Showing 3001 words to 6000 words out of 66781 words
Ina fatan Kuma zaku dauki zantuka da nayi kuyi amfani da su. Ko bayan rai na bana fatan wani acikin ku ko zuriyar sa da ya tada wata husuma ta daban. Kudi shirme ne karewa zasuyi su barku. Amman jinin Yan uwantaka na zumunta zumunci ne Mai karfi na har abada. Dan girman Allah kada ku yanke zumuntar dake tsakanin ku. Kada ku yanke alakar da kuka taso tare da ita. Kada ku bari duniya taji kan ku...kada ku bari ayi muku dariya ana zundar ku. Ku hade kawunan ku sai Allah ya shigaa lamuran ku... Hamidniyya Lebanon kada ku bari sunan zuriyar nan ya tagayyara Allah ya muku albarka"
"Aaamin suka hada baki wajen amsa ta.
Tana karasawa ta mike tana dogara yar sandar ta ta bar wajen ta koma daki.
Donma kada wani ya kawo mata wata maganar ta daban data shiga dakin sai ta sakaya kofar ta turo ta.
Ganin hakan yasa daya bayan daya suka bar wajen. Kowanne da zancen da yake azuciyarta sa.. musnaman akan jimilar kadarorin ta da tayi...
*Hamidniyya Lebanon....*
Mai karatu zai so yaji asalin tushen wannan zuri'ah dake cikin yankin bunza mai tarin albarka...
Ku biyo ni a next page don jin kanun labaran🏃
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[2/13, 5:57 PM] Hafsaat🧕: *_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾
_NA_
_NANA HAFSATU_
_MX_
*_ZAFAFA BIYAR 2024_*
*_arewabooks:mssxoxo_*
*_Free page :04_*
____
*HAMIDNIYYA LEBANON*
Hamidniyya Lebanon wata zuri'ah ce mai karfi dake shiyar sansanin yankin bunza. Yankin bunza na dauke da yarika kala kala. Mafi yawa acikin su Fulani ne, Fulani dai kabila ce da tarihi ke turke asalinta tun karni na 15 daga wasu manyan yankuna biyu da ke kasashen Senegal da kuma Guinea Conakry, wato Futa Toro da kuma Futa Jalloh... Sai mafi karfin ciki wato wadanda sukafi tarin dukiya zuri'ar hamidniyya ne wadanda usulin usulin su larabawa ne yan kasar Lebanon..
Daga su sai barebari, Yarabawa, Idoma, Igbira da sauran su. Kusan dukkanin wasu yarirrika dake kunshe cikin kasar akwai su a yankin garin na bunza..
**ASALIN SU**
Tarihi yazo da cewa usulin zuriyar hamidniyya yan kasar Lebanon ne, Lebanon kuma kasa ce a Western Asia..
Tarihi ya nuna cewa Marigayi Hamidniyyah Mohannad Lebanon Wanda sunan sa ne zuriyar ta samu asali. Ance sunzo kasar ne yin wani bincike. Jiragen da suka zo da su suna da dan yawa. Dan haka sansanin inda ake ajiyar jirgin sai a ka samu ibtila'in gobara jiragen duk suka kone... Sai jirgin su Marigayi Hamidniyyah Mohannad wanda shi Marigayi da cikin daga cikin manyan kasa alokacin sun fita yawon bude idanu a gajimare da jirgin daga nan suka biya wata kasar..
Labarin gobarar jiragen ya koma kunnuwan can kasar inda sukayi koke koken su. Ance dukkanin jiragen sun kone da Mutanen su dake ciki. Baa banbance gawa da karfen jirgin aka tarkata aka wanke aka sallace su a haka aka birne...
