Showing 63001 words to 66000 words out of 66781 words

Chapter 22 - KWANKWASON JIMINA BOOK 1 hausa novel

24 Aug 2024

13631

Layla ma taki yadda taje ita kadai sai da Nawraah. Nusaiba ta daketa ta kyareta amma kmadagas layla tace ita gaskia sai da Nawraah zata fara zuwa jami'ar.

Hakan kuwa akayi sai bayan kwanaki hamsin da uku da rasuwar Ashir tukunna sannan Nawraah ta hakura zata fara zuwa jami'ar. Kasancewar bappah Auwalu ya zauna ya sake mata nasiha Mai ratsa jiki da jikinta yayi sanyi ya karkare yace,

"Dukkanin wadandan abubuwan agaba zasu wuce inshaa Allah. Haka rayuwar take wucewa yake kamar baayi ba nawrah. Kuma akace wai mutanen kirki Allah ya ke saukewa. Bayaga haka sanin kanki mahaifan ki da dan uwan ki mutanen kirki ne na kwarai. Duk inda mutanen kirki suke masu Kuma su junaidu sun zarce. Kuma wallahi Allah ba zai barku haka ba. Akwai jin dadi agaba da yardar Allah. Domin Allah shi kadai ya barwa kansa sani Nawraah. Tabbas munyi rashi. Amman Allah dayafi mu son su ya karbe su Nawraah. Sai mu fawwala lamuran mu gareshi. Da yardar Allah Nan gaba sai kinyi dariya . Zakiga komai ya wuce. Addu'ar mu kawai sike bukata musanman taku da kuke Yaya agsre su haka zalika Ashir yake Yaya agare ku..Allah ya gafarta musu kinji? Ki shirya goben Dan Allah kuje kinji? Ki dau hakan a ranki ki saka daga gobe kin shiga wata sabuwar rayuwa wadda acikinta ne komai zai yi sauki na matsatsi kinji? Allah ya muku albarka"

"Allahumma Aameen Bappah. Inshaa Allahu zanje"

"Yauwa haka nake son ji. Mashaa Allah. Bari naje nan layin baya na dawo"

"To bappah sai ka dawo"

Fita yayi daga dakin nasu. Ta juyar da Kai tana duban Amnah dake. Bacci ta sake ramewa itama baiwar Allah duk sai Kashi baki daya sun mokade.

Mikewa tayi ta nufi baya tayi futsari kasancewar akwai rariya da famfo awajen ta dauro alwala ta dakko sallaya ta shimfidah tana sallah. Kan Allah ya shiga lamuran sun ya musu zabi nagari adukkanin abubuwan da suka saka agaba na rayuwar su Allah Kuma ya jikan iyayen su da yayan su. Ya gafarta musu. Jamia Kuma da zasu fara Allah yasa suje a sa'a Amin"

Haka ta daga hannuwa sama bayan ta idar tanata kwarara adduan daga nan juna ta dakko alqur'ani ta zauna tana karantawa. Hawaye ya shiga diga daga idanun ta rayuwar su ta baya kawai take tunowa lokacin da dukkanin su suna raye yadda rayuwar tasu ke tafiya ahankali cike da farin ciki. Amman yanzu duk sun rasu, rayuwar tasu ta jima cikin dinbin bakin ciki da ya mamaye farin cikin su na baya ...

_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_

_KU MARMATSO KUSA...🔊_


_ZAFAFA BIYAR 2024_

_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_

_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_

_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_

_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_

_________

_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_

_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_

_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_

_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_


_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*


_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[3/10, 12:23 PM] Hafsaat🧕: *_KWANKWASON JIMINA!!_*
_(MAI WUYAR SHAFAWA)_
🦩🦯🦾

_✍️: MX_

*_ZAFAFA BIYAR 2024_*

_vip pages na arewa👇_
*_arewabooks:mssxoxo_*


_*BOOK ONE*_

_paid page :50_
_(FINALE/KARSHE)_


____

*Zafi* ake yi sosai astagfirullah. Gashi babu window a dakin nasu. Dan Amnah ma da wando take kwanciya kawai. Kusan kwana Nawraah take a zaune tana mata fiffita. Gashi ciwon ta kwana biyu ya motsa ya lafa ya dawo yakeyi.

