Showing 66001 words to 69000 words out of 86608 words

Chapter 23 - DIDDIGAR ƘAYA COMPLT Hausa novel

21 Aug 2024

18448

hanya, Seda ta tabbatar sun bar yankin Abuja kan ta sauke wani nannauyar ajiyar zuciya wani wahalallen bacci ya ɗauke ta.

***

Su kuwa tashar mararraba suka fara zuwa duk motocin yola babu irin sunanta ma kuma duk yadda ya musu misalin kamanninta suka ce basu ga me irin kamannin anan ba.

Daga nan Suka yi dei-dei park nan ma neman duniya da kwatance suka ce basu ganta ba, suka nufi jabi Dukda shi kam Faizan hankalinshi Sam be bashi gida ta tafi ba sbd be san abunda ya faru da zata tafi gida ba haka dae suka je, aiko first turn da aka duba list se ga sunanta, kurawa sunan idanu yayi kwarai itace ma ta rubuta da hannunta don ga rubutunta nan zarzar.

Me makon yayi farin ciki ba ɓata tayi ba se wani sabon ɓacin rai ya ziyarceshi, ta ɗaga musu hankali a banza...
"Karka ɗauki fushi ba tare da ka san dalilin ta ba Faizan"

Faisal ya faɗa a sadda suka nufi gidan Faisal ɗin, Jafar ke tuka su da motar Faizan ɗin, sun riga sun sallami police.

"Hmmm"
Shine abunda kawai ya iya cewa tare da kwafa.

Har suka isa gidan Faisal matarshi ta gabatar musu da abincin be iya cin na kirki ba, barin ma da ta tambayi lafiyar Fauza ji yayi kaman ya tashi ya bar gidan.

Haka dae suka ta lallaɓa shi har Jafar ya maida shi gida, ɗaki kawai ya shiga ya zube yana kallon POP duk Tunanin duniya be ga abunda yayiwa yarinyar nan da ta zaɓi daga mai hankali haka ba, shine ma za'a ce ya dace yayi wannan fushi da ita tunda ta aikata mishi laifi har sau biyu, amma don ta mugun raina shi shine ta kama hanya ta tafi yola, shi kuwa ze nuna mata ɗan halak yake.

***

Zaune Jaddah take ta idar da sallar magrib kenan taji sallama da murya kaman na Fauziyya, ɗaga kai tayi tana jiran a shigo parlorn kaman daga sama kuwa ta ganta tsaye daga bakin kofa tana kallonta.

"Fauziyya!!"
Jaddah ta kirata cike da dumbin mamaki.

"Faizan be ce mana kina zuwa ba, wani irin zuwa ne haka? Baki da lafiya ne?"
Da sauri ta karasa ta kwanta jikin jaddar ta fara kuka, shafa bayanta kawai Jaddah ke yi, yin duniyan nan ta ƙi tace komai.

"Kin yi sallah?"
Ta girgiza kai
"to tashi kije kiyo alwala ki zo kiyi sallah, tare da Faizan kuke?"

Girgiza kai tayi.
"A motan kasuwa kika taho?"
Ta gyaɗa kai.

"Faizan ɗin ya sani?"
Girgiza kai tayi.

"To tashi je kiyi alwala"
Mikewa tayi ta nufi ɗakin Jaddahn a chan tayi alwala tayi sallah a cikin ɗakin kawai ta kwanta shiru, babu abunda yake mata kai kawo a rai irin daren jiya, ya yaji da ya tashi be ganta ba? Ita dae babu abunda aka mata amma ta san ta tsani gidan da garin gabaɗaya.

Har aka yi isha ta tashi ta gabatar tunaninshi kawai take yi.

"Fauziyya taso ki zo kici abinci"

Mikewa tayi ta fito, tun tea ɗin jiya ne cikinta kuma har yanzu bata ji tana sha'awar cin wani abun ba, ruwan zafi Jaddah ta fara bata kan ta saka mata tuwo da miyar lalo da yaji haɗi ta bata.

