Showing 18001 words to 21000 words out of 84387 words

Chapter 7 - ABRAHAM complete Hausa novel

09 Dec 2024

28134

ki, sunana lubabatu, kefa? 


 Aysha Indo" ta amsa mata a takaice.


"masha Allah suna mai dadi da daraja, toh na tafi sai anjima ko"

"toh Nagode sosai" Indon ta kara fada.


Ta dauki tsawon mintuna goma tana tunani kana ta ja ajiyar zuciya hadi da Bude kwanon abincin.

Tuwon semonvita ne hadi da miyar ganye daya ji namomi, sai lemon exotic hadi da swan water mai Sanyi.

Duk da yanda abincin ya yi dadi, loma biyar kawai tayi ta wanke hannun ta, domin tunanin su Innah ne ya cika zuciyar ta, "ko sun ci abinci?" Sanin bata da amsa ya sanya ta rufe abinci ta Mike, toilet ta shiga Inda shima ya hadu sosai bata wani tsaya kallo ba ta shiga daura alwala cikin nutsuwa....


Kallon dakin tayi taga babu alamar sallaya, can ta tuno yanayin madam gloria din babu alamar musulunci a tare da ita, gefen wajen karshen gado ta karasa, dankwallinta ta warware ta shimfud'a a kasa, in da take dogon gashin ta mai tsaho, baki, hadi da tsantsi ya bayyana, hijab dinta ta mayar kanta kana ta tada sallar azahar da la'asar da bata yi ba....

Bayan ta iddar ta zauna tayi addu'o'inta sosai, gashi bata taho da qur'anin ta ba, gashi ta saba duk bayan sallah ta kan yi tilawa, can sai ga lubabatu ta kara dawowa, abincin ta Bude ta ce

" la la la ai baki ci komai ba?"

"wallahi na koshi" Aysha
ta amsa tana murmurshi

"toh yanzu kina bukatar wani Abu ne?" lubabatu ta tambayeta.

"eh ina zan samu qur'ani in fansa Dan Allah, na manta nawa a gida"

"ai kuwa ina da guda biyu, ban ma fiye amfani dasu ba" ta fada a kunyace, domin sanin cewa hakan ba kyau, gashi kanwar bayanta ta fita himma wurin karanta littafi mai sarki, domin ita wani zubin a Wata bai fi tayi sau daya ba.

"amma kina kokarin yi kullum, ko da aya
biyar ce ko uku, lada zaki samu, sannan zai taimaka miki wurin rike haddar ki, bazai zube ba" Indo ta fada cikin cool voice.



"in sha Allah zan yi kokarin yi kullum, Nagode kinji kanwata? Bari na dauko miki"

Jinjina kai Indo tayi kawai hadi da zuba tagumi, Bayan mintuna shida sai ga lubabatu ta dawo dauke da qur'ani, amsa aysha tayi cikin farinciki da godiya.


Kwanukan Lubabatu ta kwashe tace "toh sai gobe idan mun sake haduwa, domin ba a bari mu hau saman nan any how, yau ma darajar ki na ci na hau kusan sau hudu madam bata min masifa ba"



Murmushi kawai Indo tayi, Bayan Lubabatu ta fita,Aysha ta Bude qur'anin ta cikin suratul maryam, Aya goma ta karanta kana ta Mike ta ajiye qur'anin saman dressing mirror.

D'an k'wallinta ta mayar kanta hadi da bud'e wardrobe ta shiga jera kayan ta da ba wani yawa ne da su ba, sannan basu cika sabun ta ba, Bayan ta gama jerawa idanun ta ya sauka kan jakar da ta dauko a dakin baffa, a hankali tasa hannu ta dauki jakar, ido ta zubawa jakar kana ta mayar cikin Ghana most go dinta, zuge zip din jakar tayi ta rufe, kana ta saka a kasan sif din inda babu komai a ciki, kofar sif din ta rufe kana ta dawo bakin gado ta zauna, haka ta wuni sukuku ba motsin kowa, har tunani take anya zata iya yin wannan aikin? Amma idan ta tuno innar ta da Rayuwar da suke ciki sai taji kwarin guiwar yin aikin...



