Showing 33001 words to 36000 words out of 66781 words
a zare suke suna kwana a bola. Nawraah lafiya kadai ma idan Allah ya barka da ita wallahi babban arziki ne. ... Ki kasance cikin hamdala ga mahaliccin ki shi Kuma zai ninka maki bukatin ki inshaa Allah"
"Inshaa Allahu ummy"
"Yauwa Nawraah,,, mace ce ke sai kiga Allah ya daga ki ya Kai ki gidan wani hadadde Wanda baki taba zaton samu ba Allah ne kadai yabar wa kansa sanin wayasan gobe. Kuma inshaa Allah khair"
"Hakane ummy.. nagode sosai da tunatarwa"
Suna tsaye a bakin kofar tun da suka danna door bell dai baa bude musu ba sai da Nawraah ta sake saka hannu ta danna madannin tukun sannan bayan yan mintina wata matashiyar budurwa kamar Nawraah tazo ta bude musu kofar
Ta sakala earpiece a kunnenta kana jiyo karar sautin wakar da take ji.. Sanye cikin kananun Kaya riga da wando kanta ba dankwalii ta yi parking gashin nata.
Wani hadadden babban parlor ne mai girma sosai yana dauke da saitin kujeru har biyu . Yayi matukar kyau parlorn kudi yayi aiki agidan domin komai Mai tsada ne sosai.
Yarinyar data bude musu kofar wadda kallo daya zakai mata kàsan yar gidan ce dubada wani zama da tayi akan doguwar kujera ta cigaba da karkada kafa tana bun wakar da take sauraron ta earpiece.
Can sai ga wata mata fara irin fararen ne don yarinyar ma data bude irin farar nance haka. Sunada kyau ba lefi . Irin buzayen nanne yan nijar
Matar ta dashare baki tana duban su tace,
"Dan Allah ku zauna... Malama Hindu ko?"
"Eh ni ce ce. Barka da rana mun same ku kalau?"
"Alhamdulillah..."
"Ina wuni?"
Nawrah ta gayshe ta
"Lafiya kalau yammata"
"Uhm lily kawo musu ruwa please"
"Mommy ni fa ba Mai aiki bace. In kawo musu ruwa Ina Dela take takawo musu mana?"
"What nonsense coman get up. Ki dakko harda lemo ki kawo"..
"Wallahi a koshe ma muke hajiya"
"To kinji sun koshi ma" yarinyar data kira da lily ta fada. Hadi da komawa ta gyara zamanta tana harde kafafun
"Bari a kawo kayan. Ah ai dole kusha ruwa malama Hindu...takanas daga gidan kawata ai dole a karramaka . Sunana Dr. Bintu... Ke dama nasan naki hajia qibdiyya ta fada wannan ce bansan sunan taba. Yar ki ce?"
"Eh yata ce... Nawraah"
"Mashaa Allah... Sunan Mai Dadi Mai kyau kamar jta tubarkallah. Ga yata can Ilham muna ce mata Lily . Sai babban 'dana Marwaan... Lily zo ga kawa na Miki"
Lily ta juya ta dube su duka a shekeke ta tabe baki tana girgiza kai,
"Not my type.... "
Dr. Bintu ta mike ta shiga wani daki tana kwada sunan,
"Dela.. Dela"
Da alama Mai aikinta ce don da sauri ta futo daga kitchen,
"Naam hajia"
"Zo ki fito da kayan nan duka please .."
"Tohm hajia yanzu kuwa"
Suna dai zaune suna kallon sarautar Allah dela ta fito da wasu manyan buhubuna dauke da kaya kaka kala.
"Kunzo da wayar ki? Ku fara dauka*
"Eh. Nawraah daukar mata"
Nawraah ta mike tana daga kayan daya bayan daya tana daukar hotunan su wasu budiyoyin su take yi.
Dela aiki ya kachame mata tamkar zatai hauka tazo tana cewa Dr bintu tuwo yayi ruwa gashi ko miyar bata hada komai ba.
Malama Hindu dake jin su tace,
"Bari na zo na kama Miki ko miyar ce"
"Kai harda wahala ayi haka?"
"Bakomai hajiya"
Malama Hindu ta futa tabu bayan dela suka je kitchen din. Nan da nan dama miyar kuka ce.
