Showing 42001 words to 45000 words out of 84387 words

Chapter 15 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28154

ji ta fada.

"Ammar! what does that means?" ya fada kasan mak'oshin sa sannan ya kurawa fuskar ta ido, yana kallo yanda take waya cikin annushuwa "da alama tana matukar son yaranta" zuciyar sa ta raya masa hakan.



Aysha kuwa biye wa Ammar ta yi suka sha hirar su sannan tace a bawa Anwar da har ya fara fushi an ki bashi waya da sauri suka sha hira sosai, har kudin wayar ya kare ba tare da ta shirya wa hakan ba, wanda har rashin jin dadin hakan ya bayyana a fuskar ta.


Ajiye wayar tayi a gefen ta ta dago kanta, idanun ta suka fada cikin nashi, sauke kanta tayi kasa tana wasa da yatsun hannun ta, tsahon mintuna biyar ta ga ya miko mata littafin hirar su mai dauke da tambaya kamar haka...



"kina da hoton yaran ki, ki nuna min ina son ganin su, I just want to see them" daga yanayin rubutun mutum zai fahimci wanda ya rubuta daga kasan zuciyar sa maganar ta fito, Bayan mintunan da ta dauka bata ce komai ba, sannan ta shiga rubuta masa reply, bayan ta gama ta mika masa.






*Afuwan my ppl ba nan naso tsayawa ba, buh I just have to*...





Share to others please.


NoorEemaan
07082281566


Thank you for reading my story #Abraham



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/13, 7:36 AM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM

*First edition*



WATTPAD
@NoorEemaan






https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



chapter 45-46


"I don't have their pictures (bani da hoton su)" ta amsa masa a takaice.

numfashi Mai zafi ya furzar a lokacin Daya karanta fassarar abin da ta rubuta kasancewar da Hausa ta rubuta masa.

Hakan Nan yaji ba Dadi, sai kuma ya dafe Kansa domin sai yanzu ya tuna cewa karamar keypad ce a hannun ta, ba kuma zai dauki Wani hoton kirki ya zama clear ba, but aleast ya so ganin hoton ko da yayi dishi-dishi kuwa daya fi farinciki fiye da amsar da ta bashi, domin sosai maganar yaran ya tsaya a ransa.


Dan satar kallon Aysha da kanta ke kasa yayi, sannan ya ja numfashi a ransa yace "mother of two, I really can't believe this" ya fada a ransa da mamakin wai yar yarinyar nan (Aysha) tana da y'ay'a har biyu.


Sha biyu ya wuce da kad'an Aysha ta bar dakin ta sauka izuwa kitchen Domin daura girki, saboda Sam bata son yin kuskure ko laifi ga Madam Gloria, domin bata ga alamun sauki a gare ta ba.


Tsaye take a kitchen ta dafa kitchen cabinets tana tunanin abinda zata dafa, can tunanin dafa alale ya fado mata domin tunda ta fara yi musu girki bata taba dafa alale ba, wake ta debo ta wanke domin already Mai kyau ne Babu bukatar sinta, sannan ta cire duka wannan baki-bakin na Saman wake, bayan ta gama ta debo albasa da attaruhu Hadi da crayfish ta gyara sannan ta zuba cikin blender ta mark'ada su duka har da waken.
Kana ta zuba a Wani babban bowl, Man kuli da manja ta zuba kan markadadiyyar kullin, domin bata so yayi ja sosai, sannan ta zuba maggi seasoning da spices masu Dadin kamshi ta sa cokali babba ta juya ingredients din da kyau sannan ta dauko dafaffen kwai da kifi wanda ta gyara ta yanyanka cikin kullin, sai ta dauko wasu mazubi masu kyau da shape kala-kala ta shiga zuba kullin alalen.
Dama already ruwan da ta daura a gas kan babban tukunya ya Soma tafasa Nan ta shiga jera alalen ciki tun kafin ya karasa dahuwa har k'amshi ya cika kitchen din zuwa falo...

