Showing 24001 words to 27000 words out of 66781 words
ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
_18_
18
*Wani* hadadden kitchen suka shiga... Kana shiga na'urar sanyin ac zata bugo sanyin ta jikin ka...
Katoton kitchen ne wanda ke luntsume da hadaddun kitchen cabinets green and yellow... Dukkanin kitchen utensils din dakin girkin nan kalolin sa kenan guda biyu kore da yalo....
Ga wani dankareren fridge mai kofofi biyu da zaa iya bude su. Yayinda kasan sa kuma freezer ce sai water dispenser daga gefe. Da wasu madannai ajikin sa da remote controller. malama Hindu ta dauki mintinan tana kallon fridge din. Azuciyar ta tana nanata mashaa Allah tubarkallah.
Ga wani daki karami shi Kuma dankali da doya da albasa ce kawai acikin sa a zube gaba ki dayan dakin.
Da manyan freezers tafka tafka guda uku ajere. Daya kayan Miya, daya snacks, daya kaji da nama fal.
Sai wani baskets Mai hawa hawa da yawa cike da plantain da crates na kwai ajiye dasu tafarnuwa da su spices.
Da manyan jars na daddawa, kuka, Yajin daddawa na tafarnuwa dana daddawa. Gishi, maggi da sauran su.
Sai gallons na farin mai da manja da su olive oils da sauran su... Komai da komai daya danganci kayayyakin abinci na alfarma Kama daga basmati rice da shinkafar tuwo data dafawa, spaghetti, garin tuwo, indomie, noodles da sauran su buhu buhu cartons cartons gasinan jibge a store..
Harda su kayayyakin shayi suma gasinan a kwali da gwangwanaye manya manya nasu mayonnaise, cream salads, waken gwangwani da nasarar sa, su ruwan robar da lemuka birjik kai da sauran su dai komai dai akwai babu ce kawai babu...
"Kinga komai na abincin ko Hindu?"
"Nagani hajia mashaa Allahu"
"Akwai abunda kike bukata da babu?"
Malama Hindu tayi hanzarin jinjina kai da sauri tace,
"A'ah fa hajia, ai babu abunda babu anan gashinan mashaa Allahu kamar shagon siyayya. Allah yakara arziki"
"Aameen Hindu. Amman ba zaa rasa ba. "
"Hakane kam. To gaskia dai a iya abunda na sani ko ince wadanda zan iya amfani dashi dai duk gasinan sai dai ko Nan gaba idan an tashi idan babu.. Don naga wasu daga cikin spices dinmu ma kuna da su. " Ta karasa tana nuna wasu spices na labarawa
"Mashaa Allah kina amfani dasu? Oh haka fa ku da jinsin ku.. girki da su akwai dadi ga nara dandano mashaa Allah"
"Sosai kam"
"Tohm bari na barki kiyi musu Abu Mai saiki kawai. "
"Su uku kikace ko hajia?"
"Eh su uku ne... Ga tukwanen Nan ga oven ga grilling machine, ga gas cooker nan. Da sauran su dai duka"
"Mashaa Allahu.... Sai dai wannan sai an koya mun amfani da su. " Ta fada tana nuni da wadanda vlbata gane ba
Hajiya qibdiyya ta gyara tsayuwarta ta shiga nuna mata aikin kowanne da yanda aje kunne su da kashe shu. Zaai mana
.
"Ga waya anan intercom ce idan kina bukatar wani abun sai ki Kira ki danna wadannan madannan. Ga ruwa Nan da lemo ki dauka ki sha duk sanda kike so. Ga rigar girki Nan idan bakyaosn kayan ki suyi kamshin girki sai ki sauya. Ga Kuma daki Nan na hutawa wanna kofar da ke kallon ki idan kin fita akwai sallaya da carbi da hijab da toilet aciki .."
