Showing 60001 words to 63000 words out of 66781 words

Chapter 21 - KWANKWASON JIMINA BOOK 1 hausa novel

24 Aug 2024

13633

tana gyara zamanta tace,

"Me kike bukata?"

"Kudi... Kayan abinci.., sutura irin ta ku ta manya. Kuma ba su Nawraah zaa kaiwa ba gidana zaa kawo. Sannan suma su Nawraah ki kawo kudi a basu. Idan kika dore akan haka to shikenan Ina Mai tabbatar Miki komai ya wuce. "

Dr bintu ta gyada Kai. Ta mike ta dakko jakarta hannunta na rawa. Ta ciro check dinta ta dakko biro ta rubuta kudi masu yawa ta mikawa nusaiba.

"Ki dauki rabi ki basu rabi su nawrahn."

"Bakida damuwa ai awajena ma suke agidana ni nake dawainiya dasu ta komai daga abinci zuwa sutura"

"Allah sarki. "

"Kayan abincin fa?"

"Zan aiko a kawo miki inshaa Allah. Zaki iya tafiya yanzu Ina da abubuwa ne agabana"

Nusaiba ta gyara zaman ta ta dakko wayarta ta rike tana gyara mayafi tace.

"Dan daukeni da wayar ki a haka sai ki tura mun dan Allah"😂

Ba abun Dr bintu tayi, Ba musu ta dauki wayarta ta dau hotunan nusaiba ta tura mata a lokacin

Sannan nusaiba ta mike ta futa sukayi sallama. Ta tsaya a gate ta gaggasawa Mai gadin magana yayi banza da ita yana Jin rediyo harda Mai dakuwa ta Zagi.

Tana tafe tana addu'ar Allah yasa kar Dr bintu ta gane batasan komai ba. Wani bangaren na zuciyar ta Kuma na mamaki hadi da tabbacin lallai akwai wani boyayyen lamari da suke boyewa. Kuma koma menene Nawraah tasan wani kaso daga ciki...

Gidah ta koma ranta fes. Ta boye kudin har nasu Nawraah ta hanasu taki basu. Taki Kuma gayawa kowa kudin data samu da inda taje. Tace wai neman aiki taje a Naduka crescent. Matar ta bata dubu goma tace tayi cefane. Ranar dai abinci har da nama akai kowa yanata mamaki.

Dr bintu na lekan nusaiba ta taafi. Jikinta na rawa ta nufi parlorn Mai gidan nata Yana zaune yana karanta jarida ta zauna akusa da shi tana yarfe hannu tace,

"Nusaiba dinnan tazo komai tac har abunda bansani ba ta sani...

A firgice ya juya ya dubeta bai San sanda ya furta Cewar,

"Tasan ni na tunkuda junaidu Mai gidan Hindu ta baranda ya mutu ma kenan."

Dr bintu ta mike tana zaro idanu tana girgiza kai tace,

"Alhaji.... Kana nufin kace shima kashe shi kayi? Kacemun ya fado bai taka tsani ba ya rasu. Ashe ashe Alhaji Kai ka kashe shi?. Ka kashe matar sa shima din kaje ka kashe shi. Alhaji wace iriyar rayuwa ce. Kisa fa? Kamai da rai tamkar kiyashi Alhaji? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un. Wallahi tallahi nagaji. Yanzu kenan tunda itama ta sani zaka bita ka kasheta kenan?"

Alhaji Sambaso ya girgiza kai yana harde hannuwa ban roko yace,

"Wallahi bada sani na kashe shi ba. Fada muke na turashi ya Fadi ya mutu. Ki yarda Dani bintu. Zancen gaskia kenan. Ita kuma bansan a inda taji ba Allah"

"To magana ta gaskia Alhaji na tsame hannuwanaa akan ka. Maganar Hindu na rufa maka asiri kace kuskure ne na bar maganar. Amman ka sake kashe musu mahaifiy saboda Allah. Wato kenan itama wannan kasheta zakai ko? Daman tazo tana bukatar kudi da kayan abinci da sutura idan baa bataba ba zaa samu matsala. Saboda tana cewa ita kadai ce tasan yadda zatai da Nawraah komai ya wuce "

"Karki damu duk abunda takeso zaa mata. Allah zaa yi. Kome tameso. Ni ki yafemun kinji?"

