Showing 75001 words to 78000 words out of 86608 words

Chapter 26 - DIDDIGAR ƘAYA COMPLT Hausa novel

21 Aug 2024

18458

motarshi Farhan ya buɗe, mammi na riƙe da Fa'iza da ta sake sakin kuka itama tana jin kunar wannan abu a ranta kaman tayiwa Fauza kuka, me mutanen nan suke nema da ita?

Amminta ma komawa sashensu tayi tana me share hawaye, jaddah kam driver ta sa ya ɗauke ta ta bi bayansu tana ta tsinewa Fatima da Aunty Albarka.

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤




32

**Assalamu Alaikum warahmatullah, fatan duk muna cikin ƙoshin lafiya, kun jini kwana biyu shiru nayi tafiya ne kuma ban zauna ba har saida na dawo jiya da dare, kwata-kwata ban samu time ɗin kaina ba se yau... Ku yi hakuri kaman yadda na yi alkawari kan azumi zan karkare wannan littafi wadda be dayawa saide na tabbatar saƙon ciki me girma ne in ka fahimta..

Abu na biyu shine KE WACCE KIKA SAYI LITTAFIN NAN MUSAMMAN DON FITARWA BA ZAN CE MIKI ALLAH YA ISA BA SAIDE IN CE KIN KYAUTA KE KIKA SANI DA FITAR RANA DA FAƊUWAR SHI IN HAR INA DA HAKKI A KANKI***

Suna fita a gidan da wannan mugun gudun basu yi wani nisan kirki ba ta ruftawa wani kwalbati duk jikin ta rawa yake na abunda ta aikata, ihun Aunty ne ya farkar da ita sama sama take jin mutane na cetonsu, basu sake sanin inda kansu yake ba se kusan bayan awanni shidda, Allah ya taimaka babu wani serious ciwo suka biya kuɗin bills suka fice, ita dae Fatima takaici da bakin ciki sun hanata cewa komai, kawai machine suka tare suka nufi gidan iyayen Aunty ɗin inda a duniya bata taɓa ƙauna ba, ta tashi ne da baƙin cikin kasancewarta ƴar talakawa Dukda iyayenta nagartattun talakawa ne masu kokarin kiyaye dokokin Allah saide ita kullum a blaming ɗinsu take na kasancewar su hakan tun kan tayi wayo ta san karyar kuɗi da bin ƙawaye ƴaƴan masu kuɗi, da wasu irin banzan buri, ta auri mahaifin Fatima wadda bashi da irin kudin da take so, sbd in ta zauna babu wadda ze Santa ta zama sannaniya wacce duk inda zata shiga a ƙasar Nigeria an san da zamanta yasa ta kashe auren bayan dogon bincike akan gidan prof, shine ta aure sulaiman dukda ba hakan ta so ba saide babu yadda ta iya, gashi yanzu zata komawa rayuwar da ta fi tsana nan duniya.

Da sallama suka shiga gidan nasu da rabin shi a zube an kare da buhu duk jar ƙasar gasu nan a barbaje ko ta ina, idanun Fatima ne ya fara kaiwa ga mawanki kwanuka ne a wurin da wasu irin bakaken tukwane waenda zan iya rantsuwa tunda aka saye su basu taɓa ganin ruwa da sunan wanki ba, kuma duk sbd rashin kuɗin sayan omo ne.

Aunty ne ta kai idanunta kan dakunan gidan guda biyu banda jar block babu abunda ke jikin ginin ko arzikin Plaster bare fenti, kuka Fatima ta fara
"Aunty kina nufin anan zamu cigaba da rayuwa?"

Aunty tace
"na lokaci kaɗan ne kan mu samu mafita"
Tana maganan ne kaman itama zata yi kukan, kanta Sara mata yake sbd tsabar tashin hankali.

Maihaifiyartace ta fito kana ganinta kaga wahala da talauci ta zuba musu idanu tana kallo..

"Yau kuma shamsiyya da mu kika tuna?"
Kuka ta fara tana cewa
"inna Sulaiman ya sake ni!"

