Showing 12001 words to 15000 words out of 66781 words

Chapter 5 - KWANKWASON JIMINA BOOK 1 hausa novel

24 Aug 2024

13618

ko ya Bata littafin sa ta koya. Harr dai ya saya mata Dan kirraci take koyan rubutu da karatun acikin sa da dan fensurin da ya bata..

Duk abunnnan babu Wanda ya sani sai Ashfeef da ashir daya sani daga baya sai Kuma autar su Amnah data kana yayar tata nawrah tana karatu inda nawrahn ta zaunar da ita ta gaya mata komai tana rikon ta duk kuwa dakankancin shekarun amnan da basu taka kasa sun karya ba.

A boye take koyan karatun da rubutun. . Ba Wanda ya sani daga wajen Yan uwa bayan yayyaun ta da kanwata Amnah Amnah sai Layla yar gidan bappah Auwalu wadda suka taso tare aminan juna. Don wata uku ne tsakanin su kawai Layla tabawa nawrah . Shekaran n su daya gashi komai tare suke yi.. Haka dai nawrah ta rike su bisaga Amana Kar su fadawa iyayen nasu don zaa hanata a Kuma mata babban hukunci. Suka rike mata amanar kuwa basu taba fada ba ita ma Kuma nawrahn ta Ina takunta ba a taba kamata ba sanda take rubutun, take Kuma karahrawar...

Haka Sika cigaba da rayuwa a sabon yankin da suka dawo ... Bappah junaidu da iyalan sa su Nawraah da Kuma bappah Auwalu da nasa iyalan..

Nusaiba itace Mai dakin bappah auwalu.. ita ba auren zumunci bane gari daya ne kawai ya hada su na bunza. Amman itama tsaton fulanin bunza ce.

Allah ya azurta su da yaran su su biyu jachak, Ahmad shine na fari Wanda saan Ashfeef ne yayan nawrah, sai Kuma Layla din da take tsaran nawrah..

___

Haka rayuwar ta cigaba da garawa da Dadi ba Dadi ... Bappah junaidu Yana aikin kera karfe zuwa na zamanj a wata masana'anta. Ya zuba dukiyar sa baki daya ya sassayi ahubbun amfani inda ya bawa matar sa jari na tafara awarar sayarwa

Nan da Nan kuwa Allah ya sanyawa kasuwar albarka. Burni da kewayen yankin zuwa ake ana saya har layi ake yi

Rayuwar sai hamrala kawai, don Ashfeef da Ashir ma sukan je masaaniyar mahaifin nasu su tayashi aikin fenti da sauran su .. da wannan sike rufawa kansu asiri musanman da yanzun babu tarin dukiyar da suke da ita a baya Kafin a yiwa yankin bunza hari......


_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[2/17, 2:44 AM] Hafsaat🧕: *_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾

_✍️: MX_

*_ZAFAFA BIYAR 2024_*

_vip pages na arewa👇_
*_arewabooks:mssxoxo_*


*_paid page :10_*

______

*BABBAN BIRNIN NADUKA*
_(FEDERAL CAPITAL TERRITORY)_

_NADUKA ZONE!!_

______
     Kasancewar yanayin damuna ne, babban birnin Naduka sun samu rahamar ruwan sama sosai tamkar da bakin kwarya...

Domin ruwan har gyara yayi awasu wajajen.... Wasu daga cikin gidajen Naduka zone da ke na kasa wasu sun zube, Wasu barin su ya rushe. Wasu Kuma ruwan ya mamaye gidan. Alhamdulillahi.

Ruwan yayi gyara sosai don kwatoci ma sun cika makil. Sai samari da dattawa mazan ne suka hada karfi wajen gyara unguwannin. Aka furfuto masu shanya nayi masu kwalema nayi .

Garin yayi matukar sanyi mashaa Allah abunda zaa iya cewa kenan... Bishiyu sai kadawa suke, Iska Mai Dadi na ratsa ilahirin birnin da kewayen sa. Ciyayi sun Kara zama koraye shar.

Alhamdulillah ni'imar Allah ta sauka a ko'ina...


'Ashir ne tsugunne agaban murhu yanata fifitawa da mahuci, Sanadin ruwan da akayi yayi gyara baki daya itatuwan mutuwa sike saboda danshi.. Sai anyita fiffitawa..Haka ya gwaggwafe Yana fifita wutar sosai tamkar wata mace... Sanye yake cikin kananun Kaya na gidah.

