Abraham yace "Am very sorry madam, please let's take you to the hosp...."


Sauri dago kanta matar tayi, wanda hakan yasa Abraham bai karasa maganar sa ba.

Cikin firgice, farinciki, hadi da mamaki tace

"Abraham!"


Cikin mamaki Abraham ya kalli matar jin ta kira sunan sa, ya kafe ta da ido, yana son tuno fuskar ta, amma hakan ya gagara.


Aysha dake ta zaro ido Saboda rudewa da tsoro, cikin Yaren Ingilishi tace itace! Itace ta ajiye su Ammar a banWaki ta gudu, tabbas itace bazan taba manta fuskar ta ba" Aysha ta faWa cikin tabbaci, nan aka shiga Kallon-kallo a tsakanin su uku.




_Manage pls, I'm damn tired, Kila ku ga typing error banyi editing ba_=?)?






*Guys new book Is loading next week, kuma paid ne #300*




Share fisabilillah


Comment for more typing



Noor Eemaan
07082281566




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/13, 2:00 PM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM



*First edition*



https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




*WATTPAD*
@NoorEemaan



Chapter 65-66


Sun dauki mintuna biyar masu kyau suna kallon-kallo ba tare da sun ce wa juna komai ba, musamman Anty Sarah dake kallon Aysha saboda jin abinda tace. Abraham da komai ya fara girmama ?wa?walwa da tunanin sa ya zuba wa anty Sarah idanu dake ta sharban kuka abin tausayi.



Cikin kuka tace"Abraham baka gane ni ba ko? i knew bazaka gane ni ba" numfashi ta sauke, yayinda ta hadiye Wani abu mai kama da tsoro sannan ta Wora da cewa "nice Sarah, kawar Gloria dake a matsayin mahaifiya a gare ka, na jima ina neman ka, har imo naje gidan ka amma na samu labarin kun tashi, sai dai ban san ina kuka koma ba"


Runtse idanun sa yayi sannan ya bude saboda sunan mahaifiyar sa da aka kira Madam Gloria da shi, a yanzu kam baya so a danganta shi da ita.


Sauke idanun nasa yayi kan Anty Sarah, tabbas ya gane ta yanzu, ko lokacin da take matsayin yar aiki a gidan ba wani kallon ta yake ba bare ya wani gane ta, ya kuma yi mamaki da ta ce ita Win kawar Madam Gloria ce, domin a iya sanin sa yar aiki ce.
Domin madam Gl??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????oria ta sanar dashi cewa Sarah yar aiki ce.

Kawar da wanna tunanin yayi, saboda Akwai abinda ya sake daure masa kai, yana son yayi nazari da kyau ta yanda akayi ta je gidan su Aysha ta ajiye jarirai, sannan jariran na waye? kuma a wani dalili take neman shi? Sosai yake son samu amsar wandannan tambayoyin, amma ya ma kasa magana, saboda abubuwan da yawa ya rasa ta ina zai fara.


Numfashi Abraham ya furzar sannan ya kalli Anty Sarah yace "come with us" yana gama fadin haka ya juya cikin sauri ya fada mota, Aysha ta mara masa baya ta zauna a kujerar mai zaman banza, yayinda Anty Sarah ta shiga baya ta zauna shiru gwanin tausayi kamar kazar da ruwan sama yayi wa duka.



Nan Aysha ta cigaba da nuna masa hanya...
sun dauki mintuna sha biyar suna tafiya sannan suka iso kofar gidan tace ya tsaya sun iso.