"Ashe muna da daraja da ƙima da har don an sake ki zaki waiwayi gidan nan? Mu da kike jin kunyar nuna mu a matsayin iyayen ki? Mu da duk yaran da kika haifa bayan wannan itama na manta shekarar da na ganta akwai wadda kika taɓa nunawa gidan nan bare mu? Shekara nawa Shamsiyya ki ci ki sha ki kwanta ba tare da mun zo ranki ko sau ɗaya ba? Aurenki na biyu fa hayan iyaye kika yi kika yi wannan aure hidimarki saide ƙawaye en karya da dangin su a haka dama kike son ganin alkhairi? Ba zamu kore ki ba ga ɗaki shiga ki zauna duniya ce ta fi bagaruwa iya jima"

Wucewa suka yi suka shiga fallan ɗakin da babu komai ciki se buhu a shimfide suka zube, kowa da abunda yake sakawa ita dae Shamsiyya Tunanin ta yafi tafiya ta yadda zata dau fansar wannan wahalar da ta sha, yayinda ta wani bangare take Adu'ar Allah ya sa ma wannan fitinanniyar yarinyar da ta tsole musu idanu ta mutu ma kan su isa asibiti.

****

Ta ɓangaren Fauza kuwa emergency aka yi da ita, Faizan ya kasa zama se jeka ka dawo yake yi hannunshi ɗaya dunkule yana dukan ɗaya dake ware, kusan duka en gidan zuwa yanzu sun iso har da su Prof da abun be faru a gabansu ba, saida likitoci suka share awanni sama da huɗu kan suka fito suna yarfa gumi a tsorace Faizan ke Kallonsu bakinshi ya gaza furta kalma ko guda ɗaya ne..

"Dr kayi magana mana kayi shiru?"
Cewar Farhan.

"Alhamdulillah mun samu mun ceto rayuwarta ba serious ciwo bane in shaa Allah, tsorata ce ta saka ta wannan doguwar sumar"

Duk ajiyar zuciya suka sauke, Faizan be jira wani bayani ba kuma ya wuce likitan ko jin kiran da yake mishi be yi ba ya tura kofan ya shige.

Tana kwance kan gadon ya karasa kaman ze zubda mata hawaye tsabar tausayi ya riƙe hannunta yana shafa kanta bakinshi ya buɗe a hankali ya fara magana
"kiyi haƙuri precious pearl I couldn't save u from that bastard attack, am so sorry da kika kasance a haka in front of my eyes... Please be fine kin ji? Just be fine ki yafemin and I promise you a happy life that will last to end"

Dukawa yayi yayi pecking goshinta yana kallon lips ɗinta da babu komai a kai se ainihin red nd black color ɗinsu da suke sarƙe cikin juna suka bada wani kala me kyau, babban yatsarshi ya sa ya shafa lip ɗin yana ta aikin kallonta a ranshi kuma yana ayyana yadda ze fara neman Fatima ya koya mata hankali don bata sha ba.

Idanunshi zube a kanta ya tafi tunani, ya sani lokaci ɗaya Fauxa ta chanza akalar zuciyarshi ta sakata rusuna bisa burin da ya ɗauka nayi mata rashin mutunci a gidanshi har se ta gudu da kafafunta, ya fara gudanar da shirin ne ta hanyar Haɗata da ayyuka kala kala a gidan nashi kuma ya barta a matsayin ta na kanwarshi a tunaninshi zata kawo mishi musu ko rashin kunya yadda ze samu hujjar ladabtar da ita da kyau sede ta cinye wannan jarabawar ta hanyar haƙuri da juriya, sanyin hali da tsabta na ban mamaki wadda be taɓa zaton hakan take ba.

Abu na biyu shine son da take yiwa iyayenshi kusan sune komai nashi duk me son su kuwa dole ya so shi, wannan ya taka rawar gani sossai wajen ganinta da mutunci da daraja, Sam baze ce ga sadda ya fara son ta ba saide ya san ya zuwa yanzu zuciyarshi gabaɗaya cike take da tsananin so da tausayinta.. Dafa shi da Baba Alhj yayi ne ya saka shi ɗagowa tare da waiwayawa iyayen nasu ne ciki se Jaddah.