Mahaifiyar su malama Hindu ta fito daga cikin gidah hannunta dauke da katon tray da awara sai turiri take da alama yanzun ta sauketa a wuta.

"Sannu Hamma (dake haka take ce mai kasancewar sa dan fari a gare ta) sannu da kokari.. kawo Nan na tayaka"

"Aa Ummy ai tama kama Ina man yake?"

"Gashi can bayan Kofa. Laa tabbas ta kama Allah ya shi maka albarka"

"Aameen ummy"

"Ina Ashfeef ?"

"Nace Masa yaje ya huta ummy. Dan Allah karki ce komai"

Malama Hindu tayi murmushi, Zancen dai kenan kamar ko da yaushe. Ta dube shi tace,..

"Ba zaka dena jika kannen naka ba ko Hamma?"

"Ummy idan ban jika su ba wasuke da shi bayanni?" Yakarasa fada Yana murmushi.

Itama murmushin tayi ta gyada kawai tace,

"Toh Allah ya muku albarka gaba daya Aameen"

"Allahumma Aameen"

Nan da nan ya dakko man ya dora akan wuta tuni daman sun rage hanya ta hanyar soyashi da lawashi sai kamshi ke tashi.

Yana fara zafi Ashir yaja kujerar tsugunno wajen murhun ya shiga tsoma awarar cikin ruwan kwai daya Sha kayan hadi yanaa saka ta amai.

Mahaifiyar ta su na gefe tana shi Masa albarka. Nan da Nan kuwa aka fara yin layin awarar wasu da kulolin su na abinci wasu Kuma a Leda zaa saka musu wasu Kuma a takeway pack zaa sa musu a nade da kyauro.

Cikin haka su Nawraah suka dawo daga islamiya itada Layla..

"Sannu da aiki Yakumbo" Layla tace da Malama Hindu

"Ummy sannu da aiki... Laa icen ya huru? Sanu ummy sannu Hamma" Nawraah ta fada tana zare hijabin makarantar islamiyar kalar ruwan omo..

"Sannun ku duka Allah yabada ladan karatu .. ungo Layla kuje ku hada da abinci"

Layla ta saka hannu ta karbi bakar ledar da malama Hindu ta Mika mata cike da awara sai kamshin yajin tafarnuwa ne ke tashi ga coleslaw shima a gefe da kayan su tumatir.

"Angode"
Ta nufi gidah da sauri tana murna, Don dama Koda yaushe sai malama Hindu ta aika musu da awara fal ko saya bappah Auwalu ya Aiko ayi hanawa take tace a mayar masa da kudin ta zuba musu kyauta.

Kamar ko da yaushe don kusan kullum ita take kaiwa saboda da yamma ake farawa wani lokacin da rana don haka da sun taso islamiya malama Hindu zata bata tace ta Kai gidah..

Ta shjyga cikin gidan nasu da sauri bakinta dauke da sallama,

"Umma gashi"

Ta mikawa mahaifiyar su nusaiba ledar awarar, bappah Auwalu na daga gefe Yana duban su,

"Meye wannan din dalla kina baromin Abu a Ido"

"Awara ce inji yakunbo"


Mtscew taja tsaki tana hararar ta,

"Awarar ce kika tsaya kerere a akai na sai kace wani babban Abu nazo mu gani ko na nama haka? Matsa daga nan Kafin na Kai Miki gula aciki na hanbare ki" ta karasa tana sake dankara mata harara,

"Kawo nan Layla. Je ki cire kayan makarantar kinji?"

"Toh Bappah" Ta nufi wajensa ta Mika amsa awarar jikinta a sanyaye ta nufi daki.

Ya dubi matar tasa ta sauke kanta tana hada yatsunta yace,

"Ba Zaki dai na wannan halayen na ki ba ko nusaiba! Awarar ajiya muka basu da kullum sai sun Aiko mana kyauta?"