Malama hindu ta hada komai da zata tanada gata da saurin aiki ta fara hada miyar nan.
Baa dau wani lokaci Mai tsawo ba kitchen din ya fara tashin kamshin Miya. Nan da Nan ta gama ta ta zuba a food flask ta dauraye hannun ta ta koma inda Nawraah ke daukar hoto da bidiyo din . Suka kammala daukar
Yayinda suka lissafa Hadi da irga kayayyakin da suka haura guda biyu iri daya suka rarraba su Kashi biyu. Kowanne nawrah ta rubuta ta wayar ta ajiye.
Suna gamawa sukai mata sallama zasu tafi.. Ta bawa Malama hindu dubu biyar ta Kuma bawa Nawraah riga da skirt na cikin kayan sabbu.
Suka mata godia suka tafi. A mota malama hindu ta curo dubu daya tabawa malam Liti Dakyar ya karba yana shi mata albarka.
Nawraah ta saka aka sauketa agidan su Kuma suka wuce. Malama Hindu ta kaiwa hajia qibdiyya wayar ta Kuma nuna mata alkhairin kayan da Dr bintu ta baiwa Nawraah. Da ita kanta data Bata dubu biyar ta nuna nata ta Kuma karin tabawa malam Liti dubu daya.
Tayita yiwa hajia qibdiyya godia. Dakyar ta tsaya taci abinci aka Kuma zuba mata wani a kwanon ta.
Hajia qibdiyya ta dauki wayar bayan ta kwashe komai ta hada da chajar ta mikawa malama Hindu Wanda saboda tsabar farin ciki har kukan dadi ta saki...
:::;
Washegari malama Hindu dataje yiwa hajia qibdiyya sallama Nan take sheda mata ai Dr bintu ta kira waya tanata yaba mutinci da iya girkin malama Hindu ta kuma roki alfarmar tunda futa qibdiyya zata tafi haihuwa waje yaranta biyu Kuma zasu yi jamia. Zatayi hutu acan sosai Kafin ta dawo tana rokon Dan Allah malama Hindu ta rika zuwa tana mata abinci saboda Mai gidan ta ya yaba kwarai da miyar da tayi yanata santi..
Dakyar malama Hindu ta amince dubada yadda hajia qibdiyya keta rokon ta...
Nan sukayi sallama da su har yaran na ta da zaa Kai makaranta, junior da Hayfa. Yayinda anees Kuma zaiyi hutu tare da hajia qibdiyya zasu huta idan ta haihu har zuwa wani dan lokaci Kafin su dawo.
Har hawaye malama Hindu da hajia qibdiyya sukayi saboda tsananin sabon da sukai da juna, malama Hindu tana katse hawayen ta tace,
"Nagode hajia .. da dukkanin tarin alkhairin ki gare ni Allah ubangiji ya saka Miki da mafificin alkhairin sa ya bude Miki kofofin albarkar sa. Ya raya Miki zuri'ah ya shriya su tundaga kuruciyar su har gidan su. Allah Kuma ya sauke ki lafiya Amin. Dan Allah idan na Miki wani lefi Wanda nasan da Wanda bansani ba dan Allah ki yafe mun.Allah ya KADDARA saduwar mu ya hada fuskokin mu da alkhairi Amin"
"Ni ce da godia Hindu Allah ya daga Miki yaran ki duk kuwa da kin mun rowar ganin su Kuma bakimin lefi ko daya ba Hindu. Sai ma ni da nasan tabbas na Miki Dan Allah ki yafe mun"
"Ku gafarce ni hajia.abubuwan ne sai ahankali, Amma inshaa Allahu har sai kin gaji da ganin su ma. Ni ke Zaki aurar da su ma. Saboda ki yafemun "
"Inshaa Allahu Hindu. Allah ya yafe mana gaba daya"
Hajia qibdiyya ta rungume Hindu jikinta sukai sallama suna daga mata hannu suka shiga mota direba oga emaka yaja suka tafi.
Yayinda ita Kuma ta shiga motar malam Liti ya sauketa agidah.
Satin ta daya agida Kafin daga bisani Dr bintu ta fara Aiko direban ta yana daukar malama Hindu tana zuwa tana abinci Yana dawo da ita...
