Showing 51001 words to 54000 words out of 84387 words

Chapter 18 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28140

ba, har ya fara kosawa da zaman, sannan ya hangota ta mirror tana tafiya Cikin nutsuwar ta.



Kasa Wauke idanunsa daga kanta yayi, duk da cewa yau kimanin sati biyu da fara zuwa makarantar ta kenan, amma yana ganin improvment daga gare ta, musamman yanda take dagewa wurin tilawar abinda ake koya mata, duk da cewa har abubuwan yan primary one ana koya mata domin ta fi gane wa sosai, amma yana ganin kokarin ta kasancewar bata taSa zama a ajin boko ba.


AYSHA
Sai faman kalle kalle take ta ina zata hango driver, Sam bata ma lura da motar Abraham ba, shima ya fahimci hakan, sai ya zuge glass din window ya leko da kan sa, karaf suka hada ido, zaro idanun ta tayi saboda mamaki ganin sa, domin bata taSa kawowa a ranta cewa zai zo daukar ta ba.


Dayan bangaren ta zagaya ta shiga ba tare da tace komai ba, shima bai ce komai ba ya tada motar suka bar haraban wajen.


Bayan sun iso gida Aysha ta buWe motar, ta saka santala-santala kafafunta kasa sannan ta waiwayo ta Wan rusuna kanta tace

"welcome tank" (ita nufin ta so take tace weldone thanks)

Jinjina kan sa kawai yayi yana matse dariyar sa, sannan ta fita izuwa cikin gida.


Ajiyar zuciya kakarfa ya sauke a lokacin daya daina hango ta.

Wasu lokutan yakan ji wani iri musamman idan ta kama shi yana kallon ta, amma ya kasa daina kallon ta, ya sani cewa ba wani abu ke burge shi a jikin ta ba bare ace shi yake kallo, domin idan diri ne bata kamo Chinonyen sa ba, amma kuma baya kallon Nonye kamar yadda yake kallon Aysha, ya rasa dalili, sai dai a kullum idan yana tambayar kansa game da yawan kallon da yake mata, his heart always tells him that hallaci da kyawun zuciyar ta yake kallon deep inside her.

Amma abinda Abraham bai sani ba shine ya kamu da son Aysha tun daga ranar da suka fara haduwa a adaidaitasahu, a kuma ranar ne zuciyar sa ta fara bugawa domin ta.

Haka ya kwashe tsawon mintuna a motar sannan ya kashe motar ya fito, direct dakin sa ya wuce, ya fada kan gado yana tunanin rayuwar sa, kewa sosai yake ji yanzu musamman da babu wani nasa da zai gani ya ji dad'i, dan ma Aysha na gidan yana ganin Allah ne ya kawo ta cikin rayuwar sa, ta masa abubuwan da ko wani dangin sa bazai iya masa ita ba, duk da cewa yana biyan ta Albashi...



Numfashi ya furzar tuno cewa kusan wata daya rabon da mummy ta bar gidan nan kenan, "where is she?" ya tambayi kansa, sanin ba shida amsa yasa shi lumshe idanun sa yana fitar da numfashi daya-daya.



Har lau yana jin mummy a ransa, yana mata kallon uwa da bai da shi, duk da cewa bai san dalilin ta na son ganin ta kashe shi ba, amma yana kokarin matuka gurin ganin ya cire ta a matsayin uwa daya Wora mata, domin babu wata uwa ta gari da zata zo kashe danta.


Aysha dake kitchen tana girki kuwa kusan tunani Waya suke yi, ita mamakin wannan abu take, ace uwa ki fita ba tare da kin damu da sanin halin da Wan ki ke ciki ba, shi ma daya warke, bai nema ta ba, kanta ya kulle ta rasa gane kan abun nasu, ganin wannan abun bai shafe ta ba ne yasa ta ta6e baki ta cigaba da hada masa had'add'en fish pepper soup daya ji vegetable da spices, sai pure orange juice da zata hada masa.