Duk yan kudaden da aka raba musu na ragowar gadon su baki daya har na wajen marigayi Ashir duk akan rashin lafiyar Amnah yake tafiya. Saboda lalurorin ta masu cin kudi ne...

Bappah Auwalu yayi yar buga bugar da zai yi ba wani kudi da yake samu. Wanda ya dan samu din Nusaiba sai ta kwace tace yara ba lafiya su Ahmad zata saya musu magani....

Ko da yake maganar zaa fasa wundo a dakin dasu Nawraah suke. Haka nusaiba a ranar tun safe ta dinga tijara har dare tana dire tsallan albarkar wallahi babu mahalukin da ya Isa ya fasa mata wundo . Ai dakin mallakin ta ne halaliyar ta ne din haka Bata amince ba.

A ranar tsabar bakin ciki sai da Bappah Auwalu ya jera mata marika har biyu a kuncinanta ta dafe kuncinta tana duban sa,

"Ka mareni Auwalu?"

"Na mareki nusaiba. Kiyi abunda Zaki. Haba mace sai kace zazzauciya ? Aradun Allah wani mai tabin kwakwalar ma yafi ki sanin abunda ya Kamata. Ace ke kwata kwata ba digon tausayi a ranki? Ke fa uwa ce. Kin haifa gasunan agaban ki. Baki tsoron ayiwa naki haka?"

"Okay baki zaka mana kenan ni da yaran? To ni na haife su da Kai na kenan? Kai ma ai jinin ka ne. Ko ka ki, ko ka so su, su din da baka son su dai sune 'yayan ka na cikin ka wadancen yayan dan uwan ka ne"

"Duk daya suke awaje na, 'yaya na ne. Wai tsaya na tanbaye ki. Baki tunanin mutuwa ne? Bakya tunanin idan kika mutu kika bar naki yaran wa zai rike mike su? Ko gani kike ba mutuwa Zaki ba jiran duniyar zaa bar Miki eh? Idan baki sani ba duk abunda kayiwa Dan wani ko kaiwa wani na badai dai ba Allah sai anyi akan naka. Musanman maraya wallahi maraya yayi kuka akan zalun tar da kake masa na rantse da Allah Allah dai ba zai barka a haka ba. Na Miki karatun nan nayi nayi amman saboda kwakwalwar kifi ce dake Sam kinki dauka to bari kiji wallahi kin Kai ni karshe. Kinsan Allah sai anyi window a dakin nan sai dai ki hadiye zuciya ki mutum ai dan uwana ne yabaki wajen Kuma mahaifi ne agare su. "

"Sai Kuma kayi. Duk wadannan zubar maganar da kake kamar rubabbiyar bishiyar kanya ba damuna take ba kaji na gaya maka. Abunda na sani wallahi summa tallahi idan akayi window a dakin nan sai kasha mamakin abunda Zan aikata narantse da Allah sai kayi dana sanin sani na"

"Ko? Yo zan nuna Miki ni ne mijin ni ke auren ki ba kece ke aure na ba. A karkashina kike. Kina wani tunkaho kina chatting da matan manya kina hada kanki da su. To bari na tuna Miki Naduka mu zuwa mukai, Baki ne ba anan aka haife mu ba. Kuma mu ba kowan kowa bane bamuda ko sisi. A baya munyi dukiya a bunza a zuriyar mu ta hamidniyya lebanon Wanda ke bakya ciki ma. "

"Yanzu ka fito da abunda yake ranka Auwalu. Gorine Allah na tuba ba yau ka saba ba. Naji bani acikin zuriyar ku ta hamidniyya Lebanon Amman Nima nawa jinin ba matsiyata bane. Allah na tuba kuda kuka Tara dukiyar yanzu Ina fake eh? Mutum ya dinga sanin maganar da zai fada ba'

"Ke dalla can sakarya. Wadda ke bude baki waaaa tana zuba agaban yaran data haifa. Allah ya jikn Hindu a ranar da zata rasu ma sai data Miki nasiha ki kula da yaranta Amma baki daya kinyi fatali da zacen ta"

