Showing 39001 words to 42000 words out of 84387 words

Chapter 14 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28142

din ya sha yana lashe lips din sa, kallon sa Aysha take da gefen ido ba tare da ta bari ya ganta ba.

Bayan ya gama ta fitar da plate din ta dawo, ta share inda ya dan bata kad'an.

Ta mike domin tafiya, har ta dora hannu a handle din kofa ta ji gyaran muryar sa, cak ta tsaya hadi da juyowa domin tun bayan da aka dawo dashi daga asibiti bata kara jin ko da tarin nan yayi ba banda da zu da yayi murmushi mai sauti, tsayawa tayi tana kallon sa, inda zuciyar ta ke bata cewa wani Abu yake bukata shiyasa yayi gyaran murya, hannu ya daga ya yafutota, cikin nutsuwa ta kara so ta tsaya a gaban sa.

"Sit"

Ta ji yace cikin karamin sauti yana dan buga kan gadon sa, ba musu ta zauna tana jin ta a takure, a hankali ABRAHAM ya juyo da keken sa, sai ya zamana suna facing din juna, ajiyar zuciya ya sauke, yana so yayi mata godiya bisa kokarin da take yi wurin kula dashi, domin samun kamar ta sai an tono, ya sha jin labari da ganin yadda wasu muslimai musamman hausawan mu da suke nuna bambamci ga chiristian ko nuna kyama, ko wariya a garesu, wanda hakan bai kamata ba, ko wani dan Adam yana da daraja, dan mutum ba Muslumi bane babu dace wa ka ce masa wai
WANNA ARNE NE, KO DUK ARNAYE WUTA ZASU SHIGA WUTA.


*(Subhanallah! Wane mutum da zai yanke wa bawa hukunci, Allah kadai ke da wanna ikon, sannan dukkanin mu Allah muke bautawa, addini ne ya bambamta mu, ba a shiga tsakanin bawa da ubangijin sa, kar mu yanke hukunci ga ko wani bawa, komai laifi da kuma tarin zunuban sa, dan haka matukar mun ga mutum chiristian ne Kar mu nuna kyama a garesu hakan zai sa su san cewa addinin musulucin addinin zaman lafiya ne da kaunar juna, wanda har hakan zai iya sawa su yi kwadayin shiga Muslunci Allah yasa mu dace)*


"Thank you for everything, i really appreciate your efforts, God bless you"

A hankali ta dago kanta dake maiko, sakamakon ruwan hawaye daya taru a ciki, domin ita kam bata fahimci abinda yace ba.

Fahimtar hakan yasa Abraham bud'e tafin hannu sa, take farar takardan da ta yi rubutu a kai ya bayyana, cikin rashin fahimta ta zuba wa soft palm din sa ido, furzar da numfashi yayi, domin zai sha ciwon kai saboda ba jin yaren juna suke ba, wani tunani ne ya fado ransa, hakan yasa shi tura keken sa zuwa gaban drawer ya dauko memo da biro hadi da wayar sa dake kan memon ya dawo.

Play store ya shiga ya yi searching App din translation daga turanci zuwa hausa, take aka fito masa da su da yawa ya zabi daya ya yi installing kana ya shiga typing turancin da yayi mata...

babu jimawa aka fito masa da fassarar, yayi copying a memon ya dora mata kan cinya, a hankali ta kai idanun ta kan kyakyawar rubutun sa mai kyau da tsari.

"Nagode sosai da komai, na yaba da kokarin ki, Allah yayi miki Albarka"

karo na uku kenan da ta maimaita rubutun cikin ranta, a hankali ta dago tana masa kallon zallan mamaki wanda hakan ya kasa buya a saman fuskar sa "Dama ya iya hausa?" ta fada a ranta.

Ya karanci hakan ta fuskar ta , hakan yasa shi dago mata wayar, yana mata alamun daga nan ya rubuta, murmushi tayi tana sunkuyar da kan ta.


A memon ita ma ta rubuta
"Bakomai, kar ka damu."

