Showing 39001 words to 42000 words out of 66781 words

Chapter 14 - KWANKWASON JIMINA BOOK 1 hausa novel

24 Aug 2024

13624

wani ciwon ne! Astagfirullah ko mutuwa ce dai tazo lokacin ta? "

"Ashe baki sani ba. Har anyi arbain dinta? Wallahi sai yau dana kira saboda Nima kwanaki biyu dinnan kinsan saboda rasa babyn da nayi Dr yasa na dau hutun komai harda rike waya. Bashine mukai waya dake ba aranar dana fara amfani da waya"

"Anyi haka ya jikin naki kuwa?"

"Alhamdulillah da sauki."

"Kwana arbain har anyi. Allah sarki Hindu Allah ya jikanta wallahi bansani ba. Kai banji Dadi ba wallahi. Don Allah ki gayamun kwatancen gidan ko Kuma driver ya Kai ki ni ai yasani tunda shi ke dakkota ya komar daita."

"Wallahi bintu . Bakiji rai na ba Kai Allah ya gafartawaa Hindu. Wallahi bantaba ganin mace irin taba na Dade banga mutum Mai saukin kai da Bai dau rayuwar duniya da komai ba irin wannan matar. Inshaa Allah aljanna makoma ce agareta "

"Tabbas tanada hakuri wallahi. Batada lafiya ne?"

"Aa yace min accident ne irin hit and run dinnan?"

Dr bintu na tsaye sai ta zauna jin kafarta ta fara rawa ta gaza daukar nauyin jikinta. Ta dafe kirjinta idanuwanta suka furfuto waje cikin tashin hankali tace,

"Mota ce kenan ta kasheta ta gudu? Innnalillahi wa Inna ilaihi raji'iun "

"Wallahi kusan haka yaronta yacemun. Yace police sun shiga case dinma, Amman dai an kasa gano Wanda yayi. Kasancewar dare ne Kuma ba haske awajen da aka kashe ta. Wai yaushe kikace tazo aiki last?"

Gaban Dr bintu ya buga fuss. Tsabar tashin hankali sai harbawa yake kamar zai fado daga jikinta tace,

"Kwanaki ne can kamar ranar larabaa date din........ Tazo da yammaci ta tafi da dare"

"Exactly a ranar ne to daga gidan ki take wlh aka samu wani Wanda yake sauri kamar zai tashi ya bugeta ya gudu saboda rashin Imani. Ai addua nake Allah ya waiwayo damu ayi mai yiwuwa a nemo koma waye da karfin ikon Allah inshaa Allah da dakarun taro. Dole suyi dubada na issue din"

Jikin Dr. Bintu asanyaye tache,

"Kwarai ma kuwa .... Kai amma banji dadi ba Allah ya jikanta da rahama"

"Toh aamen dai. Nima bari na je na kwanta dare yayi anan mu"

"Shikenan kawata. Sai da safe agayda yaran"

"Zasuji inshaa Allahu. Ki gayda mun da su Lily"

"Inshaa Allah." Dr bintu ta zare wayar daga kunnenta ahankali ta daga kai ta dubi makeken hotan mai gidan nata Alhaji Sambaso dake jikin frame tamkar shi take ganu agaske tana girgiza kai tace,

"Ko kaffara ba zan ba. Wannan aika aikan nakane Alhaji .. bayan rokon ka da nayi nace ka kyale matar nan, Ashe ashe abunda kayi kenan.. innalillahi wa Inna ilaihi raji'un yanzu ya zamuyi kenan .?"


_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/2, 7:41 PM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_✍️:MX_


_28_


:::::::::
*Zagaye* parlorn ta shiga yi taje ta dawo tanata safa da marwa cikin tsananin tashin hankali. Jikin ta ya fara kakkarwa sosai, Baki daya tsoro ya cikata ya gauraye ta.

Tabbas idan hajia qibdiyya da mijinta Dr abubakhr dollars suka dawo suka karbi ragamar case din to lallai sai an gano su, sun kwashi kashin su a hannuwan su.