"Haba nagaji ya ishe ka haka. Hindu Hindu Hindu Hindu kullum dai ba gajiyawa"

"Hmm. Faccalanci dai ba hauka bane. Wannan rashin hankalin naki tun kina amarya na daukar faccala kamar kishiya ba Zaki sauke shi ba. Ace mace ta mutu ma Amman baki dai na kishin faccala da ita ba. Bayan ita bata zauna dake a faccala bama sai yar uwa.. Allah ya wadaran halayar kishin ki ta faccaloli datafi ta kishiya wannan hauka ne. Duk wannan tsanar da kike wa halainta daga nan ta farko. Saboda ta fiki da komai ko. Ta futo a tsatson manya tsatson mu daya sannan anmata kaya na yar manya lokacin bikin su. Sannan tanada kashin samu da yalwar arziki a komai ta kere ki shine dai kike wannan abubuwan to Allah ya kyauta. Ace ta rasu ma Amman kin cigaba da bakin kishin faccalar ki akan yaranta. Suma abin Yana bi su. Allah ya kyauta."

Nawraah da fadan su ya isheta ta jima daki ta dauki hijabi ta zura ta rike hannun Amnah zasu fita nusaiba tace,

"Kagani ko? Yanzu wannan ita zataje haka? Ni fa ban yadda da wannan yawon naki ba kina wani rike hannun Amnah."

Layla ta mike zatabi bayan Nawraah. Nusaiba ta janyo ta ta bayan rigarta ,

"Ina zakije? Ba bu inda Zaki bita. Koma ki zauna ba Zaki koyo wannan halayyar tata ba ta fita gaba gadi kullum a titi ",

Bappah junaidu daya kasa magana saboda tsananin bakin ciki kawai ya durkusa ya gyara zaman takalman sa ya shige cikin gidah

Nusaiba tabi bayan Nawraah da harara tana yatsina fuska tana gatsine gatsine .

Ko da Nawraah suka futa tsayawa tayi ajikin bango tana kife kanta hawaye ne masu dimi suka shiga zirara daga idanun ta na bakin cikin kalaman nusaiba.

"Kenan zargina take? Zargina take Ina aikata wani abun awaje kenan na haramci! Yaushe nake fita nida kullum Ina gidah? Yaa Allah kana gani Allah ka mun sakayya. Allah ka dubemu ka saka mana. "

Ta share hawayen ta ta cigaba da tafiya tana rike da hannun Amnah. Baki daya ta gama tsorota da halayen nusaiba. Ta Kuma gama yanke kundurinta kawai

"Ko guduwa zamuyi mu bar garin? To muje Ina? Ko mu rama abunda take mana mu fasa window ta karfi? Kai Yaa Allah Yaa Allah" ta karasa fada tana dafe kanta dake mata tsananin ciwo

Suna ta tafiya har zuwa Naduka crescent. Suka tsaya awani shago ta dakko nera hamsin din wajenta ta sayawa Amnah biscuit da alawa kamar Koda yaushe. Ta kan Dan fitar da ita haka su sha iska saboda dakin da suke babu window. Gidan su nusaiba Kuma da sunje shan fanka take fara hararae su. Shysa Nawraah take dan zagawa da Amnah su sha iskar Allah ta waje. Ko Amnah taji dadin jikin ta. suka cigaba da tafiya..

Tana daga Kai ta sauke akan dankareriyar jami'ar nan da akace sun samu gurbin karatu ta Al-Haramein Naduka.

Tsayawa tayi sosai tana yaba kyawu da tsaruwar ginin na makarantae. Sai kache a turai.

Manya manyan gidaje ne na masu kudi a layin harda gate dinsa layin . Ya hadu kwarai matuka layin dan Bata taba zuwa nan haka ba ta shagala tanata kallon ko'ina lungu da sako.

Kallon ta ya sauka akan tankamemen wani katon gidah an rubuta masa NADUKA GRAND ORPHANAGE PALACE a kasan Kuma an rubuta (Gidan Marayu) gidan marayun na kallon wani sugnoard da taketa tunanin a inda tasan sunan wato DR. ABUBAKHR DOLLARS DWELLING....