"Ka Daena zurfafa tunani haka Faizan in shaa Allahu zata samu lafiya"
Kanshi ya mayar ƙasa yana zare hannun nashi cikin nata ya mike tare da basu kujera, fuskanshi Sam babu wata walwala.

Kwananta biyu a asibitin don ranar da aka kaita da yamma ta farka, duk shigowar shi baze shigo hannu banza ba ze shigo da abubuwan ciye ciye kuma ya zauna ya jima suna ɗan hira da Jaddah ko ya zauna shiru rike da waya ko idanunta biyu bata taɓa gaisheshi ba Kallonshi ma ta ƙi tayi, abun na damun shi amma ya bata space ta warke tukuna.

Shi aka baiwa sallamar ta, bayan ya shigo yace
"zaliha Haɗa kayan ku mu wuce gida"
Kasancewar su biyun ne kaɗai a ɗakin Jaddah ta je gida.

Haɗa kayan tayi, fauza da fuskanta ba wani fara'a ta sauko sanye da hijab maroon har ƙasa, jerawa suka yi da zaliha tana rike da wasu kaya suka nufi motar tashi, zaliha ta zuba kayan a booth yayinda ta dawo ta buɗe baya ta shiga, Fauza ta buɗe bayan da niyyar shiga ta ji muryarshi daga bayanta

"Dawo gaba ki zauna"
Bata waigo ba kuma bata saki kofan ba.

Idanu ya zuba mata se yanzu take son nuna mishi taurin kan nata? Ya ayyana hakan a ranshi yanzu baze iya fushi da ita ba in yace ze iya ma ya san babban karya yayi, hannu ya sa ya buɗe gaban ya zare hannunta daga baya ya sanyata a gaban tare da rufewa ya zagaye.

Kamshi da sanyin motar suka ratsa ta, dukda ta san abunda take yin ba daidai bane amma dole ta nuna mishi kurenshi na laifin da ya aikata mata, har a asibiti bata bar anfani da wasu magunguna da Jaddah ta jiko su a wani katon buta ba tana tsarki Dukda ta warke se abunda ba'a rasa ba amma bata manta azabar da ta sha ba, haushin shi take ji kaman ta shake shi.

A hankali yake murza stirring ɗin idanunshi zube bisa titi, babu wadda yayi magana a motan har suka isa gida, be gama parking ba ta balle murfin motar tayi sashen Jaddah, da kallo ya bita har ta ɓace mai ya sauke ajiyar zuciya yana shafa gashin kanshi.

Zaliha ce ta tattare kayan sallamar tayi sashen jaddar itama.

Daga ranar ta fara wasan ɓuya dashi, bata bari su haɗu ko a hanya, ze zo sashen Jaddah ya gama zaman shi ko kyallin ta baze gani ba, ya san tana avoiding ɗinshi ne gashi yana da tafiya tunda ya jima a gida dole ze koma wurin aiki and babu wadda yayi mishi maganan ya kamata su koma haka har ga Allah ya gaji matarshi yake buƙata

Rigingine yake a kan kujerar Jaddah, chan yake jiyo sautinsu ita da Fa'iza tana tsokanar fa'iza akan wai sun sasanta kansu da Faraj don aiki suke daga shi har Farhan yanzu fa'izar ce ke level 1..

"Gwara ma ki bari a saka mana kusa mu sha buki, yadda zan zage na aurar da ƴar ƙanwata itama"

Fa'iza na murmushin yadda Fauza bata taɓa bari ta kuntata ko ta shiga Tunanin ba, cike da jinjinawa haƙurin Fauxar ta yadda kowa ze yaɓa mata magana ko ya zage ta ko ya mata zafi babu me fahimta sbd bata nunawa tace

"waye kanwar taki? Lallai ma yarinyar nan karki manta na baki kwana dai dai har talatin da ɗaya... Rainin wayau"

Dariya Fauza tayi tana cewa
"kin manta kwana ɗari ba ɗaya kika ba ni, ke ajiye batun wannan karki manta wadda nake aure don haka duk gidan nan karkashina kuke kuma wallahi dole ku ce min Aunty"
Yadda tayi maganan ba fa'iza kaɗai ba har shi seda ya murmusa, fa'iza na shirin magana suka Haɗa idanu dashi.

