Showing 66001 words to 69000 words out of 84387 words

Chapter 23 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28157

zata fara kwana dashi.

Cikin tsoro da fushi ta bar fadar a kokarin ta na barin dajin, wanna karon kuwa zuciyarta ta k'ek'ashe ta Kuma gaji da aikin bokayen nan, sam basu da gaskiya, gwara ta nemi tantirai ta biya su, a kashe mata Abraham ta huta kawai.



Amma abin mamaki ta kasa gane hanyar barin dajin, da ta dau hanya sai taga babu hanya, sai munanan halitta da take ta gani suna bata tsoro, abin dai ba sauki domin har duhun dare ya gabato tana neman hanyar barin dajin... da ta ga ba wata mafita, haka ta dawo guiwa a sanyayye wajen bokan domin bata da wani waje daya fi nan din a yanzu.


Dariya boka Nandera ya shiga k'yak'yatawa cikin Muryar sa mara dadin amo a lokacin da ta dawo, dama yana kallonta ta cikin allon tsafin sa.



A takaice dai a wannan daren ya danne ta ta ?arfi ya kusanci ta, kusan kwana yayi yana abu Waya, wuya iya wuya Madam Gloria ta sha shi.



Washegari again ta sake gwada barin dajin, amma ta kasa, saboda da ta fito sai komai ya Sanja ta rasa hanya, haka boka Nandera ya mayar da Madam Gloria kamar matar sa, kullum babu fashi, duniyar tayi wa Madam Gloria zafi, gashi irin warin da boka Nandera ke yi ya kama jikin ta tun daga lokacin da ya fara kusantar ta, haka ta cigaba da fama cikin mayuwancin hali.



*Bayan wasu kwanaki*

Da misalin ?arfe takwas na safe madam Gloria ta tashi, kasancewar boka bai bari ta huta cikin dare ba sai kusan shida saura Bacci ya dauke ta...
Da fari wani mugun wari ta ji ya fara ziyartan hancin ta, ta kai kallonta ga inda ta ji warin...

Gabanta ne ya yi wata bugawa, Domin boka Nandera ta gani kwance flat a kasa babu numfashi a tare da shi, majizan nan sun kanannad'e jikin sa, da kyar ma ake iya ganin fuskar sa saboda Yawan macizan nashi, gashi ko wannen su na kai mai cizo ta ko ina a jikin sa, abin babu kyawun gani...



Ihu Madam Gloria ta shiga yi, yayin da tsigar jikin ta har tashi ya dinga yi, sai take jin kamar majizan nan na ya dawo a jikin ta itama, haka ta dawo zautaciyya, sai faman soshe-soshe take, duk wanda zai ganta a halin yanzu zai dauka mai tabin hankali ce da ta shafe shekaru talatin a cikin hauka.

Banda kananun surutai babu abinda take da alama ?wa?walwar ta ya fara tabuwa...

A takaice dai madam Gloria ta ga tashin hankali, wanda tsaya fayyace wa makaranta bata lokaci ne, da kyar ta iya jan kafafunta ta bar cikin fadar da gudun ta...

Kuma abin mamaki hanyar lafiya lou take yau, kamar ranar data fara zuwa dajin.



Gudu sosai ta shiga yi, domin har gizo macizan nan ke mata, saboda gani tayi suna bin ta a baya.



Tafiya mai nisan gaske tayi, amma kamar bata yi, saboda ko alamar titi da gidajen mutane bata fara gani ba, da haka ta dauki kwanaki uku cur sannan ta fara ganin titi daga nesa sosai, shi ma sai da ta kara wasu awanni kafin ta fito aihinin babban titi.




Duk abin hawan da ta tsayar tsoron daukar ta ma suke, da kyar da sidin goshi ta samu wani taxi, dama akwai kudi a aljihun wandon dake jikin ta, nan ya chaje ta sosai, a hakan ma wai bazata zauna a sit ba, sai dai booth saboda wari take, sam Madam GLORIA bata damu ba.
Booth din ta hau, ita yanzu Burinta ta isa Kaduna, domin ganin bayan Abraham, saboda wata muguwar tsanar sa ne ya sake kamata, saboda a ganin ta duk wahalar nan da take sha saboda taurin ran sa ne.