Zuciyarta da gangar jikinta nata ingizata ta shiga cikin katafaren gidan marayun janye da hannun Amnah. Ga mata nan Yara da manya harda Wanda ake rikewa a hannu Kuma duk marayun ne.

Ga Kuma wani bangare daga hagu can an saka wasu manyan wayoyi na karfe anyi Katanga an rufe wajen maza ne can kuma bangaren su

Da sauri ta shiga cikin reception/waiting area. Sukaga matar in charge of wajen Nawraah ta karasa ta gayshe da ita hakama Amnah

"Meke tafe daku Yan kanne na?" Matar ta tanbaye su.

Nawraah ta dan sunkuar da kai tana lankwasa Yan yatsunta tace

"Marayu ne iyayen mu sun rasu da babban wan mu. Daga ni da kanwata sai dayan yayan mu muka rage. Bamuda wani sauran gata da yarage mana. Shine Allah yasa na biyo nan yankin haka naga nan gidan marayun. Bansani ba ko kuna daukar marayu ko Yaya a abun yake?"

"Allah sarki Allah ya jikan su da ra rahama. Daga wace ungeua kukazo kenan?"

"Aameen Yaa rabbi. Daga Naduka zone muke"

"Okay to .. bakuda wasu Yan uwa ne haka da sauran su?"

Nawraah tayi shiru tana tunani. Wane yan uwan Zata ce bayan yan uwan nasu sun juya musu baya. Da su da babu su duk daya ne. Bappa Auwalu ne Kuma yayi iya yinsa, matar sa tafi karfin sa. Shi ma Kuma bashida halin da zai iya rike su, da sauri tace,

"Ba muda kowa. Duk sun rasu dama daga birnin bunza mu kazo da iyayen mu Kuma daya bayan daya cikin kankanin lokaci duk suka rasu kowanne ba rata da daya sosai "

"Allah ya rahama musu"

"Aameen yaa rabbi"

"Abunda za ai shine. Kuje kuzo da yayan naku da kayan ku kawai. Din yanzu ma ba paper da form da sauran su.."

"Toh inshaa Allah"

"Nagode sosai. , bari muje"

Nawraah ta mata sallama suka fita. Sunzo zasu wuce ta kofar signboard din gidan dazu taga wata zungureriyar mota da alama kaya ne aciki, sai wasu biyu masu matukar tsada da fara da blue hadaddun motoci, sun bi bayan babbar motar suka nufi gidan dataga signboard din DR. ABUBAKHR DOLLARS DWELLING. Motocin suka tunkari gate din da alama mutanen gidan ne sukayi tafiya suka dawo alokacin.

Tayar dayar motar bayan ta sache alokacin direban ya kasa jarasa shiga da motar gidan. Gashi sauran motocin ba dama su shiga. Motar ta tokare...

Wata kyakkyawa mata tafito daga cikin bayan motar owners corner tana gyara mayafin ta..

Bayan tafito ne wani matashin saurayi shima ya futa daga bayan moyar Yana latsa wayar hannun sa.

"Anees...." Matar takira shi da alama mahaifiyar sa ce saboda tsananin kamar da suke.

"Naam Mami"

"Yi sauri mu shiga mana. Ka tsaya. "

"To mami"

Yana biye da ita a baya suma yan sauran dayar motar suka fito daga ciki. Harda babban mutumi. Kana gani kasan mahaifin su ne. Yana tafe da waya a kunnen sa yana amsawa.

Can kuma sai ga mace da namiji suma da Nawraah take kyauta zaton Yan gidah daya ne. Saboda suna kama.

"Anees, junior meye haka kuzo mu shiga gidah mana. Ke Hayfa duba bayan mota na manta USB cord na ki dakkomin "

'Anees, Junior, Hayfa...." Nawraah ta shiga nanata sunayen su tana waywayawa baya har suka shige cikin gidan su.