Ba musu ya tsaya hadi da daura kansa kan sitiyarin motar, kallo shi Aysha tayi, cikin sanyin murya tace "lemme inform Inna we re together"
(bari na sanar da Inna tare muke)


Bata jira amsar sa ba ta
bude kofar motar ta fice hannun ta rike da jeka mai Wauke da hoton Album din nan, dama already sarkan yana wuyan ta bata cire ba, Anty Sarah kuwa kurawa gidan ido tayi, tana jin ?wa?walwar ta na tariyo mata zuwan ta na farko, duk da akwai yan sanjin gine-ginen a layin, hakan kuma yasa gidan ya bace mata tun zuwan ta Gombe, ta wani Sangaren kuma taji dadi, domin wahalar ta bata tafi a banza ba, tunda gashi Allah ya haWa ta da Abraham.



Da sallama Wauke a bakin Aysha ta shiga gidan, tsakar gidan su a tsaftace ko tsinke babu a kasa, Inna na zaune fess da ita tana soya wainar masa da su Anwar suka ce ita suke so yau.



Salati Inna ta yi a lokacin da ta ga Aysha, ko sallamar ta kasa amsawa tayi
"Indoooooo lafiya, mezan gani haka? Amarya da fitowa a washegarin kai ta gidan miji"


Murmushi Yake Aysha tayi tace " kwantar da hankali ki Inna, muna tare da shi ne"


"Ya Salam! in ce ba wani abu kika yi ba, lafiya ko?" Inna ta tambaye ta a dame.



"Banyi komai ba Inna, sai dai ba lafiya"





"Innalillahi wa Inna illahi raju'un, ku shigo toh Allah ya yi mana magani"

Inna ta fada hankalin ta a tashe, dama suyar karshe take yi, hakan yasa ta kwashe bayan ya soyu ta saka a kula, sannan ta Wora kular miyan taushe da ta jima ta gamawa a sama ta wainar ta kai daki...


Ta Wan gyara inda ya bace garin suya kana ta shige dakin baffa ta zauna tana jiran su shigo... tana zama kenan ta sake jin anyi sallama.




Aysha ce ta fara shiga ta zauna kan babban sallayar dake shimfid'e a kasa, sannan Abraham ya shigo, cikin karfin hali ya tsunkuyar da kansa alamar girmamawa ga surukar sa yace

"Good afternoon ma"



Inna da bata san abinda ya ce ba, amma daga yanda yayi ta fahimci gaishe ta yayi, kuma duk da bai tsugunna ba, hakan bai sa ta damu ba, domin ta san cewa kila ba al'adar su bace, ko kuma bai saba da hakan ba.

Kuma abin da ya sanyaya ranta shine ganin Abraham mai hankali, domin yanayin sa ya nuna cewa shi din mai nutsuwa ne, ya kuma dace da mijin Indon baffan! hakan yasa hankalin ta kwanciya, ko ba komai ta san kalar mijin da diyarta ta aura.



"Yawwwa sannu ku da hanya, zauna ko" tace wa Abraham.


Bai ji abinda ta ce ba, Aysha ta kalli shi, a hankali tace masa"Inna said you should sit down" ba musu ya zauna, Anty Sarah dake gefe a tsaye Inna ta kalle ta, tayi mamakin meya hada su Indo da wanna matar amma bata furta ba.


"baiwar Allah zauna mana" ba musu Ta zauna, domin dan zaman data yi a Gombe, ta na dan jin Hausa kadan-kadan.



Aysha ce ta muskuta hadi da kallon Inna tace "Inna kin gane wanna matar?"


Aysha ta faWa tana nuna Anty Sarah da ta tsunkuyar da kanta.


Dan kankance ido Inna tayi tana kallon Anty Sarah, saboda dan tsufan daya fara kamata, kana ta girgiza kai alamun bata gane ta ba.


"Hmmm! Inna ita ce fa matar nan da ta ajiye su Ammar a banWakin shekarun baya da suka wuce ta gudu"



Zabura Inna tayi, ta dafe kirjin ta kana ta saka salati. "Indo da gaske kike? Ta yaya kika gane ita ce"



Nan Aysha ta labartawa Inna yanda ta dauki sarkan wuyan ta da photo Album a dakin baffa, da haduwar da suka yi da da Anty Sarah yanzu, sannan ta sanar da Inna cewa ita kam bata manta fuskar ta ba.