Kaɗan kawai taci ta ture, Jaddah tace
"kin koshi?"
Kai ta gyaɗa.

"Tashi muje iyayen ki na son ganinki"

A tare da Jaddah suka nufi parlorn baba prof, Ammi, mammi, Baba prof, Baba Alhj se su ya Farhan ne zaune a ciki sauran matan gidan duka ba'a gayyace su ba.

Bata kalli kowa ba ta karasa gaban baba prof dake daga kan kujeranshi ta zauna daga ƙasa kanta a ƙasa, daga babanta har yayyinta wani irin kallo suke aika mata sbd ko da Jaddah ta gaya musu zuwan Fauza duk sun ajiye wani abun tayo, ko tayiwa Faizan ɗin ya koro ta.

Mammi kuwa kallon yadda ta ƙara kyau da haske take ba laifi Abujan ya karɓeta sossai alamun dae hankalinta a kwance yake kan yanzu ɗin.

Baba prof yace
"Fauziyya..! Se kawai mu ganki ba sanarwa? Ke da wa kuka zo?"

Shiru tayi, Jaddah tace
"Tun fa bayan sallama da tayi bata sake cewa komai ba professor"

Ya dube ta yace
"Faizan ne ko?"

Ta girgiza kai
"Toh Fatima ce?"

Nan ma ta girgiza kai.

"Ke don ƙaniyarki ana magana bazaki buɗe baki kiyi magana ba? Me ke damunki ne? Idan duka babu kowa to uban me ze sa ki bar gidanki ki kamo hanyar Abuja ba tare da kowa ya sani ba? Amma shi mijin naki ya sani?"
Cewar baba Alhj cikin zafi.

Kuka kawai ta fara kan ta girgiza kai.
Wayanshi ya fiddo ya kira Faizan ya sa a handsfree.

Yana kwance salla kawai ke ɗaga shi ko ruwa be sake sha ba, Tunanin duniyan nan yayi be san me ya saka yarinyar nan tafiya ba, ganin kiran baba Alhj ya sa ya san ta isa gidan.

Ɗagawa yayi cikin muryarshi da yayi sanyi sossai yayi ƙasa kaman me jin bacci ko wadda ya tashi daga baccin.
Cikin girmamawa ya gaida shi, bayan sun gama gaisuwa baba Alhj yace

"Faizan kawai se muka ga Fauziyya kaman daga sama mun yi mun yi tayi magana kuma ta ƙi shine nace bari na kira ka kila kai ka san abunda ya sa ta bar gidan ta biyo hanya"

A natse yace
"Ko ɗaya baba, nima bani da masaniyar barinta gida jiya tayi zazzaɓi kuma har karfe ɗaya na dare na bar ɗakinta, na tashi da safe kawai na neme ta na rasa har police station mun je da su Faisal sbd ban san me yasa zata tashi kawai ta tafi gida ba tare da laifin tsaye ba bare na zaune, a chan ne cikin bincikensu muka je har tasha muka ga sunanta cikin passengers ɗin yola, time ɗin karfe kusan 2 na rana shiyasa ma ban kira ku ba"

Duk kallonta suke, tana sheshekar kuka a hankali, shima kuma yana jinta.

A hankali yace
"Baba ku barta kilan akwai wani abunda aka yi mata anan ɗin in ta huce zata yi magana amma please ban amince kowa ya taɓamin ita ba"

Ƙara karfin kukanta tayi, se a lokacin ta buɗe baki ta fara magana
"Babu wadda ya min komai... Ni baba kawai na tsani gidan ne, na tsani garin...! Baba ji nayi in ban bar garin ba zan iya mutuwa... Yaya Don Allah kayi hakuri nima ban san sadda na fita ba.."
Kuka ne ya ci karfinta.

Baba prof ya dafa kanta yace
"kiyi shiru Fauziyya, yi hakuri bar kukan nan... Kin yi wani mafarki ne? Ko wani abu ya faru kan kika ji bakya son Abujan?"