Itada Nawraah suka dauki hanyar gidah a filin ball taga Ashfef Yana buga karasa ta sanar da shi duk abubuwan da akayi tundaga gidahn Bappah Auwalu da nusaiba ya zuwa gidan marayun data gani. Kan zasu koma da zama nan

Ashfeef bayi musu ba. Yayi addu'ar Allah ya zaba musu abunda yafi alkhairi idan zaman dakin tumakin ne alkhairi Allah ya zaunar da su idan kuma tashin su ne Mafi alkhairi Allah ya hada su da Mutanen kwarai

Suka koma gidah Nawraah ta fara hada musu kayan su ta gama tsaf. Asubar fari suka bar gidan suka nufi gidan marayun...


*ALHAJI SAMBASO AVENUE*

Shirye shiryen dawowar yaran Dr bintu takeyi. Kowanne da irin abincin da yake so..

Karfe hudu na yamma jirgin su ya sauka..direba yaje ya dakko su

Matashin saurayi ne mai jini a jika. Wanda mahaifiyar su Dr bintu ta nufe sy tana musu lale marhaban..

Marwan ya rungume mahaifiyar tasu Yana murmushi. Harda kunan Dadi. Lily kuwa ko ajikinta ta yi murmushi kawai tana yrigzia Kai.

:;;
..... Bappah Auwalu ya nemo su Nawraah Yana rokon su dawo kusa da shi Nawraah tace gaskia zaman su ya kare agidan nan. Yana rokon sa suna rokon sa ya kyale su

Domin dakuna ne da gado hudu a dakin gidan marayun... Kowanne daki

Itada Amnah kowacce da gadonta sai Kuma wasu yammata suma guda biyu suma da gadajen su. . Da tv dinsu harda fridge mashaa Allah ga fanka da ac, ac din kunnawa ake a kashe idan tayi awa biyu. ..

A dole bappah Auwalu ya hakura ya barsu Amman sai da yayi hawayen nadama musanman kasancewar matar sa Nusaiba itace silar komai, komai ya baci da 'yayan dan uwan nasa shakikan sa...

Haka ya hakura ya koma gidah zuciyar sa na kuna...

Ranar lahadi su Nawraah da Layla suka sukaje kasuwa suka dan sassayo kayan gwanjo.saboda zuwa school .

Suka shirya tsaf. Layla ta bugawa Nawraah suka nufi makaranta ranar washegari..

*Al-Haramein university*

Baki daya kusan rabin daliban tsayawa sukai suna kallon su Nawraah suna musu dariya. Ganin Shigar su daa kallo daya zakai musu kasan talakawa ne.

Cikin haka suna shiga ba dadewa sai ga motocin biyu sun shigo ta ciki suna yar tsere. Dalibai aka taru akan su. Motocin ma kadai abun kallo ne.

Saura kadan ya Nawraah data tsaya tana duba jakarta . Ya fito a harzuke Ya daddanna mata horn taki matsawa, ashe bataji ba hankalin ta ya tafi kan Jakarta, Yan kudin ta naira dari da Ashfeef ya bata taci abinci ne bata gani ba.

Futa yayi da niyyar mata magana a tsawace. Marwan ya futo da sauri daga tasa motar Yana rike hannun anees daya yiwa Nawraah nuni da yatsa Yana dubanta. Yasan shi da zuciya.

"Ke daga fuskar ki, How dare you? Ba ki gani ne ko ke bebiya ce. ?"

Nawraah ta daga Kai jin an mata magana kanta a kasa sa, don Sam bata ji ko gansu ba sai alokacin, hankalin ta baya jikin ta. Cikinta nata kugin yunwa..

Tana dagowa suka zuba mata idanu atare. Anees ya nemi abunda zai fada mata a abakin sa ya rasa. Haka Marwaan daya kasa hakuri ya lankwasa kansa Yana dubanta.

Tayi musu matukar kyau fiye yadda alkalami zai rubut. Rakabewa tayi ta gefen su ta wuce, ganin sun mata shiru...

"Senior man na nayi new catch ta. Ina Kai nayi mata ma ni wannan yarinyar kallo daya tatafi Dani, zan auretaa" Marwaan ya fada Yana shafa keyar sa

Anees Yana so yace shima ya fara jin wani ahu akanta sai Kuma yayi shiru jin abunda Marwan ya fada. Don dama ba iya magana zai yi ba haka halin sa yake. Kuma bayason wani ya hadasu da abokin sa, kasancewar iyayen su aminai ne suma Kuma aminan juna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login