Daga nan ta shiga hada cucumber juice Daya Sha kayan Hadi.

bayan ta gama ta zuba komai a warmer, juice din dama ta zuba a jug ta saka a fridge, sannan ta gyara kitchen din, ya dawo fess.

Warmer daya ta ajiye a dinner da cucumber juice, sannan ta dauki na Abraham da juice din shi ta nufi sama ta ajiye masa.

bata Jin cin komai, Hakan yasa ta sauko kasa ta hada quaker oat ta koma sama, har zata wuce dakin ta sai ta dawo da baya ta shiga dakin sa.


Zaune yake ya kurawa tray din abincin ido ba Tare da ya taba ba, tausayin sa taji Mai tsanani a ranta, ajiye cup din quarter oat akan centre table tayi kana ta shiga serving din shi, bayan ta gama ta ajiye masa a gaban sa sannan ta dauki quaker oat din ta daya Sha Madara ta koma gefe ta zauna ta shiga Sha a hankali, duk da cewa bata fiye son quaker oat ba saboda dan yaukin sa, amma hakan ta daure ta shiga Sha kadan-kadan.



Abraham kuwa kallon ta kawai yake, sai kuma ya dauke Kansa yayi gyaran murya, saurin dago kan ta tayi ta kalle shi, ba tare da ya kalle ta ba yace

"come and join me"

shiru tayi tana tunanin abinda yace, sai dai nuni da abincin da yayi ya sa ta fahimci abinda yake nufi, cikin sauri ta girgiza kanta, hawayen da ba ta San ko na menene ba ya cika idanun ta.


Dan zaro mata ido yayi Hadi da Kara hade fuskar sa yayi mata nuni da abincin, Wata shakkar sa ce ya shige ta, a sanyayye ta shiga can guiwa har ta iso gefen sa, da kallo ya shiga bin ta cikin admiration, domin yanda take Jan guiwar ta ya fito da yarintar ta kwarai.


Addu'ar su irin na christian a yayin cin abinci yayi kana ya sa spoon ya yanki alalen ya Kai bakin sa, lumshe ido yayi saboda zallan Dadin daya ziyarci harshen sa, sosai yake yaba kwarewar ta a ransa, domin Babu girkin wacce ke masa dadi kamar na Aysha yanzu.

A hankali ya Bude idanun sa da tun sanda ya fara tauna abinci suke a rufe, ganin kanta a kasa bama ta da alamar cin abincin yasa a hankali ya debo alalen a spoon ya mika mata, a hankali Aysha ta dago ta kalle shi, sai kuma tasa hannu kan spoon din ta dauki alalen, a hankali tasa a baki ta fara tauna, bai kara kallon ta ba ya cigaba da cin abincin sa.


Aysha kuwa ta cigaba da shan quaker oat din ta domin bata so ya kara bata alalen domin bata Jin cin abincin yanzu...



Bayan ya gama ci ya sha cucumber juice dinsa ta tattara wajen ta fita da kwanukan, tana sauka ta hango Madam Gloria hakimce kan dinning table tana cin abincin, gabanta ne ya fadi, amma ta dake....



"ke! wa kika kai wa abinci?"

Madam ta tambaya cikin muryan ta Mai kama da fada-fada.

cikin rudu Aysha tace
"hm.....hmmm yallabai na...na kai wa"


"Hmmmm... ya ci iya cin sa a yanzu, domin daga rana irin ta yau zai bar wanna duniyar yabi iyayen sa, idan yana bukatar kari ma ki kara masa, bai dame ni ba"

ta fada a bayyana, amma cikin yaren Igbo wanda hakan yasa Aysha dake zaro ido kasa gane me ta ce.


Madam Gloria kuwa hannu tayi wa Aysha alamun ta bar gaban ta, cikin sauri Aysha ta nufi kitchen har tana tuntube.

Da gayya ta shiga wanke-wanke a hankali gudun kada ta fito ta tarar da madam Gloria, aikuwa sai bayan mintuna talatin ta fito, ajiyar zuciya ta sauke ganin babu Madam a dining table, hakan yasa ta nufi upstairs da gudu kamar wacce taga abin tsoro.



