Showing 6001 words to 9000 words out of 84387 words

Chapter 3 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28136

da gyara wutan, dakin baffa ta nufa da bokitin, kana ta fito ta nufi dakin ta domin dauko roban wanka wanda tun na indo ne amma yana nan da sauran kyansa da sabunta(kun San fulani akwai iya ajiya>?)?)



Sai da ta wanke roban wankan kana ta dan sirka ruwan zafin kadan, kan gado baffa ya zauna, jariran na hannunsa yayinda indo ke gefe tana raba idanu wanda zai tabbatar wa mutum cewa har yanzu tsoron bai barta ba.




Ledar da baffa ya kawo inna ta zazzage, kayan jarirai da na Sanyi, sabulun yara da so so, man shafawar su, mataji(comb) hadi da hular Sanyi. Ba laifi siyayyar tayi daidai talaka...




Sosai inna ta wanke yaran ta kuma gasa musu jiki sosai, sai a lokacin jariran suka canyara kuka tun lokacin da suka shaki iskar duniya....



A kuma daidai lokacin ne Indo taji wani mugu_mugun tausayin yaran ya ratsa jikinta, wani Sanyi ya fara ratsa ko wani huda na gashin jikin ta, sak'amak'on hakan tsikar jikinta ya fara tashi, haka nan ta ke Jin wani yanayin na mussaman kan yaran Wanda bakinta bazai iya furtawa ba...

Ajiyar zuciya ta sauke, kana ta mai da duban ta ga yaran Inda zuwa Yanzu Inna ta shirya su cikin kayan da baffa ya kawo, sunyi kyau sosai gwanin sha'awa, karon farko da Indo taji tana son daukan yaran ta rungume su, hakan yasa ta fara takawa domin isa garesu....





*yanzu Abraham ya soma, yawan comment dinku shi zai bani kwarin guiwar cigaba da typing, idan ba comment nima bazan yi update ba*

*Sannan mai son nayi adding dinta a group ta yi chatting dina up ta lambar nan*=?G?

NoorEemaan>؋?
07082281566







Share fisabilillah

Comment

Vote




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/5, 9:14 AM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM



*WATTPAD*
@NoorEemaan



ELEGANT ONLINE WRITER'S =???
'?


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din





Chapter 9-10

Daidai ta gefen baffa ta dire gwiwowinta, kura wa yan biyun ido tayi, hakan nan taji gabanta ya bada ras! Amma sai tayi saurin aro jarumta domin so take wanna tsoron da bata san na menene ba ya barta, sosai yaran suke da kyau mai shiga rai, hannu tasa a nutse ta karbi daya, dayan kuma ta riko dan mitsilan hannunshi, kallon baffa tayi tace "baffana ina son su sosai , daga yau na dauke su y'ay'ana bama kanne ba, sannan kai da inna sun zama jikokin ku" ta fada Cikin iyakar gaskiyar ta kamar ba aysha indo mai kananun shekaru ba, domin duka shekarun ta bai wuce sha biyar ba.




Murmurshin farinciki ne ya bayyana a fuskar baffa, yasan cewa dama haka zata faru, tsoro ne dama ya sanya bata zo garesu ba, domin Indo na da son yara sosai, Allah ne ya nufa bazata samu kanne ba, domin baya mantawa Indai sunyi baki masu kananun yara ta dinga murna Kenan, amma da zaran sun zo tafiya zata fara kuka.



"toh Indon baffale Allah ya tayaki riko" dariya tayi har ya bayyana jerarrun fararren hakoranta, kana ta sanya hannu ta karbi dayan ta hada dukkansu ta rungume....



Ta dauki mintuna biyar a haka, yaran na manne da jikinta tana shakar d'adadd'an k'amshin jikinsu irin na jarirai...