**********************


*ABRAHAM*

A hankali ya d'ago kansa daga cinyar Aysha, ya dafe kansa dake sara masa, ya cije labban'sa da suka tashi daga pink izuwa red, komai da anty Sarah ta fada na yawo a brain dinsa one after another.


Sai da ciwon kan ya lafa masa sannan ya kalli Aysha cikin turanci hadi da raunin murya yace "dama ina da yara? Ina yara a doran duniyar nan ban sani ba, yaya suke Please, i want to see my kids, Ina yarana suke, please tell me"

Ya karasa yana rike hannun Aysha ga wani hawaye mai zafi daya biyo kuncin sa daya.

Komai gani yake kamar al'mara, cikin kankanin lokaci ya ji abinda ya kusan tarwatsa zuciyar sa, da ba dan yayi namijin kokari wurin danne zuciyar sa ba, da yanzu baya a zaune haka, da yana gadon asibiti a kwance.
Tabbas irin wannan abun yafi komai ciwo domin wanda baka taSa expecting ba, kana ka bashi yarda da matsayin uwa ya ci amanar ka, ya fi ciwo sosai.




Aysha zata tambayi Inna ina su Ammar suka je kenan taji sallamar su cikin Muryar su ta yara, sun shigo gidan...

Gidan iyayen anty Bintu suka je wasa da yaran anty Bintu.
Dama wani zubin har sai Inna taje ta kanta ta dauko su, saboda sun saba da gidan sosai.




Cikin muryar kuka da Aysha ta sha ta kalli Abraham tace

"Oh! they are here already"


Cikin sauri Abraham ya mike ya leko su, sosai ya kura wa gudan jinin sa eyes dinsa da suka yi matukar yin ja, tun kafin su karaso...



duk takun dayan da su Ammar zasu yi, gaban Abraham ke cigaba da faduwa saboda tsantsar kamanin su, shi da Nonye da yaran suka dauko, ya kasa yarda cewa wadannan k'yawawan yaran na sa ne, amma bai san da su ba, babu zato ya ga hawaye na zubo masa, cikin sauri yasa hannu ya share, wani mugun soyayya irin ta Wa da uba ta caki zuciyar sa, fiye da zaton mai karatu.

Hannayen sa ya ware musu, ya dire guiwowin sa a kasa... muradi, fata, hadi da burin sa yanzu yaran su zo gareshi domin yaji dumin su....










Share
Share
Share fisabilillah &?=?O?



Comment for more typing.




('NoorEemaan('
07082281566




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/13, 2:07 PM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM

*First edition*



*WATTPAD*
@NoorEemaan



https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



Chapter 67-68

Maimakon su je wajen Abraham Wa ya ware musu hannu, sai suka fada jikin Aysha bayan su karaso saboda basa san shi ba...



Cikin Muryar su ta yara suka shiga kiran "Ammuh Oyoyo" rungumesu sosai Aysha tayi a jikin ta, wani mugun son su da kaunar su fiye dana baya na sake ratsa zuciyar ta.


Abraham kuwa sauke hannun sa cikin rashin jin dadi da basu Wajen shi ba, ya kuma san rashin sabo ne yasa su hakan.

Sai ya kafe su Aysha da ido cikin burgewa ganin yadda yaran suka saba da ita, sai faman murmushi.


Aysha ta shafa kansu tace "na yi kewar ku sosai my twin" hakoran su suka washe mata suna dariya, juyo da su tayi ya zamana suna fuskantar Abraham sannan tayi musu nuni da shi tace "ga Daddyn ku, ku je ku gaishe shi"


Tsaye yaran suka yi suna kallon mahaifin su Abubakar Assadik cikin rashin sabo, sai da Aysha ta sake magana sannan suka tafi wajen shi a hankali, kana a tare suka shige jikin sa.