Wanna kenan!


" " " " " " " " " " " "


*BAYAN WATA BIYAR DA KWANA GOMA*

Cikin wadannan watannin abubuwa da dama sun faru, ciki har da zuwan Anty Sarah Gombe gidan su Aysha, ko Allah yasa mutanen su taimaka mata wajen tayata neman Abraham, domin cikin watannin nan ta sha wahala gaba-daya ta sake fita a hayyacin ta, sak'amak'on yawan mafarke-mafarken ma rasa kyau da take yi, har abun ya fara mata gizo, gaba-daya ta rasa nutsuwar ta, hakan yasa ta zo Gombe, sai dai abin mamaki duk bulayinta ta kasa gane gidan, unguwar ya sanja mata, komai ya kwance mata, amma bata hakura ba...

Kullum daddadare sai ta je kasan gada in da mahaukata da masu Bara ke kwanciya, nan take shiga Cikin su ta kwanta, washegari ta kuma cigaba da neman gidan amma bata samu ba, amma still bata hakura ba.



***. ***. ***.


*KADUNA*

"Aysha! Aysha!!"

A hankali Aysha ta waiwayo da murmushi saman fuskar ta domin ta san mai kiran ta.

Ta kara kyau, girma, da wani wayewa daya bayyana ?arara a tare da ita, komai yanzu cikin aji da wayewar addini take yin sa, saboda mu'amala da mutane musamman yammata iri daban-daban hakan yasa komai tayi tana burge mutane, gashi yanzu ta kara ilimi sosai, turanci daidai gwargwado tana yi, tana kuma ji, kana tana tana iya rubutawa, tsakanin ta da Abraham yanzu babu musayar rubuta da takarda, ta kan yi mai magana da turanci shima idan yana bukatar abu zai fada mata da turanci.

hakika MM HARUNA ENGLISH ACADEMY sun yi kokari matu?a wurin koya wa Aysha turanci, musamman da suka ga Abraham ya sake musu kudi...


"Aysha! Why are you so In hurry, Ina zaki haka?"

Bola da ta kasance yar ajin su ta fada. Ta su ta zo daya da Aysha sosai, duk da kasancewar Bola bayerabiya amma musulma ce, tana amfanin da sunan Yaren ta ne a makaranta, kasancewar tun tana karama da sunan aka fi kiran ta.



"Bola! my boss is coming back from Dubai today, i have to rush home so that I can made him some meals"




"Oh yeah i remember, that's nice, shall well?" Bola ta fada tana mata nuni da hanya alamun su cigaba da tafiya...

Yanda Bola tayi da hannu sai ya bawa Aysha dariya...


Nan suka cigaba da hira har suka zo wajen driver, suka yi sallama da Bola, Aysha kuwa ta shiga Mota suka nufi gida.



Tana zuwa gidan jakar makarantar ta kawai ta ajiye ta shiga kitchen, tunani tayi tunda yaje dubai kusan wata Waya tasan ba lallai ya samu abinci irin na nan Nigeria ba, hakan yasa tayi tunanin dafa masa abinda zai rike cikin sa sosai, had'add'en miyar efforiro tayi masa daya sha namomi da ganda, s?kw?r? take son Yi Amma Allah ya gani bata da karfin dakawa, hakan yasa ta tuka masa *pando yam* na leda, ai kuwa sak s?kw?r? haka yayi danko ya kuma yi kyau, bayan nan tayi masa pepper chicken, ta zuba komai ta jera a dining table sannan ta gyara kitchen.

Dakinta ta nufa domin yin wanka saboda har an fara kiraye-kirayen Sallah....


A gurguje tayi wanka ta shower gel wanda Abraham ya siyo mata, har yanzu bai kare ba domin bata fiye amfani da shi ba, gashi 2.5L ne gashi da kumfa sosai, ita kam bata fiye son shower gel ba, sai mita take a ranta wai sabulun nan bata son shi sai ya yi ta sa jikin mutum sulbi kamar tayi wanka da klin ko da ruwan sama.



