Showing 57001 words to 60000 words out of 66781 words

Chapter 20 - KWANKWASON JIMINA BOOK 1 hausa novel

24 Aug 2024

13634

iya hanbare ki na sumar da Ke yanzu..."

"Ni dai na gama magana.... Idan Kuma baa daiku mataki ba zan dauka da Kai na".

Mtsceww..." Allah wadaran hali irin na ki nusaiba" bappah Auwalu ya fada Yana grigiza Kai

"Aa karka sake tanka ni wallahi. Magana ce ta gaskia nayi. " Ta shiga daki ta dakko pillow ta dora akan kujera,

"Ka kwana a parlor banason hayaniya yau" Ta shige daki ta bugo kofa tana murza mata mukulli.

Yaran duk suna saukar da idanun su kasa. Kunya ta dabaibaye shi. Nusaiba ta gama renashi yarasa yadda zai yi da ita.

Ashir ya mike yana kara waya a kunnen sa ya fice. Ashfeef ma yabu bayan sa. Can daga baya Nawraah ta ja hannun Amnah sukayiwa bappan sai da safe suka fita.

Dakin su suka koma. Ashir yasa suka dakko katifar su shida Ashfeef suka shimfida awaje saboda zafi sika nada net. Sai aka yaye labulen su Nawraah su kuma saboda iska ta dinga shigar musu. ..

Haka suka cigaba da rayuwar su gwanin ban tausayi. Lalle iyaye bango ne kuma fukafukai ne dake lullube yaran su

Wai yau yayan bappah junaidu ne da malama Hindu suke kwana a dakin ajiyar tumaki da kaji. Ba wuta a dakin ba bandaki. Ba wajen girki da ga su sai yan kayan su gwanin ban tausayi. Ko window babu a dakin, Wata iriyar rayuwa sukeyi, Mai ban tu'ajjabi Wanda dole Mai Imani sai ya tausaya musu da hawayen tausayi .

Amman duk da haka basu karaya ba. Ashir zai fita tasha da safe yayi lodi yana saka matafiya a mota. Kuma Yana zuwa wajen wanke mota dake tsallaken tashar nanma yana taya maaikatan wajen wanke mota suna bashi dan wani abun...

Sannan duk inda ake gini zai shiga ya musu leburanci ya daukar musu bulo ya ebo musu ruwa idan suka bukata ya kwashe baraguzai na gini...

Sannan idan sun samu aikin yin fenti na wani gidan ko wata ma'aikatar suna zuwa suyi shi da Ashfeef. Ta haka suke samu su rufawa junan su asiri.

Ashir na tsaye tsayin daka akan yan uwan nasa. Duk dai burin sa bai wuce ya wayi gari yaga farin ciki lullube a fuskokin yan uwan nasa ba shakikai da suke uwa daya uba daya ..

Ahakan Kuma kullum sai Ashir ya sayo biredi da kudin daya samu ya Kai wa nusaiba sunyi karyawar safe dashi kullum ba gajiyawa wata rana harda madara ma Yana hadawa idan ya samu faraaga... Idan Bai samu ba Kuma Yana sayo biredi da sukari da lipton daya, su sha ruwan bunu.

Amman duk da wannan wahalhalin buga bugar da suke suna kawo cefane ana abinci. Nusaiba Bata gani idan Bata ga dama bama sai tace abincin ya kare ko tace ya kone ta zubar ta hanasu abinci ta bawa yaranta kadai..

°°°°°

Ashir da Ashfeef a yanzu sun dawo kwanan waje gaba daya sun barwa su Nawraah dakin. Net suke kafawa su saka katifa su kwanta.

Da rana kuma su dan zauna suyi hira ko suyi karatu Ashir Yana kara musu duk asubah. Da safe Kuma Nawraah ta koyawa Amnah dai dai hizb din da take.

Ashir ya kurbi ruwan dake cikin kofi Yana duban Nawraah dake kalabewa Amnah Kai yace,

"Ina takardar makarantar da kika samu? Dakko mun muga"

"Hamma kakka damu wallahi ni baki daya karatu yabar Kai na. Allah kuwa"

"Banason musu dakko mun. Akwai lissafin da nake acikin Kai na"

"Tohm Hamma Yi hakuri"

mikewa tayi ta nufi akwatinta ta daga kayanta daga can kasa ta zaro paper ta Mika masa da hannu biyu ya karba yana karantawa...