Kuka mai dauke da abubuwa da dama Anty Sarah ta saki saboda taji wasu abubuwan da Aysha ta fada, nadama da kunya mai tsanani na sake lullube ta.


Fuskantar Abraham tayi cikin turanci tace "WaWannan yaran da na ajiye a banWaki gidan nan....."

wani abu mai daci ta hadiya, sannan cikin kunya mai tsanani hadi da sabon nadama ta Wora da cewa "yaran ka ne daka haifa tare da Nonye!. Sannan ban ajiye su da mugun nufi ba, illa saboda na tseratar da rayuwar su daga hannun kishiyar mahaifiyar ka Gloria!"


A haukace Abraham ya kafe ta ido, yayin da bugun zuciyar sa ke ta karuwa yana bada sautin fat! fat!! fat!!! har yana nuna wa ta saman rigar sa, ya haWa uban gumi, yayinda ya kasa ko da motsa yatsa ne, saboda dumbin al'ajabi daya tsinci kansa a ciki, ?wa?walwar sa ta tsaya cak da aiki, bangaren Inna da Aysha ma suna cikin shock jin abinda ya fito daga bakin anty Sarah, Aysha mai raunin zuciya tuni ta fara kuka, infact dukkaninsu su shiga wani hali da damuwa mai tsanani bare ma Abraham da al'amarin ba mai sauke bane a gareshi.




Tsahon mintuna goma babu wanda ya sake magana, ko wa da abinda zuciyar sa ke saka masa, Abraham kuwa har yanzu bai dawo dai-dai ba, sai da anty Sarah ta Wora da cewa "na san labarin da zan baka yanzu zai iya tarwatsa zuciyar ka, amma kayi hakuri ka yafe Ni, tun bayan da muka aikata mugun nufin Mu da Gloria na nemi salamar zuciya na rasa, burina na ganka na nemi yafiyar ka...."

Kamar yadda Kuka sani reader's tiryan-tiryan haka Anty Sarah ta shiga gayawa Abraham abinda ya faru....

Tun daga lokacin da Gloria ta hadu da mahaifin Abraham, da asirin da tayi masa, da yanda ta kashe mahaifiyar Sa, da yanda ta cigaba da farautar rayuwar Abraham domin malleki dukiyar sa, da yanda ta kashe Nonye, amma su Ammar na motsi a cikin ta duk da ta mutu, da yanda ta tseratar da su Yan biyu tun daga asibiti a imo har izuwan Gombe gudun kada Gloria ta gano komai, da hoton album hadi da sarkan Nonye data dauko a dakin ita Nonye a lokacin da zasu tafi asibiti cikin dare, da kiran Madam GLORIA data yi ta Sanja murya tayi karyan ta mu saboda duk kada Madam GLORIA ta gano komai ta biyo ta .


Haka dai ta cigaba da gaya masa komai tana kuka mai ban tausayi.


Jikin Abraham rawa yake kamar wanda zafaffan zazzaSi ya kamasa, ya kai mintuna goma a haka, sannan ya ja guiwar sa har gaban Aysha ya dora kansa kan cinyarta, ya saka karfafan hannunwan sa ya zagaye waist (kugu) dinta dashi, ya matse ta sosai, mafaka yake nema, mafakan da zai samu ko da dan sanyin ne a zuciyar sa, cikin tausayi Aysha ta nausa hannun ta cikin gashin sa, tama manta Inna na zaune a wajen, sai a lokacin Abraham ya samu wani kuka mai sauti ya kufce masa, kukan da amon sa duk ya taba zuciyoyin su bare ma Aysha, hakika duk wanda ya ga Abraham a wanna halin dole ya tausaya masa ainun.