"Wace bintu ce zata yafe maka? Ka nemi yafiyar Allah dai ka Kuma roki gafarar iyalin su. Ba ruwana acikin Allah kuwa."

"Trust me baa abunda zanwa matar nan Allah shima shi ya takalo ni Yana gayamun maganganu Yana marina kinga abunda ya faru kenan"

"Alhaji koma meyake maka sai kayi enduring ka kashe masa mata,shi tunda acikin bacin rai yake. Idan ya huce sai ka gyara amma ka kashe shi?"

"Tasu ta kare ne su. Ya za'ai da wannan matar. "

"Yanzu dai inada aiki asibiti idan na gama cikin week dinnan zanyi tunani"

"Yauwa bintu na Allah ya miki albarka."

Mikewa tayi ta fice ta nufi asibutin tah dake bayan unguwar, gabanta nata faduwa . Ko da direba ya sauketa ma ta dade Bata futa daga mota ba saboda tunanin data tafi

:;;;


Kwanaki suka shude. Alokacin Ashir har ya fara hada kudade sosai na Sanya Nawraah a jamia.

Ranar wata laraba da yammaci Dr bintu taje gidan na nusaiba ta Sha mamaki dataga gidan dama aciki suke rayuwa

Ta zauna tana kyamatar ko'ina. Aka kawo mata ruwa ma taki Sha. Suka gaysa da nusaiban ta tambayi nusaiban abinda take so.

Nusaiban tace yaran su sun samu gurbi a jami'ar Al-Haramein. Amman ba kudin da zasu shiga. Kuma an dena daukar daliban tallafi.

Dr bintu tace ba damuwa. Satin sama zaa biga musu admission letter. Makarantar harda share din mai gidan ta Dana hajja qibdiyya. Don haka zaa basu scholarship khauta su nawa ne. Nusaiba tace su hudu ne . Layla, Nawraah, Ashfeef da Kuma Ahmad.

Dr bintu tace ba damuwa zaa basu gurbin karatu. Itama yayanta biyu daya zata fara daga kevel one . Dayan Kuma a babban gurbi yake zai karaa karatu ne . ..

Hakan kuwa akayi ana shiga satin aka bugo admission letters aka Aiko dasu akace nanda sati biyu suzo su fara daukar darasi a jami'ar Al-Haramein dake Naduka crescent.

Hakika su Nawraah sunyi murna. Musamman Ashir daya kasa boye farin cikin sa. Ashfeef da Nawraah ma harda su a gurbin karatun.

Wani bangare na zuciyar Nawraah Kuma na kokonto akan amincin Dr bintu da Nusaiba. Don haka ta zuba musu Ido kawai tana nazartar su....

:;;


Ashir na zaune akan kujera... Ya sayo second fairly used din waya dake hannun sa..

Ya ciccire komai na wayar ya mayar kan second din daya saya. Ya kuma bar su akan ta ainhin. Recordings din wakokin Nawraah data yiyyi ya ajiye mata su ya Kuma tura wasu a wadda ya sayo ..

Daya bayan daya ya shiga danna wakokin larabawa yana saurara duk Wanda batai masa ba ya goge akan wayar daya sayo yayinda dayar Kuma ya ajiye don Nawraah yake son ya barwa duka tunda yanzu ta shiga jamia tana bukatar browsing assignment da sauran su. Tasa Kuma sai Ashfeef ya dinga amfani da ita.

Yaje kan wani recording na wakar Maher Zain. Har zai goge sai Kuma ya cigaba da saurara jin tanada dadi. Maganganu ya fara ju suna fitowa daga wayar yayinda recording din wayar baa jinsa sai can daga kasa.