Ko da ragowar jirgi daya ya dawo wato nasu Marigayi Hamidniyyah Mohannad. Sai suka samu mummunan labarin abunda ya faru..Gashi babban lefi ne ya koma kasar su shi da sauran wadanda basu rasun ba. Su ce dalilin daya faru sun bar kasar hakan ta faru to akan me zasu tafi yawon bude idanu su bar sauran mutanen su da aiyukan da aka turo su suyi? Wannan dalilin ne yasa suka yanke zama anan kawai. Domin idan suka koma kasar su ma hukuncin kisa ne za'ayi musu.
Anan suka kafa sansanin su suka auri junan su.. su da fulanin wajen suka zama mutane daya...Suna daya daga cikin manyan kabilun da suka taimaka wajen sama wa kasar 'yanci daga turawan mulkin mallaka.
Baya ga zaratan sojoji na Fulani da suka yi gwagwarmaya, akwai kuma fitattu da suka taimaka wajen sama wa kasar 'yanci.
Daga nan ne suka ci gaba da bazuwa cikin kasashen duniya musamman yammaci da kuma tsakiyar nahiyar Afirka domin nema wa dabbobinsu abinci da kuma ingantacciyar rayuwa.
Ko da yake babu tsayayyen adadi na yawan Fulani a duniya, amma kiyasi na nuna yawansu ya kai akalla miliyan 45, kuma sun fi yawa ne a kasashen yammacin nahiyar..
Kamar yadda Fulanin ke da masarautu da dama haka ma kuma suke da karin harshe kala-kala wanda masana tarihi suka kasa kashi shida.
Wannan ne ma ya sa ba lallai ne wasu Fulanin Najeriya su fahimci fulatancin wasu 'yan uwansu da ke kasashe kamar Senegal da Gambiya ko kuma Burkina Faso ba. Ko da a Najeriya, akwai wani karin harshe da wasu Fulanin ba su fahimtarsa.
Akwai aminta sosai tsakanin fulanin yankin bunza da zuriyar Hamidniyya Lebanon.. Tun shekarun baya ya zuwa yanzu. Kuma Allah ya sanya musu wata albarka ta tarin dukiya. Basu da wani yawa. Dan sun rarrasu da yawan su. Sai 'ya'yan 'ya'yayan su da sukayi aure sika hayayyafa suma suka tada tasu zuri'ar amman duk da haka basu da wani tarin yawa sai tarin dukiya .
Danma dukiyar ta babu koda kwatan rabin ta yanzu. Hakan ya samo asali ne kuma alokacin da yankuna suka hada karfi da karfe suka ci garin na bunza da yaki. Suka kwashe musu tattalin arzukan su da tarin dabbobin su sai wadanda ba'a rasa ba. Wanda suka fita kiwo hatsarin bai auku akan su ba..
Dan tattalin arzikin zuriyar ta hamidniyya kuma wadda ta ragu ce na daga abunda mahara yaki basu kwashe ba a babban dutse mai suna bunza. Wanda shine duk tarin zinaran cikin sa dama na zuriyar hamidniyya ne. Da mayakan suka raba dutsen biyu suka kwashe abunda zasu kwasa. Sai Allah bai basu ikon ganin sauran zinaren dake gefen dutsen ba daga daya bangaren.. wannan zinare shine zuriyar suka raba aka fitar wa Yafendo (Dadaa) kaso daya mafi yawa acikin . Kasancewar ta itace uwa datayi ragowa. Duk sun rasu sai 'ya'ya'ye da jikoki...
Tana dauke da rashin lafiyar hauhawar jini da sukari. Sai ciwon kafafu suma da sukarin ne yayi silar su da Kuma girma na shekaru. Wannan dalilin ne yasa zaa kaita kasar waje afura da ita Domin duba lafiyarta sosai acan din.
Ita kuma bayan tayi wasu tunani nata na daban. Ga ganin girma daya zo mata sosai.gashi an talauta zuriyar tasu ba kamar a baya ba. Domin rabin rabin rabin dukiyar tasu ta baya basu da kwatan kwatankwacin ta a yanzu.