Tamkar zararriya ta shiga magana ita daya tana girgiza kai,

"Sai da na roke ka nache dan Allah kada ka mata komai . Amman ka aikaita wannan mummunan hukuncin? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un."

Jikinta na rawa tamkar mazari ta dauki wayarta ta kira shi har sau biyu bai dauka ba. Nanma ta masa message tace tanason magana da shi urgently ba reply.

Mayafinta ta zura ta fita daga cikin gidan zuwa parking lodge. Wajen mai gadi ta nufa dake rike da makullayen motocin gidan,

"Hajia ranki ya dade"

"Barkan mu... Bani mukullin Glk"

"Tohm gashi hajia. Allah ya dawo dake lafiya"

"Amin"

Direban ya taso da sauri ya gayshe ta ya karbu mukullin ya bude mata ta shiga sannan ya zagaya shima ya shiga ciki.... Baki daya bata cikin nutsuwa..

"Da gudu zaka tuka yau"

"To hajiya.. Ina zamu je?"

"Wajen Alhaji"

Suna tafe tana dukan bayan kujerar gaba, kasancewar a owners corner take, Idan ta tuno mummunan hukuncin da ya zarce ya aikata musu,

Cikin bacin rai da fargaba data gauraye ilahirin jikin ta har suka karasa kanfamin direban ya ajiye motar ta a ma'adanar motoci

Ta shiga cikin kamfanin bayan ta gyara facemask din data saka acikin mota.

Wasu maaikatan suka gane ta. Duk da facemask din data saka suka shiga gayshe da ita ladabce cike da girmamawa ta amsa tana tambayar daya daga cikin su,

"Yana ciki?" Ta nuna kofar ofishin sa dake kallon su

"Eh yana ciki hajia"

"Okay nagode"

Kofar ofishin ta nufa ta tsaya. Ta saka hannu tayi kicking har sau uku.

Yana daga zaune akan doguwar kujera makeken ofishin nasa dake dauke da bangaren desk da kujera da computer da mini fridge da kayan kallo

Sai kuma daga gefe set din kujeru ne suma da makekiyar tv da dispencer.

Sai wani drawer kuma da murfin ta garai garai ana hango komai na ciki. Su plates da cups ne da tissue da sauran su.

Shiga tayi ciki bakinta dauke da sallama. Ya daga kwalbar sugar free lemo yana sha

Dubanta yayi ta gefen idanu, ya sake karkata kwalbar cikin bakinsa ya shiga zuka ahankali yaki ajiye kwalbar,

Zama tayi a kujera mai kallon sa tana masa wani irin kallo tace,

" Ko shekara zakai kana shan lemon nan cikin kurbar tafiyar kunkuru da yardar Allah zan jira ka gama sha ka amsa mun tambayoyi na. Ko ince ka mika kanka ga jami'an tsaro bisaga mummunan ta'asaf d akai"

Ya shanya lemon ya ajiye kwalbar yana duban ta. Ya dakko wani lemo a gefen sa daya ajiye ya mika mata yana murmushi,

"Ungo sha... Haba rabin rai na"

"Ba maganar wasa ce ta kawo ni ba" ta hade rai tana amsa shi

"To fa menayi? Wait ko dan ban miki sallama ba na futa dazu? Sauri nake zamu shiga meeting. Kiyi mun afuwa"

"Kaga Alhaji ka dena wani kwana kwana . So nake ka fito a mutum ka gaya mun dalilin ka na aikata abunda kayi jiya"

"Jiya? Menayi jia?"

"Kafini sanin abunda kayi ai. Ka kyauta kenan haba Alhaji wane irin roko ne ban maka ba kan ka kyale matar nan wallahi nasan ba zata fada ba. Amman Alhaji kaje ka...

"Kinga ni bansan maganganun da kike magana akai ba. Wace mata kikace na kyale? Shin me na aikata?"

"Har kanada bakin magana ? To bari na fito maka a mutum tunda Allah yasa kaki magana... Mena ce maka akan mai aikin mu Hindu? "

"Me kike nufi ne? Wace mai aiki?

