Showing 81001 words to 84000 words out of 84387 words

Chapter 28 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28145

sai dai basa bari fadan su ya kai dare ba tare da sun shirya kan su ba.


"Ammuh!!!" Ta ji yaran duka sun hada baki wurin kiranta har da uban su.

Dariya tayi kasa-kasa tace "Am coming guys"

Wanke hannun ta tayi, ta goge da towel sannan ta fito, waje ta samu ta zauna cikin su tace "gani"

"Surprise!"

Suka hada baki wurin fadin haka, sannan suka fito da ticket da ke boye a hannunsu masu yawa, Abraham ta kalla ya kanne mata ido daya, dauke kanta tayi cikin sauri saboda yaran.

Sannan cikin farincki ta bashi side hug domin ticket din zuwa aikin hajji ne ya biya musu gaba-daya, sannan ya biyawa Inna da Anty bintu, kuma tare zasu tafi cikin satin nan...

Yaran ma gaba-daya suka rungume shi ya kuwa saka karfaffan hannunwan sa ya zagaye su duka.

Kallon Aysha yayi yace "how will I say i Love You all in Hausa?"

"Ina son ku duka" Aysha ta fada masa.

"i...in...a son....ku... du... ka" ya maimaita kalmar a rarrabe kamar mai koyan magana, har yanzu kam Hausa taki zama a Bakin sa.

Gaba-da?a suka fashe da dariya jin yanda yayi Hausar, shi ma biye musu yayi suka dinga dariyar a tare, abin gwanin kyau da burgewa, what a happy family!.




I believe every ending is another beautiful begining.



Alhamdulillah!







Special thanks to:
Noor novelist world
Sarautar's library
Safrat group
Mijin yarinya group
Neat lady palace
Ranar nadama group
Aludra group
Elegant online writers group
Matan buri fans
Taskar real ladingo
Surrayhms novels
Taskar mammy Kabeer
Kwaila fans group
Nana haleema palace
Gidan girki da gyaran jiki group
Fitar rana comments section
Mi Amour world
Fataucin mata fans
Hausa novels group



Dama sauran groups da Abraham ya je ina godiya a gareku Allah ya bar kauna...
Bazan manta da wattpad fans dina ba, Nagode muku sosai.



*Ya rabb Nagode bisa Ni'imar ka gareni, ya rabb na gode daka bani ikon kammala wanna book na Abraham cikin koshin lafiya. Ya rabb kuskure dana yi cikin littafin nan ka yafe min, wanda na fada daidai ka bani ladan sa da Ni da reader's*



*Masoyan littafin NoorEemaan ina mai godiya a gareku da yadda kuke karban duk wani novel dana kawo muku hannu biyu-biyu, tabbas na ga kauna a Abraham, zan kuma cigaba da kawo muku d'ad'add'an labari mai cike da abubuwa da dama in Sha Allah, just keep on following my pen*=؋??

_in Sha Allah kamar yadda na fada new book zai fara sauka cikin satin nan, fatan zaku so shi kamar sauran domin zai yi matukar kayatar daku saboda salon daban yake, much love habibte's_




*Hoorain mai kusumbi (the hunch back girl) shine first paid novel Dina, yanzu haka Ina da complete pages da kuma complete document, duk wacce ta biya ni kuma zan bata complete pages and document din.*





Wed, may 11 2022

Share share share fisabilillah.




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
ABRAHAM


*First edition*




*WATTPAD*
@NoorEemaan



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.


_@sis Mariam jumare, @Ak saraki, @sdeentm, ina godiya sosai da sosai, hakika kuna taimaka min da posting tun daga farkon fara posting book din nan har harshe ba tare da gajiyawa ba, Allah ya sa muku da alkhairi_.>?
?d'?>?
?



Alhamdulillah
#ending


Chapter 71-72


Baccin awa daya kadai suka yi. Abraham ne ya fara tashi, ya kura wa fuskar Aysha ido, gani yayi ta kara haske sosai kamar ka taba ta jini ya fito, har kumatu ta ajiye kai kace kwai ta boye a ciki, gwanin sha'awa da kyau.