Ta mika masa, karba yayi ya shiga typing abinda da ta rubuta, dama already ya sauke App din translation daga hausa i zuwa turanci tun ranar da Aysha ta tafi gombe...

ya shiga typing, bayan ta gama app din ya fito masa da amsa kamar haka...

"it's nothing, never mind"

Hakan nan yaji baya so ta tafi, so yake hirar kuraman ta su ta cigaba, a hankali ya rubuta da turanci

"is it true that you gave birth to twins as small as you re?"

Bayan fassaran ya fito ya rubuta ya mika mata, murmushin daya Bayyana siririyar wushiryarta tayi, saboda tuno lovely twins dinta, ga kuma kalaman sa da suka bata dariya wai ita karama, a hankali ta kara karanta abinda ya rubuta,


"da gaske ne cewa kin haifi yan biyu duk kankantar ki?"


Amsa ta bashi da "Eh! da gaske ne, ina da yara maza biyu, suna wajen mahaifiyata"

Bayan yayi typing fassarar ta fito da masa da amsa kamar haka "yes! It's true I have kids, two boys, they are with my mother"



Jinjina kai yayi, yana mamaki wanna abun, kamar ta ace tana da yara, sai yaji wani iri ba dadi, shi a ganin sa iyayen ta sun cutar da ita.



Aysha kuwa ta zabi boye wa ko ma waye gaskiyar lamarin domin ba ta so ko da wasa su Ammar su tashi su San cewa ba ita ce ta haife su ba har akan ya shafi rayuwar su, bata so suyi kukan maraici, ko a ina ne zata fada, idan ma aure zata yi sai ta fada wa Mijin da zata aura cewa tana da yara.


*ABRAHAM*
Sai after 11 yayi mata alamun taje ta kwanta, a hankali ta tashi ta fita, yabi bayan ta da kallo, numfashi pya sauke yana jin wani yanayi na musamman daga gareta, wanda har yanzu ya kasa gane ko na menene, domin Sam tunani da k'wak'walwar sa basu taba bashi cewa wata kalma ta SO zata shiga tsakanin su ba.




"amma meyasa na damu da rashin ta kusa dani?" ya tambayi kansa, sai kuma ya kau da tunanin daga ransa, kan wheelchair ya cigaba da zama har bacci ya dauke sa yana jin gab'obin jikin sa na masa ciwo, saboda zaman da ya jima yana yi a waje daya.


*(lafiya babban jari inji masu iya magana. Da Abraham na da lafiya yanzu zai tashi ya kuma kwanta a duk lokacin da yake so ko da babu mai taimaka masa, shiyasa komai da mutum zai yi maka ba zai taba zama yanda zaka yiwa karan kan ka ba, Allah ka wadata mu da lafiya)*



*BAYAN KWANA UKU*
Tsaye Aysha take a gaban sif dinta bayan ta fito daga wanka, Riga da skirt na wani lace din ta mai saukin kudi ja hadi da touches din fari a jiki ta sanya kana ta saka wani madaidaicin farin hijab mai roba, as usually fuskar ta fess babu ko digon make up, zata rufe sif din Kenan idanun ta suka sauka kan Ghana most go din ta mai dauke da photo album dinan, a hankali ta kai hannu da niyyar budewa domin ta ga abinda ke ciki, har ta fara zuge zip din taji horn daga bakin gate, mayar da zip din tayi ta rufe kana ta nufi window din dakin ta cikin sauri ta zuge, domin iya sanin ta dai babu bai shigowa babu kuma mai fita a mota tunda Abraham ba lafiya gare shi ba, Wacce ta gani ta fito daga mota ne ya sanya gaban ta fad'uwa fiye da ganin farkon da ta fara yi mata tun zuwan ta na farko gidan.




_Idan ina free gobe zaku iya ganin update_



Share fisabilillah
Comment
Vote



Thank you for reading my story #Abraham



NoorEemaan
07082281566





2:33pm
Saturday 12, 2022




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851

[10/13, 7:25 AM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM

*First edition*



https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




Chapter 43-44


"MADAM!"