"Yo ai sunada kudin ne. Don sun tsinnana mana da awara da me Allah zai rage su"

Tsaki yaja shima Yana karkada mata hannu yace,

"Dakin da kike kiwon ki kudi kike biya ko kyauta sukutum junaidu ya dauka ya baki iye? Ko wani abun ki saya ki basu na karamci amman kin ki"

"Kyauta ce mana.. yo wancen akurkin dakin ai sai da ya tabbatar Dan Adam ba zai iya kwana aciki ba ko da kuwa Rai daya ne bare yace zai ci moriyar sa shine ya jefe ni da shi. Su kansu kiwon Dakyar suke nunfashi saboda azabar zafi da dubu ba wundo ba a dakin haba haba Dan Allah. "

Mikewa bappah Auwalu yayi Yana girgiza kai cike da Takaici Mai tattare da dinbin bacin ran dake fitowa daga bakinta yace,

"Tunda hakan be Miki ba kyautar tazo da sakayya Mai cin mutincin to ki tattara ki kwashe kiwon ki ki mayar musu da mukullin dakin su"

Dariya ta saki tana tabe haba Hadi da tada hannuwa tana shewa tace,

"Lalle Auwalu wallahi ni dariya ma kake bani wai daki . Wancen akurkin ne daki? Wancen Dan ficicin wajen kamar bandakin kaji zaka ce mun daki? Koda yake banga laifin ka ba duk wata Yana sanmaka sadaka fisabilillahi ai shysa idanuwanka sika rufe baka ganin lefin su. Batin na mayar musu da mukullin na kwashe kiwon na Kuma ba zan ba. Nace bazan kwashe din ba. Raba Arne da makami ibada ne. Don sun dau wancen shirme wajen cikin tarin dukiyar su ta Ina Allah zai rage su? "

Bappah auwalu yayi kwata Yana cije kasan labban sa yace,

"Wadatar zuciyaa ce kawai da junaidu da iyalin sa alhamdulillah. Domin kowa sheda ne junaidu ya sayar da sauran kadarorin sa da sukai ragowa ya fara harkar kasuwancin Nan da ita ya sanwa Mai dakin sa take awara suka taru suke rufawa junan su asiri. Nan danacee maki ga dubu uku ki fara sanaa kema ai kikayi don haka karki sake kawo mun sukar Yan uwan kinji na gaya Miki" Yana gama magana ya saka Kai ya shige kitchen tabi bayansa tana sakee fashewa da dariya tana harara tana mita,

"Dubu uku... Allah ya kwashewa dubu ukun Nan albarka. Wallahi Auwalu nafi karfin dubu. Wacce sanaar Zan fara da dubu. Har da wani mun gori wai kar na karar kawo sukar Yan uwan ka. Yo ai ba sai kamin gori ba. Abunda naka gajiya da fada kullum nasan junaidu da Hindu Yan uwanka ne na jini dukkan su. Mtscew aikin kawai"

Ta shige daki ta tana bugo kofar garam. Bappah auwalu ya tabe kansa kawai yana juye awarar ababban tray...


::::::::

Wata hadaddiyar luntsumemwniyar mota ce ta faka a daidai kofar gidan... Sliding mirror din bayanta tayi na owners corner tana hangar dandazon layin awarar..

"Hajiya kinga layin ko! Yasin Kuma duk Wanda na roka abani basa yadda Yan taurin Kai ne Mutanen dake layin"

Agogonta ta sake kalla lokaci na gogawa. Cikin ta sai kugin yunwa yake gashi awarar kawai take son ci.

Batace masa komai ba ta bude kofar motar ta futa...Kallo daya zakai mata kasan wannan daga jinsin masu farcinan Susa tafito. Dubata kayan dake jikinta kadai ma abun kallo ne tabbas kudi yayi kuka awajenta.

Agogon dake daure awutsiyar hannunta Rolex ne latest design na shekarar. Jakar hannunta samfurin hems. Fara ce sosai tamkar baturiya, fatar ta sai sheki take duk kuwa da katon sunglasses din prada designer dake sakale a idanunta...Kai tsaye ta shige cikin gidan tamkar ta San masu gidan.......


[2/21, 6:52 AM] Hafsaat🧕: *_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾

_✍️: MX_

*_ZAFAFA BIYAR 2024_*

_vip pages na arewa👇_
*_arewabooks:mssxoxo_*


*_paid page :11_*

______

::::::::::::::::


  ***Bakinta dauke da sallama a gayance ta shiga cikin gidan har yar rumfar da Malama Hindu da yaran nata ke zauna suna ta tuyar awara har kasake biyu manya. Ga layi mashaa Allah anata shige da fice na sayan daddadar awarar...