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/9, 4:58 PM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_✍️:MX_


_47_

_Assalamu alaikum... HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me naira hamsin me naira dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata mai albarka..._

_idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo unguwar tarauni dake garin Kano sai akira number opay dincan dake sama_

_zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki.._

_kofa a bude take ga duk Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin_..
:::::::::

:::

"First choice Jami'ar Al-Haramein Naduka mai zaman kanta da ke Naduka crescent (apple island) dinnan? Second choice jami'ar gwamnatim tarayya ta Naduka dake baya, Third choice Kuma makarantar polytechnic ta koyan jinya ta cikin babban asibitin na Naduka.. mashaa Allah. Allahumma barik"

"Nagode sosai Hamma. Amma dagaske ni banason zuwa wata jamiaa Allah kuwa"

"Kede kita addua Nawraah. Da yardar Allah Zaki karatu a jami'ar nan ta farko kamar yayan kowa. Inshaa Allah Zaki karatu Nawraah. Burin ki da kokarin ki ba zasu salwanta ba inshaa Allah. Fatana dai Allah ya shige mana gaba ya zama gatan mu a dukkanin lamuran mu Allahumma Aameen"

"Aameen Aameen Hamma."

"Aameen Hamma. Allah ya amince" Ashfeef ma ya amsa.

"Eh abunda nake so dake kawai ki cigaba da addua kuma inshaa Allah muna tayaku . Kowane tsanani Yana tare da sauki Nawraah komai daren dadewa. Rayuwar biyu shi akwai gidan duniya da lahira. Allah ba zai bar mu haka ba. Inshaa Allah wannan kaddarar tamu sai ta zama tarihi agaba Nawraah. Ki rubuta ki ajiye. Ko da rai yayi halin sa Nawraah ba zaku wulakan ta ba ni na sani. Ina Kuma da hope akan ki kinji ko?"

"Ina sauraron ka Hamma. Amma ka dena fadan haka don Allah Ina jin wani iri Hamma. Inshaa Allah dukkanin mu zamu rayu har ya zuwa lokacin da zamu samu sauki acikin wannan matsatsi da muke ciki. Zakayi aure ka hayayyafa ka tara iyalin da yawa Kai ma Hamma"

Murmushi yayi Yana kada Kai yace,

"Ba Wanda yasan gobe sai Allah Nawraah. Kuma dan ku ai ba zaa barni ba. Hakama dan ni ai ba zaa bar ku ba. Kawai dai Ina magana ta ne. Zance ne ya shigo cikin zance. Kita addua kede kada ki karaya. Inshaa Allah sai kin zama cikakkiyar babbar maaikaciyar a fadin kasarar nan sai an dinga kwatance dake ana yaban kyawawan halayen ki da temakawa mabukata da Zaki dingayi masu karamin karfi. Hakama Ashfeef Kai ma Allah zai cika maka naka burin ka zama babban dan ball Wanda kasa da ketare zasu yi alfahari da kasancewar sa gwarzo jajirtacce. Sai kayi fice ana nuna ka sai kere su messi su Ronaldo inshaa Allahu. "

"Hamma ni fa?"

Amnah ta tambaye shi tana mitstsika idanu zatai kuka. Duk ta sake ramewa gwanin ban tausayi daman ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba kullum a kwance. Itama har biscuits da cheese balls Ashir ya saya mata ya ajiye ake bata kullum . Ashfeef Kuma ya saya mata bobo guda goma shima tana sha sosai.

Ashir ya riko hannunta ya taso da ita ya zaunar da ita akan cinyar sa. Ya saka hannunsa yana tallabo habarta yace,

"Ke?.... Amnah ta ai ke babbar maaikaciyar lafiya zaai. Babbar likita Zaki zama inshaa Allah ki dinga temakwa marasa lafiya kina basu kulawa ta musanman cike da tausayin su da kyautata musu kinji.? Allah ya muku albarka gaba daya Allah ya tsare gaban ku da bayan ku Allah ya shiga lamuran ku ya iya muku a dukkanin komai. Allah Kuma ya kare ku daga sharrin masu sharri. Allah ya muku katangar karfe da azzalumai. Allah ya daga darajar ku duniya tasan muhimmanci ku, Ta Kuma yi alfahari da kasancewar ku acikin, Al'ummar ta. "

"Aameen Hamma, Amma dan Allah ka dena irin wannan maganganun" Nawraah tace dashi tana hawaye sosai.

Bude baki yayi Yana murmushi ya dubi Ashfeef yace,

"Kaga? Jaruma ce fa ke Nawraah bansan ki da laushi ba. Banason wannan emotional yanayin naki Allah. Ki jajirce ki tsaya tsayin daka wajen ganin komai ya tafi yadda ya kamata. I count all my hopes n you Nawraah. Ke din KWANKWASON JIMINA ce MAI WUYAR SHAFAWA...."