Hakan yasa ta tara yaran nata take sanar dasu tayiwa dukiyarta rabo gida uku bisa hudu.
Kamar yadda na zayyano muku a shafin baya... Inda dadaan ke kasafce dukiyar ta... Gata kamar haka,
Sai magana ta karshe.... Dukkanin dukiyar data ragemun a duniya na hadeta waje daya na kasata kashi uku. Kashi daya zaa ajiyeta ayiwa Yara sure idan sun tasa... Su sameer, khaleed,Ashiir da ashfeef, Kashi daya zaa bawa miskinan yankin nan wajen mararrabar Ballo Mai sardii.. kashi daya na rabata tsakanin sani, salisu , Auwalu da Kuma ke Aminatu.....
Duk sukayi shiru suna sauraron ta. Ta daga Kai ta dora akan autan ta Bappah Junaid da kansa ke a kasa tace,
"Kason daya rage na karshe kuma na barwa junaidu shi kadai.... A Nan na kawo karshen maganganun da zanyi. Ina fatan Kuma zaku dauki zantukan da nayi kuyi amfani da su. Ko bayan rai na bana fatan wani acikin ku ko zuriyar sa ya tada wata husuma ta daban. Kudi shirme ne karewa zasuyi su barku. Amman jinin Yan uwantaka na zumunta zumuncii ne Mai karfi na har abada. Dan girman Allah kada ku yanke zumuntar dake tsakanin ku. Kada ku yanke alakar da kuka taso tare da ita. Kada ku Bari duniya taji kan ku...kada ku bari ayi muku dariya ana zundar ku. Ku hade kawunan ku sai Allah ya shigaa lamuran ku... Hamidniyya Lebanon kada ku bari sunan zuriyar nan ya tagayyara Allah ya muku albarka"
"Aaamin suka hada baki wajen amsa ta.
Tana karasawa ta mike tana dogara yar sandar ta ta bar wajen ta koma daki.
Donma kada wani ya kawo mata wata maganar ta daban data shigaa dakin sai ta sakaya kofar ta turo ta.
Ganin hakan yasa daya bayan daya suka bar wajen. Kowanne da zancen da yake azuciyar sa.. musanman akan jimilar kadarorin ta da tayi...
Anan mun karkare ASALIN tushen zuriyar hamidniyya Mohannad Lebanon dake a yankin birnin bunza..
Sai kuma SHAFI na gaba zamu dora daga inda aka tsaya...
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[2/13, 9:22 PM] Hafsaat🧕: *_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾
_NA_
_NANA HAFSATU_
_MX_
*_ZAFAFA BIYAR 2024_*
*_arewabooks:mssxoxo_*
*_LAST FREE PAGE: 5_*
_____
*Suna* kan hanyar layin su zasu koma gidah suka hadu da Hammah Ashfeef ..
Yana hango su ya yafuto su da hannu da sauri yana dafe kansa saboda yadda rana ke dukan goshin sa..
Karasawa sukayi wajen nasa.. Ashfeef ya dube su duk sunyi futu futu yace,
"Tun dazu nake neman ku... Yafendo tace daga aiken data muku ku Kira Bappah ba a sake ganin ku ba. Hankalin ta ya tashi sosai. Saboda tace ke bakida lafiya ashe ko? Wai ko jikin naki ne ya tashi a hanyar dawowa? " Ya karasa fada dan yatsantsa na yin nuni ga Nawra dake kikkifa idanu
Nawra ta bude baki zatayi magana Layla tayi saurin cewa,
"Eh kanta ne yake ciwo shine muka shiga gidan su Nano umman su tabata magani "
Ashfeef ya kada Kai Yana kallon Nawra yace,
"Ya jikin naki to?"
"Da Sauki naji Sauki ...Amma"
Bata karasa fada ba Layla ta saka hannu ta mintsino hannun ta,
Hakan yasa tayi shiru tana mai duban Layla ta wutsiyar idanu. Sam batason halin Laila nayin karya akan abunda ba haka ba.