"Mai aikin gidan Dr dollars da mu kai magana. "

"Oh mai akai! Kudin ta zaa bata kome?"

Dr bintu taja dogon tsaki cike da takaici ta mike tsaye ta karasa daf da shi tace,

"Ni renin hankali ne wataran banason sa wallahi. Kayi abu ka nuna kai atafau bakai bane. "

"Bintu me ya sake samun ki ne wai eh? Idan kudi kike bukata ga atm din kinsan pin ai je ki spoiling kan ki"

"Banason kananun maganu wallahi. To tunda kaki amincewa Kanata nuna bakasan me kake nufi ba. Matar da ka buge a mota kana sane akan sani. Ta mutu ... "

"Wace mata? Wane buge? Bangane me kike nufi ba"

Murmushi tayi tana girgiza kai tace,

"Ni ce ba wata ba... Yusuf" ta karashe maganar ta cikin fadar ainihin sunan sa na yanka

Ya dubeta yana maze fuska. Domin duk sanda ta kira ainihin sunan sa to lalle babban lamari ne Kuma cikin fushi take fada . Su kanyi haka daman idan yan fadan sun tashi..

"Magana nake maka"

"To me kikeson nace bayan tambayar danayi mi ki?"

"Yusuf a ajiye maganar raha a gefe. Tunda kaga na tako da Kai na nazo kasan ba karamin abu bane. Kai kanka kàsan akwai abunda kake boyemun. Sau nawa Ina kiran ka kaki dauka? Ga wayoyin ka nan, daya agaban aljihun ka dayar gatanan a kusa da Kai. Amman kaki dauka. Don haka duk wani boye boye da kake banaso ka fito ka gayan gaskia ",

"Wai maganganun me kike haka ne? Ba Kai ba ...

"Yusuf dan Allah banason jayayya. . Ka futo ka gayamun gaskia boye boye ba naka bane. Case yana nan yana nisa awajen iyalan marigayiyar, Yusuf. Kai kanka kasan sai kanada babban issue ne kake zama a office baka dawo gidah ba. Kaki daukar waya da sauran su. Matar ka ce ni nasan halayen ka bari na fito maka a mutum . Hajia qibdiyya ce take sanar da ni, Rasuwar Hindu case din hit and run exactly ranar datazo mana ta karshe ta taafi da daddare dinnan. Daman Kuma na gaya maka nace wayar ta bata shiga a kashe ko yaushe idan na kirata saboda hakkin ta na kudin aikinta na wannan watan... "

"Ni menene hulda ta da rasuwar ta yanzu? Allah ya jikan rai"

"Yusuf boye boye ba naka bane. Case hana kokarin komawa hannun su hajia qibdiyya kasan su da hin diddigi da dakarun tsaro na kasa. Ka dena wannan kunbuya kunbuya din ka fito ka sanar mun komai musan yadda zaai maganar nan ta bata"

" Ke menene damuwar ki aciki ne?

"Yanzu ka amince kenan. Yusuf meyasa zaka kashe ta?"

"Kisa fa kaman na chaka mata abu ko na tura an kasheta . No ko daya. Kawai dai na bige ta da mota hoping ta samu karaya da sauran su"..

"To ta mutu Yusuf ta rasu. Case din hit and run ne yanzu. . "

"Ki kwantar da hankalin ki ba abunda zai faru"

"Yaya zan kwantar da hankali na Yusuf! Ya Yaya! Sai da nache maka dan Allah karkayi mata komai matar nan ba zata fada ba na sani. Ka amince kace ba abunda zakayi iska kawai zaka sha haba yusuf"

"To nj dai ban kasheta ba na dai bige ta da mota tabbas, wait yanzu me kike so ayi tsoran me kike ne?"

"Yusuf itace fa as head of her family. Itake shiltering yaran ta da sauran su"

"Kakki damu. Everything is under control. Zan saka a aika musu da kayan abinci. "

"Dan Allah kayi kokari kaji? Ko Kuma zanje da Kai na store din na karba komai"

'karki damu"

"Zanje na Kai kudin aikinta na"..

