Showing 3001 words to 6000 words out of 84387 words

Chapter 2 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28138

tabbas madam Gloria ta cika shu'uma.


"Likita Allah ya jikan su, amma bazan iya kallon yaran ba, da wanne zan ji da mutuwar Nonye ko da rasa Y'ay'an dana saka ran zasu maye mun gurbin Nonye" sai ta saka kuka kana ta cigaba "a binne su kawai a makabartan asibitin nan, amma bazan juri ganin gawar? su ba" ta karasa tana sakin sheshekan kuka...




Biyar saura na asuba aka basu gawar Nonye suka saka a mota, sai a lokacin madam Gloria ta Lura babu anty Sarah amma bata tsaya neman ta ba, domin bata so gari ya waye basu koma gida ba, a cewar ta Sarah zata zo gidan tunda ba bakuwar ta bane....

Wanna karan da kyar Emma da madam Gloria suka shigar da Nonye, suna yi suna hutawa har suka kaita dakin ta, hadi da rufe ta da bargo, falo suka fito ta sallami Emma ya tafi, kana ta koma dakin ta, tana fatan gari ya waye sosai domin yanzu karfe Biyar da mintuna ashirin ne.


*WASHEGARI*

Kamar yadda madam Gloria ta fada karfe shidan safiya ta gwala ihun mutuwar Nonye

sosai take kuka tana birgima a kasa tamkar gaske, hakan yasa ma'aikatan gidan suka shigo part din halin tashi, suma kuka suka saka sakamakon Jin abinda madam Gloria take fada, "ewooooo Nonye yata kin tafi kin barmu, tayaya zamu kasance cikin farinciki bayan babu ke, kin tafi kin barmu da son(ABRAHAM) ya zamu yi da rashin ki, bayan kece cikon farincikin mu, mutuwa kin min yankan kauna " sosai take maganganu cikin fitar hayyaci kai ka rantse da gaske take



Kowa na gidan yaji mutuwar Nonye matuka, domin macece mai son kowa, bata raina mutum komin kaskancin sa, haka zalika tana da son mutane sosai...


Kamar yadda yake a al'adar inyamurai idan mutum ya mutu basa binne shi a take, mortuary ake kai shi zuwa wasu lokuta kafin ayi bikin binne shi, hakan yasa madam Gloria da ta sanja shiga zuwa bakake tare da wasu yan'uwan su.

Haka al'adar su take idan anyi musu mutuwa komai na jikinsu yana kasancewa baki ne har izuwa wasu kwanaki.





*GOMBE STATE*

Bayan anty Sarah ta sauka a garin GOMBE ta shiga raba Idanu domin babu inda ta sani, ga yaran Allah ya basu wani mugun hakuri domin har yanzu basu yi kuka ba, daga karshe ta yanke hukuncin fara tafiya, tayi tafiya mai dan nisa kana ta shiga wani layi, gida na hudu idonta ya sauka a kai, haka kawai taji gidan ya kwanta mata a rai, shiga gidan tayi inda ta tarar da wata k'yakyawar yarinya fara sol hadi da iyayenta dake zaune a gefen ta suna hira cikin annushuwa





Da kallo duk suka bi anty Sarah ganin ta shigo musu babu sallama, "lafiya baiwar Allah" uban yarinyar ya tambaya a tausashe.




Jim anty Sarah tayi domin bata ji ko kalma daya daga abinda yace ba, dan haka tace "please can I use your toilet? Am really pressed"


Duk shiru suka yi domin babu mai Jin turanci cikinsu gwara-gwara baffa ya fahimci kalmar toilet din cikin abinda tace Dan haka yace "shalelen baffa zuba mata ruwa a buta"


Take yarinyar ta yi yanda yace kana ta kalli anty Sarah tace "gashi"

Amsar butar tayi, duk da a yawan lokuta idan fitsari zasu yi basu fiye amfani da ruwa ba, shiga bandaki tayi da jariran inda babu wanda ya lura cikin su Baffa cewar yarane sabuwar haihuwa a hannunta


Ta kai mintuna biyar a ciki kana ta leko ta kofar langa-langan inda ya huje ta ga baffa da Inna(matar baffa) sun shige daki, ya rage saura k'yakyawar bafulatanar yarinyar nan mai suna Aysha, ita ma daga karshe mikewa tayi zuwa nata dakin, duk anty Sarah na kallon su...


