Showing 30001 words to 33000 words out of 66781 words
ta nana a cinyarta tace,
"Auwalu kenan.. inbanda matsalar gida data fara bada matsala idan baa gyaraba damuna zatai gyara shine kake tunanin tun safe ka fita nema? to namiji ai da nema aka san shi ba zama agidaah ba kamar mace. Mace ce akasanta agidah. Dole ne namiji ya fita ya nemo ya bata. Duk mazan kwarai haka suke idan ka tsame kan ka. Har ni zaka cewa yaushe zanyi hankali Auwalu? Ai babu mai hankali da zata zauna da Kai wallahi kaji rantsuwar Allah. Duk nace mai hankali ishasshe data san mutinci da daraja ta ya mace wallahi ba zata zauna dakai a matsayin matar ka ba. Domin kuwa ta gama tabewa. "
Mtsceww, Tsceww, Mtw... Ya saki tsaki har Kaso uku a jere. Ya dubeta cike da tsananin bacin rai yace,
"Duba kiga ni... Kaf birnn nan kadan ne inda ban zagaya ba Ina neman rance na kudi da zanyi wannan gyaran na rasa. Har sauran yan uwa na Kira a waya kowannen ya bani uzurin sa kan babu. Wanda dai banason gayawa din saboda kowane hali yake zaije ya nemo wallahi kafin nace ya samomin ma don munyi maganar gyaran amman bance inaso ya nemo mun ba wallahi sai gashi yazo da kansa dauke da kudin ya kawo mun fiye da adadin yadda nake bukatar ma. A duniya idan ban godewa junaidu ba wa zan godewa! Kaf Yan uwana babu Wanda keda zuciyar Yan uwantaka da dinbin zumunci irin junaidu.." ya karasa fada yana mai zama akan kujera hadi da dafe kansa da hannuwan sa biyu ya tallabe.
Leka ledar tayi idanuwanta suka sauka akan farare kal bugun Abuja .. Ta silale ta zauna a kusa da shi hadi da saka hannu ta janyo ledar sosai ta buda ta hango bandir din dubu dubu mash tarin yawa.
Jikinta har rawa yake ta dau bandir daya tana gwalalo idanun . Bappah Auwalu ya wafce kudin ya rike ledar a hannun sa yana kallon ta
Nusaiba akwai makirci nan da nan ta kwabe fuska ta rausayar da Kai tana jan kasan jelar gashin ta tace,
"Naga ranka ya baci akan maganganun dana fada . Kayi hakuri kuskuren harshe ne... Bazan sake ba"
Bappah Auwalu yayi murmushi kawai ya gano ta sarai. Amman saboda tsabar sonta ya rufe masa idanu kawai ya girgiza kai,
"Allah yása mu dace Amin"
"Aamin..yanzu yaushe zaai gyaran gidan"
"Ko gobe ma inshaa Allahu.."
"Auwal......" Ta Kira sunan sa irin yadda take Kiran sa tun suna saurayi da budurwa.
Yana jin sanda ta kira shi ya sake murmushi kawai, don Sam bata Kiran sa da haka sai idan ya samu kudi tanason ya bata wani abun. Don rabon data kira shi haka tsakani da Allah tun suna saurayi da budurwa da Kuma farkon satinnai na auren su
"Auwal magana nake maka"
"Auwalu nake Nusaiba "
"Nusaiba gatsal? Kai ma kadan saya mana... Nusyn Auwal... Ko ka manta wakar tamu ne da muna saurayi da yammata?"
Mikewa yayi zai tashi ta mike itama tana riko hannun sa
"Ka tsaya kaci abinci mana Ina zaka?"
"Wanka zanyi Nusaiba. Ki kyale ni"
"Aa bari adan kashe sanyin ruwan yanzu. Sai kayi kaci abinci kaji. Zauna mana"
Komawa yayi ya zauna Yana grigiza Kai. Nusaiba akwai ta da salo kala kala duk yadda yask yaki biye mata hakan yaci tura.
