Showing 1 words to 3000 words out of 63435 words

Chapter 1 - Amanata HAUSA NOVE

ASMAU   

11 Nov 2024

19011

[9/4, 12:57 PM] Asmau: AMANATA 1

SHIMFIDA
"A bamu na Allah......
A bamu na Annabi........"

'Yar yarinyar ke fada cikin zazzakar muryarta kamar gyare, tana rike da jagorar mahaifiyarta, a kofar wani shagon dinki dake cikin Tashar Dukku a cikin garin Gombe.
Ta kara da cewa ".....Gafaranku dai bayin Allah, na Annabi muke nema........" Ta fada, tana mika dan kwanon bararsu.
Wani bawan Allah ya zaro naira hamsin daga aljihunsa ya saka mata cikin kwanon, na kusa da shi ma ya jefa musu ashirin cike da tausayi, ganin yadda idanun 'yar yarinyar ya yi jajawur jikinta sai rawa yake yi sabida yunwa da wahala.
"Allah Ya karba........."
Ta fada, harshenta na sassarkewa. Ta ja gorar mahaifiyarta suka bar shagon suka yi gaba.

Mutumin da ya basu naira ashirin ya dubi mai shagon ya ce, "Almajirar nan da 'yarta suna bani tausayi wallahi, kullum na shigo tashar nan sai na gansu. Duk sammako na da asubancina sai sun riga ni. Watakila cikin tashar nan suke kwana".
Mai shagon ya ce, "Karkashin gadar can nan ne makwancin su, ko tsoro basa ji. Ko abin rufa basu da shi, komai sanyi ko zafi, haka za ka ga sun kankame juna suna barci idan dare ya yi.
Kai Allah mun gode maka, talaka yana cikin gararin rayuwa a wannan zamanin. Su shuwagabannin babu ruwansu tunda su dai da iyalansu sun gama tsallake 'Siradin Rayuwa".
Wani mai amsa sunan Haruna ya ce,
"Ni yarinyar ma na fi tausayawa, kada yaran banzan cikin tashar nan su lalata ta, don ba kowa ke da imani ba".
Mai shagon, wanda sunansa Abdu, ya ce, "Allah Shi ke kare bayinSa cikin kudura da iradarsa. Ban da haka ko ita kanta makauniyar uwar tata ai za su iya far mata tunda ba wani tsufa ta yi ba.
Sannan gasu kyawawa dasu, ban da dauda da rashin gyara da ya boye kyawun halittar su. Ko ina uban? Oho!".
Dayan ya ce, "Yanzu haka ya mutu". Haka suka yi ta tattaunawa akan su.

"Kinga Umma mun samu naira dari kenan, muje in mai dake karkashin gada sai in je in sayo mana dan wake".
"A'a 'Muhaseen', muje tare mu sayo, sai mu koma tare, bana son ki dinga yin nisa dani ko yaya ne".
Ta kara damke hannun diyar tata.
"Wuce muje".
Suka ci gaba da tafiya.