"Allah ya sawwake ya kara sauki. Muje gidan. Don yafendo hankalin ta atashe ganin ba kudawo ba an je har gidan bappan ko kuna can bakwa nan."
Yayi gaba. Suna biye da shi a baya.
"Toh Yayaa.."
Nawra ta juya ta dubi Layla cike da takaici kasa kasa yadda Hamma Ashfeef ba zai juyo ba tace,
"Me karya fa dan wuta ne...kina ji dai malam Yana fada mana Kuma ma yafendo tana mana tuni akai"
Layla ta tabe baki tace,
"Fada zamu sha idan ba haka na fada ba"
Nawra ta girgiza kai kawai tayi gaba abunta. Layla tabi bayanta tana Kiran sunan ta a haka suka karasa gidah..
Da yafendo suka fara cin karo a zaune ta zabga uban tagumi tana kallon babbar kofar da Zata sadaka da wajen gidan da shigowar sa.
"Assalamu alaikum.." suka hada baki wajen yin sallama..
"Waalykm Salam... Ina kukaje ne haka iye? Nawrah Layla tun dazu ake tsumayin ku shiru. Ko jikin ne?" Ta tambaye su cike da kulawa.
"Wai kanta ne ashe yake ciwo..." Ashfeef ya amsa yafendo.
"Shine mukaje tasha magani ta kwanta agidan su .......
Layla bata karasa fadar abunda Zata karasa ba Nawra ta yi hanzar cewa da yafendo,
"Dandagi muka biya ganin noman farisu angon Fiddau.. Bamu ma gama kallon Fiddau dake daukar ruwa daga Rafinrau ba.."
Tana karasa fada tayi shiru kanta a kasa tana lankwasa hannuwan ta. Duk da karancin shekarun ta hakan bai sanya ta dinga karya ba...
"Kiyi hakuri yafendo..." Ta sake fada kanta a kasa.
Layla dake gefenta kirjinta ya cika fal da tsoron abunda zai biyo ba. Dama tun ba yau ba Nawra tasaba kwafsa musu. Don haka itama ta sadda kanta a kasa cike da muryar ban tausayi tace,
"Kiyi hakuri yafendo"
Ashfeef yayi kansu zai dake su yafendo ta hana shi,
"Kyale su....Ai Nawra kamar ko da yaushe ba itace me laifin ba. Ni nasan yau dinma kece Layla.. Allah ya shrya mana ku..."
"Kiyi hakuri yafendo bazan sake ba. Allah so nake kawai naga yadda farisu zai noman." Layla ta tsugunna tanata bawa yafendo hakuri
Nawra ma ta tsugunna agaban yafendon suka shiga bata hakuri a tare.
"Ku tashi kuje.. Allah ya muku albarka ya yafe mana baki daya"
"Aamin Aameen"
Kowaccen su tayi bangaren su sumi sumi.
Nawra cike da madaukakin farin ciki ta shjga sashen su. Don Sam batason ta dinga karya akan abunda ba hakan bane. Gwara kowane lefi ne ta fadeshi awuce wajen. Domin malaman islamiyar su suna koya musu haramcin karya da illolin ta...
::::::::::::::
Ranar wata jumuah. Yanayin damuna ne dama. Garin yayi sanyi ya Kuma yi shiru ba hayaniya. Ni'iimar Allah a ko'ina, ciyawa tayi kore gaba daya. bishiyu nata kadawa. Ga kamshin kasa dake tashi..
A ranar ne Kuma ahalin zuri,ar hamidniyya suka tsinci kansu cikin tashin hankalin da suka Dade basu tsammaci kansu aciki ba.
Wannan tashin hankalin Kuma shine na babban rashin bango majinginar su ne wato yafendo... Daadaa.