Da wannan suka cigaba da rayuwar su.sabo sosai ya shiga tsakanin malama Hindu da Dr bintu. Itaxe yiwa mijin Dr bintu abinci Kuma ya aminta da abincin sosai yana masa Dadi don har kyautar kudi yake bayarwa ayiwa malama Hindu
Wanii lokaci takan tafi da Nawraah don ta tayata wasu aiyukan na gidan aikin nata...
Ranar wata asabar da yammaci.....
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[2/29, 2:02 PM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_25_
:::::::::
*Ranar* wata asabar da yammaci... Malama Hindu nata sauri kasancewar Dr. Bintu tace mata kada tazo da safe ta bari da yamma tazo tayiwa mai gidan nata girki zai ci da daddare ba zai samu cin na ranar ba saboda wani meeting da yake da shi,
Don haka malama Hindu ta karasa aiyukan da zatayi a gaggauce.. Ta zura hijabin ta tanata sauri ta sauka kasa.
Duk yaran suna nan har da Layla yar gidan Bappah Auwalu tana zaune a kan kujera mai cin mutum biyu tana yiwa Amnah kalaba kanana a kanta.
"Ummy tafiyar za ki yi yanzu ji rani.?"
"Eh Nawraah kilama na so na makara."
"Bari na saka hijabi na nazo"
"Ai Nawrah baki gaji ba? Da kin zauna yau"
"Aa zanje"
"Tohm.shikenan shiryo da sauri"
Malama Hindu ta karasa fada tana zama akan hannun kujera ta dubi Ashir tache,
"Hamma dan Allah idan abbiey dinku ya dawo ga abincin cin sa nan a food flask na saka a kasan kantar kitchen. Idan yanason shayi kuma akwai ganyan shayi acikin kwanon nan na kan freezer."
"Tohm ummy inshaa Allah."
"Allah ya muku albarka baki daya... Ashfeef naga ka wanke takalman ball dinnan dan Allah dai karkayi dare kar ka dinga dare ma dai kaji ko?"
"Ummy kwana zaki acan ne?" Ashfeef ya fada Yana kallonta Jin tamkar kwana zatayi tana bashi sallahu
"Aa inshaa Allah komai dare da zan Kai a gidah zan kwana... "
"Tohm Allah yasa"
"Amnah banda wasan ruwa kinji? Kinga mura kike yi"
"Tohm ummy"
"Zo nan"Ta fada tana duban ta
Amnah ta mike daga kalbar da ake mata daman saura daya. Ta karasa wajen ummy . Ummyn ta rungumeta tsam a jikin tana shafa gadon bayan ta
"Allah ya miki albarka Amnah. Allah ya raya ku ya tsare kuruciyar ku har girma Aameen"
"Aaameen.. "suka amsa ta baki daya
"Layla bappah Auwalu Yana nan ne?"
"Eh Yana gidah"
"Okay. Idan nawrah tafito kuce ta sameni agidan Bappah Auwalu."
"Tohm ummy,"
Fita tayi da sauri ta nufi gidan Bappah Auwalu... Ta kwankwasa kofar nusaiba ta bude tana mita ta dauka Layla ce,
"Dan uban ki kinje kin zauna. Marar zuciya kawai. Kullum bini bini kina hanyarr gidan su dan uban ki. Uwar taurin Kai"
"Kai Nusaiba.... " Ummy ta fada tana girgiza kai ta Kara da cewa,
"Assalamu alaikum ga bakuwar yammaci"
"Waalykm Salam Hindu ce Ashe. Na dauka Layla ce"
"Uwar Layla ce wannan. Kai Nusaiba kiyi waa kanki fada dan Allah ki dinga shan ragowar ruwan alwala ance Yana saka hakuri ya tausasa zuciya"
"Fada mata dai Hindu."
"Ah Bappahn su ashe kana ciki,? Barka da yammaci?"
"Barkan mu dai. Ina ciki . Duk Ina jiyo ku Ina jin maganganun da take yi ai kinsan mai hali baya fasa halin sa" ya fada yana hararo nusaiba.