Muhasin ta mikawa Iya Ladi mai dan wake naira hamsin tare da mika mata kwanon su. Ta kirga dan wake ta zuba musu daidai kudinsu.
Ta ce, "Manja ko man kuli?"
Muhasin ta ce, "Man kuli".
Ta gama zubawa ta mika musu, suka nufi karkashin gadar su.
Suka zauna suka ci dan waken suka koshi, Muhasin ta dauki robar ta je tuka-tuka da ke nan kusa dasu ta daurayeta. Ta tara ta sha ta koshi, ba tareda ta damu da maikon robar ba, sannan ta tarowa Umman ta.
Umma ta sha ruwa ta koshi ta yi gyatsa, ta yi hamdala ga Allah. 'Yar ta zuba mata ido tana kallon ta. Kafin ta amayo mata tambayar da ke zuciyarta.
"Wai ni Umma ina Babana ne? Umma ko ni bani da Baba ne?'
Ummar ta yi murmushi idanunta a bude tas, farare kal da su, amma ba ta ganin komai sai inuwar diyar tata.
"Kin taba jin wanda ba shi da Baba Muhaseen? In ba wanda ya fado daga sama ba?"
"To in haka ne Umma ina ya ke? Umma ina so in ga Babana, Umma ko ni daga saman na fado?"
Yarinyar 'yar shekara goma, ta fadi, idanunta narai-narai da hawaye. Kana iya karantar damuwar ta karara, cikin sautin muryarta.
Ummanta ta mika hannuwa ta jawota jikinta.
"Kada ki yi kuka Muhasin, kina da ubanki kamar kowa. Wata rana ko bayan raina Allah zai hada ku. Nice dai baya so saboda ni 'yar kauye ce ban yi karatun zamani ba, makantar ma ta dalilinsa ne na same ta".
Ta yi shiru.
"Ta dalilinsa Umma?" Muhaseen ta tambaya a kidime.
Ta yi murmushi ta ce,
"Kwarai, Babanki shi ya mai dani makauniya, sannan ya sake ni sakin wulakanci har ukku, saboda ya nakasa ni. Shi yasa kika ga ko zancen shi bana so ki dinga yi mini.
Amma a yau zan baki labarina da na mahaifinki, sai dai hakan ba yana nufin zan gaya miki don ki kullace shi bane, a'ah, sai don hankalinki ya kwanta. Ki san ko ke wace ce? Daga ina kike? Ni wace ce? Shima mahaifinki wane ne? Saboda halin rai.
Ranar da babu ni, dole ki je ki nemi mahaifinki, don in ya ki ki saboda ni, iyayenshi za su karbe ki muddin suna raye".
"Umma ki daina fadin haka, insha Allah ke za ki binne ni, ba ni in ga mutuwarki ba".
Umman ta yi murmushi ta mika hannu ta shafo hawayen fuskar Muhaseen, wadanda ke zuba tarara! Kamar an kwance famfo.
Ta ce,
"Kuka Muhasin? Muhasin me yayi zafi na kuka?''
Cikin rishin kuka ta ce,
"Ba ke ba ce kike cewa za ki mutu ki barni ba?" Ta idasa rushewa da kuka.
"Ki yi hakuri Muhasin, ban fada don in saki kuka ba. Amma ki sani mutuwa dole ce, tana kan kowa. Ko ba dade ko ba jima zamu yi ta dukkanmu".
"Ni kam bana sonta Umma, don Allah ki daina fadarta".
"Na bari Muhasin, Allah Ya raya min ke, Ya yi miki albarka".
"Amin Umma, to ki gaya min labarin ina sauraro".
Ta yi murmushi ta soma.

****


FARKON LABARIN
Garin Dukku, dake cikin jihar Gombe, gari ne na Fulani masu asali da tushe, gari ne da Allah Ya yiwa albarkar kasar noma da ciyayin kiwo, Ya kuma azurta Fulanin wannan gari da shanu da tumaki masu albarka.
A wannan lokacin za ki samu saurayi dan shekaru ashirin da biyar da garken shanu buka-buka nashi na kashin kansa, sai dai a wancan lokacin babu wutar nepa babu ruwan famfo a Dukku, sai dai albarkar rijiyoyi, fadamomi da koramu da Allah Ya bamu, dasu ne muke gudanar da al'amuran rayuwarmu na yau da kullum, cikin wadatar zucci da godiyar Allah.
Ni da mahaifinki Umaru, 'yan asalin garin Dukku ne, anyi mana aure tun ina da shekaru sha biyu.
Aure irin na iyaye da kakanni, wanda babu sanayya ko wata soyayya a cikinsa. Ban sanshi ba, bai sanni ba, sai ranar da aka kai ni.
Umaru dan sarauta ne a Dukku, mahaifinsa ke rike da sarautar San-Turakin Dukku. Fulani ne usul, wadanda suka gaji Sarautar San-Turaki tun daga kakannin-kakanninsu.
Yayin da ni na kasance diyar talakawa, mahaifinshi shi ya nemi Babana Malam Sajoh da ya ba shi ni ya aurawa dansa Umaru, saboda kaunar da yake yiwa mahaifina, da irin tarbiyyar da yayi mana.

Zamani ne farkon zuwan boko, lokacin da duniya ke kwance; abin nufi, laifuffuka basu yawaita ba, haka boko bai fantsama ba. Sarakunan gargajiya sune suke mulki ba Gwamnati ba.
Umaru da 'yan tsirarun 'yan'uwansa sune kadai suka samu damar yin ilimin boko a Dukku, yayin da Turawan wayar da kai suka kawo ziyarar wayar da kai fadar Sarkin Dukku.
Umaru shi ya fara cewa zai shiga, suka bude makarantun firamare da sakandire wadanda basu samu goyon baya sosai ba daga al'ummar garin, musamman malaman addini, sai daidaiku irin su Umaru, da suke 'ya'yan masarauta.