*************

Haka ta dinga juyi da daddare ta kasa bacci, Kiran sallar farko a kunne ta, Mikewa tayi domin bata ga amfanin kwanciyar ba tunda ba baccin take ba, toilet ta shiga tayi alwala kana ta fito, nafilfili ta shiga jerawa har aka tada sallar asuba, Bayan ta iddar ta shiga rera karatun qur'ani cikin zazzak'ar muryar ta mai sanyin amo.



Shida saura mintuna biyar ta shiga toilet, wanka tayi, hadi da brush kana ta fito daure da zanin ta, kurawa kanta ido tayi ta cikin madubi inda direct kan sarkan nan idonta ya sauka, hannu ta kai ta shafa sarkan, kullum sarkan kara kyau da sheki yake duk da dashi take wanke kullum.



Pomade din stella (mai gurguwa) da ta taho dashi ta shafa a jikin ta, wanda Inna ce ta siya mata ana yi gobe zata taho kaduna.


Doguwar rigar atamfa roba-roba ta sanya, d'ankwallinta ta daura hadi da sanya hijab dinta, duk da babu Kwalliya ko digo a fuskar ta amma tayi kyau ba laifi, sai dai rashin tsad'add'en mai na gyaran fata da karancin wayewa ya tauye tarin baiwar kyawun da take dashi.



Dan gyaran dakin ta tayi duk da bai yi wani datti ba, zama tayi na almost 1hr kana ta sauko down stairs...


Da wasu yammata biyu ta fara cin karo inda suke gyaran yalwataccen General falo, gaishe su tayi suka amsa hadi da bin ta da kallo....

Madam Gloria ce ta fito cikin takun dai-dai, kallo daya tayi wa aysha ta dauke kai hadi da cewa "shiga ki gyara dakin, if you're done sai ki hau sama ki gyarawa son na shi, anjima chef din zata zo"


"toh!" Aysha ta amsa cikin ladabi, duk da bata fahimci kalmar "chef" ba.



Falon madam Gloria ta fara gyara mata, kana ta shiga bedrooms din daya kasance biyu ta gyara ta goge, sai toilet da ta wanke ta goge, komai dai fess sai gyalli yake kai baka ce this is her first time ba, inda aikin ya dauke ta tsahon awa biyu.



Bayan ta gama ta fito, ta tarar da madam gloria hakimce a dinning area da alama breakfast take son yi.

" idan kin hau sama ki kira min son ya zo yayi having breakfast"

madam Gloria ta fada da wani irin tune daya Dan tsorata Indo domin kamar da fada-fada tayi mata.


"toh!" ta amsa a sanyaye yayinda ta cigaba da taka step case din, duk da ba duka abinda madam gloria ta fada ta gane ba.


Sama ta hau inda ta ga wasu kofofi biyu d'aya na zallan glass ne, shi din ta nufa wanda take Kyautata zaton shine dakin sa...

Gabanta na bugawa ta shiga knocking shiru,... Jin shiru yayi yawa ba motsin kowa sai kawai ta tura kofar hadi da zura kafar ciki inda ya sauka kan lallausan door mat...





*kuyi hakuri sisters ban samu zama bane shiyasa kuka jini shiru, kuyi manage da wannan, sai mun hadu a next page*




Share fisabillahi

Comment for more typing



NoorEemaan
07082281566



Thank you for reading my novel



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851




https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din


https://chat.whatsapp.com/JwYkGXFKcLH95WSHP9QoUg
[10/8, 8:42 AM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM


*first edition*



*WATTPAD*
@NoorEemaan



*please Don't forget to vote my story and also follow me on WATTPAD @NoorEemaan*
love you all guys.




https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din





Chapter 21-22

(Not edited)



Lumshe sexy lulu eyes dinta tayi sak'amak'on sanyayyar kamashin room freshener daya daki hancinta, kana a hankali ta ware idanunta ta sauke su kan kayataccen falon daya gaji da haduwa, sai dai shiru ba motsin kowa sai k'aran Ac.