*********

6:00pm
Bayan Aysha ta gama dinner Mai sauki, ta ajiye na madam a dining table, sannan shima ta kai masa na sa dakin sa...

Dakin ta ta fada tayi wanka, bayan ta gama ta daura alwalan magriba ta fito, tana cikin shiryawa aka kira magriba.


Bayan tayi sallah ta kishingida da jikin gadon ta, ba tare da ta shiryawa Hakan ba Wani bacci Mai Dadi ya dauke ta.



*1:45pm*
AYSHA

A firgice ta farka cikin tsoro, sak'amak'on baccin da ta Yi Mai tsayi, cikin sauri ta mike salati dauke a bakinta, dafe gefen kanta daya tsara mata tayi, sannan ta nufi toilet domin daura alwalan Isha da bata Yi ba.


*********

Mintuna goma Sha biyar ya dauke ta yin sallah'n Isha Hadi da sha'afi da wutiri.

Bayan ta iddar ta zauna shiru, tunanin Abraham ya shiga yawo cikin brain din ta, kasa zama tayi Hakan yasa ta mike domin ta je gareshi, duk da cewa dare ne Amma ta San cewa matuk'ar bata je ba hankalin ta bazai taba kwanciya ba.


A hankali ta tura kofar dakin ta shiga, gabanta ne ya bada ras sak'amak'on ganin sa zaune ya kura wa hanyar shigowa ido, tamk'ar Yana jiran isowar ta ne.


Kallon gefen da ta ajiye masa abinci tayi, taga ko taba wa bai yi ba, sosai taji ba Dadi a ranta...


"Kila yunwa yake ji shiyasa ya kasa bacci"

Ta fada a ranta yayin da fuskar ta ke k'wabe kamar zata saki kuka...

A hankali ta karasa Wajen abincin domin zuba masa sai dai...

Karfaffan hannun sa Mai tsayi ya daga mata alamun ta barshi, mamaki Hakan taji, a sanyayye ta dago tace

"Dan Allah ka bari na zuba Maka, wallahi bacci ne ya dauke ni kaji"


Sleepyn face dinta ya kalla kana ya jefa mata Wani kallo daya sa ta sulale kasan tiles ta zauna.

Abraham kuwa Bai fahimci abinda tace ba, Amma duk Wanda ya kalle ta a wanna lokacin zai fahimci cewa bacci tayi, ba kuma fushi yake da ita ba, domin Yana ganin kokarin ta sosai, Hakan Nan tana da kima a zuciyar sa sosai, sannan baya jin yunwa ko kadan.



Duk da cewa ya gaji matuk'a da zaman wheelchair din, domin ba Abu bane Mai sauki, Amma ya yarda da kaddara mai kyau da akasin ta, yasan cewa Allah ne ya jarrabe shi, ba kuma zai Yi butulci ga Allah ba, illa yayi addu'a Allah ya bashi lafiya, domin yasan Babu kaddara mara kyau da zai dawwama.

Aysha kuwa kasa komawa dakinta tayi... karaf idanunta suka sauka kan qur'anin da ta ajiye a bedside drawer din sa tun da rana, ajiyar zuciya ta sauke domin zama shirun ya soma gunduran ta, cikin sauri ta dauko shi ta koma ta zauna, suratul yasin ta Bude tayi Bismillah ta shiga karantawa cikin zazzak'ar murya kasa-kasa tana bawa kowacce harafi hakkin ta.



A kuma daidai lokacin ne Madam Gloria ke tsaye a dakin ta rike da kwaryan nan Mai dauke da wanna abun Mai tsananin haske , sanye take da wasu jajayen kaya Mai ratsin Baki.


Wanna abun na cikin kwaryan ta Sanya a tafin hannun ta, sosai hannun ta ya shiga rawa saboda karfin abun, wasu kalamai marasa dadin ji ta shiga karantawa da Wani yare, idanun ta kyaar kan wanna abun na cikin tafin hannu ta....






=؞?NoorEemaan=؞?



Thank you for reading my novel #Abraham.