Ganin babu kowa a tsakar gidan ya Sanya ta ajiye jakar hannunta hadi da jariran a kasa cikin bandakin, kana a hankalin ta Bud'e kofar cikin sanda ta fito, sai da ta je soron gidan ta fara sauri-sauri gudu-gudu domin barin Layin.....







Ga wacce take bukatar ayi adding dinta a group chat this num=?G?
07082281566


NoorEemaan >؋?




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/4, 10:42 AM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM



WATTPAD
@NoorEemaan




ELEGANT ONLINE WRITER'S =???
'?



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da facebook su yi join ta wanna link din.




Chapter 5-6


Sai da anty Sarah ta fito babban titi kana hankalin ta ya kwanta, ba tare da ta bata lokaci ba ta nufi tasha domin hawa mota da zai sadata da asalin kauyan su, Sam bata damu yamma tayi ba, haka zalika bata damu ko jin tsoron tafiyar dare ba, duk da yanda ta kai ga tsanar zaman kauye amma shine waje da zai sa hankalinta ya kwanta, domin bata son abinda zai sake hada ta da madam Gloria, ta kuma sani cewa har abada zasu da sauran kwannciyar hankali, domin kashe rai ba abun wasa bane.





Fatan ta daya mutanen nan su rike yaran amana, kuma in sha Allah zata yi kokarin sada Abraham da y'ay'ansa a lokacin daya dace matuk'ar tana raye, hawayen nadama ne ya saukar mata tuno cewa sune silan mutuwar Nonye, yanzu meye ribar su?





*GOMBE*

Baffa ne ya fito daga daki inna na biye dashi, "indo! Indon Baffa!!" baffan ya kira ta yana lekan Dan karamin dakin ta



"na'am baffana" ta fada cikin murya kasa-kasa wanda ke nuni da bacci ke shirin daukar ta.



Fitowar ta yayi daidai da dariyar da Baffa ya saki, kana cikin tarin kaunar tilon 'yarsa yace" shalelena ba dai bacci kike shirin yi ba ga magriba ta gabato"


"wallahi baffana bacci nake ji sosai" tafada a shagwabe tana dago lumsasun fararren idanunta da ya dan rine kadan sak'amak'on baccin da take ji.



"kinga ki danyi hakuri kiyi sallah idan yaso sai ki kwanta, zo mu zauna a tabarma kafin ayi kiran"

"toh Baffa bari nayi fitsari Ina zuwa" tafada tana daukar buta domin shiga bandakin.



Inna dake garken dabobbi tana tasar nonon shanu ta saki murmushi hadi da girgiza kai, domin sosai? indo da Baffa ke kaunar juna wani zubin 'yar kallo take zama...



Kafar hagu indo ta saka a bandakin bakinta dauke da addu'ar shiga bandaki, sai dai addu'ar makalewa yayi sak'amak'on abinda tayi tozali dashi a kasan bandakin, shin mafarki take ko gaske? Ko ko shin aljanu ke kokarin bud'e mata ido?



Sanin cewa bata da mai bata amsa ya sanya ta kwala ihu daya yi matukar gigita su Baffa, hankali tashe suke nufi bandakin dan ganin abinda ke faruwa, ya kuma saka Indon su ihu...



*IMO STATE *
Zaune madam Gloria take sanye da bakaken kaya kamar yadda yake al'adarsu idan anyi musu rasuwa, idanunta sunyi luhu? sakamakon kukan karyan da take yi ba dare ba rana matukar a idon jama'a ne, sosai mutane ke tausaya mata, domin har tafi iyayen Nonye nuna mutuwar ta girgiza ta...