Sunana Halimatus-Sa'adiyyah, mahaifina Malam Sajoh manomi ne mai rufin asiri, domin ya fi karfin abincin da iyalinshi za su ci, da sutturar da za su daura. Mahaifiyata Innayo, (Habibah), ta rasu wurin haihuwar kanina Bello.
A lokacin ina da shekaru hudu, amma duk da karancin shekaruna ni ke kula da Bello, har zuwa lokacin da Baffanmu ya auri Inna Baddo, a lokacin ita ma mijinta ya rasu ba ta taba haihuwa ba.
Don haka ta kama mu ni da kanina Bello ta rungume tamkar ita ta haife mu. Don haka zan iya ce dake ban tashi tare da mahaifiyata ba, amma kuma ban san maraici ba.
Da zuciya daya Inna Baddo ke rike damu, har zuwa sanda mahaifina ya aurar dani ga mahaifinki.
Rana ta farko da ya shigo dakina ya fada min cewa shi fa ba sona yake yi ba, saboda ni jahila ce, yana da wadda yake so a birni mai ilimi 'yar'uwarsa.
Don haka zai zauna dani ne kawai don ya zauna da mahaifinshi lafiya, don haka in na ga zan zauna, in zauna, in ba zan zauna ba in koma gidanmu in ce bana son auren. Amma ya ja kunne na kada in sake sunan shi ya fito a ciki.
Ban yi magana ba, har ya gama rashin arzikinshi ya tafi. Daga ranar ban kara ganin keyarshi ba, ya tattara ya koma birni, inda ya ke karatu.
Sai da aka share watanni uku rannan sai gashi. A lokacin na yi nisa da sana'ar saka da nake yi na kayan sanyin yara da huluna, don tun bayan tafiyarsa mahaifina ya bani jarin sakar ya ce in riki sana'a kada in dogara da miji ko zaman banza.
Don haka ne duk wannan dadewa da Umaru ya yi bai waiwaye ni ba, ko a jikina. Sakata da ibaduna kawai nake yi, kuma Allah ya sa min nasibi a ciki, ina samun ciniki sosai.
Don in na gama a take ake sayewa, daga baya ma har kamu ake yi cewa da na gama ana bukata.
Tunda Umaru ya dawo na aje saka gefe na shiga kula da al'amarinshi tsakanina da Allah. Kamar yadda kowacce mace ta gari ke yiwa mijinta. Amma bana burge Umaru ko kankani. Rashin arziki da rashin albarka iri-iri babu wanda ba ya yi min.
Abu kadan zan yi ya yi min gorin jahilci da kauyanci. Ke kya ce shi ba asalinshi kauyen bane. A haka Allah ya nufe ni da samun cikin ki, inada shekaru sha shidda. Na yi shiru ban fadawa kowa ba. A lokacin Baffanmu ya kai kanina Bello almajiranci hannun wani babban malami a Maiduguri.
A hanyarshi ta dawowa Allah ya saukar da ajalinsa, domin mota ce DAF ta danne karamar motar da suke ciki babu wanda ya tsira a cikinsu.
Tunda na samu wannan labari ne na fadi. Ban farfado ba sai a hannun Inna Baddo. Tana kuka ina yi kamar ranmu zai fita. Babban tashin hankalinmu bamu san inda Baffa ya kai Bello ba, ya dai ce da Inna Baddo Maiduguri zai kai shi. Maiduguri a ina? Bamu sani ba.