Yana kwance lub yana sauraren ta, a hankali ta basu labarin abunda ya faru na tun tsakiyar dare bata yi bacci ba, bata samu natsuwa ba kuma seda ta bar garin wlh ko sunan garin bata sha'awar taji an kira.

Rarrashinta baba prof yayi tayi akan ta bar kukan haka, ita damuwanta tana ta ɓata mishi rai kusan kwana huɗu kenan koyaushe ranshi a ɓace sbd ita, Baba Alhj yace
"Toh me ke faruwa ne?"

Kusan tambayar da kowa ke yi kenan a ranshi har Faizan, Baba prof karan kanshi a dame yake don wannan kowa ya ji ya san ba Alkhairi bane aikin asiri ne to amma wa ze mata? Sun san dae Fatima ciki da bai yarinya me natsuwa da hankali, ta taso a gidan cikin tarbiya irin na yaran gidan to Alamar tambayar tana kan waye?

A hankali Faizan ya sa hannu ya yanke wayar, se ya miƙe ya nufi ɗakinta.. Ya jima tsaye yana karewa ɗakin kallo kan ya fara gyarawa a natse har ya gama tsab tsab kaman tana nan.

Bayan ya saka turaren wutan da ta saba sakawa yaje kan kujera ya kwanta idanunshi na kallon sama.. Fatima ce tayi knocking ta shigo.

"Abinci fa ya gama ɗazu na leƙa ka a ɗakinka na samu kana bacci!"

Idanunshi ya buɗe ya zuba mata Su kawai ba tare da ya ce uffan ba.

***

A yola kuwa cike da damuwa suka yi ta Rarrashinta har tayi shiru, Baba prof ya rubuta abubuwan da bashi dashi a gidan ya ba Farhan akan ya je ya samo mishi ze Haɗa mata maganin kariya.

Farhan ya mike ya tafi, Ruwan zamzam ya bata wadda akwai ayoyi ciki ta sha yace taje ta kwanta ta huta kar tayi Tunanin komai.

Mikewa tayi ta nufi sashen Jaddah, Amminta da tun aka fara bata ce komai ba se lokacin tayi kwafa ta mike kawai ta fice duk da kallo suka bita.

Sun ɗan kara tattaunawa akan matsalar ta sede basu bada kofan zargi ba sun dae ajiye kila akwai aljanin da ya aureta ko kuwa suna so su shafeta.

Farhan ya dawo da aikan baban, bawan Allah daren gabaɗaya be runtsa ba seda ya karance baqara kap a cikin ruwan zamzam da ya zuba mishi garin bagaruwa, ya cigaba da karatun ayoyi har uku kan ya gama se kawai ya hau jera nafilifili da Adu'ar Allah ya bayyana duk wani abunda ke boye akan Fauza sbd tun farkon fari dama shi hankalinshi be bashi haka kawai take ba.

Kaman yadda be yi bacci ba haka Fauza da Faizan, bayan dogon tunani kusan a tare suka miƙe suka fara jela nafilfili haka jadda ma tsakiyar dare ta yanke baccinta dama tun lokacin ƙadangaren nan bata wani sakankance ba Fauza take nemawa sauƙi a wurin Allah da ko ma menene yake rayuwarta...

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤




29

*BAYAN SATI ƊAYA*

Yau satin ta kenan da zuwa garin yola, kuma sossai take jin daaɗin garin sbd yadda kowa ke ina za'a saka ina za'a ajiye da ita, daga mammi, Jaddah, babanta, Baba prof, su ya Farhan da su Fa'iza duk ji da ita suke kaman me sede in bata ambaci abu dayansu ya ji ba haka za'a je a nema mata, yanzu ita da kannenta ba duka ba zagi se jansu a jiki da take yawan yi, magungunan ta kuwa kullu yaumin safe da dare cikin kariya take na irin ayoyin da Baba prof ke mata anfani dashi, duk da waennan gabaɗaya a maimakon ta kara ƙiba tayi kyau ta Daena Tunanin komai se farin ciki duk hakan be yiwu ba.