Wata yar'uwar su ce ta kalli madam Gloria hadi da cewa "Gloria kiyi hakuri hakan nan, sannan ya kamata zuwa yanzu ki kira ABRAHAM domin ya sani, saboda babu amfanin cigaba da boye masa"



Wani kuka madam Gloria ta saki har da majina tace "tayaya zanyi in sanar da dana wanna mummunan labarin? Banason hankalin shi ya tashi" ta karasa cikin kuka tana bubbuga kafafunta a kasa, riketa duk sukayi suna bata hakuri hadi da karfafa mata guiwan ta kira shi kan cewa ya dawo gida amma kada ta sanar dashi mutuwar Nonye sai idan ya dawo kasar.


Tana Jan majina ta fara dialing number'n shi kana ta daidaita muryar ta...


*KOREA*
Kwance yake gefen beach a wani had'add'en kujera sanye da boxer, sai sunglass dake manne a idanun sa, haka zalika sauran mazan sanye suke da boxer musamman masu shiga ruwan yayinda matan ke sanye da bikini wanda daga kirjinsu sai al'auransu ya rufe. Kyakyawane, chocolate color mai haske, yana da kirar nan da akewa lakabi da *giant* sai had'add'en six-packs dinsa idaunsa bai fiye girma ba, amma suna da matukar jan hankali, hancinsa dogo ne mai dan kauri, yana madaidaicin lips daya kara fuskar tasa kyau ainun, akwai wani karamin dankunne a kunnensa yayinda ya rataya cross + a wuyansa wanda hakan ke nuni da cewa shi din mabiyin addinin chirista(Christian) ne.




Burinsa yanzu ya gama abinda ya kawo shi kasar nan ya tafi domin yayi kewar gida sosai, kasancewar agajiye yake dawowa ko damar Kiran nonye da mummy baya yi, dan karamin tsaki yaja wanda sautinsa bai fito ba sai labb'an bakin sa ne suka motsa.


Haka kawai yake jin ranshi ba dadi, latsa wayarsa yake kokarin yi Kiran madam Gloria ya shigo, yaji dadi sai dai Sam babu alamar hakan a fuskar sa, domin shi mutum ne miskili da zurfin ciki wanda kai tsaye mutum bazai iya karantar abinda ke fuskar sa ba.

Latsa kore yayi hadi da kara wayar a kunnensa "good evening mummy, I was trying to call you guys now" ya fada da turanci.


Daga bangaren madam Gloria kuwa sosai ta daidaita muryar ta kana tace " yes son! Ya kamata ka zo kawo gida hakan gobe, idan yaso ka koma daga baya" ta fada masa da yaren igbo


"mummy is everything alright? How's Nonye and my baby doing?" kit madam Gloria ta kashe wayar ta, domin batasan sauran amsar bashi ba.




Haka nan yake Jin cewa there's something wrong Dan haka babu bata lokaci ya shirya kana yayi booking flight Inda yaci sa a samun jirgin da zai je Nigeria, amma sai karfen taran dare.




Dan haka gida ya dawo ya shirya cikin wasu had'add'un kaya da ganinsu kadai zai tabbatar maka da tsadar su, wayoyin sa hadi da system dinsa kadai ya dauka kana ya tura sakon Gmail ga company daya zo takanas domin su cewa akwai dalili mai karfi daya sanyashi komawa kasar sa, amma zai dawo as soon as possible, daga nan filin jirgi ya koma domin zuwa lokacin takwas ta wuce, ba kuma yaso yayi missing flight.




*NIGERIA*
IMO STATE
Bayan ya sauka a airport ya kira lambar driver gidan hadi da sanar dashi yana Airport, babu Jimawa yazo amma wanna karon driver'n bai yi masa surutunsa irin yanda ya saba ba, hakan ya dan bawa Abraham mamaki domin yasan driver akwai surutu sosai, amma Sam bai nuna ba


Tafiyar mintuna ashirin ya sada su da Abraham mansion, sauka yayi, bai jira driver ya Bude masa ba, direct ya shige general parlour sai dai abinda ya gani ya sanya gabansa fad'uwa sosai domin a iya saninsa a kuma al'adar su ta igbo sai idan mutum ya mutu ake sanya bakakken kaya irin haka, toh me yasa duk suka sanya bakin kaya? Waye ya mutu? Yayi duka tambayar a ransa yana bin fuskar kowa da kallo


Da sauri madam Gloria ta taso, ta isa gareshi kana ta fashe da kuka sosai tace....