Ta gatsina fuska tana juya baya tace,
"Maganar gaskia ce ai. Layla kaman taci kafar kare saboda yawo,kullum tana gidan su haba ai da gajiya "
"Gajiyar me Nusaiba? Kada ki manta da nan da can din duk tsatso daya ne. Ko yau Layla ta tattara kayan ta ta koma can wallahi gidan su ne, Haka zalika idan Nawrah ta dawo nan ma gidan su ne, Nusaiba ke fa uwa ce. Maganar dama da nazo miki kenan nace miki ke uwa ce. Ta iya yiwuwa agaba ke zaki zama mahaifiyar su gaba daya ke zaki aurar da su. Ba wai sai bayan rai na ba ko a yanzu. Yanzu ace idan rai yayi halin sa Nusaiba ke ce mafi kusantakar zama uwa agare su wadda zata share musu hawayen maraicin su Nusaiba."
"Haba Hindu maganganun me ne haka kikeyi? Ai babu Wanda yasan gawar fari sai Allah. Kuma 'yayan ki ko taki ko ta so 'yayanta ne. Haka zalika nata 'yayan naki ne"
"Kwarai dagaske baooan su. Don ni anawa rashin hankalin wallahi gani nake ko ba rai na ba zasuyi kukan maraici ba saboda Ina da ku"..
"Bar ma wannan zancen ta iya yiwuwa ma duk mu mutu mu bari ki. Yaran namu ma ke zaki cigaba da renon su . "
"Sai dai idan kai ne zaka mutu ka barta Allah . Inshaa Allah sai na zama mai uban kudi na tara dukiya na zagaye kasashen duniya , na taka nera na bada dollar na lika yan dubu dubu da kyautar motoci sai na zama babbar attajira tukui" Cewar nusaiba tana murmushi da girgiza kafa
"Toh Allah ya kyauta..." Bappah Auwalu ya fada
Malama Hindu tayi murmushi ta mike tsaya jiyo muryar nawrah tana cewa ,
"Ummy na gama ki fito mu tafi"
"Bari muje bappan su. Dama gidan aiki nazan leka. Allah ya kaddara saduwar mu"
"To masha Allah, Allah ya dawo daku lafiya"
Sa kayi ta fita. Nusaiba taja dogon tsaki tana bankawa kofar da malama Hindu tabi ta futa da harara. Ta mike tamkar jirgin sama kamar zata tashi sama ta shige dakinta tana rufo kofar da karfi ji kake 'kauuuu'
Malama Hindu ta fita suka jera sika nufi titi kasancewar direban da zai dauketa ma ba zai samu damar zuwa ba. Don haka titi suka fita ta saka sika tsaya awajen aikin kai gidan nata wato bappah junaidu.
Nawrah na daga can gefe ta basu waje tana wasa da kasan hijabin ta.
"Hindu na...."
"Naam junaidu na..... Ya aikin naku ?"
"Alhamdulillah... Ai na gaya miki mai gidan dakike aikin ogan namu sun shiga meeting dazu ai yace mu taya shi da addua wasu manyan kadarori yake so ya mallaka inde ya samu dama zai mana manyan kyauta sosai . Kinga sai mu sake gyara gidan nan sosai"
"Oh shi ya saka mai dakin sa tace ya shiga meeting kar nazo da safe sai dai da yamma kenan. Allah sarki to Allah ya amince. Amma abbiyen su ai gidan mu babu abunda ya same shi kasa ka wani damu kanka Allah "
"Shagon awara nake son na bude miki daga gefen baya dinnan zaa tada shago a dingah sayar da awarar da sauran abubuwa."
" Allah sarki junaidu. Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Hakika bani da bakin godia agare ka. Ka a sani har kullum ba zan taba dai na godewa Allah da kasancewa mata agare ka ba. Allah yabar mun Kai har gaban abadan abbiyen su. Allah ya hada fuskokin mu da alkhairi yasa ko a aljanna mu kasance atare da juna. Nagode kwarai... "
"Wadannan kalaman fa Hindu? Sai kace wadda zatayi tafiya. Toh Allahumma Aminn ai komai na miki ban fadi ba Hindu. Domin duk inda matar kwarai ta Kai kin Kai kin zarce ma"
Murmushi tayi ta dan kallo gefen Nawraah taga ta juya baya tana danna wayar ummyn dake hannun ta yayinda ba maaikaci ko daya awajen. Ta rungume da shi da sauri ta sake shi tana goge hawayen dake neman zubo mata,
"SubhanAllah kukan meye wannan,?"