Wasu hawaye masu sanyi ne suka zubo kuncin sa, hakika yau ya dawo mai rauni, saboda abubuwa mabambamta masu cike da al'ajabi da ya ji cikin rayuwar sa a yau, ashe all this year's cikin duhu yake, sai yanzu haske ya bayyana, duhun ya yaye...

Kara rungume ya'yan sa yana basu sumbatar ta ko ina, abin so heart touching and lovely. Aysha ma sai ta data share hawayen tausayin su.


Muryar Anty Sarah ya ji tana sake bashi hakuri da neman yafe, su Ammar da suka lafe a jikinsa ya sake ri?e su da kyau sannan yace " bani da abinda zan ce miki, wadanda kuka zalunta basa duniyar, dan haka ki koma ga Allah kawai" yana gama fadin haka ya mike, sannan ya riko hannun yaran sa suka bar gidan izuwa masallaci domin ya ji kiran sallah.



Kuka mai suna kuka Anty Sarah ta fashe dashi, ina ma ina ma hannun agogo zai dawo baya da ta gyara kuskuren ta.

sai ta dawo bawa su Inna tausayi, domin duk da tarin laifukan ta, amma duk wanda ya ganta a halin yanzu zai matukar tausaya mata.

Baki suka shiga bata kan ta daina kuka, ta cigaba da neman yafiyar Allah, domin Ubangijin talikai gaffurul Raheem ne.



Nan Inna tace mata ta je tayi wanka, saboda maganar gaskiya wari take, bata Musa ba, saboda ita ma ba jin dadin jikin ta take ba, bayan ta yi wanka Inna ta bata wata doguwar rigarta ta atamfa ta saka, sannan aka zubar dana jikin ta a shara.



Abraham kuwa suna fita ya hango masallaci, nan suka karasa suka yi alwala a bakin masallacin domin akwai ruwa da butoci, a gurguje ya karasa alwalar domin har liman ya tayar, su Ammar ma suka yi alwalar su yanda yara suka yi ya rike hannun su suka shige masallacin.


Bayan sun iddar sun fito, yara da manya sai kiran Ammar da Anwar suke, yaran kuwa su dinga amsawa da na'am, yayin da wasu kuma mamakin kamanin yaran da Abraham suke.


Abraham kuwa abin yayi matu?ar kayatar da shi, ya kuma ji dad'i saboda yanda jama'a ke son yaran sa.

Yana so suyi hira amma basa jin wani turanci, shi kuma baya jin Hausa, sai yanzu rashin iya Hausar sa ke damun sa.

Amma yasa a ransa cewa yaran su iya turanci hadi da Yaren sa na Igbo, numfashi ya sauke, duk da bai san akwai su a doran duniyar nan ba, amma yaji dadi ganin su cikin koshin lafiya da kulawa.




Bayan sun iso kofar gidan, ya buWe musu mota suka shige hadi da kunna musu Ac yaran suka hau murna, suka kalle shi suka ce "wannan motar ka ce?" Be ji abinda suka ce ba, amma haka ya daga musu kai alamun eh yana murmushi.


Su Twins suka hau murna wanda hakan ya sa zuciyar Abraham yin sanyi.
Kurawa Ammar ido yayi yana tuno ranar farkon da Aysha ta fara shiga dakin sa, tabbas wannan sunan ta faWa, kenan ta ga kamanin su shi yasa cikin rashin sani ta kira shi da sunan Ammar....

Ya sake mai da duban sa ga Anwar, sak Nonye kamar an tsaga kara, nan fa Abraham ya maida su tv ya dinga kallon su, labarin komai da Anty Sarah ta bashi na dawo masa daki-daki.



Inna data ji shiru bai dawo ba, sai tace Aysha ta leka waje ko yana nan, su zo su ci abinci, ba musu Aysha ta mike, domin ita ma ta damu da rashin shigowar su, kawai ta maze ne kar Inna ta ga rashin kunyar ta.