Inna dake kallon su da murmushi a saman fuskar ta ta Mike domin zubar da ruwan da ta yi musu wanka hadi da wanke towel din da baffa ya jika, Bayan ta gama komai ta dawo dakin, baffa ya kalle ta yace "ina ga nonon shanu ya za a tasa a fara bawa yaran kafin mu ga yanda Allah zai yi, domin ragowar kudina nayi musu siyayyar nan dashi, naso dai siya musu madaran yaran"





"toh malam, bari na tasar musu, in sha Allah ma zasu karba, karka damu" ta fadi hakan domin kwantar wa da baffan hankali.



"Allah yasa" ya fada yana maida kallonsa da indo hadi da tsokanar ta, ganin yadda ta rike yan biyu gam bata da alamar kwantar dasu....



Bayan Inna ta kawo madarar shanun da ta dumama, ta wanke feeder ta zuba a ciki, cikin sauri indo ta karba ta fara sawa daya a baki, wani ikon Allah kuma ya karba ya fara tsotsa wanda hakan ya faranta ran baffa, yana fatan dayan ma ya karba.




Bayan dayan ya koshi, ta fara bawa dayan, shima ba laifi ya sha amma bai kai na farko ba, Bayan ya gama sha Inna tace indo ta kwantar da yaran hakan nan, basu da kwarin da za a yi ta daukar su sosai....


Ai fa nan indo tace bata San zance ba, ita haka zata rike su har gari ya waye, dariya su Inna suka saka mata kana da kyar aka lallaba ta kan cewa tare dasu za ta kwana, ganin lokacin isha ya karato ya sanya baffa ficewa zuwa masallaci, inda bayan sun iddar da sallar ne ya yi sanarwa abinda ya faru a yau na ajiye jariran da anty Sarah tayi, bai boye komai ba, ya kuma bayyana din ne saboda sanin halin jama'a, ya kuma yi hakan ne ko dan nan gaba, domin wasu zasu iya tunani, ko yin sharri ga tilon yarsa...




Nan fa mutane suka fara fadin albarkacin bakinsu, wasu ma har cewa suke sun ga shigowar anty Sarah Layin a firgice da farin towel , wasu kuma sun ce sun ga fitar ta cikin rashin gaskiya amma basu kawo komai a ransu ba, maganganu dai kala? kowa na fadin albarkacin bakinsa.






*IMO STATE*
Kwance yake flat kan had'add'en kuma yalwataccen gadon sa, azahiri idan mutum ganshi a yanda yake zai yi tunanin kallon pop'n daya k'awata saman dakin yake, sai dai sam ba haka bane, domin sosai ya zurfafa a tunani, Nonyen sa ta mutu? Abin ya yi matuk'ar tabashi fiye da zaton mutum, ganin abun yake kamar a mafarki, ji yake kamar yanzu zata shigo dauke da cikin sa ta zo gareshi, yanzu ta tabbata bashi da kowa sai mummy(madam Gloria) daddynsa ya mutu, mummy'nsa ma haka, tun daga lokacin daya rasa su ya rasa dukkanin farinciki kana walwalar sa ta ragu, shigowar Nonye cikin Rayuwar sa ba tare da ya shirya ba ya rage masa wasu abubuwan, duk da a lokacin babu soyaaya a gaban sa, ya kuma ki sauraran ko wacce mace, amma haka Nonye ta d'aure ta jure duk Wata shariya da yayi mata, ta kuma cire kunya ta furta tarin kaunar da take masa a matsayin ta na 'ya mace...



Hak'ik'a bai taba kawo wa ransa cewa zai rasa ta yanzu ba, ya kuma kasa yafe wa kansa kan me yasa bai nuna mata zallan soyaaya ko da rabin wanda take masa ba, gashi yanzu ta tafi tafiya ta har abada, ya tabbata bashi da kowa sai step mummy'nsa(kishiyar mahaifiyarsa wato madam Gloria)

Kasa rike kukan daya taho masa yayi, sosai ya saki kukan da sautinsa ke fidda zallan kunci, maraici, hadi da kewar da yake ciki, dole Abraham ya bawa mutum tausayi, domin cikakken namiji kamar sa na kuka tamkar karamin yaro.