"Mashaa Allah sannu da kokari hajiya. Allah yakara arziki"
"Aameen Hindu. Allah ya jara mana baki daya "
"Aameen Yaa Rabbi"
"Toh bari naje na yo wanka Nima. Sai na sakko ko. Dukabunda kike bukata dai ko Karin bayani wannan number jikin takardar Dana baki uta Zaki Kira ta wannan wayar. Idan abunda Kuma ya kulle Miki Kai nema Zaki iya tambayar mama Talatu . Idan dakko Abu ne Kuma ki saka basariya. "
"Tohm hajia sannu da kokari. Allah ya saka da alkhairi. Aamin Yaa Rabbi"
"Aameen Yaa Rabbi. Allah yasa ki fara a sa'a"
"Aameen"
Ficewa yayi daga kitchen din. Ya yinda malama Hindu ta sauke katuwar bahaguwar zuciya tana karewa kitchen din kallo. Harda TV tanata yi ga kujerar zama har biyu.
"Wannan ba zaka Kona girki ba kana kallo?" Ta tambayi kanta
Ashe mama Talatu ta shigo ta jita. Tayi dariya tana dubanta tace
"ba zaka Koma ba Hindu indai ka mayar da hankali. Koma kallon na debe kewa sai kiga duk daddawar da zakai a kitchen baka ganin dadewarr"
"Mashaa Allahu .. Allah yakara arziki Amin"
"Aameen Yaa Rabbi... Sunana na yanka Asma'u amma ana Kirana da Mama Talatu."
"Mashaa Allahu sunana Hindu .kema anan garin kike?"
"Aa a daga kauyen kusa da Nan din nazo dai. Amman ni anan nake a zaune aikin kwana nake. Na Dade anan gidan"
"Mashaa Allahu. . Ni Kuma daga baya muka dawo Nan birnin Naduka. Da a bunza muke"
"Mashaa Allah ai kuwa kinyi kama da Mutanen bunza mashaa Allah tubarkallah "
Malama Hindu tayi murmushi... A nutse tace,
"Nagode .. Allah yasa mu fuskanci juna. Dan Allah duk abunda zanyi ba dai dai ba ki gyara mun nagode"
"Inshaa Allahu... Bakida damuwa. Matsalata daya dama reni abundna ke hadamu da indo kenan data tafi. Amman ke naga zubin kima na muminai ne don haka banjda matsala da ke inshaa Allahu."
"Inshaa Allahu Zaki sameni me biyayya mama Talatu. Nagode kwarai"
"Allah ya bamu sa'a."
"Aameen Yaa Rabbi...Mama Talatu idan ba takura zan iya samun abincin da kowannen su yafu so?"
"Wia ai tsurfar su Hayfa ce sai su wallahi. Kawai ki dafa abunda Zaki iya. Zasuci a hakan. Wancen yace kayan fulawa wancen kayan ganye wancen Abu me yaji. Haka suke ki dafa duk abunda zai fi Miki guda daya zasu ci"
"Allah sarki bayin Allah... Nagode sosai mama Talatu"
"Ba damuwa... Nima bari natafi nawa kitchen din girkin gidah gaba daya na oga zan fara sai namu "
"Okay ba anan kike ba akwai wani kitchen din!"
"Eh akwai kitchen har uku ne ai. Nan abincin Yara ake ko Mai sauki da daddare haka. Wancen na barandar Kuma shine ake na gidah gaba daya da gayshe gayshe idan da yawa zaai. Sai abincin azumi Dana sallah Dana sadaka Kuma a kitchen din waje wajen gate anan akeyi"
"Mashaa Allahu komai dai a tsare to Allah ya jara dafa musu Amin"
"Aameen.."
Mama Talatu ta nufi nata kitchen din donyin girkin bangarenta. Yayinda malama Hindu ta zare hijabibta ta zura rigar girki da aka bata.
Ban da Nan ta shiga sarrafa girkunan da ta saka zatayi.
'Tayi Naan bread da chicken wings sauce, Sai spaghetti mai veggies, da sauce na Hanta sai ta hada fruit salad da madara ta saka flovor ya bada wani hadadden kamshi da gardi. Ta Kai musu kan dinning duka ta ajiye ..
Nan da Nan ta gyara dukkanin abubuwa da ta bata. Ta shiga dakin da hajia qibdiyya ta nuna mata dazu. Tafkeken gado da setin sa da kayan sallaya da hijabi da Qur'an da Kuma bandaki aciki tsaftatattce.