Kamar zai goge sai Kuma ya cigaba da saurara Yana ji....jikinsa ya dau rawa jin maganar da macen da mijin keyi. Da sanda ummy take basu hakuri tana bataji komai ba.

Mikewa yayi a tsaye . Whatsapp dinsa ne yayi kara. Ya duba wayar dake hannun sa. Ganin fefen bidiyo ne aka tura Masa da wata number ta waje. Yana budewa hankalin sa ya tashi na daga abunda ya gani

Jikinsa na bari ya tura budiyon daya wayar daya barwa Nawraah . Ya sake dubawa zai kira number data turo yaga ta bace bat bata kan WhatsApp gaba daya idan ya kirama sai ace batakan network

Fita yayi ransa na zugi. Har zai fuce baki daya sai Kuma ya kwaso shanyar da Nawraah tayi ya Kai mata dakin ya koma ya gyara ko'ina ya shigar musu da takalman su da kayan wasan Amnah daki ganin garin da hadari.

Ya koma ciki ya dakko Dan balangun daya sayo musu basanan ya dora akan katifar su ya fita

Yana rufo kofar sai ga Nawraah ta dawo rike da hannun Amnah

"Hamma Ina zaka?"

"Ba nisa zanyi ba yanzu zan dawo inshaa Allah. Ungo rike wayar nan taki ce. Ki dinga browsing na assignment da itaa idan kin fara jamia..duk rintsi duk wuya kada ki bari wayar nan fa subule daga hannun ki. Kar ki bawa kowa, Na roke ki da girman Allah kuma recordings din wayar nan kada ki jisu har sai kin shig aji na biyu zaki shiga na uku, sai na hudun kammala jamia kinji ko? . Allah yabada saa"

"Hamma meye haka kamar Wanda zaiyi tafiya ba dawowa? Nagode Allah ya saka da alkhairi Amin"

"Aameen ya Hayyu waayum. Sai na dawo. "

Ficewa yayi dasauri bayan ya yiwa Amnah wasa Yana lakuce mata kumatu

Kai tsaye ya nufi ofishin Alhaji Sambaso ya ci sa'a kuwa yana nan. Akayi masa iso ya shiga

Yana shiga dama Alhaji Sambaso shi kadai ne. Ashir cikin zafin nama ya cikumi wuyan sa yana kunna masa recording din wayar nan.

'kai ka kashe ummy.... Kuma ka kashe abbiey..." Ya karasa fada Yana daga wayar sa.

"Kaga komai nan evidence ne cikin nan. Inshaa Allah rayuwar ka sai ta tagayyara sai ka zama abun tausayi. Zakasha mamaki"

"Ka tsaya muyi magana yaro"

"Magana? Hahaha zakayi magana aagaban hukuma da gaban Allah ranar gobe kiyama"

Ficewa yayi. Alhaji Sambaso ya saka hannu ya shafo habar sa Yana furzar da iskar bakinsa Mai zafi . Wayar sa ya dauka ya rubuta sako ya koma ya zauna Yana shafe kansa.

Ba jimawa can wayar sa tayi haske ...ya dauka yana dubawa hamdala yayi ya kwantar da kansa akan kujera Yana sauke ajiyar zuciya..

°°°°°


Zaune suke baki daya sai ga waya akan kira number Ashfeef ance suje asibitin Naduka na gwamnati bangaren yan accident da quna.

Suna zuwa suka tarar da wata leda an nannade da kyalle. Tamkar an Kona takarda ta yayyanke dinnan tayi baki tayi toka.

"Menene wannan din?" Ashfeef ya tanbayan bakinsa bude ..

Sauran kuwa suka kasa magana.

Daya daga cikin maaikatan wajen yace,

" sunyi hatsari ne da wata tankar mai sun kone baki daya. Su bama a gane komai nasu. Kai ma dakyar aka samu wani dan area ku ya bada number ka .... "

"Bangane ba 'da na. Me yake faruwa? Konuwar me? . Motar mai kuma?" bappah Auwalu ya tambaya baki daya kamar mahaukaci yama rasa mai zai ce.