Da sauri tayi kasa tana gaisheshi ya amsa cike da kulawa ta wuce, yayinda Fauza ta nufi wucewa ba tare da ta ce mishi komai ba, cikin zafin nama ya miƙe ya taka biyu ya cabke hannunta, juyowa tayi se idanunsu suka sarƙe.. Kallonta yake da gabaɗaya idanunshi, a hankali cikin kasa sossai da murya yace

"Fauziyya ni kike yiwa rashin kunya yanzu?"
Kau da kai tayi tace
"me nayi kuma?"

Yace
"yanzu kin ga ya dace ki wuce ni ba tare da kin gaisheni ba?"

Ba tare da ta kalleshi ba tace
"Good evening..!"
Ta zare hannunta zata wuce ya sake janyo ta,
"Fine and why are you avoiding me?"

Ya faɗa yana riƙe da kafadar ta.

Kanshi ta maida idanunta tace
"Gaskiya kake son sani? Toh ina kaucewa ganinka ne sbd bana so idanunka su cigaba da kallon wannan mashayiyar kuma mazinaciyar fuskar t...."

Bakinta da ya buge ne ya saka ta maida kanta ƙasa hawaye ya fara zuba a fuskanta..

"Baki da hankali ne kike danganta kanki da waennan kalamai?"

"Au wai har ka manta? Ba ni ce na dangata kaina da hakan ba Kaine ka jefe ni da waennan kalamai, akwai saura ma ai cewa kayi bazaka iya cigaba da zama da me bin maza ba.... Nima kuma ba zan iya cigaba da zama da me saurin fushi da zargi ba don haka kaman yadda na yiwa su Baba biyayya a auren nan yanzu ya zama wajibi a dubi lamura na a raba wannan aure Ka sake n...."

Rufff ya rufe bakinta da nashi tare da matsota gabaɗaya ta shige cikin kirjinshi, baze iya cigaba da ɗaukan kalaman ta ba, tayi babban zunubi da kunnuwanshi bazasu juri ji ba bare har ya wassafa aiwatuwarshi..

Takarkarewa tayi ta ture shi da iya karfin ta, jikinshi a mace yake don haka kujera kawai ya zube yana dafe goshi a hankali har muryarshi na cracking yace
"Am so sorry... Pls karki sake faɗar irin wanchan Kalmar yayi min girma zuciyata bazata iya daukarta ba.."

Kuka ta fashe dashi kawai ta juya da gudu tayi ɗakinta, a gado ta zube ta sha kukanta ta more kan ta miƙe ta faɗa toilet tayi wanka ta san kilan ya zuwa yanzu fa'iza ta gaji da jiran ta a ɗakin Jaddah ta wuce...

Fita tayi ga mamakin ta har lokacin yana kwance cikin kujeran parlorn idanunshi a lumshe hannunshi kwance bisa kirjinshi, daga yadda yake karkada kafa zaka san ba bacci yake ba.

Idanun da suka yi laushi ya buɗe ya kure ta da kallo, baki ta taɓe ta wuce ta fice daga sashen gabaɗaya.

Bayan isha tana kwance kan cinyar Amminta dake taje mata kai a hankali Falaq tace
"ji wani sabon iyayi yanzu Fauxa Ammin ce zata miki taza?"

Bakinta ta murguda tace
"Ina ruwan wani? Amminki ko Ammina?"

Tahowa tayi da nufin gwabe mata baki Ammi tayi saurin riƙe hannunta
"Ke Falaq Rabu min da yarinya akan me zaki daketa bayan kece kika fara tsokananta?"