A hankali ta fara buWe idanun ta...karaf idanun su suka sarke dana juna, murmushin ta mai kyau ta sakar masa, ya sumbace goshin ta sannan ya mayar mata da martani yace
"Nwunye mm" (my wife/matata).
Murmushi tayi domin a duk lokacin data ji yayi yare abin burge ta yake, har tana ji dama ta iya ita ma.

"Meye ma'anar abinda ka fada yanzu" Aysha ta tambaye shi cikin turanci.
"It means my wife" ya mayar mata da martani.
Jinjina kai tayi alamun ta gane kana tace

"I love You so much my husband"
Cikin zallan mamaki Abraham ya kafe Aysha da ido, sai yake jin kamar kunnuwan sa ne basu jiye masa daidai ba, Aysha ta fahimci hakan sai ta kara maimaita masa tana kifa kanta a kirjin shi...
Wata wawuyar runguma ya sake mata, duk da tana saman kirjin nasa ya shiga birgima da ita kan gadon kamar wasu kananan yara sai faman dariya suke.

***************???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?***

Haka rayuwar su ta cigaba da tafiya, A kullum kaunar da suke wa juna kara yawa take.

*ANTY SARAH*
Bayan ta koma kauyen su, a ranar tayi kuka sosai kamar ranta zai fita, tayi nadamar mugayen halayen ta na baya ya fi cikin kwando.
Kudin da ABRAHAM ya bata da shi ta fara sana'a inda anan take samu tana rufawa kanta asiri, amma bata jin dadin komai a rayuwa, sakamakon mugayen halayen ta na baya, domin hakkin rai ba wasa bane, duk da ba ita tayi kissan ba, kullum cikin kuka da nadama take, a haka ta cigaba da rayuwar ta...

Bayan kwana biyu Abraham yayi musu booking flight suka je har wajen dangin iyayen sa, abin mamaki sun karbi shi hannun biyu-biyu, duk da ya sanar da su ya zama muslumi sannan ya auri Hausa Fulani
Ya basu labarin Madam Gloria, sun kuma yi mamaki da Allah wadai da mugayen halayen Madam Gloria.
sannan sun karbi Aysha a matsayin suruka a gare su, sosai Abraham yaji dadi dama tsoron sa kenan kada a samu matsala, kuma gashi alhamdulillah an samu akasin haka. Hak'ik'a addu'a bata taSa faduwa kasa a banza...



*****&**********&******


*SOME MONTHS LATER*

A parking lot ya daidaita parking din motar sa kirar Mercedes Benz white color, kana ya fito rike da brife case a hannun sa, ya kara kyau hadi da dan jiki kadan wanda yayi matu?ar amsar sa, rufe motar yayi kana ya nufi cikin gidan.

Sallama dauke a bakin sa ya shige falon, inda ya tarar da Ammar da Anwar sun baza littafan su da alama home-work suke, da gudu suka ruga jin muryar mahaifin su suka dane shi, cikin kaunar ya'yan sa ya rungume su yace
"Uma aka mm how are you doing?" (Y'ay'ana ya kuke)

"We are Fine Daddy" suka amsa a tare, domin yana dan koya musu Igbo, kuma yaran na da kunnen ji, domin suna saurin rike wa.

Sauke su yayi ya shafa kan su... rarraba idanun sa ya shiga yi amma bai ga abinda yake nema ba.
Kallon su Ammar yayi yace "where is Ammuh?"

Suka ce "tana bacci".

Jinjina kai yayi cikin tausayin ta kana ya nufi saman, a ko ina zai fada cewa matar sa jaruma ce, domin duk da cikin ta ya tsufa amma haka take ?o?arin kula da su daga shi har su Ammar, wani zubin sai ya bata rai take barin aikin, domin shi kam tausaya mata yake amma ita kam ce masa take tana jin dadin aikin, wai motsa jiki take.

A hankali ya sanya kafar sa cikin dakin sanyi Ac da dadaddan k'amshin dakin ya bugi hancin sa, lumshe ido yayi kana ya ware su kan Aysha dake bacci da tulelen cikin ta haihuwa ko yau ko gobe.