_A GASKIYA COMMENT DINKU YANA KADAN HAKAN KE SANI RASA KARFIN GUIWAN TYPING DAN ALLAH IDAN KUN KARA YAWAN COMMENT ZAN DINGA YI MUKU KODA BAYAN KWANA DAYA NE, IF POSSIBLE KULLUM, DOMIN INA DA AIKI SOSAI NAKE DAUREWA NAYI MUKU DAN HAKA KUMA KU FARANTA MIN DA COMMENT DINKU_





Noor>؋?


26/12/2021
9:41am



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/4, 8:22 PM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM

*First edition*



*WATTPAD*
@NoorEemaan




ELEGANT ONLINE WRITER'S =???
'?


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din


_note wanna ba sabon typing bane, reposting nake, so duk mai so ya fara bi yanzu ba sai nayi nisa ace daga farko ba_




Chapter 7-8

Yana shirin yin magana Kenan yaji muryar madam Gloria na fadin

"son munyi rashi,?munyi rashi babba, Nonye ta tafi ta barmu, tafiya ta har abada, Nonye is gone for ever son" ta karasa tana fadawa jikinsa hadi da rungumeshi, yayinda sautin kukan ta ya karade gabadayan falon.



Tamkar wanda aka watsawa barkono haka ya runtse idanunsa, ji yayi gabadaya dakin na juya masa, sosai gabansa ke faduwa tamkar zata Faso kirjin sa ta fito



Nonyen sa ta mutu, ta tafi, tafiya ta har abada? abinda madam Gloria ta fada ya Shiga dawowa kunnuwansa , a karo na biyu madam Gloria ta kara cewa "ta haifi yan biyu wanda suma a take suka mutu, wayyo ni Gloria ya zanyi da raina" wanna karon k'wak'walwar Abraham ce ta daina gane komai sak'amak'on abinda madam Gloria ta kara fada, wanda ya sanya guiwowin sa yin Sanyi har ya gaza daukar gangar jikinsa, tilas ya? sulale kasa, gabadaya jikinsa ya dauki rawa tamkar wanda yake cikin kankara, sabanin hakan gumi ne ke keto masa, na zallan tashin hankali, ga gashin kansa sun mimmike, duk da cewa babu ko digon hawaye a jajayen idanunsa, amma dole dukkanin wani mai tausayi da imani ya tausayawa halin da Abraham yake ciki a yanzu.




Rikeshi madam Gloria tayi tana kuka hadi da bashi hakuri, ko kala ya gaza furtawa domin nauyi da labb'ansa suka yi, hannu biyu ya sa ya rike kanshi dake barazanar fashewa, haka ya kasance cikin wanna halin fiye da awa uku kuma ko motsi bai yi ba, banda zuciyarsa dake bugawa da sauri? mutum zai yi tunanin matacce ne....




*GOMBE STATE*

Ba tare da su baffa sun lura da jariran dake kasa ba suka riketa hadi da cewa "aysha lafiya meya same ki, yi magana meya same ki aysha? " suka fada a tare suka duba jikinta...




Idanunta ta runtsa, sakamakon hakan hawaye ya zubo kan kyakyawar fuskar ta, hannu ta mika ta yiwa su baffa nuni izuwa ga kasan bandakin inda? babies din ke kwance wanda zuwa yanzu sun fara mutsu? sak'amak'on sanyin ruwan bandakin daya fara ratsa ta cikin towel din zuwa fatar jikinsu, a tare suka zaro idanun su ganin abin al'ajabi, da ba dan kada su kara firgita tilon diyar su ba, da ihun suma zasu zunduma, a take kuma k'wak'walwarsu ya tariyo musu sanda anty Sarah ta shigo da farin towel din nan, amma basu taba tunanin cewa abu mai rai ne a ciki ba, a tunanin su ko wani kayan ta ne bata son ajiyewa a waje shiyasa ta shigar dashi bandakin.




Sosai mamaki da al'ajabi ya rufe su, babban tambayar su anan shine menene dalilin ajiye yaran da anty Sarah tayi? Domin basu ga alamun tabin hankali ga anty Sarah ba, bare su ce rashin cikakken hankali ne ya sanya ta manta yaranta? a Bandakin, shakka babu wanna babban al'amari ne ya shigo cikin Rayuwar su...