"Kuma dadi ne.. kukan farin ciki ne, kuka ne mai dauke da tarin ma'anoni. Kasancewa ta mata agare ka. Kasancewar uwa ga yarana. Kasancewar suruka ga su bappah Auwalu. Abubuwa da yawa. Nagodewa Allah da samun zuri'a ta gari wato hamidniyya Lebanon. Allah ya biyaka da aljanna Junaid .. Allah kuma ya cigaba da bude maka kofofin alkhairi ka cigaba da kula da yaran mu. Gasunan amana ne Allah yabamu. Kaga nj dai bana nan yanzu aiki zan tafi. Ka Kula da su don Allah.."
"inshaa Allah Hindu... Wannan kalamai haka? Yanzu zan koma karki ji komai Allah. Nasan dama saboda su kiketa maganganun akai kwantar da hankalin ki kinji?"
"Inshaa Allah. Abincin ka Yana can na bawa Hamma sallahu. Bari mu tafi kar lokaci ya kure"
"Sai kun dawo Allah ya bada sa'a ya miki albarka "
"Aameen abbieyn su . Komai dare ai inshaa Allah gidah zamu dawo"
"Tohm Allah ya amince Hindu"
Daga masa hannu tayi shima yana daga musu suka nufi tasi suka shiga ta Kai su can unguwar ta su Dr bintu
Gidan sika shiga bakunan su dauke da sallama suka gayshe da ita tana parlor itada mai gidan nata
Kitchen suka zarce nan da nan ummy ta fara hada abubuwan abincin da zata dafa yayinda nawrah ke tayata.
A haka har suka kammala komai. Ummy da nawrah suka nufi parlorn suka jera komai akan dinning
Dr bintu da Alhaji Sambaso mijinta sunata magana a parlorn dauke da wasu takardu agaban su...
Ya yinda tashar talabijin ke nuna wakar Maher Zain ta rahamatun lil alamin
Nawrah na son wakar don haka ta danna recording ta ajiye wayar daga can gefe don ta tariyo mata muryar Maher Zain da ke raira baitin
Waya Alhaji Sambaso ya daga ya gama amsa kiran ya saki Kara da karfi Yana jijjiga Dr bintu yace,
"Alhaji ateeks ya amince.... Plazas dinnan din sun zama mallaki na. Harda estates din mejesa da guzare dana Gpo da na bayan Maduki., shikenan nayiwa Dr abubakhr warwas matsiyaci duk tarin arzikin sa da sannu sai sun zama mallaki na..."
"Alhamdulillah.... Dama naki jinin munafukar matar sa sai uban izza da iyayi. Allah yasa su mutu acan duka kowa ya h...
Ji kake taratsats malama Hindu dake tafiya tana jinsu zata ajiye tray din jikinta sai rawa yake jin maganganun da suke kafafunta suka fara rawa tray din ya kufce daga hannuwanta ya fadi..
A matukar razane suka jiyo gaba dayan su suna kallon ta. Duk sai suka sha jinin jikin su,
"Me kike anan Hindu?" Dr bintu ta fada da karfi
"Ba abunda naji Dr.. Dan Allah kuyi hakuri santsi ne ya kwashe ni"
"Bangane ba abinda kikaji ba me kike nufi.?"
Nawrah na daga kitchen tana jiyo su ta fito da sauri ta janyo wayar ta,
"Menene wannan din me kike da waya?"
"Wayar ummy ce na ajiye" ta fada tana futa daga wajen recording din"
"Hajia sai da safe" malama Hindu ta fada tana kamo hannun nawrah
Dr bintu ta juya ta kalli mai gidan nata. Ya saka yatsa a hannu yana ciza shi.
"Hindu... Hindu?"
"Naam hajia dare yayi tafiya zamuyi"
"Ai baki gama ba, dama mana kunu" ta fada tana nuna mata kitchen
Jikin malama Hindu ya cigaba da kakkarwa tana yarfe yatsa tace
"Dan Allah hajia"
"Banason musu jeki dama mana kunu nace"
"Toh"
Komawa tayi kitchen ta janyo hannun nawrah jikinta na rawa suka futa tsakar gidan ta zaro