Gaban gadon ya karasa ya zauna a kasan tiles ya tankwashe kafafunsa, kafar ta daya kumbura ya sumbata kana ya shiga yi mata tausa tsawon Mintuna goma, sannan ta motsa, cikin sauri ya matso gab da ita, yace "You re awake"

Jinjina masa Kai tayi tana Murmushi, dan kara kan sa yayi kan cikin ta dake ta motsi yace "how are my babies doing?"

Cikin shagwaba tace "babies? "

Dariya yayi yace "yes nah"

Dan ture kanshi tayi kana tace "i'm carrying baby, not babies" ta fada cikin iyakar gaskiyar ta, domin idan yace babies dinnan tsoro yake bata.

Dan girgiza kan sa yayi da murmushi kan fuskar sa, ya lura ta koyi rigima kwanan nan. Hannunta ya manna wa sumbata yace "A h?r? m g? na ?ny? ?wammm, i mara mma"
(I love you my life, you re beautiful)

Dan far da ido tayi cikin jin dadi, a duk lokacin daya ci mata yana son ta, tana da kyau wani girma kanta keyi, duk da cikin ya sata dan muni amma bai fasa gaya mata haka ba, kullum a sallar ta sai tayi godiya ga Allah daya bata miji kamar Abraham, ko a aljanna tana fata da addu'a ya zama miji a gare ta.


**********************



_*INNAH*_

Ta bangaren ta kuwa Abraham ya siya mata gida a nan Kaduna domin ta dawo kusa da su, amma tace ita kam bata so ta fi zama a tushen ta, Abraham ya bawa Anty Bintu gidan halak malak saboda hallacin data yiwa rayuwarsa (Aysha).

ANTY Bintu tayi godiya ba iyaka, tana kuma taya Aysha murnan samun miji Waya tamkar da dubu.

Abraham bai kyale Inna ba sai daya sa aka fasa gidan ta na Gombe aka dawo mata da komai ginin zamani, sannan ya bata kudade masu yawan gaske ta fara business. Inna fa ta dawo yar business ta yi sharrrr ta ita ainayin skin color dinta ya fito saboda jindadin rayuwa da kwanciyar hankali da ta samu .

Yan'uwan su baffa da suka ji Inna tayi arziki suka kwaso kansu suka zo suna bata hakuri cikin borin kunya, Inna abu Waya ta duba ta yafe masu darajar mijin ta baffa duk da baya raye, amma har gobe kaunar mijin ta na manne a ranta.

Wanna kenan.


____&________& __


_*2:00pm*_

malam bahaushe yace dare mahutan bawa, ko ina yayi tsit sakamakon baccin da mafi yawan mutane ke yi, hakan take ga su Abraham, domin kwance Aysha take ta Wora kanta kan kirjin sa suna baccin su cike da nutsuwa, can cikin bacci Aysha taji kamar wani abu ya karce ta, a dan zabure ta mike zaune, nan ta kara ji mararta ta kulle sosai, yarfa hannun tayi tana cije labb'an ta, domin zafin ya fara zama unbearable, hakan yasa ta saki kuka, ta shiga girgiza Abraham...

A rude ya tashi ganin tana kuka ya tada hankalin sa, take ya fahimci nakuda ce ta zo, cikin sauri ya mike ya buWe sif dinta ya dauko mata daya daga cikin maternity gown dinta ya sanya mata, sannan shima ya saka riga da wando, mukullin mota ya dauko da jakar da suka hada kayan haihuwa kana ya dauke ta kamar yar jaririya suka sauka kasa...
Gaban Mota ya buWe ya saka ta a ciki bayan ya kwantar da kujerar, sannan shima ya shiga ya danna horn wa mai gadi dake gyangyadi, a 360 mai gadi ya buWe kofar Abraham ya cilla hancin motar sa waje, yama manta da su Ammar dake bacci a dakin su, Burin sa a yanzu shine matar sa ta rabu da wanna zafin da take ji.

Had'add'en private hospital ya kawo ta, inda cikin sauri da sanin makamin aiki suka karbe ta, kana suka yi *maternity ward* da ita ba tare da sun yarda ya shiga ba.