Don bayan da ta dafa ruwan yayi wanka. Ta zuba masa abinci yaci. Haka ta dinga jansa da hira har yaran su da ta aika siyo gawayi suka dawo. Su kansu Layla sunyi mamakin ganin iyayen nasu zaune suna hira.
Nan suka zauna suma anatayi da su. Yake gaya masu ya samu kudin da zaa gyara musu gidan sunata murna.
Har lokacin kwanciya bacci yayi Layla ta nufi daki ta kwanta. Nusaiba ta tasa bappah Auwalu suka tafi daki. Yayinda Ahmad ya dakko katifar sa ya saka a parlor ya makala net ya kwanta...
Duk yadda bappah Auwalu yaso zillewa haka ya hakura ya bada kai bori ya hau. Dole sai da Nusaiba tasaka ya saya mata waya da ake latsa ta wato torch screen ta yan gayu.
Sai wani yauki take tana rike da wayar duk inda zata.. Yan layin nasu kowa ya sheda tayi wayar masu kudi
Har gidan bappah Junaid ta shiga tanata fiili da wayar a hannunta. Lamarin ma daria ya bawa Malama Hindu. Don sarai tasan da kudin da aka bawa bappah Auwalu ne zata tursasa shi tasa ya saya mata wayar adole...
============
Toh haka rayuwar ta cigaba da kasancewa. Kowanne bangare ana samun cigaba musanman gidan bappah Junaid.
Su Nawrah sunyi sauka mashaa Allah. A Kuma shekarar ne su Bappah sani zuka ziyar ce su
Inda bappah sanin ya Kira meeting duka Yan uwan suka taru. Akayi magana kan matsayar karatun yara matan na boko.
Lalle burin Nawraah ya cika duk kuwa da makaranta ce ta gwamnati zaa saka su tayi murna kwarai matuka don har hawayen farin ciki tayi.
Dakyar aka shawo kan bappah Junaid daya ki amincewa kan wasiyyar yafendo ce yara mata kar suyi boko. Nan yan uwan nasa suka wayar masa dakan ba haka tace ba. Tace dai ga yaran nan kar dai amatsa Idan Kuma rayuwa ta sauya to sai abita da yadda tazo akuma yi addua...
Don a rayuwar da suka samu kansu Idan Yara matan basuyi bokon ba Koda kadanne to akwai natsaloli da zasu fuskanta masu tarin yawa musamman da yanzun sabuwar rayuwa ce suke ginata wadda suka shiga ta zama a birnin Naduka garin yan boko da wayewar kai....
Lamarin ya cigaba da tafiya yadda ya kamata Alhamdulillah lalle Allah qadirun ne ala manyashau.
Su Nawraah an fara zama yammata yanzu sosai cikar budirc ta fara bayyana atattar da su. Wani irin musulmin kyau ne ke kara haskakata.
Wanda wani lokacin saboda tsabar maza samari dake cewa ana sallama da ita gata da kananun shekaru hakan yàsa ummyn ke cewa ta dinga saka niqab idan zata futa.
Unguwa ma sai aka dena zuwa da ita ba kowacce ba. Don hajia qibdiyya ma tayi tayi taga yaran, ummy tace zasu zo mata In shaa Allahu nan da wani lokacin idan komai ya dai dai ta...
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[2/27, 11:26 AM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_23_
_DR. ABUBAKHR DOLLARS DWELLING:_
Bakın ta dauke da sallama ta shiga cikin gidan bayan Malam Liti direba ya sauke tah.
Ja tayi ta tsaya alokacin da basariya ta bude mata kofar parlorn ta shiga, Sakamakon manyan akwatinan data gani a parlorn an ajiye su.
“Hajiyan na sama ne?” Malama Hindu ta tambayi başarıya mai aiki
“Tana bangaren baba yanzu zata dawo amma ai tafiya zasu yi ma.”
“Ah tafiyar ta tabbata kenan? Mashaa Allah Allah yasa aje a sa’a. Kafin ta dawo bari na rage wani abun” kitchen ta shiga ta zare hijabin ta ta rataye shi a maratayi, ta dauki rigar girki ta zura ajikin ta.