Gaban Nawraah ya tsananta bugawa tammar zai zullo ya fado,

Maaikacin yace.

"Bayan dogon binciike da mukai.Sunan sa Ashir junaidu. Ko daga Naduka zone.. Allah ya masa rasuwa"

Diiiiim komai ya dauke. Tamkar duniyar ta tsaya chak.baki daya haka suka zama tamkar mutum mutumi dukkanin su aka rasa mai cewa komai.

Idanuwa na zubar da hawaye. Hanci na tsiyayar majina ta tashin hankali. Yayinda fitsari ya cika marar su. Kafafuwa sun gaza daukar nauyin su. Hannuwan su na lankwasar tashin hankali, Ya yinda sassan jikin su baki daya suka yi laushi..

"Allah ya jikan ka da rahama... Hamma Ashir."

Suka jiyo muryar Amnah daga gefe ta kwanta akan ledar da aka sanya shi namansa sun kone kurmus kamar babbakakken kan rago gaba daya shine sanye acikin ledar sai gutsattarin naman jikin sa kamar an soya su sun babbake sun kone. Yayinda sauran rassan jikin nasa kuwa ma babu sun nike a titi sun kone da mai. Wasu kuma bazasu ganu ba. Kasancewar direban motar. Da shi Ashir din da yaran motar tirelan man duk sun mutu...



🥴🤐Acigaba da bin littafin KWANKWASON JIMINA MAI WUYAR SHAFAWA...... A kuma yi hakuri, bana labarin haka yazo 🙏🤭

#RICH VS POOR
#ANEES
#MARWAAN
#NAWRAH.....
#LIFEPARTNERS
#AL HUB HAYAT


_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/10, 12:23 PM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_


_✍️:MX_


_49_

_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_


https://chat.whatsapp.com/Cce1etNkvVKCBlgSqXa4Ek
:::::::::

Allahu Akbar! Lalle Allah buwayi ne gagara misali, Ya azurta wanda ya so a sanda ya so. Ya talauta wanda yaso a sanda ya so. Ya raya wanda yaso a sanda yayi iko. Haka zalika ya kashe wanda yaso a sanda ya so. Kuma dukkanin abubuwan nan kaunar da Allah ke wa bawan sa yafi karfin alkalami da bakin da zai furta .....

Hakika ahalin Hamidniyya sun shiga dimuwa wadda ta kere duk yadda alkalami zai fasalta. A gub'i a gub'i sun rasa rayuka hudu ... Daga kan kaka, Uwa, Uba zuwa 'Da wato marigayi Ashir ... Marigayiya yafendo, Marigayiya Hindu, Marigayi Junaidu, da kuma marigayi Ashir.

Kuma dukkanin su ba wasu lokaci mai tsawo aka dauka na tazara tsakanin rasuwar ta kowanne ba.... Lalle bawa ya kamata ya koma ya tuba ga ubangijin da ya halicce shi. Domin shi din buwayi ne gagara misali. Mamallakin kowa da komai ...

Dakyar likitoci da maaikatan asibitin bangaren sashen suka tausashe su duka tun daga kan Bappah Auwalu zuwa Amnah .suka saka su a mota suka mayar da su gidah dauke da ledar da ragowar naman gawar marigayi Ashir ke ciki...

Aka wanke shi aka nannade shi a likafani. Haka dan tsakuren sauran naman nasa sai ya zama kamar jariri ne ya rasu aka nade shi...

Akayi masa sallah aka kai shi gidan sa na gaskia wato makabarta gidan kowa... Ba tazarar kaburarruka tsakanin kabarin marigayi Ashir dana iyayen sa marigayi junaidu da marigayiya Hindu...

Ashir ya samu mutane, Mutane sosai da sai ka dauka wani babban maaikacin gwamnati ne ya rasu, ko wani babban dan siyasa ko kuwa mashahurin dan kasuwa ne..