Ya jima sosai yana kuka kana ya yi shiru yana sauk'e tagwayen ajiyar zuciya, k'amk'ame jikin sa yayi hadi da takurewa kan gadon yayi, duk da Sanyin da yake ji, amma ya kasa tashi ya kashe Ac ko kuma ya rufe jikinsa...




*Bayan Kwana Biyu*

Garin enugu a kauyen Nusukka anty Sarah ce ke zaune a asalin jahar ta, dakin karami ne ginin Jan kasa, duk da Rayuwar kauyen na matuk'ar bata wahala, domin ta jima rabonta da kauye, Rayuwar birni yagama ratsa ta, amma duk da haka ta fi Jin kwanciyar hankalin zaman nan din, Abu na karshe take son aiwatar wa kafin ta yanke duk Wata alaka dake tsakaninta da madam Gloria, hakan yasa ta fara latsa wayar ta, ta saka magic voice muryar namiji kana ta kara wayar a kunne ta mai dauke da barima guda shida....





Bangaren Madam Gloria kuwa zaune take a gadon ta da plate din kaza tana ci, key ta saka wa kofar domin bata so kowa yasan tana cin abinci, domin nuna wa take a gaban mutane cewa bata iya cin komai saboda tsananin damuwa da alhinin mutuwar Nonye, sosai take yagar kazar ta tana korawa da sanyayyar juice, Kiran daya shigo wayar ta ya sanya ta ajiye juice din hannunta, daukar wayar tayi, dam taji gabanta ya buga, ita kam har ta manta da anty Sarah, saboda yawan jama'a dake zuwa kullum yasa ta sha'afa.....





Latsa kore tayi ta kara a kunne ta, "Sarah ina...." kasa karasa maganar tayi a dalilin muryar namiji data ji, kara kallon number'n tayi taga dai number anty Sarah ce, tana cikin wanna tunanin taji muryar ta ce da yaren igbo "ba Sarah bace, Sarah ta mutu, ni yayan ta ne, Ina ta Kiran lambobin wayar ta ne ina sanar musu, hatsari tayi, Sarah ta tafi ta barmu, jiya aka yi burial din ta" muryar anty Sarah da ta rikide ta dawo ta katon gardi sakamakon magic voice din da ta saita a wayar ta.


"wayyo kawata Sarah! Sarah ta tafi itama? Ya zanyi da raina" madam Gloria ta fada tana fasa kuka, itama shesheka Anty Sarah ta fara kana ta katse Kiran tana dauke ajiyar zuciya, cire magic voice din tayi hadi da Layin da madam Gloria ta santa da ita, murmushi mai ciwo ta saki, domin tasan cewa ba lallai kukan da madam Gloria ke yi ya kasance har zuciyar ta ba, ta kuma god'ewa Allah da plan dinta ya tafi a daidai domin madam Gloria na da Wayo sosai.




Bangaren madam Gloria kuwa dariya ta tunsire dashi bayan Kiran ya katse, Abin mamaki kuma ga hawaye na zuba a idanunta, a fili ta furta "tabbas mutuwar ki ta shige ni Sarah aminiyata amma naji dadi ta wani fanni, domin kece kadai kike San sirrina na shekaru masu yawa, Dan haka hankalina ya kwana yanzu bana da matsala ta Bangaren ki, Abu daya ne ya rage ta yanda zan ga bayan Abraham, sanda na more dukiyar shi ni kadai " ta karasa tana sakin murmushin nasara...




*GOMBE*
A cikin kwanakin biyun nan mutane unguwa, abokan arziki, hadi da yan'uwa sai tururuwar zuwa ganin 'yan biyu suke, domin baffa Sam bai boye wa kowa ba, gudun abinda ka je ya dawo...