"Ai kuwa dai Hamma gaya mata. Wannan idan ta fara kuka samari da alama kowanne sai ya sakata kuka Allah kuwa. " Ashfeef ya fada Yana Kai mata rankwashi ta goce tana dariya.

Suka saka dariya baki daya ciki harda Amnah dake kyakyatawa. Ashir ya dube su daya bayan daya Yana goge hawayen fuskar sa dake tsiyaya yace,

'haka nake son ku kasance ko da yaushe cikin farin ciki . Da dariya dauke a fuskokin ku. Allah ya dawwamar daku cikin farin ciki ya yaye muku dukkanin damuwa ya nisanta ku da damuwar dake cin ku ya lullube ku da rahamar sa allahumma Aameen"

"Aameen Hamma tare da Kai."

"Eh mana hamma ka dena cire kanka dan Allah"

Murmushi yayi Yana gyara Kai yace,

"Ai idan kuka kasance cikin farin ciki ku kadai ma ya wadatar. Ni kune nawa farin cikin. Farin cikin ku shine nawa, ganin ku cikin farin ciki shi ke faranta rai na da zuciyata da gangar jiki na. Yan uwana, Ashfeef , Nawraah da Amnah kune farin cikina,. Da ke sanyaya ya Kuma lullube zuciya da ran Hamman ku Ashir a Koda yaushe. Allah ya jikan iyayen mu da rahama Allah ya gafarta musu Allah yasa aljanna makoma ce agare su"

"Allahumma Aameen Hamma"

"Inshaa Allah Hamma"

"Aameen"

Yauwa Amnah ta. Ya ce da Amnah Yana lakutar kumatun ta.

"Zaki Sha alawa?"

"Eh" ta fada tana tafa hannuwan ta.

"Nawraah jeku sayo alawa please. Ungo ki taho da omo da sabulu zan mana wanki sun taru. Kowa ya curo nasa"

"Tohm Amma dan Allah Hamma ka bari muyi kowa yayi nasa"

"Aa ban amince ba. Illa dai Ashfeef zakayi dauraya ka shanya. Ke Kuma ku zauna da amnah idan Kun dawo daga sayo alawar ki koya mata karatu"

"Tohm Hamma inshaa Allah. Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa"

"Aameen Yaa Rabbi jam'an..."

Mikewa yayi ya shiga hada kayan su da sukai datti Yana kaiwa wajen rariya zai wanke. Ashfeef ma ya dakko bokitai ya fara ebo ruwa Yana tarawa a babban baho Wanda zasuyi wankin dashii....

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/9, 6:10 PM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_✍️:MX_


_48_

_ADVERT👇👇_

_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_


_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_

_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_

_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._

_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_

_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._

_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_

_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_

_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
:::::::::

::::


Rufe kofar gidan tayi ahankali, Ta shirya tsaf cikin riga da zani na atamfa ta yafa mayafin ta ta rike yar jaka. Ta sauka daga yar matattakalar da ake haurawa ahau gidan nasu

Da sauri ta wuce har tana tuntube ta rankwafa kasa dataje wajen dakin su Amnah ta durkusa ta wuce da sauri tana saye fuska.

Dan adaidaita ta tare ta shiga ciki . Bata mance da kwatancen gidan data karba ba awajen direban daya kawo wa su Ashir kayan abinci kwanakin bayan tun da ran bappah junaidu.

Har kofar gidan ya kaita ta sauka ta lalubo kudin sa a jaka tana kallon darin biyun ta dan adaidaita, ya wafce da karfi ganin taki bashi, ta tsirawa wa kudin idanu. Alokacin Kuma Nusaiba tunani take dama bata zo ba da ta kafa ta daba don tanason ta saka data ta hau duniyar online.

Baki ta wangame alokacin data Isa kofar gidan tana yaba tsaruwa irin tasa tamkar a gidajen da ake nunawa a talabijin na masu kudi.

Ta nufi gate din tanata sauri masu gadin suka tareta.

"Ya ke Ina Zaki?"

"Wajen hajiya nazo."

"Wacace? Bantaba ganin ki ba anan gidan"

"Tabbas bakuwar fuska ce kam, Bana kasar ne"

Nusaiba ta dashare baki tana sosa kasan keyarta ta sake cewa,

"Kawatace matar gidan"

daya daga cikin masu gadin ya bushe da daria har yana rike ciki ya kalleta tun daga kasan kafarta zuwa fuskar ta . Gaba daya ko alamar daukar kalar ire iren kawayen hajiyar tasu batai ba. Don haka ya grigiza Kai hana tabe baki yace,

"Ba nan gidan bane Ina tunanin kinyi batan Kai"

"Banyi ba fa. Gidan Dr bintu mana. Zan maka karya ne"

"Kirata awaya " ya fada yana rera fito.