Inna kuwa kauda kanta gefe tayi, saboda kara, tunda Aysha na matsayin yarta ta fari kamar yadda aka san Fulanin Usul da kunya, amma ta tausaya wa Abraham sosai duk da bata gane komai da anty Sarah ta fada ba, amma ta tausaya masa matuk'a.



Ba tare da ta kalli Aysha ba saboda har yanzu Abraham yana runkumkume da ita, tace "Indo wai menene, duk ban fahimci abinda matar nan take fada ba" Cikin kuka Aysha ta shiga gayawa Inna komai, amma a takaice kamar yadda anty Sarah ta faWa.



Girgiza kai Inna ta shiga yi, har kwalla ta zubar saboda tausayi, sannan ta jinjina rashin imani irin ta Madam Gloria cikin dumbin al'ajabin yadda mutanen yanzu suka fifita duniyar su fiye da lahirar su, bayan duka wanna abin duniyar mutum bazai tafi da su lahira ba, kana mutuwa shikenan, wasu ne zasu cinye abin duniyar, amma saboda imani da tausayi yayi karanci yanzu sai ka kashe rai Saboda kwadayin mata'ul hayat (kyale-kyalen rayuwa).


Anty Sarah ta ja hanci saboda mugun muran daya kamata a dalilin kukan da ta sha, kana ta hade hannayenta waje daya alamun roka, ta Wora guiwarta a ?asa tace "dan Allah kayi hakuri ka yafe Ni, kullum cikin tashin hankali nake da mugayen mafarke, matu?ar baka yafe Ni ba bazan taba ganin haske ko da kadan ne a rayuwata ba, ban kuma ajiye yaran nan a toilet din gidanan saboda wata manufa ba, a lokacin ina cikin wani hali ne, burina a lokacin kawai na nisantar da su daga GLORIA, sannan a ganina gwara na barsu na gudu ba tare da bayin Allah nan sun sani ba(, tana nufin su Inna) a ganina hakan zai sa su karbi yaran, sannan zasu yi nisan gaske daga wajen GLORIA, duk da an sanar mata cewa yaran sun mutu, amma nasan Gloria, shu'uma ce, zata iya gano komai, hakan yasa na iya takuna wurin ganin ba ta gane cewa yaran na raye ba, kullum tunanina a wani hali yaran suke, amma idan na tuno karamcin bayin Allah nan a zuwana gidan nan na farko sai hankalina ya Wan kwanta, domin na ga suna da zuciya mai kyau, dan Allah ka nemi waje ko yaya ne a zuciyarka ka yafe min, na tuba, ka yafe min dan Allah!" ta karasa tana buga hannunta a kasa, alamun tayi nadamar abubuwan data aikata a baya, Sannan tana jin ciwon su.



Ido duk suka zuba mata, babu mai kuzarin sake magana ma a cikin su, domin Abraham har yanzu bai gama dawowa hayyacin sa.




*MADAM GLORIA*

Tun daga lokacin da ta je wajen boko Nandera kullum da irin aikin tsafin da yake yi a kanta, Burinta a kullum watanin daya diba hadi da kwanakin su cika domin ta bar wannan dajin, domin ta gaji sosai, sannan hankalin ta ba a kwance yake ba, saboda macizan nan dake ko wani kusurwa na fadar Boka Nandera, a haka ta cigaba da lallabawa tana jurewa har watanin da kwanakin daya diba suka cika...



Sai dai me, a ranar boka Nandera ya fito da abinda ya dade a ransa muraran.
Ma'ana dai yana bukatar ya kusance ta, a ranar Madam Gloria ta ga tashin hankali, ya Kada ya raya taki yarda, ita kam iskanci baya damunta, sam bata damuwa da shi ba, ita matsalar ta son kai, rashin imani, hadi da son abin duniya ne ya dame ta, ya kuma rufe mata ido.
Sannan kuma tana k'yank'yamin wanna bokan, ta ina ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login