Watsa ruwa ta yi ta kodauro alwala Dan anata kiraye kirayen sallar azahar dama. Tayi sallah tana zaune akan sallaya hajia qibdiyya ta kwankwasa ta shiga dakin tana sallama.
Malama Hindu ta amsa. Hajian ta zauna a bakin gado ,.
"Har kin gama? Sannu da kokari"
"Na kammala gidah ma zan tafi"
"Ah ki tsaha kici abinci "
" A mozge nake hajia"
"Ai ko ba Zaki ci ba sai kin tafi dashi kwanon ma zan saka maki kullum sau kin tafi abinci Allah. Dama na gayawa mama Talatu ta zuba Miki."
"Nagode Allah saka da alkhairi"
"Aameen."
Har bakin kofa ta rakata ta shiga mota direban ya mayar da ita har gidah tanata yaba karamci da dattako irin na hajia qibdiyya....
Hajiya qibdiyya na shirin komawa sama ta jiyo karar horn din ribadu driver yadakko su hayfa daga school sun dawo. Ta kallii agogo lallek lokaci i har yayi.
Komawa tayi kasan ta fasa hawa. Kamshin dake tasowa yasa tayi wajen wajen dinning ta fara bude warmers din...
Sukayi knocking ta saka basariya ta bude musu kofar. Hayfa ce ta fara shiga ciki ranta a matukar bace.......
[2/25, 2:56 PM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_19_
_ADVERT👇👇_
_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA NA GIDA, KAYA, JIKI, TSUGUNNO, GASHI... AKWAI KHUMRAHS MASU DADI YAN BORNU, CHADI, SUDAN DAMA SENEGAL, AKWAI OIL PERFUMES, DA TURARUWAN MOPPING DANA WANKA DANA WANKI DANA GADO DA KUJERU DA BANDAKI DA DRAWER DA MOTOCI.._
_AKWAI MAN GASHI NA FESAWA ME SA KAMSHI DANA KITSO. AKWAI KAYAYYAKIN KAMSHI DANA GYARAN JIKI SOSAI AKAN FARASHIN SARI KO SAYI DAYA DAYA. •_
_ADIRESHI: KANO.. AMMA SUNA TURA KAYAN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE..._
_INGANCI KYAU RAHUSA DA DADEWA A GIDAH DA KAMSHI SAI KAYAYYAKIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE_
_NAMBAR WAYAR SU: 08095215215, INSTAGRAM/THREADS/TWITTER:yerwaincense_and more_
_YOUR NUMBER ONE STOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS... THEY 'VE GOT YOU AND YOUR HOME COVERED_
:::::
19
*Hajiya Qibdiyya* ta juya tana duban kofar. Ganin yanayin Hayfa yasa ta kira sunanta,
"Meye haka kika shigo kina zunburo baki gaba, ba sallama?. koma ki sallama"
Komawa tayi baya ta shigo tana sallamar ta zube akan kujera tana mayar da numfarfashi.
Junior ma ya shiga bakin sa dauke da sallama ya saqala earpiece a kunnen sa.
"Waalykm Salam.... " Hajia qibdiyya ta amsa sallamar ta su tana duban su tache,
"Ina Anees?"
"Yana baya Mami.... Woahh kamshin meye haka?"
"Oh abincin ku ne da aka dafa."
"Ai kam nima naji kamshin mai dadi"
"Meye kika dawo da fari fuskar ki akumbure ke kuma"
"Ko ba Yaya junior bane Mami. Ya kwace lipgloss dina a school na Kylie dinnan"
"Ke meye na zuwa da lipgloss school saboda Allah Hayfa?"
"Tohm Mami ba ita kadai aka karbewa ba classes da yawa duk an kwace ai ba zanyi favoring nata ita daya ba ko?" Cewar junior.
"Eh hakane... Kuje ku zuba abincin. Anees!!" Ta wuce ta nufi wajen tana kiran sunan sa.
"Naam Mami...." Ya amsa ta ahankali yana shafa magen sa dake zagaye shi tana kuka.
Hajia qibdiyya tayi murmushi. Ashe dashi da magen sa ne.
"An bawa Vanessa abinci kuwa?" Ya fada kansa akan magen tasa dake ta zagaye shi tana' meow meow'
"An bata dazu basariya ma na saka ta zuba mata an bata ruwa na. Madarar ta kuwa sai zubarwa akai aka wanke kwanon nata."