"Laaa Ammi yau bayan Fauzar kike bi? Lallai ma Ammi"

Ammi tace
"eh na bi ɗin"
Ficewa tayi fuu sbd yadda Fauxa ke mata dariya Ammi na murmushi tace

"Auta tashi mu yi magana"

Mikewa zaune tayi tana fuskantar Ammin tace
"Toh Ammina"

"Kowa a gidan nan ya fahimci tsakaninku da Faizan babu daaɗi har ma mahaifinki ya so ajiye ki se kuma baba prof ya hana, nima shawara zan baki a matsayina na mahaifiyarki, ko menene Faizan ya miki kiyi hakuri ki bishi ku koma yana da aiki amma yake ta faking excuses duk sbd ke, ya samu baba prof akan a bashi ke ku koma baba prof kuma ya ce in har ba ke kika shirya komawa ba babu ruwanshi, kin ga dae irin karamci da soyayyar da iyayenshi ke miki ko don wannan zaki duba mafi soyuwar ɗan su ki kyautata mishi sbd su ma su ji daaɗi..."

Fuskanta tayi kicin kicin dashi har hawaye na shirin zuba tace
"Ammi fa zar..."
Ɗaga mata hannu Ammi tayi tace
"bana son jin komai in dae har don abunda ya Haɗa ku ne, shawara ce kawai na baki kiyi tunani"

"ni dae Ammi ba zan iya komawa ba, baya sona nima haka kuma yanzu duk abunda ke boye ya riga ya bayyana kowa ya kama gabanshi kawai.."
Kallonta kawai Ammi ke yi, zata yi magana kenan suka ji an shigo da sallama...

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤



33

"Sannu da dawowa baba"
Fauza ta faɗa tana ɗaukan dankwalin dogon Rigan jikinta tana ɗaurawa a kanta, Ammi ma sannu da zuwa ta mishi ta mike don kawo mishi ruwa, Fauza bata motsa ba don ta san ko ta tashi Ammi cewa zatayi ta dawo ta zauna kar ta hanata samun ladarta.

Gaisawa suka yi da baban Dukda sun gaisa da safe shima cikin hikima yayi mata hannunka me sanda Dukda be fito kai tsaye yace maganansu da Faizan bane sede ya nuna mata rama Alkhairi da Alkhairi abu ne me kyau, kuma Hausawa sun ce ka gaida me gaisheka ko da kuwa baze amsa ba, shigowar Ammi ne ya katse su.

Abinci da ruwa ta kawo mishi, Fauza ce ta zuba mai yace ta matso su ci rana na farko kenan tun wayaunta ta sanya hannu suka ci abinci kwano ɗaya da mahaifinta Ammi na zaune daga gefe suna hira jefi jefi ranar har kuka tayi, Aunty ba karamin cutar ta tayi ba ta hana mata wananan shakuwa da soyayyar na tsakanin iyaye da 'ya'yayensu, se da taji bacci kan ta sallamesu bayan tayi waya da husna a wayan Ammi tana ta shagwaɓa akan ita kam zata dawo gidan Fauza, da wayan ta fita parlor ta Haɗa conference da Ya fadeela take ba su labarin abunda ya faru.

Sbd duk bata yi natsuwar magana da yayyun nata ba se yanzu, duk seda suka zub da hawayen jimami, suka yi mata barka sannan suma duk sun roketa ta koma gidan Faizan Dukda sun fahimci haushin abunda ya mata har lokacin yana ranta sede ta ƙi nunawa ne kawai har fadyaa ke rantsuwar ita tun randa suka je gidan ma ita da Ya Faahim seda suka yi gulmar soyayyar da suke yiwa juna a ɓoye.

Ita dae fadeela se dariya take yayinda Fauza ta shagwabe akan lallai lallai ita ba haka bane tana Haɗa ya Fadyaa da Ya fadeelah, sun sha hira kan suka yi sallama don ma what'sapp call ne da ta tabbatar ko biyar baze saura a wayan Ammin ba.

Anan kan stand ta bar mata ta wuce sashen Jaddah, kan ta shige ta hangi fitowanshi daga mota yana waya a natse yake tafiya yayi sashensu na ƴan maza, ta jima tsaye tana Kallonshi seda ya wuce kan ta juya itama ta shiga sashen, ɗakin Jaddah ta shiga suka ɗan yi hira kan taje ta kwanta bayan ta rufe kofan ta.

Washegari da safe ko karyawa bata yi ba ta dae yi wanka ta sanya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login