Bayan ta iddar da sallar ta sauko falo ta zauna shiru, so take ta kira Inna amma kuma bata son damun su, saboda kafin ta tafi makaranta sun yi waya.




Har aka fara kiraye-kirayen sallar Ishaq bai zo ba, har ta kosa da zaman sannan ta damu da rashin karasowar sa har yanzu, fatan ta Allah yasa lafiya.



Kasancewar ta na da alwala ga Kuma hijab a jikin ta yasa ta mike ta koma gefe ta kalli gabas ta tada sallah, cikin sallah taji abu na dan kauri daga kitchen, amma bata motsa ba, haka ta cigaba da salla domin bazata iya katse sallar ta ba.



Daidai lokacin Abraham ya karaso gidan...
tun kafin ya shiga falon yaji kauri sosai, mamaki ne ya kama shi, yana murda kofar ya shiga yaga Aysha tsaye a gefe tana sallah a nutse, taku biyu kacal yayi Cikin falon yaji bumm!!!
?aran ya fito daga kitchen, ga wuta daya fara ci bal-bal...

Cikin sauri da tashin hankali ya kalli AYSHA a tsawace yace "hey! Run, i said run outside my friend"

Amma Ina Aysha'n ka bata ko motsa ba sai sallar da ta cigaba da yi nutsuwa.

Cikin sauri ya nufi abin kashe wutar nan da ake manna wa a bangon ( fire extinguisher) ya zaro ta ya shiga fesawa cikin kitchen din, shima ya kare, wutan bai mutu ba ya sake zaro dayan ya c??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????igaba da kashe wutan har ya mutu, sai mugun hayaki daya cika kitchen din har ma da falo, fitilar wayar sa ya kunna da kyar ya karasa shiga kitchen Win domin hayakin yasa baya gani sosai, murda gas din yayi zuwa off, inda ya tabbatar Aysha ta manta ne bata kashe ba, tukunyar mai dake kan gas ne yayi mugun zafi har ya kama da wuta, Allah yaso wutar bata ratsa pipe din silinder ba da tuni labari ya sha bambam.


Fitowa yayi falo ya zube kan kujerar yana sakin tari saboda hayaki daya shaka over, ya kuma gode wa Allah daya takaita.

Sai faman fadin "Thank you Jesus, Jesus is Lord yake". (Allah ya ganar da duk Wanda yake hanyar bata Ameen!)

Sai da tarin ya lafa ya d'ago kansa, a razane ya kai idanunsa inda Aysha take dazu, so his greatest surprise har yanzu tana nan hankali a kwance tana sallah...

Zaro ido yayi, "Jesus Christ" ya fada kana ya nufi wajen ta, yana zuwa daidai wajen ta tana sallame shaf'i da wutri.

Hannun ta ya ja da karfi ya mikar da ita, cikin fadan da bai san ya iya ba yace "Are You insane? Did you want to kill your self huun? da ban zo da wuri ba haka zaki bari wutar ta kama ta kona ki, bayan Kina da halin guduwa, ki tsaya all in the name of praying, wait! like are you for real?" Ya fada unbelievable yana jijjiga dan kafadar ta da karfi"



Kuka mara sauti Aysha ta sakar masa, cikin rawar murya tace "Am sorry! My religion, or i should say Islam is beyond your expectations, i have already started praying, i can't run, na yarda cewa idan yau kwanana zai rage ko na gudu ko na tsaya zan mutu, addinin Muslunci ba kamar sauran addinai bane, zan iya guduwa na katse sallar sannan na roki Allah yafiya, amma katse sallar is not Good ln Islam sai da wata Babbar hujja da zai iya fadawa Allah idan ya mutu, but na zabi na tsaya ne, domin Ina son gwada zama muslumar kwarai, jaruma kan addinin ta, zan iya sadaukar da rayuwa ta ga Muslunci and I will be happy idan na mutu ta silar hakan"



Jikin sa ne ya mutu, zubewa yayi kan cushion ya zuba mata ido kamar ya samu hoto, tabbas addini Muslunci ya girmama tunanin sa kamar yadda ta fada, suna kaunar addini su, sannan suna bada dukkanin nutsuwar su wurin yin ibada basa wasa, Musliman kwarai zasu iya sadaukar da rayuwa da dukiyarsu wurin kare addinin su.