Allah ya karbi ran yafendo da asubahin ranar bayan an idar da sallah.
Kuma a satin ne sun gama shirya komai tsaf don yin hijra daga garin bunza zuwa yankin gaban sa..
Abunda yasa basu koma din ba ma.. jira suke su karasa sayar da kadarorin su gaba daya sai su bar garin na bunza.
Allah cikin ikon sa da kudurar sa da hikimar sa Domin shidin mamallakin kowa da komai ne.. Kuma kowanne rai sai ta dandani zakin mutuwa. Domin Allah daya halicci kowane dan Adam yafu kaunar sa akan komai..
Yafendo ta cika ne alokacin tana zaune akan sallaya ta idar da sallah tana azkhar. Daman jikin ya sake tsananta. Har ya Kai ga sallah ma azaune take yi. Idan zata mike ma sai an taimaka mata. Haka idan zuwa bayi ne nanma haka.
Hakika alokacin da rashin lafiyar yafendo ta Kara tsanani. Ahalin sun shiga madaukajin rudani Mai wuyar fassarawa. Domin ko menene sai da yafendo. Itace a tsaye akan kowannen cikin su.
Don haka rasuwar yafendo ta taba dukkanin su. Manya da kananan cikin zuriyar.
Lungu da sako sai koke koke suke yi.... Hakika yafendo bango ce majinginar bayi.. ita din itace tsintsiya mai daure da zumunci, temako , dattako, tausayi, kyautata wa gaba ki daya na ahalin zuriyar hamidniyya.
Ba zuriyar hamidniyya kadai rasuwar yafendo ta taba ba. Ciki harda yarika daban daban na zuri'ah da dangi na mutanen birnin bunza.
Sunji mutuwar yafendo sosai. Garin yayi shiru. Anata koke koke. Haka aka wanke yafendo. Alhamdu Lil Laah yafendo tayi cikawa Mai kyau da kalmar shahada. Ta Kuma rasu tana kan sallayar da take ibadah. Da asubah sannan kuma a cikin babbar Rana Mai tarin albarka da alkhairai wato ranar jumuah...
Bayan an gama mata wanka. Aka Kira dangi Kashi Kashi na ahalin hamidniyya don yin sallama da yafendon.
Kowannen sai da ya zubar da hawayen babban rashin jigo da sukayi na yafendo.
Suka yiyyi mata addua. Aka nannade ta aka zura a makara... Aka sallaceta aka tafi kaita gidan ta na gaskiya..
Acan dinma iyalan nata Maza sunsha kuka. Musanman Dan autan ta Bappah Junaid. Wanda banbare shi akai daga kan kabarin yana ta rusa Kuka tamkar karamin yaro..
-------
Hakika rashin yafendo ya haddasa rabuwar kayuwa da dama na daga cikin ahalin zuriyar hamidniyya...
Koda wajen gado ma sai da aka samu dan hargitsi Kafin dai daga baya Kuma su sulhunta. Duk kuwa dawasun su ne daga ciki suka kawo husumar.
Sai da sukayi kwanaki hamsin da biyu... Sannan suka tashi baki daya kwansu da kwarkwatar su daga yankin na birnin bunza suka koma can babban birnin Naduka.........
....
_Anan karshen shafukan free pages suka tsaya...zamu shiga kundun labarin a cigaban paid pages Inshaa'Allah_
_shin wacce iriyar rayuwa ahalin Hamidniyya Lebanon zasuyi a birnin Naduka?_
_Ya labarin zai kasance mai dauke da suna mai tafiyar harshen damo ... KWANKWASON JIMINA!! MAI WUYAR SHAFAWA.... !?_
_#Hamidniyya Lebanon family_
_#Dr. Abubakhr dollars family.._
_#Alhaji Yusuph Family_
_#Twist of fate, Destined lovers#Life-partners#Al-Hub-Hayaat#Rich vs poor...._
✔️✔️
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_