Nan da nan ta shiga hada girkin su Hayfa, kasancewar yanzu ta gane kowannen su abincin da yafu so dan haka Kowanne tana dafa masa daga cikin cimar sa iyakar bakin kokarin ta. Kuma yaran suna yabawa sosai suna jin dadin girkin ta..
Tana çıkın aikin ne Hajia qibdiyya ta dawo sashen nata bakin ta dauke da sallama.
Malama Hindu ta fito daga kitchen tana goge hannunta da tissue kafin ta jefar acikin dustbin ta tsugunna tana gayshe da ita.
“Da Allah tashi Hindu. Nace ki dai na tsugunnawar nan Allah. Yaushe kikazo? Ina wajen baban su ne.”
“Ban jima can ainun ba dai. Eh haka başarıya tace mun da nazo ta bude mun kofa. Har na dubi akwatinan ma nace Allah sarki Hajia tafiyar ta tabbata kenan?”
“Wallahi kuwa Hindu. Tafiya ta tabbata inshaa Allah. Sai gobe da daddare ne amma jirgin mu zamu tashi yanzun dai nace akai akwatinan booth na mota kar mu wasu abubuwan manta”
“Hakane kam gaskia don tafiya tagaji haka. Toh Allah ya tabbatar da alkhairin sa yasa kuje a sa’a yasa ki sauka a sa’a Amin”
“Aameen Yaa Hayyu yaa Qayyum. Godia nake kwarai Hindu. Dan Allah Idan kin gama aikin ma zan aike ki gidan wata kawata ko ince yar uwata ma don mun zama yan uwa, matar aminin mijina ce. Malam liti zai kai ki please”
“Tohm Hajia bari na kammala. Yanzu”
“Yauwa eh zan baki daya wayata ma sai ki tafi da ita ki dakko samfarin kayan hotunan su. Kaya ne ta kawo zamu zuba a store . To wasu sunyi extras haka double shine zaku daddauka da kuma rubuto jerin samples “
“Toh Hajia amman dai daukar hotan ne dai da duk ma abunda za’a iya miki ta wayar wallahi ban iya ba kasancewar bana rike da babbar waya. Amman Idan ba damuwa sai mu biya na dau matar yayan mijina taşan kan waya Idan kuma Nawraah sun dawo daga makaranta ma sai muje da ita”
“Toh shikenan duk yadda kukai ba damuwa. Ai kuwa yakamata ace kin fara amfani da babbar waya Hindu. Daman wayar ba wani amfani nake da ita ba sosai saboda inada ipad da ita nake amfani. Inshaa Allah Idan kika dawo na kwashe komai na kai sai na bar miki. Ma dinga vedio call Idan na tafi inshaa Allah”
“Nagode Hajia, Nagode Allah ya saka miki da alkhairi Allah ya biya miki dukkanin bukatun ki na duniya da lahira Allah ya saukeki lafiya Allah kuma ya raya miki yaran ki ya iya miki ya daga ki amin.”
“Aameen Yaa rabbi Hindu. Jam’an inshaa Allahu”
“Bari na karasa girkin sai na zo”
“Tohm Hindu. Nima bari na cire rigar nan na saka marar nauyi….”
“Tohm Hajia”
Hajia qibdiyya ta haye sama dakin ta. Ya yinda Malama Hindu ta koma kitchen ta cigaba da girki.
Nan da nan kuwa cikin ikon Allah ta karasa duka girkunan abincinnan data yi na Junior da Hayfa da kuma Anees.
Ta jere musu kulolin abincin akan dinning ta dakko plates da serving spoons da fork da komai dai ta jera musu kowanne sannan ta shiga dakin hutawar su tayi wanka hade da dauro alwala ta mayar da kayanta. Sannan ta hau kan sallaya jin ana kiraya kirayen sallar azuhr ta yi sallah hadi da addu’oin ta..