Ta fada cikin cracking voice tana jin wani irin tashin hankalin sak'amak'on ganin ta, hakan nan taji rashin nutsuwa da ganin ta.


"ya Rahman!" ta furta a fili hadi da dafe kirjin ta dake bugu da sauri - sauri...


A sanayaye ta fito daga dakin ta, wani bangare na zuciyar ta na mata fad'an cewa "Aysha me kike yi haka ne? Mata da gidan ta amma kina jin rashin dadin ganin ta, bayan ita ce dalilin kawo ki wanna gidan"

Numfashi mai dumi ta furzar Kamar zautaciyya a fili tace "na sani, nima na san abinda nake ji a raina bai dace ba, amma na kasa sarrafa zuciya ta, ban San meya sa ba"

ta karasa kamar zata saki kuka, domin har ranta tana son daina jin wanna yanayin amma ta kasa.


Dakin madam Gloria ta nufa domin gaishe ta, saboda rashin zuwa gaishe'n ta kan iya janyo wata matsala da bata San abinda zai haifar ba...

A hankali ta shiga k'wank'wansa kofar tsahon mintuna hudu kana madam Gloria ta bud'e kofar, hadi da tsare hanya, kamar yadda zuciyar ta yake baka haka fuskar ta yake, Sam babu alamun fara'a bare Imani.


Cikin tsora da Aysha ke k'ok'arin boyewa ta dan russuna alamun girmamawa tace
"Madam ina kwana, Sannu da dawowa ya hanya?"


"Lafiya" Madam Gloria tace a dak'ile hadi da bango kofa, wanda hakan ya sanya Aysha firgita.


A sanyayye ta juya ta koma sama, tana jan Numfashi, saboda wani karni-karni da wari-wari da madam Gloria ke yi a lokacin da ta fito, inda har yanzu warin bai bace ba, sai ma yanzu ta tuno da maganin da Inna ta bata tace ta hada wa Abraham.


Madam Gloria kuwa lock ta saka wa kofar, domin a halin da take ciki bata kaunar ganin kowa har sai ta cimma ma burin ta, ga wani mahauk'acin tsanar Aysha da ta kara ji yanzu da ta ganta.

Wata bakar leda dake kan gado ta dauko a hankali, cire ledar tayi, inda wata madaidaiciyar k'warya ta bayyana, an zagaye k'waryan da Jan kyalle, murfin
K'waryan ta bude inda take wani hayaki ya fito, sai wani abu kamar kwallo karami mai tsakanin haske kamar an saka k'wan lantarki a ciki yana ta birgima cikin kwaryan.


Murmushin zallan mugun ta ta saki, tana mai rufe murfin, kasan gado ta mayar da k'waryan, kana ta nufi bathroom domin yin wanka, saboda ita kanta tana shak'an warin dake?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? fita a jikin ta, wanda baya rasa nasaba da jimawar ta a garin kwara da kuma aikin da bokan ya gudanar a kanta, domin wasu abubuwa da bata San ko meye ba yake ta watsa mata a jiki...



AYSHA
Bayan ta dauko duk abinda Inna ta bata inda yake cikin Wata leda ta hado da qur'ani kana ta nufa dakin sa, Bayan ta Bude kofar ta jingina kanta da kofar tana kallon sa, duk da shi ma ita yake kallo amma a yau ta kasa janye idanun ta domin wani mugun tausayin sa take ji a ranta wanda bata taba Jin kamar sa ba, ajiyar zuciya ta sauke bayan ta karasa shigowa cikin dakin, ajiye jakar bakon tayi kana ta nufi kitchen dinsa inda yaune karon farko da za a fara amfani dashi, ta kuma zabi hakan ne saboda bata son madam Gloria ta ganta.