Nusaiba ta zaro idanu tana janyo wayarta ta fara latse latsen karya ta danna wajen kira ta kara a kunnenta,

"Eh nazo bintu. Okay bari na shigo. Ai masu gadin nan naki ki canza su basuda kirki. Na gidah na kin manta korarsu nayi alokacin da suka hana hadiza shiga? Okay gani nan"

Ta nufi kofar kantar kantar zata shiga Mai gadin ya tare kofar da hannun sa yana hura hanci yace,

"Aa... Duk munsan ire iren ku. Ba wata hajia da kika kirawo dan Allah malama ki kama kafa ki koma inda kika fito"

Nusaiba ta saka hannu tana mai nuni da shi tace,

"Ka bude mun na shiga... Ya sunan ka ne?"

"Sunana Naziru gidah Kuma nace ba Zaki shiga ba don bansanki ba bakuwar fuska ce, na biyu Kuma ba wata hajia da kikai waya da ita. Yadda kika zo baki a abude tamkar Zaki handame mu ma kina kallon gidan kowa yasan bakuwa ce ke kuma marar karfi iri na. Don haka ki koma inda kika fito kada kisa na saka miki shocking wallahi" ya karasa fada Yana daga shocking din hannunsa. Wata waya Mai karafuna ajiki tanata hartsatsi

"Naziru ko? Ka kyauta ko? Zan nuna maka wacece ni a kasar nan"

"Mtsc" Yaja tsaki yana komawa kan kujerar sa Yana rera baitin wata waka,

Cikin ikon Allah sai ga fitowar motar direban rannan data gani. Ta dashare baki tana daga masa hannu. Ya yi murmushi shima yace,

"Ina wuni? Hajia ta...?"

"Kwarai ta Naduka.... "

"Tasan Zaki zo ne?"

"Munyi waya ai tana ciki"

"Eh tana nan. Ya haka nazman ka barta a tsaye ko wani abun kake?"

Naziru ya dube shi yana kallon nusaiba yace,

"Ka Santa ne?"

"Na kakkai su hajia gidan ...........

Ta katse shi da sauri tana murmushi tace,

"Bai sanni ba ne na masa uzuri. Bari na shiga"

Ta kutsa Kai ta gaban Naziru Mai gadi ta shiga ciki. Ba yadda ya iya ya koma wajen zaman sa ya zauna. Shi Kuma direban ya wuce tsalallaken titi wajen masu kankana...

Ko data shiga bata San kan gidan ba sai da sata Mai aiki ta nuna nata kofar da zata shiga.

Ta shiga ciki bakinta dauke da sallama. Kai tsaye ta shiga parlorn ta hakimce ta zauna ba kowa aciki

Sai daga baya Dr bintu ta sakko tana gyara dankwalin ta. Ta dubeta tana kallonta sama sama,

"Wacece wannan din?"

"Ah hajia ni ce fa. Matar bappan su nawrah "

"Oh" ta fada tana dubanta shekeke. Dake Itama Dr bintu akwai jin Kai

"Baki iya gaisuwa bane? " Ta sake tambayar ta tana mata kallon tara saura kwata ganin yadda ta babbake akan kujera ta harde kafafu..

"Oh Ina kwana?"

"Lafiya. Meke tafe dake?"

"Dama zuwa nayi akan kayan abincin da kuke bayarwa kwana biyu shiru. "

"Ajiya kuka bamu ne? Na dauka niyyace da temakon musulunci mukayi iyayinmu ko dolen ku akan mu take?"

"Hajia kwantar da hankalin ki ni bada wani abun na ce haka ba. Kuma ni a bayan ki nake wallahi"

"Bangane me kike nufi ba malama"

"Ina nufin rannan ba Nawraah na fadin wasu maganganu ba da kukazo? nufina ki kwantar da hankalin ki nasan komai Kuma bazan bar wani abu ya taso ba muddin kika bani bukatin da nake nema"

Dr bintu tayi shiru gabanta na bugawa tasan komai? Kenan tasan Alhaji Sambaso mijinta shi yake kashe malama Hindu

'kjnsan komai fa kikace .?"

"Kwarai na sani harda wani abun da ke bakida masaniya ma akansa" Nusaiba ta kara da qarya tana karya Kai bayan ba abunda ta sani

Dr bintu ta gyada kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login