Sannan ta mike ta gyara zaman hijabin ta ta fita... Ta nemi gefen carpet ta zauna tana jiran sakkowar hajia qibdiyya.
Bata jima sosai ba da zama hajiya qibdiyya ta sakko daga saman sanye cikin kaya marar nauyi.
"Hindu har kin kammala?"
"Na gama hajiya. Ya jikin?"
"Alhamdulillah Hindu"
"Zaa karbi sakon yanzu ne?"
"Eh, Amma kinci abinci ne? Kici abinci tukun ko?"
"A koshe nake hajia"
"Wane irin a koshe. Ki ce dai idan kika dawo zaki ci banason musu Hindu"
"Tohm hajia inshaa Allahu... Nagode Allah ya saka da alkhairi "
"Ba godia a tsakanin mu Hindu. Yauwa ga wayar na cire password"
"Tohm" ta saka hannu biyu ta karbi wayar tana riketa da kyau
"Wayar ki ce fa atoh ki kalleta da kyau"
Malama Hindu tayi murmushi tana jujjuya wayar a hannun ta. Hadaddiyar waya kallo daya zakai mata kasan me kyau ce da tsada kuma.. Samsung ce latest design.
"Nagode sosai hajia. Allah ya biya miki dukkanin bukatin Ki. Yadda kike faranta mana Allah ubangiji ya faranta Miki. Ya sauke ki lafiya Amin"
"Aameen Yaa Rabbi Hindu"
'B'it pi'pi' pit B'it' Malam Liti ya nata danna horn ta motar.
Malama Hindu ta fita da sauri tana rufe kofar parlorn ta shiga motar da sauri malam Liti yaja suka futa daga gidan,
"Mu biya ta gidah zamu dau Nawraah da zata dakko hotunan sakon da hajia ta ce"
"Okay tohm"
Naduka zone ya nufa da motar tasu. har kofar gidan su malama Hindu ya sauke ta.
Ta shiga da sauri tana kiran Nawraah. Nawraah da bata jima da dawowa daga makaranta ba tana zaune a parlorn su tana karanta wani littafi na 'computer science'
"Naam ummy"
"Ina Amnah?"
"Sun fita da Hamma"
"Okay! Maza shirya ki mun rakiya zaki dakko wa hajia qibdiyya wasu hotuna. Da wayar nan rike ta ma tace ba password."
Nawraah ta karbi wayar tana zura hijabi,
"Tohm ummy "
A tare suka fito daga cikin gidah sukayi kicibus da Nusaiba tana tafe tana yamutsa da wayarta a hannu. Suka tsaya suna gaysawa tana daga wayar hannun ta ummy dai tayi murmushi kawai...
"Fita zakuyi a motar can?" Nusaiba ta tambaye su tana kallo motar da malam Liti ke tukawa hadaddiya sai sheki takeyi.
"Eh futa zamuyi "
"Ungo Nawraah dan dauke ni anan wajen motar haka ki tabbatar ta fito"
Nusaiba ta karasa fada tana gyara tsayuwar ta ajikin motar.
Nawraah ta karbi wayar ta yiyyi mata hotunan. Ta mika mata. Nusaiba ta karba tana duba hotunan tana murmushi.
Suka bude motar suka shiga ciki ita Kuma ta koma cikin gidah tana sake zooming hotunan tana murmushi musanman da motar ta dache da ita kamar ta ta..
Ta daga Kai ta dubi gidan su ranta ya sosu sam bata kaunar zaman ta agidan dan tafi son gidan nasu kudi inama ace ita mayar mai kudi ce, ta fantama inda take so acikin shiga ta alfarma da hawa manyan luntsuma luntsuman motoci da masu aiki suna take mata gaba da bayan ta...
"Nusaiba Ina kokon?" Ta jiyo muryar Auwalu ta doki dodon kunnen ta
.
Ta yamutsa fuska tamkar yana ganin ta cike da kufulewa tace,
"Dan Allah ni kakka ishe ni. Koko! Koko! Koko sai kace a karkara" ta tabe baki ta shiga cikin gidan...