"okay ba damuwa"

Mikewa tayi ta gyara zaman gilashin fuskar ta ta zura takalman ta ta bar kamfanin....

Gidah suka koma tanata sauri ta sauya kayanta cikin wasu kayan da suka sha duwatsu da ado masu matukar kyau da tsada .

Ta sake shiga mota suka dau hanya,

"Muje kamfanin Alhaji na kayan abinci, daga nan zamuje gidan Hindu mai aikin nan nawa da kake Kai wa da dakkowa, Allah ya mata rasuwa"

"Hindu ta rasu? Kai Kai Kai duniya, mace mai kamala da kirki. Allah ya gafarta mata."

"Aamin"

Suka dauki hanyar babban katafaren kayan masarufi na Alhaji sambaso. Wato,

*SAMBASO PRODUCTIONS*


_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/2, 8:04 PM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_✍️:MX_


_29_


:::::::::

...


Motar na fakawa... Ma'aikatan wajen suka tattaso... Dr bintu ta zuge glass tana daga musu hannu. Suka shiga gayshe da ita daya bayan daya kasancewar sun san mai dakin mai gidan su..Wani lokacin yakan zo da motar da tazo da ita ma.

"Akwai Kaya ko?"

"Akwai hajia"

"Mota fa?"

"Itama akwai. Aciki za'a kai miki kayayyakin?"

"Eh... "

"Tohm hajia me da me akeso?" Cewar wani daga cikin su don shine in charge na maaikatan wajen.

"Inason buhun shinkafa ta tuwo data dafawa, buhu daya daya kowanne.. Inason taliya cartons uku. Macaroni cartons uku. Indomie cartons uku. Sai garin tuwo buhu biyu. Akwai mai ko sun kare?"

"Akwai ranki ya dade."

"Okay inason 25 litres na man gyada da manja kowanne jarka daya daya. "

"Tohm hajia bari a saka miki a motar. "

"Godia nake"

Ta fada tana zuge glass din zuwa sama. Maaikatan suka sassaka mata kayyakin a daya daga cikin motocin da ake delivery na kayan abincin idan customers sun saya suna son dispatch.

"Hajia gidah zaa kai?"

"Aa yabiyo motar mu. Naduka zone zamu shiga"

"Tohm shikenan bari ya biyo ku a baya"

"Nagode"

"Munda fa godia hajia. Allah ya saka da alkhairi ya biya bukatu"

"Aaameen"

Baki daya a atsora ce take. Gabanta ya shigaa bugawa fat fat alokacin da direban ya gangara da motar zuwa kofar gidan marigayiya Hindu.

"Hajia min karaso"

"Ta jiyo muryar sa ta daki dodon kunnenta"

"Okay..." Fita tayi ahankali tana gyara zaman mayafin jikin ta

Yayinda motar data dakko kayan abincin itama tayi parking a bayan tasu,

"Hajia ya za'ai da su?" Direban motar kayan ya tambaya

"Ku shiga dasu nan gidan"

"Okay tohm"

Ya fita daga cikin motar shi da direban motar tata suka fara kama kama da buhunhuna na shinkafar da kayan abincin cikin gidan na Bappah junaidu.

Alokacin duk suna parlor a zaune. Bappah Auwalu, Bappah junaidu, Nusaiba, Ashir, Ashfeef, Nawraah, Layla, Ahmad da kuma Amnah.

Suka jiyo bakuwar sallamar su direbobin,

"Waalykm Salam. Suwaye?"

"Aiko mu akai aina zamu saka kayan nan?" Cewar daya daga cikin direban

Ashfeef daya amsa musu ya juya yana kallon mahaifin sa yace da su,

"Anya ba batan kai kukai ba.? Ba nan gidan bane"

"Ba manne gidan marigayiya Hindu ba?"

"Eh nanne. " Ashfeef ya amsa su

"Kai suwaye ne?"