Safa da marwa ya shiga yi fuskar sa na bayyana tsananin damuwar da yake ciki, fata da muradin sa Aysha ta dawo gareshi, domin bazai iya juran rasa ta ba.

Daga karshe ma famfo dake cikin asibiti ya nufa yayi alwala kana yaje mota ya dauko sallaya ya dawo ya fara nafilfili...

Bayan ya gama ya zauna kan sallayar yana addu'o'in sa, ya ga wata nurse ta zo wajen shi murmushi dauke kan fuskar ta, boyayyen ajiyar zuciya ya sauke kana ya mike cikin sauri yana tambayar ta ina matar sa, nurse ta sake Murmushi tace
"congratulations sir, please come with me"

Nan Abraham ya bita zuwa dakin hutun da aka mayar da Aysha kamar zai tashi sama... Bakin kofar nurse din ta tsaya ta nuna masa ya shiga dakin yayinda ita kuma ta koma domin kula da wata patient da aka kawo Sakamakon barin cikin da ta yi, dama haka rayuwa take, wani yana farinciki at the same time wani yana kuka.

BuWe kofar yayi ya shiga, kwance ya hango Aysha da fuskar ta yayi fayau tana jefan sa da murmushin kauna, da sauri ya karasa wajen ta, dan dago ta yayi hadi da rungume ta yana faman jere mata sannu, ga sumbata da yake ta faman sarkar mata a ko ina, shi kam yama manta da wani cikin jikin ta balle ya damu da abinda ta haifa, shi dai burin shi ya cika tunda tana cikin koshin lafiya.

"Wai ina su Ammar ne" ta tambaye shi cikin muryar ta da ta yi sanyi kalau saboda wuyan haihuwar da ta sha.

Sai a lokacin gogan ya tuna, dan shafa kansa yayi yace "wallahi yanzu na samu nutsuwa uwammm! suna bacci, kuma kin san gobe Saturday baza su tashi da wuri ba tunda ba school"

"Uhmmm uhmmm ban yarda ba, jeka dauko min yarana Please, su kadai ne fa" tace tana shagwa6e masa.


Zai yi magana kenan suka ji kukan jarirai sai a lokacin Abraham ya tuna ashe fa ta haihu, da sauri ya nufi gadon da suke kwance, wani murmushin farinciki ya saki kana yace "yes! I told you ?wammmm! I told you that you re giving birth to twin but you don't believe me, thank you so much for giving me these babies... ooh my cuties welcome to the world, come, come, come to daddy" yace yana daukan su hadi da rungume su a jikin sa, yana jin kaunar su na ratsa shi.

Aysha kuwa ta zama yar kallo, murmushi take yi, tana kallon zallan farinciki da zumudin dake shimfide a kyakkyawar fuskar mijin ta.

Da misalin ?arfe bakwai na safe aka sallami su, kasancewar an gwada su an tabbatar daga uwar har jariran suna lafiya.

Tun kafin su zo gida ya fara kira yana sanarwa yan'uwa da abokan arziki.
Suna shiga gida suka tarar tashin su Ammar kenan daga bacci suna neman Ammuh'n su, ai da suka ga jarirai suka hau murna wai sun yi kannai, Ammar yace ya dauki hassana itace tasa, Anwar ma yace ya dauki usaina, ha?a dai suka dinga shirme kala? cike da yarinta.

A ranar Abraham ya sanjawa Aysha waya zuwa kirar iPhone latest.
Murna sosai Aysha tayi, ta kuma gode masa sosai duk da ya nuna baya son godiyar.

A daren Abraham ya bawa Aysha damar zabar w yaran suna, ba kuma Wan ba zai iya zaba musu ba, domin yayi zurfin a sanin addini sosai fiye da tunanin mai tunani, wasu lokutan Aysha tana yaba masa ta yanda baya wasa da addinin sa, babu wanda za a faWa wa musulunta yayi ya yarda kai kace a ciki ya taso tun yana karami.
Kawai ya bawa Aysha daman ne domin ta cancanci fiye y hakan a wajen shi.