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/13, 12:13 PM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM

*First edition*


*WATTPAD*
@NoorEemaan




https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




Chapter 47-48


Ta dauki tsawon mintuna goma tana karanta suddabarun ta kana ta hura iskar bakin ta izuwa ga abin tsafin dake hannun ta, kamar a mafarki abin ya bar hannun ta ya shiga tafiya shuuuuu ya bi ta bangon dakin ya fita...



Murmushin farinciki Madam Gloria ta saki ganin burin ta na daf da cika. Bayan Mintuna biyu kacal murnan ta ya koma ciki, firgice da tashin hankali suka maye gurbin farinciki da take ciki sak'amak'on abin tsafin daya dawo hannun ta, Wanda hakan alamun rashin nasara ne.


Gabanta ne ya bada ras! domin lalacewar wanna aikin daidai yake da lalacewar dukkanin Shirin ta, kamar zararriya tace "meyasa? Meke Shirin faruwa ne, Wani irin taurin rai ne da kai Abraham, wallahi bazan bar ka ba, har sai na ga ka zama gawa!" Ta karasa a tsawace.


A karo na biyu ta Kara Yi, Bai je ko ina ba ya sake dawowa ya fada cikin tafin hannun ta. Wani fushi ya zo mata, dukkanin nutsuwarta ta tattaro ga abin tsafin kana ta shiga karanta suddabarun ta, sai ta hura iskan bakin ta izuwa ga abin tsafin, wannan karon abin tsafin ya koma cikin kwaryan, a hankali launin kwaryan da abin tsafin Nan ya dawo Wani bakinkirin, jikin ta ne ya shiga rawa, Hakan yasa kwaryan ya subuce daga hannunta ya fadi kasa ya tarwartse, zubewa tayi a kasa ta saki Wani Kara, yayinda hawaye Mai zafi ya biyo kuncin ta hugu...


Kamar zararriya ta shiga birgima a kasa tana surutai, so take ta mike domin zuwa duba Abraham ta ga abin sa ya hana aikin ta cika, domin ta ga dalilin da ya hana shi mutuwa, Amma ta kasa tashi saboda tashin hankali da fargaban da take ciki yasa jikin ta mutuwa, tsoro sosai ya shige ta domin bata manta da abinda bokan Nan yace Mata ba, kafin ta karbo kwaryan tsafin.


Kamar almara, wanna fashashen kwaryan nan Mai dauke da abin tsafi ya shiga tattara Kansa waje Daya, kana ya bace bat, daidai inda kwaryan ya bace Wani bakin hayaki ya tashi yayi sama Wajen pop'n dakin.

Duk Madam Gloria na kallon abinda ke faruwa Amma ta kasa motsa ko da yatsan ta ne, kamar wacce aka datsa haka ta kasance.



ABRAHAM
Cikin birgewa yake kallon Dan tsut din bakin ta dake karanta littafi Mai sarki, his attention is hundred percent with her, har lau Bai San abinda take karantawa ba, Amma Yana sintar Kansa cikin nutsuwa a duk lokacin da yake Jin zazzak'ar muryan ta Mai sanyin amo na karatun qur'anin, ji yake dama su dauwamma a haka, iska Mai sanyi ya furzar daga bakin sa Yana sake mayar da hankalin sa gare ta.


Aysha kuwa bata San ma Yana Yi ba, karatun ta ta cigaba da Yi tana Jin fargaban da ke damunta tun safe da bata San Kona menene ba na barin zuciyar ta, salama da Wani sanyin ni'ima daga Allah ya maye gurbin tsoron ta, haka ta dauki tsahon lokaci tana karatu, har bacci yaci karfin idanun ta, ba tare da ta shiryawa Hakan ba Wani bacci Mai dadin gaske ya dauke ta a zaune qur'anin ta na rungume a kirjin ta.



ABRAHAM
Kallon innocent face din ta yake, Yana Jin Wani nishadi da Bai San Kona menene ba na ratsa shi, yanda numfashin ta ke fita a hankali da yanda zararran eyelashes dinta ke rufe yafi komai Jan hankalin sa.