Baffa da tausayin yaran ya gama rufe shi ya tsunkuya, amma gabansa na faduwa, amma ya dake, domin abu ne w??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????anda bai taba ji ko gani ba ne ya ratsa gidan sa, sosai ya dake gudun kada ya kara firgita su Inna, addu'a dauke a bakinsa ya hade yaran a jikinsa, kana ya kalli su Inna yace "ki dauko jakar nan ku fito daga bandakin hakan nan" ya fada yana barin bandakin, sai a lokacin indo ta Bude idanunta dake ziraro da hawayen zallan tsoro, cikin tsoro Inna ta sanya hannu ta dauki jakar hadi da riko hannun indo suka fito daga bandakin....





Direct dakinsa baffa ya nufa da yaran, hakan yasa cikin muryar tsoro? indo ta ce "wayyo baffa nah! kada ka shigar dasu dakin ka, Kar su cutar da mu, kila ba mutane bane, ni gaskiya bazan iya kwana a gidan nan ba, Dan Allah? baffa ka fitar dasu daga gidan nan, muje mu nemi matar mu bata yaran ta " ta karasa cikin zallan tsoro mai hade da kuruciya hadi da sakalci....



Itama Inna irin tunanin Indo ne a ranta na cewa
Yaran ba mutane bane, amma bata furta ba, sai sai tsaf baffan ya karance ta, hakan ya sanya shi sakin murmushi, ya kuma girgiza kansa, tabbas duk shekarun mace da kaifin tunanin ta namiji ya fita koda bai kai ta yawan shekaru ba, ba tare da kuma yayi magana ba ya ida shigewa dan karamin dakin sa, ya kuma san cewa zasu biyo bayan sa domin basu taba ketare umarnin sa...





Wata jibgegiyyar kodaddiyyar malum-malum baffa ya janyo cikin kayansa ya saka yaran a ciki ya lullube su kana ya kwantar dasu kan gado irin dai na kauyen nan, towel din ya fitar waje ya saka cikin roban wanki ya saka kilin da ruwa ya jika shi, kana ya saka kilin ya wanke hannunsa sosai sannan ya koma dakin....





Gyaran murya yayi hadi da mai da duban sa ga Aysha Indo yace "shalelen baffa ina so kwantar da? hankalin ki, ta ina kike tsamanin zamu ga matar? Wacce hanya tabi? Ba mu sani ba, Allahu masani.
Sannan ba fa manta yaran tayi ba, ko mai tabin hankali ta san kaunar abinda ta haifa, Allah ka dai yasan dalilin daya sa ta ajiye mana yaran, wadannan yaran mutane ne kamar mu, ki cire tsoro a ranki kinji, Allah kadai yasan dalilin daya sanya wadannan bayin Allah shigowa cikin Rayuwar mu, ko nace kaddarar mu" ya fada yana nuna yaran kana ya cigaba "domin akwai gidaje bila adadin a unguwar nan, amma nan gidan yaran suka fado,? Dan haka nayi alkawarin kula da yaran nan har sanda zan daina numfashi, ina fatan zan samu goyan baya daga gareku"




Jinjina kai inna ta yi, wanda tsoron ya?dan ragu sak'amak'on maganganun da baffan yayi, zai kara magana yaji an kwala Kiran sallar magriba a wani masallaci hakan ya sanya shi barin dakin da sauri yana gayawa su inna suma su hanzarta yin alwala kada su rasa jam'i domin su kan bi jam'i domin masallacin yana kusa da gidan su, wanda baffa shine Limamun masallacin....




Bayan an iddar da sallah da kamar mintuna talatin baffa ya shigo hannun sa dauke da bakar leda, kallon inna dake kokarin yin tarke/talke yayi, Cikin sauri yace "da kin fara yi wa yaran wanka da ruwan zafin nan, idan yaso sai a sake dora na tuwon" ba musu ta ajiye kayan tuwon, wani tsaftataccen bokiti ta dauko ta juye ruwan, kana ta zuba wani, hadi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login