Kamar yau duk suna zaune da misalin karfe sha daya na safe, suna hirar su amma banda Indo da take ta faman yiwa yaran wasa, duk da suna bacci amma bata hakura ba.


"Baffa nah kasa wa yan biyu na suna, na dinga Kiran su kaji"




Kallonta duk sukayi suna mamakin tsananin soyaayar da take musu, murmushi dauke a fuskar Baffa yace "toh shalelen Baffa maganar da muke yi Kenan da Innar ki, na saka musu suna Abdul-jalal da Abdul-jabbar ya fada yana karban yaran hadi da yi musu huduba da sunan, lumshe ido Idon tayi, sosai sunan ya mata dadi....

" amma Baffa ni Anwar da Ammar zan dinga Kiran su kaji" kasancewar tana son sunan sosai, domin sunan wasu kyawawan yara ne a islamiyar su.


Babu musu Baffa ya amince domin yasan ma'anar sunan. Inna dai 'yar kallo ce, banda murmushi babu abinda take yi, dama macece mara son magana, amma idan ranta ya baci Abin ba dadi shiyasa Indo ke Tsoron bacin ranta.




Ranar da Ammar da Anwar suka cika sati daya baffa ya yanka musu ragon sunan daga Cikin dabobbin sa, Bayan an gyara an soya aka rabawa yan'uwa da abokan arziki....





_Har yanzu bamu shigo Cikin labarin ba, yawan comment yawan typing_





Share &

Comment





Noor
'?>؋?



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/5, 7:52 PM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM


*WATTPAD*
@NoorEemaan



_masu following account dina a Wattpad, Ina godiya, i love You guys_>???>?p?




ELEGANT ONLINE WRITER'S =???
'?

https://facebook.com/groups/943534712916776/masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.




Chapter 11-12

(not edited)


Sosai jama'ar unguwa suka yabawa baffa da namijin kokarin da yayi, domin tabbas ya cika Muslumin kwarai mai yarda kaddara mai kyau ko akasin hakan, duk da baza a rasa masu tsegumi ba.



Yan biyu kullum suna tare da indo ko nauyin daukar su ma bata ji, ko aiken ta aka yi sai ta tafi dasu, ta goya daya ta rike daya, idan ma Inna tace kada ta tafi dasu sai ta fara kukan rigima, hakan yasa Inna ke kyale ta ta tafi dasu...



*IMO STATE*

Kamar yadda muka sani gawar Nonye na nan har yanzu, a kuma yau za a binne ta, kowa ka gani sanye yake da bak'ak'en kaya, wasu har da glasses baki, ciki har da Abraham wanda ya boye k'wayar idanunsa saboda jaa hadi da kumburin da suka yi, ko ina ya cika makil da jama'a ba masaka sinke, an shirya Nonye kana aka sakata a wani tsad'add'en akwati wanda kudin wanna akwatin ba kananun kud'ad'e bane, haka kowa ya shishiga mota ake tafi makabarta, inda suka tarar an hak'a rami da za a sa ta a ciki, gaban ramin aka ajiye akwatin, su pastor's, sister's hadi da wasu members na church din da Nonye ke zuwa a lokacin da take raye sun taru gaban akwatin domin yi mata addu'a, dama sun jima da zuwa makabartan isowar gawar suke jira.



Sosai su pastors din suka yi preaching (wa'azi) hadi da addu'o'i iri na addinin kirista (Christian) bayan sun gama wasu daga cikin mazan masu dakakiyar zuciya suka daga akwatin hadi da saka wa cikin ramin kana suka shiga watsa kasa a kai, cikin sassarfa Abraham ya koma cikin mota yayinda wasu hot tears suka biyo kuncinsa, wani mugun son matar sa ta shiga ratsa shi, har yanzu bai daina jin haushin kansa ba, a dalilin rashin mallaka mata zuciyar sa dabe yi ba a lokacin da ta fi bukata , tabbas a da ko digon sonta babu a ransa, amma ta jure ta cigaba da zama da shi hadi da bashi dukkanin Wata kulawa da soyaaya ba tare da gajiyawa ba, ina ma ana dawo da abinda ya wuce da ya nuna mata soyaaya ko da rabin wanda ta yi masa ne, wani tagwayen ajiyar zuciya ya sauke tamkar yaron goye kana ya saka hankici(handkerchief) ya shiga goge hawayen fuskar sa...