"Oh! Jesus Christ" Ya fada a hankali Yana lumshe idanun sa, haka ya cigaba da zama har akayi Kiran sallah daga masallacin unguwar...



Idanun sa da suka bata awannin a rufe, ba kuma bacci yake ba ya Bude a hankali, ya ga sai bacci take, domin zuwa yanzu ta sulale kasan tiles din Amma still qur'anin ta na rungume a kirjin ta.


A hankali ya tura keken sa zuwa gaban inda take kwance, yace "hey!"
Shiru Aysha na duniya bacci bata San Yana Yi ba, kafarta ya kalla, kana ya daga kafar sa ya Dora kan tafin kafarta...



Can cikin bacci Aysha ta ji Wani sanyi na ratsa ta, a hankali ta shiga Bude idanun ta, sai kuma ta sake rufewa alamun baccin Bai ishe ta,
"hey! Wake up it's time for your prayer (ke! Ki tashi, lokacin sallar ku yayi)" fada da turanci Yana Dan murza kafar sa kan na ta kafar.


Cikin sauri ta mike salati dauke a bakinta tana murza idanun ta, kalle-kalle ta shiga Yi, taga dai tabbas dakin sa ne, cikin muryan bacci tace" yaushe nayi bacci a dakin Nan ban sani ba?"
Ganin bata da Mai bata amsa yasa ta mike a hankali ta bar dakin tana waiwayen sa, da kallo ya bi bayanta Yana sakin ajiyar zuciya, Wani Abu kamar rashin jin Dadi game da barin ta dakin na ratsa zuciyar sa...


************************

9:05am
A daidai lokacin Aysha ke haurawa da breakfast din sa sama, a hankali ta shiga dakin bakin ta dauke da sallama, dago Kansa yayi ya shiga bin ta da kallo, bayan ta ajiye ta Dan risina tace

"Ina kwana"

Daga mata Kai kawai yayi, domin zuwa yanzu yasan Ina kwana kamar gaisuwa ce, duk da Bai San ma'anar ba, Amma ganin tana yawan fadin Kalmar ya sa ya zauna a Kansa..


Bayan tayi serving dinsa sannan ta Kara warming maganin jiya ta bashi, Babu tunanin komai ya karba ya shanye. Ganin Haka yasa ta barin dakin domin tayi wanka sannan tazo tayi masa rubutu. Da shigar ta wakan da shiryawan mintuna ashirin ya dauke ta sannan ta dawo dakin sa tayi masa rubutu a allo ta bashi, Nan ma babu musu ya karba ya Sha, domin ya gama bata dukkanin wata yarda...



Bayan Nan ta gyara masa dakin sa ta sauka da kwanukan, dakin madam Gloria tabi da kallo ta girgiza kanta kana ta hayo sama abinta, domin taje kofar dakin ta ta dinga kwankwansawa domin ta Yi mata gyaran dakin Amma bata Bude ba, dakin ta ta koma domin Wani mugun bacci take ji.




MADAM GLORIA

Sai safa da marwa take saboda tashin hankali, rashin cikar burin ta a daren jiya yafi komai daga hankalin ta, hanyar kofar ta nufa tana huci kamar wata zak'anya, cikin ranta take fadin "yaro yaro ne! Yaro man kaza, idan ka San wata baka San wata ba" ta karasa fada kana cikin sauri ta nufi dakin sa.
Tana shiga ta tarar da Abraham zaune Yana bacci a tunanin ta, , domin idanun sa a lumshe suke, sa dai abinda bata sani ba, duk Yana sane da shigowar ta, duk da idanun sa a rufe suke Amma Yana kallonta ta tsakankanin eyelashes dinsa.



Kallon shi take daga sama izuwa kasa saboda ganin Bai yi rama ko lalacewa kamar yanda tayi tunani ba, "Amma wake kula dashi haka?" Ta fada a ranta tana tabe Baki tare da Jin haushin ganin sa tsaf tsaf duk da bawai kamar lokacin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login