A duk lokacin daya ji Aysha na karatun qur'anin ya kan ji tana burge shi har baya son ta daina, amma a yau saboda jarumtar ta, son addinin Muslunci ne ya mamaye ilairin zuciyar sa. (Allahu Akbar!)

Cikin mutuwar jiki ya mike bayan ya gama tunani, daf da ita yazo yace "Am sorry too for yelling at you" ya karasa cikin sanyin murya sannan ya ra6a ta gefen ta cikin sauri ya haura sama...



Yana shiga dakinsa ya cire kayan jikin sa, Sannan ya nufi toilet, shower ya sakar wa kansa, ya shiga dukan kansa zuwa murd'add'en jikinsa

sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke, fuskar Aysha ke masa gizo, murmushi tattausa ya saki, domin hakan ba bakon sa bane cikin kwanakin nan, musamman da yayi tafiyar nan, tunanin ta yaki barin zuciyar sa, da yayi tunanin ta sai ya dinga sakin murmushi shi kaWai, tun yana ?aryata cewa baya kaunar ta, basu dace da juna ba, addinin su da Yaren su ba daya, ta yaya zasu so juna har ya saduda, domin har lau abubuwa uku zuwa huWu ke hana mu cigaba a ?asar mu, nuna kabilanci, addinin, hadi da son kai.


Bai damu da kome mutane zasu ce ba, domin abinda mutane zasu ce bazai cuce kan sa ba, tunda ba abu mara kyau yake kokarin aikatawa ba.


Cikin wata murya mai cike da shauki yace "Yes!i can't deny or hide it any more, i love her, and I'm saying this from the bottom of my heart"
ya karasa faWa yana shafa kirjin sa..



A gurguje ya gama wankan ya shirya cikin wasu pyajams masu taushi farare masu touches din green, ya fesa body spray din NIVEA DEEP FOR MEN.


Tun kafin ya karasa sauko wa ya hango ta zaune shiru tayi tagumi, sai ta bashi tausayi, bayan ya sauko direct dining table ya nufa, domin yayi missing abincin ta sosai, gyaran murya yayi, Cikin sauri Aysha ta taso ta fara serving din sa, Bayan nan ta nufi hanyar kitchen domin haya?in ya gama washewa, so take ta gyara.



"Where are you going to?"

" I want to clear up the kitchen" ta fada a sanyayye


"No come back, you can't do that alone" ya fada yana kai abincin bakin sa, bayan ya gama ci sannan ya ciro wayarsa dake aljihun wandon sa ya kira wani number inda ya ce gobe da safe yana so a zo a gyara kitchen din, sannan abubuwa da suka lalace a cire a saka sababbi...


Aysha dake jin duk wayar da yake taji ya bata tausayi, domin yayi tafiya mai tsayi ya kamata ace ya huta amma gashi daga dawowarsa ba hutu zai fara kashe-kashen Kudi.



Kasa shiru tayi, tace "Am so sorry please, it was a mist...."



"Shhhh! You don't have to apologize, you did absolutely nothing, and that's how God want it, so cheers ok?"

"Ok" tace tana jinjina kan ta, Sanyi taji a ranta ganin bai yi fushi da ita ba, hakika kyawawan halayen sa na burge ta, duk da kasancewar sa ba Muslimi ba, amma yana da zuciyar musulmai kwarai masu yarda da ?addara.