Saboda awarar na da matukar dadi ga laushi mai tattare da kwai daya lullubeta. Tasha kayan hadi. Ga tumatir da albasa cucumber a yanke a gefe da Kuma yajin tafarnuwa sai kamshin kayan kamshi yake yi...

Babban al-muhim Kuma awarar akwai tsafta. Komai a tsaftace idan kaje saya. Harta abun daukar awarar aware yake a gefe da ledar hannu ta dauka itama. Don haka Yan hayu masu kudin birnin Kai har ma da talakawan ma siya sukeyi... Ga faraa da karanci da malama Hindu da yaranta ke nunawa masu sayar awarar ta su....

Wannan yasa da karfin addua da istigfari da shimfidar fuska da Kuma kyautatawa irinta Hindu da ahalin ta yasa baki daya mutane ke kaunar awararta. Don kullum sai ta kare idan anzo saya babu duk yawanta....

   Ta lumshe idanun ta ta bude a lokacin data karasa inda suke suyar awarar. Malama Hindu ta daga Kai da sauri duk suka juya suna kallonta hadi da amsa sallamar da tayi Kafin daya bayan daya su shiga gayshe ta.

Ta amsa fuskar ta a sake. Malama Hindu ta mike da sauri tana cewa

"Hajiya shigo ciki"

Murmushi tayi cike da mamakin bata taba zuwa ba, Amman tamkar sun Santa har da cewa ta shiga cikin gidan?

Bakinta dauke da sallama ta shiga parlorn malama Hindu ta amsa tana daga tsaye .

"Ga wuri ki zauna, mu Kara gaisawa . Barka da yammaci? Iyalin kalau?"

"Alhamdulillah." Ta amsa ta tana duba parlorn dan karami madedeci, Amman a killace ko'ina tsaf tsaf a gyare sai kamshin turaren wuta ne ke tashi...

Lalle suna da tsafta . Ganin ba wani baki dake ciki ko masaaniyar zuwan ta balle tace shiryawa sukai .

"Ma shaa Allah" malam Hindu ta fada...

"Kinsan gidan Dr. Abubakhr dollars?"

Malama Hindu ta girgiza kai da sauri tana mai him ta da kallon Karin bayani,

"bansan shi ba gaskia"

"Hakane kam ba lalle ki San shi ba. Dubada bangaren ku daban namu damu. To shi Dr. Abubakhr din miji na ne. Ni Kuma sunana hajiya qibdiyya. Kusan kullum ai Ina aiko a saya mun awara a wajen ki"

"Allah sarki. Nagode Allah ya saka da alkhairi. Da ke mutanen da yawa bazan waye wanene ke zuwa ba"

"Hakane kam..." Hajiya qibdiyya ta fada tana murmushi hadi da duban agogon da ke daure a wutsiyar hannun ta tace,

"Yanzun ma shine mun fito tare da shi tun dazu yacemun layi yayi yawa Dakyar idan zaa samu.."

Malama qibdiyyah ta kada Kai Kafin tace,

"Eh wallahi.. masha Allah Nan da Nan da anyi take karewa. An goggode muku baki daya masu saya Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa. Aameen"

"Aameen"..

"Shysa na fito da Kai na .. naji zan iya samun awarar ko kuwa. Wallahi wannan ne shi ya saka " ta yi shiru bata karasa ba.

Malama Hindu na nazarce da ita daman tun shigar ta gidan dazu a farko ta hango cikin da ke jikin ta. tayi murmushi tace,.

"Allah ya raba lafiya hajiya. Ba matsala wallahi. Zaki ci anan ko a zuba Miki a pack ki tafi da ita?"

"Aah mashaa Allah, Nagode kwarai. Gashi" ta Mika mata Yan dari biyar guda biyu.

"Ta dubu biyu kenan? Har zaki cinye ta dubu biyu?

"Karki damu. Zubamin a plate kawai na ci anan. Kamar guda takwas ta Isa"

"To bari a kawo. Amman dan Allah ki rike kudin nan wallahi zan baki kyauta. Uwa uba Kuma kudin sunyi yawa "

"Ahh yar uwa banason musu "

"To shikenan nagode Allah ya saka da alkhairi Amin"

Malama Hindu ta nufi wajen babbar food flask da suke saka awara ta dakko plate ta zuba awarar fal da kayan hadi da yaji aciki..