Tana fitowa ta hango shi zaune ya kurawa yaran sa ido a mota, hannu ta Wora a kugu tana kallon su murmushi dauke a fuskar ta, domin su burge ta, kai kace sun dade da sanin juna.



Jikin Abraham ne ya bashi ana kallon shi hakan yasa shi dago kan sa ya kalli direction din da take, murmushi yayi kana ya kira ta da hannu.

A nutse ta shiga takawa har tazo bakin motar, su Ammar na ganin ta suka shiga kiran "Ammuh!" Sannan suka fito daga motar suka rungume ta.

So take ya saki ransa, hakan yasa cikin tsokana tace "kazo kaci abinci inji Inna"


"What!" Yace yana kafe ta da ido.
Dariya ta sa, dama so take ta tsokane shi, kasancewar ba Hausa yake ji ba.




Ya fahimci tsokanar sa take, sai ya girgiza kansa yana murmushi.

Sai ta dawo serious ta fada masa abinda Inna tace da turanci, baya jin zai iya yin musu ga surukar tasa, saboda girman da take da shi a idanun sa, amma maganar gaskiya sam baya jin yunwa, amma bazai iya cewa a'a ba, fitowa yayi daga cikin motar ya sa key sannan suka jera zuwa cikin gidan.



Dakin ta dake a gyara suka shiga, domin duk da bata nan Inna na gyara mata.
suna shiga kuwa suka tarar Inna ta jere musu wainar shinkafa da miyar taushe da ya sha tantakwashi da nama, sai had'add'en fura da nonon kindirmo zallan sai ruwan randa mai sanyi.


Aysha ta zuba musu komai, tayi wa Abraham Bismillah, Dan yamutsa fuska yayi alamun baya ci, domin duka cimmar bai taba gani ba bare ya ci, nan Aysha ta shiga mai daWin baki kan ya dandana akwai dad'i Sosai.

Domin ya faranta mata yanka daya ya ci na wainar bai kara ba, domin bai yi masa ba, ko dan bai taba ci bane.

ya sha fura ludayi biyu, sannan ya sha ruwan randa mai yawa bai yi k'yamk'yami ba.



Aysha dasu Ammar kuwa suka ci, duk da ita Aysha Bata wani ci da yawa ba, saboda ganin har yanzu da damuwa a tare da Abraham, wanda hakan kuma dole ne domin rasa uwa, da mata sannan kashe su akayi ba abu bane mai sauki da kuma saukin mantawa a gare shi bane.

Haka dai suka kasance har dare.
Bayan sun yi sallar isha Abraham yace Aysha da su twins su raka shi ya ga gari, ya kuma yi hakan ne domin ya rage damuwa dake damun sa.



Aysha ta sanar da Inna, sannan ta rike hannun Ammar, Abraham kuwa ya rike hannun Anwar suka fice...

Sunyi yawo ba laifi, sun je dandali sunyi kallo, Daga nan suka dan zaga gari Aysha na masa bayanin duk inda suka wuce, daga nan suka je kasuwar dare, Abraham ya siya musu tsire da doya da kwai, da haka suka dago gida gwanin sha'awa, su twins sai surutu suke musu a hanya, Aysha na biye musu, Abraham kuwa sai dai yayi murmushi, domin zuciyar sa cike da farin ciki, ya kuma godewa Allah da ?a?an sa suka fada hannun na gari.



Bayan sun iso, Abraham yace zai kwanta a mota, su Aysha su shiga ciki...ya sumbace yaran sa, ya shige motar.


Bayan sun shiga ciki Inna tace "ina mijin ki yake?"

Cikin kunya tace "Inna wai a mota zai kwana"


"A'a A'a ba za a yi haka dani ba, Meye amfanin dakunan nan? Maza ce masa ya shigo dakin ki ya kwana, sai mu kuma mu kwana a daki na"



"Toh Inna"
ta ce tana fita, Abraham da har yayi nisa a tunani ya ji ana k'wank'wansa kofa, glass din motar ya zuge ?asa, ya ga Aysha tsaye hannun ta rungume a kirjin ta "?mammm! Hope all this well?"