Mikewa yayi daga dining table, ya dawo falo ya zauna yace

"come with me"

"Okay" tace tana nufar kitchen, domin ajiye kayayyakin daya ci abinci dasu, sakin baki tayi tana kallon barnan da wutar tayi a kitchen, a sanyayye ta dawo falon ta zauna.



Gyaran murya yayi yace "so tell me about religion, i mean Islam"







Share
Comment



Noor Eemaan
07082281566




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/13, 1:21 PM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM





*WATTPAD*
@NoorEemaan



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din




Chapter 57-58

Cikin zallan mamaki ta kafe dashi da ido, yayin da shi ma Abraham ita ya ke kallon hadi da gyada mata kai cikin tabbaci.


Zaro beautiful eyes din ta tayi cikin mamaki, domin bata taSa tunanin abinda zai ce kenan ba, "amma shi da ba Muslimi ba, meyasa yake son sanin abinda ya shafi addini Muslunci?"
ta fada a ranta, amma ko ba komai taji daWi duk da bata san dalilin sa ba, amma tana son hira ko magana kan abinda ya shafi addinin Musulunci.


"You...you... mean i should tell you about my religion?" Aysha ta tambaye shi domin ta kara tabbatar wa.




"Exactly that's what I want, tell me come on" ya fada cikin k'aguwa da son ta fara gaya masa.


"Okay" Aysha tace tana dan murmushi.

Gyara zama tayi, ta saki, jikin ta tama manta cewa gaban yallabai Abraham take zaune, nan ta shiga gaya masa Meye Muslunci, abubuwa da Muslunci ya koyar, da yanda Muslimi zai tafiyar da rayuwar sa, da yanda annabawa suka bauta wa Allah, sannan da yanda Mala'iku suka bauta wa Allah, da kuma yanda yan zamanin da suka shude suka yi rayuwar su, sannan ta bashi labarin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.

Sannan ta Wora da bashi labarai kan rayuwar iyalan gidan sa, kissoshi dai kala-kala ta dinga bashi, a takaice komai dai wanda ya shafi addini da ta sani ta fada masa, tsikar jikin Abraham sai tashi take saboda abubuwan da take fada duk suna shiga kwakwalwar sa, suna ratsa jijiya da tsokar jikin sa, sannan sun samu muhallin zama a zuciyar sa.




Aysha kuwa sosai tayi kokarin wurin hada turancin ta domin yi masa bayanin yadda zai fahimta, domin wasu manyan kalmomi dake cikin abinda take fada masa, fassara su da turanci wuya zai yi mata, amma tayi ?o?arin fassara masa da sauk'ak'ak'iyyar turanci, kuma Thank God ya fahimta.



Shiru falon ya dauka, babu mai magana, domin ita Aysha har bakin ta ciwo yake mata saboda dadewar da ta yi tana Magana, idan bata yi karya ba, zata iya cewa tun da aka haife ta bata taSa magana mai tsayi irin wannan ba, kallon agogo Abraham yayi ya ga karfe biyu saura Mintuna biyar, kenan haka suka jima suna magana bai sani ba ya fada a ransa.



Duk da yasan dare yayi, amma bazai iya yin shiru bai yi mata tambayar da ta fi makalewa a ransa ba, dan gyara murya yayi wanda hakan ya zame masa dabi'a, hakan yasa Aysha dago kanta, domin ta fahimci matu?ar yayi hakan toh akwai magana a bakin sa.



" Am.....You said every child was born as a Muslim, expect lf his parents changes his religion, how sure are you. (Kin ce ko wani d'a ko y'a a Muslim ake haifan sa sai dai iyayen sa su sanja masa addini, taya kika tabbatar da hakan)".


Murmushi mai sauti Aysha tayi tace
"Am not the one who say it, Allah subhana wata'ala said so in the Qur'an(bani na fada ba, Allah subhanahu wata'ala ne ya fada acikin kur'ani)"



Jinjina kai Abraham yayi cikin gamsuwa da amsar ta, sannan yace "one more question, you said earlier that i

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login