Wata kofa dake kallon gabas ta sauke idanunta a kai, a hankali ta fara takawa domin isa ga kofar, a gefe daya kuwa gabanta na tsananta fad'uwa...
Hannu ta dora kan handle din kofar da niyyar bud'ewa, sai kuma tayi saurin dauke hannun ta, a hankali ta fara knocking... Shiru ba amsa, sannan ba motsin kowa har na tsawon mintuna biyar, gajiya ta fara yi da tsayuwa kasancewar ta mutum mara jurar tsayawa, shahada tayi ta bud'e kofar a hankali, kana ta shiga....




Ya subhanallah! Ta fada tana runtse idanunta da karfi sakamakon hangoshi da ta yi kwance kasan tiles babu riga a jikin sa sai dogon wandon jeans kirar company'n gucci, wanda hakan ya bawa manyan six packs din sa bayyana hadi da karfaffan hayyensa daya yi mata shi dasu.




A kafatanin rayuwar ta bata taba ganin da namiji haka ba, duba da irin gidan da ta fito, ta dauki tsawon mintuna bakwai a haka, kana kamar mai tsoron ganin wani mugun abu ta shiga Bude idanunta a hankali ta sauke kan k'yak'yawar fuskar sa dake bacci a tunanin ta, wanna karon gabanta ya fi d'azu fad'uwa saboda ganin kamanin Ammar dinta da Abraham, ba tare da kuma ta san maganar ta ta fito fili ba tace "Ammarrr" cikin sautin amo dake bayyana zallan mamaki,
Ji tayi idan ta cigaba da tsayuwa a dakin komai zai faru, domin k'wak'walwarta ya gaza dauk'an abinda take gani, musamman kamanin su daya firgita ta, dan dai shi babba ne da ta ce tabbas Ammar din ta ne, cikin sassarfa ta juya domin barin dakin kamar a sama taji husky voice dinsa yace "hey! what did you want?" tilas ta tsaya cak! Gashi ya sake rudata da turanci sa da bata fahimci koda kalma daya ba... Abraham kuwa duk da yana cikin bacci, amma shigowar ta dakin ya sauya bugun zuciyar sa, wanda ya tilas ta masa farkawa daga dan baccin daya dauke sa, tabbas murya yarinyar daya ji a cikin adaidaita sahu ce, ya kuma sake tabbatar da hakan ta dalilin bugun zuciyar sa da ta sauya, wanda akan ta ne ya fara Jin hakan, mamaki yake kan meya kawo yarinyar cikin gidan su har dakinsa.




Jikin ta na bari, cikin rawar murya tace "ehm... Is your,? is na mahaifiyar ka ta ce kazo kasan bene" ta fada cikin duburbucewa idanunta taf da k'walla...



Yamutsa fuska yayi domin ko kalma daya bai fahimta daga abinda tace ba,? a hankali ya bud'e idanunsa da suka dan rine saboda jimawa da suka yi a rufe ya sauke su a kwanta, sai dai bayan ta kadai yake hangowa, ita kuwa jin bai sake magana ba yasa ta fita da gudu, ta nufi dakinta dake da dan nisa da nashi duk da saman bene ne.




ABRAHAM kuwa da kallo yabi bayanta, kana ya tabe bakin sa hadi da mikewa tsaye, toilet ya nufa domin yin wanka, shower ya kunna inda ruwan ya shiga dukan kansa zuwa jikinsa, a hankali muryata ya amsa kuwa a kunne sa "Ammarrr" ya maimaita kalmar can kasan makoshi, duk da bai san ma'anar sa ba, kawar da tunanin yayi ya cigaba da wankan sa inda mintuna ashirin ya dauka kana ya fito daure da farin towel.




Tsad'add'en lotion din sa ya shafa, kana yayi oiling kansa hadi da tajewa, gaban wardrobe din sa ya nufa, inda wayar sa ta fara ringing... Dubawa yayi ya ga MUM ce.