Ta San kowacce uwa da danta ke fama da irin wanna lalurar zata yi farinciki idan aka ce yau ga wani magani a jarrraba masa, ko wata hanya ta samun lafiiyar sa, amma ita kam zuciyar ta yafi kwanciya kan ta boye mata, ba tare da ta San dalilin hakan ba.



*ABRAHAM*
Da kallo ya bi Aysha yana ganin yanda fuskar ta ke bayyana damuwa. "what's wrong with her?" ya tambayi kansa, sai kuma ya Lumshe idanun sa yana tsammanin fitowar ta domin ya tambayeta waya shigo ko ya fita kasancewar daga gidan, kasancewar yaji horn dazu.


Aysha kuwa electric cooker dake kitchen din ta jona, tukunya ta dauko ta dauraye, kana ta tari ruwa a ciki, ta sink din dake kitchen ta dora a wuta.

Kara fitowa tayi, ba tare da ta kalle shi ba ta dauki wasu magunguna kana ta koma kitchen...

Abraham kuwa ya bita da kallo yana mamakin meya sanja mood dinta haka.


*AYSHA*
Ta bata wasu mintuna kana ta fito da maganin cikin jug sai ta dora karamin cup a saman sa, gaban sa ta zauna ta zuba maganin daya d'an huci a cup ta mika masa, k'urawa maganin dake da kalar ruwan hanta yayi, yana mamaki ko meye wanna.


Idanun ta dake cike taf da ruwan hawaye da bata san ko na menene ba ta kura masa, ba tare da ta damu da ya ji, ko kar yaji ma'anar abinda zata fadi ba tace "ka sha Dan Allah! magani ne, Inna ce tace na baka domin samun lafiyar ka in sha Allah, ka yarda dani, bazan cutar da kai ba, bazan taba cutar da kai ba, ka sha Dan Allah kaji"

ta karasa cikin zubar hawaye hannun ta har k'ak'arwa yake wanda yasa maganin cikin cup din ya shiga rawa kamar zai zube, bata san meyasa yau raunin ta ya fito fili ba, ji take kamar tayi kuka sosai.


Tunda ta fara magana ya kurawa cute lips din ta ido, ko kalma daya bai fahimta daga maganganun ta ba, dadin amon muryata dake fita daki-daki hadi da dark pink lips din ta sune suka ja hankalin sa har ya kasa d'auke idanun sa daga kanta, amma abu daya ne, abu daya ne ya sosa masa zuciya ganin hawayen ta...


Bai kara bari zuciyar sa ta yi wani tunani ba ya zagaye hannun sa kan hannun ta dake jikin cup din, hakan yasa hannun ta ke kasa, yayin da nasa k'arfaffan hannun yayi wa na ta rumfa.

Numfashi mai tafe da shesheka Aysha ta saki, sakamakon taushi da dan Sanyi da tafin hannunsa ke dashi wanda ya ratsa har tafin kafar ta, hakan bai taba faruwa da ita ba, baya ga baffan ta, Abraham shine mutum na farko daya fara taba mata hannu.


Abraham kuwa a hankali ya zare hannun sa, sannan ya zari cup din daga hannun ta, without even a second thought ya kai cup din bakin sa, ya sani cewa bazata cutar da shi ba, yayi yarda da ita hundred percent, zargin da yayi mata a baya na tunanin cewa ko itace tayi poisoning din sa kuskure ne, zama waje daya da yake yawan yi da ita ya fahimci wacece ita da kuma dabi'unta, dan haka baya shakku a kanta ko kad'an, a hankali ya shiga sha yana yamutsa fuska saboda baurin maganin, amma haka ya daure ya cigaba da sha saboda da ita, domin a ganin sa idan bai sha ba kuka zata cigaba da yi.



Aysha kuwa ganin cewa ya karba ya sanya ta sauke Numfashi kana ta fito da wani madaidaicin Allo hadi da tawadda Ledan, wasu surori cikin Alqur'anin mai girma da Inna ta fada mata ta shiga rubutawa cikin k'warewa, Bayan ta gama ta ajiye qur'anin kan dayan drawer, tashi tayi ta shiga kitchen ta dauko wani bowl ta dawo ta zauna, zama tayi ta dauko ruwan zam-zam dake cikin ledan kana ta shiga wanke rubutun cikin bowl din bayan tayi bismillah.