"Nothing much, Inna said you should come inside"

Dan shiru yayi sai kuma ya bude kofar motar ya fito, ya saka lock sannan ya mara mata baya zuwa cikin gida.

Har ba?in kofar dakin ta Aysha ta kara shi, sannan yta juya zuwa dakin Inna, ba tare da tace komai ba, ta lura har yanzu bai gama sake wa ba, ba kuma ta so ta takura masa.


Da kallo ya bi bayan ta, tana dab da shige dakin Inna taji Muryar sa yace ta kawo masa su Ammar su kwana tare, ba musu ta ce masa toh.

iska ya furzar daga bakin sa, sannan ya shige dakin ya fada kan gadon yana rub da ciki...

Bayan ta kawo su Ammar ta sake fita tana mai sai da safe ya amsa...
haka yasa yaran a gaba yana kallon su cikin kauna har suka yi bacci.

Shi kam babu alamun bacci a idanun sa, haka dai ya dinga juye-juye baccin yaki zuwa har aka kira sallar asuba.




*WASHEGARI*

Bayan duk sunyi sallah, Abraham da ya je masallacin tun asuba bai dawo ba, Aysha kuwa ta fara Wora musu abincin karin kumallo, bayan ta gama ta share tsakar gida ta gyara sannan tayi wanka hadi da brush.
kayan jikin ta na jiye ta mayar, domin bata dauko kaya ba, sam basu zo da niyyar kwana ba.

Su Ammar ta taso tayi musu wanka da brush, kana ta shimfida tabarma babba a waje, tace su zauna bari ta dauka kayansu da man shafawa...

Anwar ta fara shafawa mai, sannan ta saka masa kananan kaya riga da wando, ta taje masa gashi, ya koma ya zauna, kana ta fara shirya Ammar kenan taji sallamar Abraham.

Amsawa tayi tana satar kallon sa, gefen su yazo ya zauna Aysha ta gaishe shi ya amsa cikin kulawa, su Yan biyu ma suke ce Ina kwana ya shafa kan su yana murmushi.


Inna ta fito duk suka gaishe ta cikin girmamawa ta amsa, Anty Sarah da tun jiya bata bari sun sake haduwa da Abraham ba saboda kunya ta fito yanzu a sanyayye...

gaishe su tayi, duk suka amsa, amma Banda Abraham, dake wasa da yaran sa kamar bai ji ta ba.

Ko da yaji bai ma san mezai ce ba, baya so ya dinga ganin ta, saboda yana tuno masa da abubuwan da suka aikata a gareshi, ana haka wayar Abraham yayi ringing ya duba ya ga mai gadi ne, ya picking call din inda mai gadi ke sanar masa cewa ga fa Madam Gloria ta zo, amma yaki barin ta ta shiga domin yaga kamar ta haukace, zuciyar Abraham na suyo, ransa ya Saci amma ya danne yace a barta ta shiga amma Kada su bari ta wuce farfajiyar gidan
gasu nan zuwa yana fadin haka ya kashe wayar sa.


Ya kalli Aysha da jajayen idanun sa yace ta shirya su wuce, Inna ta ce ya bari suyi karin kumallo, bai musu ba, duk bai iya cin komai ba, sai ruwa kadan daya sha, wanda ma ya kara kulle masa ciki amma bai damu ba, saboda halin da yake ciki.

Bayan ta shirya suka mike domin tafiya, Cikin turanci ya shiga yiwa Inna godiya sosai da yaba karamcin su, da ?o?arin su wurin kula da yaransa, ya kara da cewa bazai iya biyan su ba, Allah kadai ne zai biya su, ya kuma yi wa baffan addu'a sosai.

Inna bata ji duk abubuwan da ya ce ba, Aysha ce mai fassara mata, cikin jindadi addu'ar Inna ta shiga amsawa da Ameen.


Sai ya ajiye wa Inna bandir hudu na dubu Waya-daya, taki karba, da kyar da roko Inna ta karba daga hannun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login