Amsawa yayi hadi da karawa a kunne sa,,
"Good morning Mummy"

"morning my son, I sent the house-maid to tell you breakfast is ready and.........."

"am coming mum" ya fada yana katse Kiran ba tare da ya bari?ta karasa maganar ta ba, sai yanzu da mummy ta fada ya san dalilin shigowar Yarinyar nan dakin shi, wardrobe din ya bude ya fito da wani crazy Jean trouser white, sai bakin riga mai botira hadi da dogon hannu, cikin mintuna biyar ya shirya cikin su, gaban inda tarin takalman sa suke ya nufa ya dauki wani black palm sandals na company dolce and gabbana ya sanya, agogon zallan sliver ya manna a hannun sa, ba karamin kyau mai tsayawa a rai yayi ba , Bud'e kofar yayi ya sauko kasa...




Aysha da ta kasa kunne, jin motsin ya fito ya sanya ta fitowa da sauri, duk da faduwar gaba da Tsoron da take ji amma dole ta gyara masa dakin tunda aikin ta ne, baya ga haka bata ma so abinda zai hada ta da madam Gloria, dakin sa ta koma ta fara gyara falon da sauri? inda ba wani datti yayi sosai ba, bedroom dinshi ta nufa shima ta gyara kana ta yi mopping a ranta tana mamakin yanda ya iya kwanciya kan uban sanyin da tiles din ke da shi, domin ita kafar ta kadai dake taka shi yanzu ya sa ta jin Sanyi.



Bayan ta gama, ta wanke toilet ta fito, wani kofa ta gani by the left, Bude kofar tayi ta ga kitchen ne, a gyare yake babu wani datti, wani kofa ta sake gani ta cikin kitchen din ta bi, take ta bayyana a gyming room dinshi wanda ke gyare tsaf, "Dama makeri ne shi" ta fada tana kallon karafunan da? abubuwan motsa jikinsa, wanda ita bata San amfanin su ba.





Sosai ta shagala ta kallon dakin motsa jikin, can ta tuno cewa zai iya shigowa yasa ta fita cikin sauri, dakinta ta koma tana sauke ajiyar zuciya, yayin da har yanzu tana mamakin wannan kammanin, daga kashe dai ta basar, tasa a ranta cewa kawai kama ce....




ABRAHAM kuwa tea kawai ya sha, dama shi ba ma'abocin cin abinci bane sosai, madam Gloria tayi-tayi yaki ci, dole ta hakura, fita yayi zuwa unguwar rimi, domin so yake ya je su yi magana da wani attajiri mai harkan filaye wanda ya ga ya dora wani fili mai girman gaske a Instagram din shi wanda na siyarwa ne, wanda tun yana dubai yaga tallan, luckily kuma yaga kaduna state ne , so yake ya siya domin ya gina company a nan kaduna, wanda hakan zai yi keeping dinsa busy...





Babu jimawa da fitarsa professional chef din? da zata fara koyawa indo girki-girki tazo mai suna miss Zaynab Akindele yar jahar ogun ce, ba bata lokaci madam Gloria tayi Kiran Indo ta sauko suka shiga kitchen....



____________________




*Gombe State*

Bangaren su innah kuwa sosai suke fama da tsananin kewar Aysha indo, bare ma su Anwar, ranar farkon da basu kwana da Ammuh din su ba, cikin dare Inna ta ga ta kanta, domin zazzabi ne ya rufe su, babu abinda suke kira sai Ammuh! Ammuh! Suna kuka, innah bata taba sanin cewa haka suke da Wayo ba, domin ta yi iya yinta sun ki hakura...




Washegari da asuba zazzabin ya sauka, suka fara dan wasan su, amma abu kadan sun kira sunan Indo ko su je dakinta, lallaba su innah ta dinga yi tana musu Wayo da haka ta samu dan sauki.