Duk abinda take Abraham yana kallon ta, sosai rubutun ya burge shi, bama kamar saurin daya ga hannun ta nayi alamun ta k'ware sosai, bai ankara ba yaga ta miko masa ruwan rubutun, kurawa ruwan ido yayi, musamman bakin daya ga yayi, a tunanin sa wani abu ne daban.

"Ka sha kajiiiii" ta karasa tana mai Jan karshen maganar.


Kawai kallon rubutun yake cikin wani yanayi, Aysha kuwa Dama tayi sammanin hakan, ta San Mawuyaci ne ya karba kai tsaye, Numfashi ta furzar tana kara matsowa kusa dashi, ta mika masa kawar da kan yayi domin scent Din tawaddar daya bugi hancin sa, kara mayar da kallon sa ga Aysha yayi, cikin marairaita tace masa

"Dan Allah!"

A hankali yasa hannu ya karba, toshe hancin sa yayi kana cikin sauri-sauri ya shiga shan rubutun, murmushi Aysha tayi ta kuma San kamshin tawaddar ne baya so shiyasa ya toshe hancin sa, ruwa ta bashi ya dan sha, sannan ya Lumshe idanun sa, Numfashi ya shiga saukewa kamar wanda yayi tseren gudu...



Aysha ta kai Ledan kitchen ta ajiye sannan ta wanke bowl da cup din hadi da tukunyar dafa maganin daya dan sanja wa tukunyar launi, Bayan ta gama ta fito, hanyar barin dakin ta nufa, kamar daga sama taji yace

"hey!"

cikin sauri ta juyo, hannu yayi mata alamun ta zo, ba musu ta dawo.
Da littafin hirar su ya rubuta mata tambayar da yake so bayan App din ta fito masa da amsa.

Karba tayi ta karanta sannan ta dan yi Jim kana ta masa reply da cewa

"MADAM ce ta dawo"

Bayan yayi typing fassarar ya karanta sai ya dafe kan sa kawai, yana jin wani daci a ransa sosai, har yau yana ganin kamar mafarki yake, kamar ba mummyn sa bace wanna.



*AYSHA*
ganin yanayin sa ya sanja ya sanya ta kasa tafiya, kasan tiles din ta zauna duk suka yi zaman kurame na tsahon mintuna goma, sannan tunanin Kiran Inna yazo zuciyar ta, contact list ta shiga inda lambobin mutane biyu gareta, daga na lnna sai na Anty Bintu, number'n Inna ta shiga sannan ta danna dialing hadi da sakawa a loudspeaker, domin taji da kyau Idan an bawa su twins waya.


Ringing uku kacal tayi taji kamilaliyyar murya Innar tayi sallama, amsawa Aysha tayi cikin farincikin jin muryar Innar ta, Bayan sun gaisa tace a bawa su Ammar taji muryoyin su, tana jin Inna tace

"karbi kai Anwar kuyi magana sai ka bawa Ammar, Ammuh dinku ce"

A rude yaran suka shiga Kiran "Ammuh! Ammuh!! babu k'ak'autawa tamk'ar zasu fasa wayar su shigo ciki...

Aysha kuwa dariya ta shiga yi, da k'yar tace " yarana ku nutsu, daya bayan daya zamu sha hira kun ji"

A tare da suka ce "toh" yayinda daga can bangaren Ammar yayi nasaran warcen wayar a hannun Anwar yace "Ammuh nah! Ammar ne"
Abraham da idanun sa ke a Lumshe yayi saurin bude ta, saboda muryar yaron daya tsaya masa a rai kwarai.

Ga kuma k'wak'walwar sa da ta tuno masa shigowar Aysha dakin sa na farko, idan bai manta ba wanna sunan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login