Bayan Inna Baddo ta gama takaba ta koma garinsu Billiri. Amma ta yi min alkawarin kawo min ziyara a duk lokac in da ta samu dama. Wani abin haushi irin nawa ko Inna Baddo ban taba gayawa irin zaman da muke yi da Umaru ba, ba don komai ba sai don wata nasiha da Baffa ya yi min a lokacin da za a kaini gidan miji, cewa in yi hakuri, shine jigon zaman aure, domin shi hakuri baya baci, kuma shine babban jari a rayuwa.
Bayan rasuwar Baffanmu, San-Turaki (mahaifin Umaru) ya dauki dukkan kulawarshi ya dora a kaina. A lokacin ne cikin dake jikina ya fito kowa ya gani.
Mahaifiyar Umaru kullum cikin yo min dafe-dafe take. Irin wadanda masu ciki ke sha'awa. Watan Umaru biyar a birni bai zo ba, don haka har cikina ya cika watanni bakwai bai sani ba.
Da ya tashi dawowa ya dawo da kyankyasheshiyar matarshi Hafsatu. Kwanan shi uku cikin gidan bamu hadu ba, don bai neme ni ba, bai zo inda nake ba.
Na dai ga ana ta shiga da kaya daya sassan dake rufe. Iya Ramatu (mahaifiyar Umaru) ta aika na zo. Ta fara da bani hakuri da kalamai na kwantar da hankali, ta gaya min Umaru ya kara aure in yi hakuri mu zauna lafiya, suma basu san da neman auren ba sai Baffannin shi ya aikowa su je su karba mishi aure a birnin Kano.
Na ce da Iya babu komai, Allah ya bamu zaman lafiya, ya hada kan mu. Ta ce, "Amin, Allah Ya yi miki albarka Halimah".
Bayan kwanaki bakwai da zuwan amarya Hafsatu, kamar yadda addini ya tsara, na danne zuciyata na yi wanka na yi kwalliya na nufi turakar maigida, na yi sallama na tura kofa na shiga.
Dukkansu su biyun suka zubo min ido kamar sun ga wani sabon abu, idanun Umaru kyar a kan cikina, ita ma amaryar kallo na take.
Ban yi aune ba sai saukar wasu gigitattun mari na ji a kuncina dama da hagu. Na rude na gigice na kidime, na nemi ji da ganina na wucin gadi na rasa.
Cewa yake, "Me zan gani haka? Ciki a jikinki Halimah? Uban wa ya yi miki?"
Na durkushe a nan ina dafe da kuncina ina kuka, yasa kafa ya yi fatali dani daga cikin dakinsa zuwa waje, na kifa a kan dutsen da muke rufe rijiya da shi, a take na ji wasu abubuwa sun tsinke a idanuna, suka fara zub da jini, ya yin da marata ta daure tam!
Bai ji tausayina ba balle ya ji tsoron aika-aikar da ya yi, ya tankadani waje da kafafunshi yana fadin.
"Ki tafi gidan ubanki ki nemi uban shegen cikinki, amma ba ni ba. Sau daya na taba kusantarki kuma ban zuba kwai na a jikinki ba (azlu). Muddin kika sake kika doshi iyayena sai kin yi nadamar zuwanki duniya, kuma sai na tona miki asiri. Ki san inda za ki kai shegen cikinki tun wuri, amma ba gidana ba, bana iyaye na ba.
Na sake ki.... na sake ki.... na sake ki.....!" Ya maimaita har sau uku.
Da yake dare ne kowa yana cikin gidansa. Babban tashin hankalina bana ganin gabana bare bayana, face wani irin duhu. Ga ruwa da jini suna ta bulbula daga idona. Ga tirtsetsen ciki ga ciwon mara da ya turnike ni. A haka na ci gaba da jan-gindi na bar kofar gidan.
[9/4, 12:57 PM] Asmau: ****