&&&







*KADUNA STATE*

Kiamanin sati daya Kenan da miss Zaynab Akindele ta fara koyawa Indo girki, kuma ba laifi tana fahimta sosai wanda hakan ke sa miss zaynab kara himma wurin koya mata, domin ita macece mai son ta koyawa mutum abu ya dauka da wuri, ta bangaren Aysha kuwa tana jin nishadi a duk lokacin da ake koya mata girkin, karin dadi kuma miss Zaynab na jin hausa sosai duk da kasancewar ta yare, wanda hakan ke sa Indo saurin fahimta.




Ta bangaren Abraham kuwa yayi nasaran siyan filin nan, inda babu bata lokaci aka fara gini, abinka da kudi, sosai ya zama busy baya samun zama...




Ta bangaren madam Gloria kuwa tana nan tana shirya yanda zata kashe Abraham, sai dai kwatsam wani tunani ya zo ranta yasa ta dan dakata, domin tabbas Abraham ya wuce duk tunanin ta, shi din ta kasa kashewa har yanzu saboda taurin ransa, da asirin ta ya tono a idon duniya bata more dukiyar da ta dade da burin mallaka ba gwara ta sanja salo, sai kawai ta yanke shawarar amfani da? AYSHA Wacce tasan yar gidan talakawa ce, domin kashe shi, ko da bincike yayi bincike aysha za a kama...





KO TA YAYA MADAM GLORIA ZA TA YI AMFANI DA AYSHA WURIN KASHE ABRAHAM??? KU BIYO ALKALAMIN NOOR...
'?=?
?




Share'
Comment '
Vote '




Editing is not allowedN'





NoorEemaan>؋?
07082281566



Thanks for reading my novel >??




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851
[10/8, 8:28 PM] =ؖ?NoorEemaan=ؖ?: ABRAHAM

*First edition*


https://facebook.com/groups/943534712916776/
Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din


*WATTPAD*
@NoorEemaan


*NOTE*
*_dan Allah masu tura Abraham Daga page 30 zuwa gaba ku daina, kuna rudar min da reader's, ina ta samun tsakonnin a yau saboda kun fitar fiye da page din dana tsaya, Ni a page 23-24 na tsaya, baku fini son Ganin na kamalla posting din ba, mun sani cewa Abraham ba sabon typing bane, idan kin san kin karanta complete Fyn, ba sai kun turawa mutane ba, alhalin Ni ban zo wajen ba, saboda irin wanna issues din yasa ban mayar da complete ba tun da Yawan mutanen da suka bukaci hakan, saboda Wani dole Sai ya fitar, ina da both pages da document complete Amma ban mayar ba Saboda kada a rude, Ina bada pages biyu kullum still hakan bai isa ba har sai an tura daga Page 30 zuwa karshe, wasu ma pages din a hargitse, Dan Allah ku bari nayi reposting din yadda na tsara abu na, da sannu zamu gama Kamar yau, na san kauna ce tasa kuka yi haka, amma wasu na shiga rudani, Wan Allah in dai ba daga farko zuwa inda Ni na tsaya aka nema ba, karku fitar, duk wanda baxai Iya jira ba, ya je Wattpad akwai complete a can, ngd habibte's_*>???=ؖ?



Chapter 23-24

(Not edited)



Kimanin wata daya da kwana biyu Kenan da zuwan Aysha gidan su Abraham, inda yanzu ta iya kalolin girki? da Dama, domin miss Zaynab akindele na matukar Kokarin wurin koya mata musamman da ta ga Aysha na da interest akai.




Da safe ita ke preparing musu breakfast, haka zalika dinner, inda na rana ne kawai suke yi tare da miss zaynab, domin madam gloria ta kara cika miss zaynab da kudi kan ta kara koyawa Aysha har na tsawon wata uku gabadaya Kenan domin ta kara zama expact.





Ta bangaren Abraham kuwa ginin company'sa yayi nisa sosai saura kadan, kasancewar k'wararrun ma'aikata ya dauka masu sanin
makamin aiki...




____________________




Misalin karfe biyar na yamma Aysha na zaune saman bed dinta, ta kara kyau kana jikinta ya murje, duk da cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login