"Okay" ya amsa mahaifiyar ta su yana mai mikewa tsaye daga tsugunnawar dayayi.
A tare suka shiga parlorn shi da ita bakin su dauke da sallama..
Hayfa ta zuba nyaan bread da miya. Junior ya debi spaghetti.
"Kamshin meye haka?"
"Abincin new cook dinmu ne. Mami macace ko namiji?"
"Macece sunanta Ummy ...haka zaku dinga kiranta kuma bata dade da tafiya ba."
"Mashaa Allah gaskia she's a great cook. "
"Wallahi kam dan words aren't enough to express how delicious abincin nan yayi Mami. Kai gaskia she's talented. Duk alokaci daya tayi kaman tasan kowa da abun da yake so?" Cewar Hayfa.
"Wallahi kam . Don ni banma gaya mata abubuwan da kuke so ba. Amma bari na tambayi mama Talatu. Mama Talatu! Mama Talatu"
Mama Talatu tafito daga daki da sauri tache
"Naam hajia "
"Ni ke kika gayawa Hindu abincin da zata dafawa yaran nanne ?"
"Aa wallahi. Nasan dai ta tambaye ni me yaran ke so? Nace kawai ta dafa abunda zata iya. Don kusan kowannen su da abunda yake so. Ban kuma lissafa mata nace wancen da wane abu kaza suke so ba. Nasan dai nace mata akwai me son taliyah da kayan fulawa da kuma abinci marar nauyi ma akwai me so acikin su. Wani abun ne ya faru?"
"Kai amma gaskia an gayshe da Hindu. Wannan kokari haka? Kinga tayi Naan bread da sos din chicken wings tayi spaghetti da veggies shima da sos na hanta ga fruit salad da madara shima bakiji yadda ko'ina ya gauraye da kamshi ba wallahi"
"Ga kamshin nan kan da an shigo. Gaskia tayi kokari abubuwa da yawa haka cikin kankanin lokaci. "
"Mashaa Allah kam. Kin zubawa su basariya da kowa a kwanon sa?"
"Eh na zuzzuba musu na Alhaji ma na kai masa bangaren sa. "
"Yauwa sannu da kokari"
"Yauwa hajia bari na je idan shikenan"
"Eh shikenan mama Talatu."
Anees ya ebo fruit salad sosai ya koma gefe yana sha. Sai lumshe idanu yake,
"Da dadi shima?" Hajia qibdiyya ta tambaye shi
"Beyond words"
"Mashaa Allah... Bari dai na zuba naci nima" ta fada tana mikewa tsaye
"Mami kar ki cinye mana please"
"Da yawa ai tayi gashinan. Ai daga yanzu har ni zata ringa dafawa zan yiwa girkin mama Talatu bankwana"
Suka kyalkyale da dariya baki daya banda anees da ya mayar da kansa kan TV dake nuna shirin labarai a tashar larabawa ta aljazeera....
"Auta ya school?"
"Alhamdulillah Mami ..."
"Mashaa Allah..Allah ya temaka kaji.? Akwai abunda kake so yanzu?"
"Banason komai Mami. Thanks a lot"
"Allah ya maka albarka"
"Aameen Mami... Wa iyyakum"
"Mami school Alhamdulillah mu da baki tambaye mu ba" Cewar Hayfa
Junior yayi dariya yana girgiza kai kawai. Hajia qibdiyya itama murmushi tayi tace,
"Toh Hayfa ya school? Junior ya school?"
"Alhamdulillah Mami Amma Ina bukatar abubuwa gaskia"
"Kai Hayfa..." Cewar junior
"Yaya ai gaskia ne"
Mami dai bata ce ya school din ba sai ma dariya da tayi kawai tace,
"Idan Baban ku ya dawo ki same shi ki gaya masa.. Allah ya muku albarka Amin"
"Aamin Mami"
"Aameen duk da dai kinfi kaunar autan ki .."
Mami tayi murmushi tana mikewa tsaye ta Isa wajen wanke hannu dake gaban dinning din ta tatsi hand washing mist ta wanke hannun nata.