Suhailat da Safiyya Aysha ta zama musu. Abraham kuma ya saka musu sunan yare Amanda da Chioma... da Aysha taji ma'anar sunan sai ta kamu da son sunan sosai wani zubin da shi take kiran su...

Ranar da su Amanda suka cika sati Daya da haihuwa aka sha sunan su daya kawatu sosai sannan mutane sun hallara sosai, an ci an sha an raba kyaututtuka masu Wauke da hotunan yan biyu...


*****. . *****. *****.

BAYAN SHEKARA BIYU
Hayaniya ke tashi a falo inda Abraham ke zaune cikin yaran sa hudu, Ammar, Anwar, Suhailat (Amanda), Safiyya (Chioma) suna buga game.
Yanda yake biye musu sai ka rantse ba shi ne mahaifin su ba, haka suke tamkar abokai, amma hakan baya hana idan sun yi laifi yaki hukunta su ba, duk da tarin kauna da shakuwa dake tsakanin su.

Aysha dake tsaye a kitchen cikin shadda tsad'ad'iyya maroon color tana girki sai faman girgiza kanta take tana jin draman su tana murmushi, kamar yadda akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin shi da yaran sa, haka itama ya dauke ta kawar sa, kanwar sa, abokiyar shawarar sa, sannan matar sa abin son da kaunar sa.

Aysha ta kara kyau, aji, wayewa, hadi da girma, soyayyar ta da Abraham kullum karuwa take, duk da ana samun sabani, saboda masu iya magana na cewa tsakanin ha?ora da karshe na samun sabani, sai dai basa bari fadan su ya kai dare ba tare da sun shirya kan su ba.


"Ammuh!!!" Ta ji yaran duka sun hada baki wurin kiranta har da uban su.

Dariya tayi kasa-kasa tace "Am coming guys"

Wanke hannun ta tayi, ta goge da towel sannan ta fito, waje ta samu ta zauna cikin su tace "gani"

"Surprise!"

Suka hada baki wurin fadin haka, sannan suka fito da ticket da ke boye a hannunsu masu yawa, Abraham ta kalla ya kanne mata ido daya, dauke kanta tayi cikin sauri saboda yaran.

Sannan cikin farincki ta bashi side hug domin ticket din zuwa aikin hajji ne ya biya musu gaba-daya, sannan ya biyawa Inna da Anty bintu, kuma tare zasu tafi cikin satin nan...

Yaran ma gaba-daya suka rungume shi ya kuwa saka karfaffan hannunwan sa ya zagaye su duka.

Kallon Aysha yayi yace "how will I say i Love You all in Hausa?"

"Ina son ku duka" Aysha ta fada masa.

"i...in...a son....ku... du... ka" ya maimaita kalmar a rarrabe kamar mai koyan magana, har yanzu kam Hausa taki zama a Bakin sa.

Gaba-da?a suka fashe da dariya jin yanda yayi Hausar, shi ma biye musu yayi suka dinga dariyar a tare, abin gwanin kyau da burgewa, what a happy family!.




I believe every ending is another beautiful begining.



Alhamdulillah!







Special thanks to:
Noor novelist world
Sarautar's library
Safrat group
Mijin yarinya group
Neat lady palace
Ranar nadama group
Aludra group
Elegant online writers group
Matan buri fans
Taskar real ladingo
Surrayhms novels
Taskar mammy Kabeer
Kwaila fans group
Nana haleema palace
Gidan girki da gyaran jiki group
Fitar rana comments section
Mi Amour world
Fataucin mata fans
Hausa novels group



Dama sauran groups da Abraham ya je ina godiya a gareku Allah ya bar kauna...
Bazan manta da wattpad fans dina ba, Nagode muku sosai.



*Ya rabb Nagode bisa Ni'imar ka gareni, ya rabb na gode daka bani ikon kammala wanna book na Abraham cikin koshin lafiya. Ya rabb kuskure dana yi cikin littafin nan ka yafe min, wanda na fada daidai ka bani ladan sa da Ni da reader's*



*Masoyan littafin NoorEemaan ina mai godiya a gareku da yadda kuke karban duk wani novel dana kawo muku hannu biyu-biyu, tabbas na ga kauna a Abraham, zan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login