Ba ahalin Hamidniyya Lebanon ko ince ahalin marigayi junaidu su Nawraah ne kadai suke alhini ba. Baki daya mutanen Naduka zone suke alhinin rasuwar Ashir.

Ya samu yabo sosai daga bakunan mazauna yankin Naduka zone, Dana unguwar da sike da ma yan layin su, da wajen aiyukan sa. Bangaren lodin tasha, Da na gangaren wajen wankin mota, Da inda yake leburanci idan ana gini... Magina sun shiga dimuwa wanda suka san shi. Da ma masu fenti Wanda suke harka daya...

Banda tarin mutane da suka zo daga yankin bunza da rasuwar tasa ta riski kunnuwan su. Sun shiga dimuwa sosai.

Haka zalika Ashir ya samu jamaa da suka dinga biyan duk wasu bashikan da ake binsa... Suka koma harhada yan kudade suka ce a bawa yan uwan mai rasuwar Allah ya gafarta masa ya kai masa ladan Amin.

Haka aka dinga zuwa ana taaziyya. Saboda kowa yayiwa marigayi Ashir shaida ta kirki, Babu ruwan sa da shiga harkar da ba tasa ba, Yana mutinta kowa ga ladabi da biyayya, Bai taba fada da kowa, Kuma kowa nasane, komai kankantar aiki inde halal ne zaiyi a biya shi. Don haka kowa yake shedar sa ana masa addu'oin halayen sa nagari su bishi Allah ya haskaka makwancinsa.

Haka aka share makoki... Duk wannan Kwanakin da akai ana makoki. Hankukan kannen marigayin sun tabu sosai tamkar zararru wadanda basa hauka. Don kuwa magana ma sai an tsawatar musu da fada da magig sannan sike yi

Sun koma haka haka gwara Ashfeef da Amnah ma. Amman Nawraah mutuwar ta daketa sosai. Don har karin ruwa ma sai da akayi mata na leda biyar .

Sun Sha zazzabin na rashin lafiya sun kwanta ciwo dukkan su. Abun ya tayarwa da mutane hankali musanman bappah Auwalu da ya Dan sayi alawa ya Kai islamiyar kusa da su yace arabawa Yara akuma yi addua dan Allah Allah ya sanyawa Yan uwan Ashir su Nawraah hakuri da dangana Ameen..

Sannan ya sake sawa aka musu saukar karatu na alqur'ani. Shi ma Kuma ko da yaushe a sallah da bayan yayi karatu, Yana yi musu adduoi Yana gayawa Allah kan ya farfado da zukatan Yan uwan marigayi Ashir

Sai da suka dau dogon zango sosai Kafin su farfado. Amman duk da haka ba wata magana suka cika yi ba daga uhm sai uhm uhm kawai. Kullum cikin Nawraah take. Bappah Auwalu yayi yayi amma Ina ta kasa hakuri kullum sai tayi Kuka sosai idan ta tuno da shi kadai ne dama ya rage musu tamkar shine mahaifi da uwa agare su. To gashi shima an wayi gari Allah daya fi su kaunar sa ya dauke abun sa.

Maganganun Ashir su nata dawo mata Kai. Daman wasiyya yake musu duk maganganun da yake fada a baya.tamkar yasan mutuwa zaiyi kullum cikin yi musu nasihar rayuwa yake Yana kara Dora su akan hanya madaidaiciya.

::

Toh haka rayuwar ta cigaba da tafiya ta kowanne bangare na cikin sashen littafin.

Ko'ina ana samun sauyi na rayuwa wani na dadi wani akasin haka.

A yanzu dai babu wadanda duniya ta sauyawa ta kuma juyawa baya fyace su nawrah da suka sake zama abun tausayi. Sun rame baki daya sun jeme.

Gashi makarantar tamkar da aka basu gurbi gini har an fara karatu basu taba zuwa ba saboda alunin rashin Dan uwan na su.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login