Daya bayan daya kowanne ya tashi. Hayfa dakinta a sama yake . Yayinda dakin anees, daban dakin junior ma daban kowanne da parlorn sa da kayan kallo da saitin kujeru hakama dakunan su da kayan kallo ..
::::::::: ::::::::::
Sai da akayi sallar isha'i zungureriyar motar Dr. Abubakhr dollars ta kunno da kan hancin ta mai nishi gate din gidan ..
Oga emeka driver dinsa ne ke tuka babbar motar da alkalami yayi kadan wajen bayyana maku adadin kyawun ta da tsadar ta. Ta matukar haduwa fiye da yadda kalamai zasu bayyana muku ita.
Kalar ruwan bula ce mai turuwa amma turuwar sheki take bayarwa. Masu gadi da security suka taso kan motar duka suna yi masa sannu da zuwa.
Da sauri suka bude masa gidan gaba inda yake zaune ba abaya ba kamar yadda da yawan masu kudi kan zauna a owners corner. Shi din agaba yake zaune tare da direban sa dake tuqawa .
"Sannu da dawowa yallabai.... " Cewar Mudi ya karbi brief case din hannun Dr.
Yayinda sauran ma suka shiga doka masa sannu da zuwa.
"Sannun ku dai.... Nagode kwarai. Ga wannan aje wajen nai tsiren can aci." Ya mika musu kudi a dunkule yace su raba ya shiga ciki bayan ya karbi brief case dinsa
Sukayi ta doka masa addua suna masu shi masa albarka.
Sashen sa ya wuce... Wanda zaa iya shiga ta bangaren hajia qibdiyya ma.
Babban parlor ne mai matukar girma da dinning area. Sai dakuna manya guda biyu.
Komai da komai na rayuwar masu kudi an tana deshi abangaren sa kai harda abubuwa da yawa ma da wasu masu kudin basu samu iko ba..
Bandaki ya shige yayi wanka. Ya sauya kayan sa zuwa jallabiya. Yana fitowa ya iske matar sa hajia qibdiyya.
Itama taci ado cikin wata atamfa riga doguwa samfurin a shape. Cikinta ya dan tillo kadan ya kara mata kyau sosai.
Tayi daurin ture kaga tsiya. Wadataccen gashin kanta yazubo har kafadar ta.
Sai kamshin turaren kaya na kamfanin yerwa incense and more ne ke tashi a jikin ta. Ga na gidah data kunna a burner shi ma na kamfanin tiraren yerwa incense and more ko'ina sai tashin kamshi yake uwa uba ga na'urar ac dake sanyaya wajen .
Ya sauke idanun sa akanta...suka sakar wa juna wanj tsadaddan murmushi .. ba kadan ba tayi masa kyau kamar ko da yaushe cikin cin kwalliya take. Da yawa wasu matan idan suna da ciki zaka gansu da daurin zani kansu a taje ba kitso da leda ko gwangwani suna zubar da yawu aciki ..
Ita kuwa ko da yaushe tana kokarin zama tsaf tsaf cikin cin uban su ado juma. Duk kuwa da rabin zaman mai gidan nata a asibuti yake yi, Amma hakan be hanata gyara kanta ba
"Tsarki ya tabbatata ga Allah madaukakin kowa da komai .... An gayshe ki kujerar tsakar gidah uwargidah sarautar mata.....Kinfi kyawu kyau... Yake mabudin zuciyata.... MARIYATUL QIBDIYYA!!!...
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[2/25, 3:10 PM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_20_
_ADVERT👇👇_
_YERWA INCENSE AND MORE_
_(DUNIYAR KAYAYYAKIN KAMSHI MASU MATUKAR DADI DA KAMA JIKI, GIDAH, KAYA DA SAURAN SU)_
_INA MA'ABOTA TURARE? KADA KU MANTA SHI FA KAMSHI RAHAMA NE, KUMA TSAFTA CE_
_TSAFTA KUMA TANA CIKIN IMANI… TOH KU MAR-MATSO KUSA_
_MUN KUMA ZUWA DA HAJAR KAYAYYAKIN_
_*YERWA INCENSE AND MORE*_
_DOMIN SAMUN ZAFAFAN TURARUKAN WUTA