:::::
Babu nisa ainun suka karasa unguwar da gidan aminiyar ta hajia qibdiyya. Dankareren sign board ne an rubuta da manyan baki...
*ALHAJI SAMBASO AVENUE*
_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_
_KU MARMATSO KUSA...🔊_
_ZAFAFA BIYAR 2024_
_ZAFAFA BIYAR!!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_ZAFAFA BIYAR!!_
_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_
_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_
_GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_
_________
_1_
*_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_
_2_
*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_
_3_
*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_
_4_
*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
[2/28, 2:22 AM] Hafsaat🧕: _K'K'J_
_(M/W/S)_
_✍️:MX_
_24_
:::::::::
*ALHAJI SAMBASO AVENUE*
*Wani * tafkeken gidah suka nufi gate din sa.. Manyan masu gadi majiya karfi a mummurde su biyu ne suka taso sukayi kan motar da malam Liti ke tukawa ganin ya tunkari gate din..
Ja yayi ya tsaya da motar. Masu gadin suka leka suka saka ya bude har booth dinsa tukun sannan dayan ya janyo wata aba kamar rediyo baka ya koma gefe Yana magana. Can ya dagawa dayan me gadin hannu ya koma ya zauna
"Ku shiga" Ya fadawa malam Liti Yana rufe masa murfin booth.
Malam Liti yaja motar Yana zakin siririn tsaki yace,
"Na tsami zuwa gidan nan yadda kikasan gidan gwamna wallahi tsare tsaren su yayi yawa. Sun san nafi shekara nawa ko muzo da hajia ko ta aiko ni ni kadai amman masu gadin nan sai sun tsayar dani..."
"Kayi hakuri. Inaga yanayin aikin nasu ne yazo da tsauri haka" malama Hindu tace da shi
"Allah ya kyauta kawai. Abun nasu ne yayi yawa kam"
"Ayyah"
Ita dai nawrah na zaune tana raba idanu. Ta saba ganin hadaddun gidaje a dramas da labari idan ana basu. Amman bata taba ganin gidah me kyawun wannan ba..
"Allahumma arzuqniy" ta fada tana sake duban gidan alokacin da suka shiga harabar gidan da mota
Malam Liti ya nemi wajen parking ya faka motar. malama . Hindu suka fita da ga ciki ta riko hannun Nawraah dake kalle kallen gidan.
Murmushi malama Hindu tayi tace,
"Ai gidan hajia qibdiyya yafu wannan kyau fa? Su gate dinsu da kansa ma yake budewa Nawraah"
"Mashaa Allahu sunji dadin su"
"Mashaa Allah! Kuma Allah ya Kai ku inda zakuje ku huta sa kwanciyar hankali Amin"
"Toh Aaameen.. Amma ummy samun irin wannan gidan kan nasan ko a mafarki"
"Yi sauri kitchen astagfirullah. Waye me azurtawa?"
"Astagfirullah Allah ne"
"Waye me talautawa?
"Allah ne"
"Waye me bayarwa"
"Allah ne"
"Waye mai rayawa"
"Allah ne"
"Waye me kashewa? Ya bayar asan da yaso ya hana asanda yaso"
"Allah ne"
"To ki yi maza ki roki gafarar Allah mumini baya yanke rai ga rahamar ubangijin sa. Allahn daya basu bai manta da mu ba kina ji na?"
"Astagfirullah... Eh Ina jin ki ummy "
"Shysa a har kullum ake son ka kalki na kasa da Kai kada ka kallo na sama da kai lalle idan ka kalla na kasa da Kai Wanda ka fishi komai tanan zaka Kara godewa Allah da rahamar da yayi maka. Nawraah wasu suna nan basu da matsugunin da zasu zauna Ina nufin gidah.. wasu basu da abincin da zasuci bara suke. Nawraah wasu suna nan kayan da zasu saka ma basu da shi sutura tayi karanci Nawraah. Wasu Kuma suna asibuti ma sai dai a kwantar a tayar basusan Wanda ke kan su ba. Wasu ma hankali ne basu da shi