"Wane ne a nan?"
Malam Tanko makwabcinmu yake tambaya, yana haskani da cocilan dinsa.
"Subhanallahi! Halimah ce?"
Ya fada a hankali.
"Halimahh.....!".

Daga wannan ban kara sanin inda kaina yake ba.

Sai bude ido na yi na ganni rungume a jikin Ta-Birni matar Mal. Tanko.
Fadi take, "Ta farka Malam, maza kawo ruwa!".
Na shafa cikina na ji wayam, babu, ai sai na fashe da kuka.
Ta-Birmi ta miko min wani abu kunshe cikin tsumma yana wutsil-wutsil ta ce,
"Karbi kyautar da Allah Ya baki Halima, 'ya mace ce, mai kama da Ubanta. Rungume ta sosai, ta ji dumin jikinki, bakwaini ce".
Ta kwance tsumman da Mal. Tanko ya daure idanuna dasu ta ce, "Yanzu kina gani?"
Na kara rikicewa da kuka na ce, "Bana ganin komai sai inuwa".
Malam Tanko hankali tashe ya fita ya dinga bugawa Umaru kofa kamar zai balle ta. Daka ciki Umaru ya amsa.
"Wai wane mahaukaci ne ke buga min gida da asubahin nan?"
Malam Tanko ya ce,
"Ka bude sai ka gani".
Jin cewa makocinshi ne ya san kwanan zancen. Ya bude kofar a fusace ya ce, "Mene ne?"
Don takaici Malam Tanko kasa magana ya yi. Baram! Umaru ya doko kofa a kan fuskarsa ya ce,
"In dai Halima ce na sake ta saki har uku, saboda ba zan karbi cikinta ba, ban san wa ya yi mata ba.
Sannan ina gargadinka kada ka sake ka doshi iyayena a kan maganarta. Idan ba haka ba wallahi-wallahi sai zaman garin nan ya gagare ka".
Malam Tanko ya ce, "Iyayenka kamar sun ji sun gama, sai in bana numfashi. Mugu azzalumi. Ilimin Nasaran bai amfane ka da komai ba sai tabewa, insha Allahu sai wata rana ka nemi 'yar Halima da kanka. A lokacin da nadama ba za ta yi maka amfani ba".
Ina jin Malam Tanko yana gayawa Ta-Birni yadda su kai da Umaru. Ya kara cewa, "Jira nake gari ya dan yi haske sai mu kai wa San-Turaki jaririyar, ita kuma Halima mu kaita asibiti a duba idanunta. Har yanzu bakya ganin mu Halimah?"
Muryata ta dushe saboda kuka da bakin ciki na ce,
"Bana ganin kowa sai inuwar ku, na rokeku, ku bar min 'yata, ku bar Umaru da halinsa, in aka rabani da ita wa nake da shi a duniya?
Tunda ya ce ba 'yarshi ba ce, suma iyayen babu amfanin sanar dasu. Na yarda ni 'yata ce ni kadai, kuma ina so. Na gode da taimakon ka, na gode Malam Tanko".
Na mike rungume da jaririya, ko mayafi babu a jikina. Ta-Birni ta ce, "Me kike nufi Halima? Ina za ki je da jaririya bakwaini da danyen jego haihuwar fari? Ki yi hakuri in yi muku wanka ko na sati biyu ne, lokacin kun ji kwarin jikinku, sai mu zauna a san abin yi. Yanzu miko min 'yar in goyata muje nan asibitin Dukku a duba idon ki".
Ban yi mata musu ba na mika mata 'yar, ta sa zani ta goyata. Ta janyo mayafinta jikin kyaure ta yafa, ta kama hannuna Mal. Tanko yana gaba muna binshi a baya har dakin shan magani na garin Dukku.
Ya duba idon ya wanke da magani, ya like da bandeji, ya ce bayan sati daya a cire a dawo ya kara sa maganin shi kenan zai washe.
Mal. Tanko ya biya kudi muka dawo gidansa. Ta-Birni ta tada wuta nan da nan ta gargasa ni ta yi min wankan jego da runhu, sannan ta zuba min wanda zan zauna a ciki, ta fito ta barni ta dawo kan jaririya ta yi mata wanka duk da kankantarta kuwa.
Sai dai an rasa suturar da za a sanya mata. Ta-Birni ta aika gidan 'yarta Lami da yake goyo take ta ba da kayan 'yarta kala biyu aka sanyawa jaririyar, aka kunshe ta cikin zani bayan ta yi mata gashin cibi.
Nan take 'yar bakwaini ta yi barci. Ba ta ajiye ta ba, rungumeta ta yi a kirjinta har na fito ina bin bango.
Ba zan taba mancewa da Ta-Birni ba, har ranar da na daina numfashi. A take ta kama zabbinta biyu ta bararraka min farfesu.
Bayan magariba sai ga Mal. Tanko shi ma da gasasshen nama fal leda. Ta-Birni ta shirbine shi da yajin daddawa ta sa min a gaba sai da na cinye shi tas sannan ta kyale ni.
Ranar da muka yi kwana bakwai Mal. Tanko ya kama tikeken ragon sa da yake kiwatawa na babbar sallah, ya yanka da sunanki dana zabar miki, sunan mahaifiyata Habibah, nake kiranki MUHASIN. Wato (mai kyautatawa)
Haka bayin Allahn nan suka ci gaba da kula damu har tsayin sati biyu. Ido kuwa an yi jelen asibiti har an gaji ba abinda ya canza.
Don haka na rungumi kaddara ta da hannu bibbiyu, idan jarrabawa ce Allah ya bani ikon cinye ta.
Ranar litinin ita ce ranar da Malam Tanko ya yanke cewa zamu je gidan San-Turaki don ga dukkan alamu basu san komai ba, domin babu wanda ya biyo baya.
Ba yadda ban yi da shi ba a kan ya bar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login