"Bappah wasu ne suka kawo kayan abinci nace ba gidan nan bane shine suka ce bananne gidan marigayiya ummy ba?"

Bappah Auwalu ya mike Kafin ya taka ya tafi tuni nusaiba ta wuce da sauri ta isa wajen su tana kikkifta idanu sai hucin iskar tafiyar ta yaji ta kunnen sa😂

"Nan ne ku shigo da su" ta amsa su tana bin kayan da kallo

Suka sauke suka sake komawa.

"Nusaiba menene hakan wai! Ya haka kawai bamu san mutane ba zaki ce musu eh nanne su ajiye ke meyasa ne har yanzu ... Ya kasa karasawa kawai ya girgiza kai hadi da sakin tsaki. .."

"Kayan abincin zasu mayar da su muna nema?"

Tsabar bakin cikin kalamanta wai"suna nema" tamkar kayan abincin su aka kawowa ba gidan na Bappah junaidu ba. Bappah Auwalu baki daya halayen Nusaiba sun dai na bashi mamaki..

Suka shigaa kawo kayayyakin suna ajiyewa har suka kammala suka koma suna gayawa Dr bintu sun Kai musu kayan .

Nusaiba sai leken su take tana sake daga kafafunta don hango su sosai. Tun daga tafukan kafafun ta ta shiga kallon ta cikin kayan ta masu matukar tsada ya zuwa fuskar ta data sanya facemask .

Takawa tafara yi har ya zuwa kofar gidan da zaka shiga ta rangada sallama,

"Shigo ciki yar uwata"😂 cewar nusaiba tana dashare baki taga kalar masu kudi da suke burgeta.

Dr bintu ta dan kalleta tana kakaro murmushi itama ta facemask ta zare takalman ta ta shiga parlorn

Sallama ta sakeyi. Suka amsa baki daya aka nuna mata wajen zama ta zauna,

"Uwar dakinta ce ko? Hajian Naduka crescent ?" Nusaiba ta tanbayeta tana kallon fatar dr bintu dake shekin masu kudi.

"Eh yar uwar ta ce ni, Amma ba ita bace. Hajia qibdiyya kike nufi ita suna kasar waje basu dawo ba. Ta haihu dan ba rai sai Kuma ta hadu da rashin lafiya. Shine suka sake daga dawowar tasu zuwa wani lokacin a gaba "

"Okay ko kece wadda takewa abinci ta biyu bayan tafiyar h..

"Nusaiba haba. Ki dakata mana tayi magana da kanta" bappah Auwalu ya tsawatar mata.

Dr bintu da dama nusaiba ta isheta da magana tayi hamdala kasan zuciyar ta. Ta gayshe da su suka amsa kananan Kuma suka gayshe da ita ta amsa musu,

"Ya Karin hakurin mu? Ashe Hindu lokaci yayi? Toh Allah ya jikanta da rahama ya gafarta mata."

"Aamin... Aamin" suka amsa baki daya.

"Wallahi bamu sani ba. Mai gidah nama Yana muku taaziya yace zai zo inshaa Allah abubuwa ne suka rike shi. Yace ga kayan abinci nan ba yawa dan Allah adafawa iyali su ci. "

"Allah sarki angode kwarai"

"A ranar da muka zo ni da ummyn mu.... Lokacin data ce na taho gidah ta koma ciki bansan meya faru ba. A tsorace take dai. Kikace lalle ta dama muku kunu Kafin ta taho.. A ranar aka bige ummy a mota ta rasu a hanyar ta dawowa daga gidan ku"

Kofofin kunnuwan Dr bintu suka jiyo mata kalaman muryar Nawraah data karashe zancen tana sake nanatawa da,

"Ba kece Dr bintu ba inda ummy ke miiki aikin abinci da rana. A ranar kikace taje da yammaci?"

Nusaiba ta juya ta dubeta tana kallonta da Karin bayani. Bappah Auwalu ya dan zunguri kafar bappah Junaid dake kusa da Nawraah, daya kishingida kansa Yana kallon sama. Baki daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login