"Gashi ranki ya dade... Bari a kawo ruwa"..

"Kakk takura kanku bari na ce driver din waje ya kawo"

"Aa dan Allah . Ki bari nima na sami lada tukun"

Hajiya qibdiyya tayi murmushi kawai hadi da kada Kai tace,..

"To shikenan tunda haka kikace. Nagode kwarai "

Malama Hindu ta sake fita tana Kiran Nawraah. Nawraah dake zubawa wani coleslaw acikin kwanon abinci ta mike da sauri,

"Naam ummy"

"Ungo rike. Ki sayo lemo daya karami da ruwa babba shima daya. Kiyi sauri banda wasa akan hanyar"

"Tohm ummy" ta fada da sauri harda hadawa da gudu. Malama qibdiyya ta koma wajen su Ashfeef dake tuyar auren Ashfeef ya hanata ta hanyar rcewa,

"Ummy kin har bakuwa ita kadai fa. Ki koma zamu karasa Allah"

"Hamma kaji abunda yace ko"

Ashir yayi murmushi Yana sosa keyar sa yace,

"Kije ummy ku cigaba da hirar ku aii sauran kasko daya daya mu karasa"

"Tohm sannun ku da kokari. "

"Yauwa ummy"

Komawa parlorn tayi wajen hajiya qibdiyya. Hajiya qibdiyya dai sai zura lomar awara take. Tamkar zaa kwace mata saboda yadda ta gigice tana wani lumshe idanun

Hajiya qibdiyya ta saci kallon malama Hindu. Jikinta a tsaftace ba akanta irin masu sayar da awara ba shadda suke tashi idan kaje kusa da su sai hamamin wari ne ke tashi. Amman malama Hindu daga ita har yaranta tsaf tsaf suke. Uwa uba ko'ina a killace musanman parlorn da take a zaune...

Ga plate din da aka zuba mata shima tas a wanke yake...tana cikin ci sai ga nawrah ta dawo rike da lemo da ruwa a hannun ta,..

"Ummy gashi"

"Yawwa an gayshe ki. Mikawa anty qibdiyya abincin"

"Tohm ummy"

Nawraah ta karasa wajen hajiya qibdiyya ta ajiye mata lemon da ruwa. Hajiya qibdiyya ta daga Kai da sauri ta kallo malama Hindu tace

"Ruwa kawai fa nace. Don Allah a mayar da shi. Kinji?"

"Ki dubi girman Allah ki amince kinji? Hindu ta fada mata.

"Ai shikenan ... Bata ta shanye naga wata karama awajen. Dake bana shan Zaki yanzu sosai Ina kan dieting ne"

"Allah ya bada sa'a. Shikenan, dauki kije ku shanye"

Amnah ta durkusa har kasa ta karba da hannu biyu. Hajiya qibdiyya na kallon ta dakyau kwarai matuka ta birgeta. Yar karamar yarinyar da bata shekara biyar ba amman take ladabi haka! Lalle iyayen ta sun bata kyakkyawar tarbiyya, ta Kuma luraa dukan su yaran nada hankali da biyayya. Ta kasa hakura bayan ta dangwali yaji ta afa a baka tana taunawa tace,

"Wannan ma yar kice ko?"

"Eh...Amnah ce"

"Mashaa Allah su nawa kenan kaman uku ko?"

"A'ahh su hudu, Biyu mata, Biyu maza.... Akwai Ashir shine wancen nawaje me tuyar awarar .sai Ashfeef sai sai nawraah wadda ta kawo lemon nan da ruwa. Sai kuma autar mu Amnah.."..

"Mashaa Allah Allah ya raya su ya musu albarka"..

"Allahumma Aameen"..

Ta matso da robar wankin ruwan da aka kawo gabanta ta wanke hannuwan ta..

"Nagode sosai.. Allah ya kara kasuwa mai albarka Amin"

"Aameen" ,

"Bayan awara sai mai kike sayarwa?"

"Awarar ce kawai ba wani abu"

"Mashaa Allah... Idan ba takura ko zaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login