madam Gloria kuwa ganin an fara zubawa akwatin da Nonye ke ciki kasa ya sanya ta ruga da gudu gaban kabarin ta shiga kuka hadi da birgima, mutanen wajen kuwa sunyi matuk'ar tausaya mata, da kyar wasu yan'uwan Nonye suka janye ta daga kabarin suna kuka suna bata hakuri, hak'ik'a madam Gloria ta Shahara a fagen makirci, domin abinda take aikatawa a gaban mutane ba shi bane a ranta...




Bayan sun dawo gida, da karfe hudu na yamma aka yi weak-keeping inda aka cika har yafi na safe, an yanka shanaye guda uku, an yi girke-girke sosai tamkar gidan biki, ga palm wine, barasa, hadi da sauran abubuwan sha da yawa, ga waka dake tashi cikin yaran igbo, a takaice dai an yi bikin weak-keeping, an ci an sha sosai tamkar bikin farinciki ake, inda ba sabon abu bane a garesu domin al'adar su ce haka.


ABRAHAM da tun bayan dawowar su daga makabarta ya shige dakinsa ya danna key, domin a halin da yake ciki bayason hayaniya sam, Ji yake komai ya daina yi masa dadi bashi da sauran farinciki yana kuma ganin ya rasa dukkanin farincikin rayuwa, mutum daya yake gani yaji dadi a yanzu itace madam Gloria domin a tunanin sa ta dauke shi tamkar dan cikin ta, ga hayaniyar bikin weak-keeping din dake kara dagula masa lissafi, sam ko hayaniya d'aya baya bukatar ji, garin imo ma ya fita a ransa gabadaya l, duk da kasancewar sa garin sa na asali.





Tsaye madam gloria take a kofar da zai sadata da dakin Abraham rike da tray mai dauke da abinci different varieties, sai da ta bata tsawon mintuna biyar tana k'ak'alo hawayen karya kana ta shiga knocking kofar, Abraham daya ji knocking din har tsakar kansa ya runtse idanunsa da karfi hadi da cije pink lips dinsa masu dan duhu, " son! Open the door" madam Gloria ta fada cikin muryan kuka da ta san zai gigita masa lissafi kasancewar abinda ya tsana yaji Kenan kuka, kukan ma na mace, macen ma ita da take taka rawar uwa a gareshi, ba shiri ya mike ya bude kofa kana ya dawo da baya ya zauna kan gado hadi da rike kansa dake Sara masa, wanda hakan yasa jijiyoyin kansa suka fito suka yi rudu?.



Ajiye tray din tayi kan wani had'add'en sofa peach color daya kara kawata dakin, kana ta zauna dab dashi ta dora hannun ta a bayan sa, cikin sanyin murya tace "son! You have to bear it, Nonye is gone forever and will never be back, ka cire damuwa a ranka, sannan kayi Mata addu'a, kalli yanda kayi loosing a lot of weight, you no more talk to anyone nor eat food, I no it's painful, amma ka jure, Nonye will remain in our hearts forever, But please be patient OK? I brought your favorite food for you" ta karasa ta nufar sofan domin dauko Abincin.




Tun da ta fara magana ko motsi bai yi ba, haka zalika bai amsa mata ba, "oya open up" ta fada bayan ta debo had'add'en jollof rice daya ji kayan lambu hadi da namomi, ganin bai motsa ba ya sanya ta fara kuka, a firgice ya dago kansa, gwanin tausayi ya bud'e bakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login