Ta ɗan zube kadan sbd yawan tunani, be taɓa kira ya ce a bata ba kuma wallahi bazata yi karya ba zuciyarta ta riga ta gama yaudararta akan Faizan bata san ta kamu da mahaukacin soyayyarsa ba se da suka nesanta da juna ta san yana fushi da ita abunda ke hanata walwala kenan gashi ita kuma ta kasa ɗaga waya ko na Jaddah ne ta kirashi.

Tana kwance a parlorn na Jaddah a kan kujera Fa'iza ta shigo tana cewa
"Fauza kin yi bacci ne?"

Jaddah dake fitowa daga ɗakinta tace
"Ina ita ina lafiyar baccin yamma Fa'iza?"

Tana kallon fa'izan tace
"Ya aka yi ne?"

Fa'iza tace
"dama zan fita ne chan farkon layi zan karɓi handout ɗina wurin wata friend ɗina shine nake so in ji har yanzu kina sha'awar cin farar ne? Don ba'a rasawa ta wurin"

Mikewa tayi zaune tace
"Jaddah Eyya bata ɗari biyu in tana dawowa ta sayo min fara"

Jaddah tace
"Toh"
Ta fara duba gefen zaninta ta fiddo ɗari biyar, tana kallon Fauza tace
"To da kwanciyar nan ko zaki bita ne Fauziyya? Tunda kika zo ko gate baki kara leƙawa ba kika ɗan fitan kema zaki ɗan ji daaɗi"

Kaman zata ce bazata je ba se Fa'iza ta kama magiya akan su je tare ɗin wlh dama tana ta Tunanin tafiya ita kaɗai su faazila na islamiyya, ya Falaq kuma tace ita ba sa'ar mata rakiya bace.

Mikewa tayi kawai taje ta wanke fuskanta ta ɗan gyara kan ta fito tana ji su Jaddah na maganan shiru shirunta ko ciwon ne oho. Fa'iza tace
"ko tana kewar mijinta ba Jaddah?"

"Zaki tashi muje ko zaki zauna gulmata in fasa rakiyar?"
Ta faɗa tana maka mata harara duk dariya suka yi tuni ita tayi gaba, fa'iza ta miƙe da gudu ta bi bayanta.

A natse suke tafiya tunda suka fito taga motar dake bin su, fa'iza dae bata kula ba, mai motar kuwa tun yana bin su a baya a baya har ya iso saitinsu ya musu horn.

Kallo ɗaya tayi mishi ta ɗauke kai suka cigaba da tafiyar su, Fa'iza ma ba gwanar kula irin su ba ce se kawai suka maida kansu hanya, har suka isa gidan mai motan nan be bar binsu ba basu wani jima chan ba suka fito, suka tsaya suka saya fara tana lura da wasu dake gulmarta ana ta mamakin Fauziyya ce shiru shiru haka? Ita dae bata bi ta kansu ba suka ɗauki hanyar gida.

Mai motar nan again ya cigaba da bin bayansu, gab sun iso farkon layinsu ganin bazasu tsaya ba gashi yana hangen gidansu yasa yayi saurin parking ya sauka ya biyo bayansu

"Fauza...! Fauza!!"

Fa'iza tace
"ke fa mutumin nan ke yake kira"

Yi tayi kaman bata ji ba kaman daga sama taga mutum a gabanta.

"Fauziyya ni kike wulakantawa? Ni ne fa Zubair ɗin ki"
Ya karashe yana nuna kanshi.

Tana Kallonshi tace
"Na gane ka mana amma bani da business kuma da kai Zubair hakan yasa ban ga anfanin kulaka ba, please ka kyaleni karka manta da Aurena"

Hannun fa'iza ta kama suka fara yunkurin wuce shi ya sake shan gabanta..

"Fauza akan ki rayuwata ta shiga cikin barazana, a kan ki saida na shafe sama da watanni huɗu a prison amma sakamakon da zaki yi min kenan? Wallahi gayen chan ba son ki yake ba, na rantse miki da Allah ina son ki kuma in har ba zan sameki ba saide kowa ya rasa"
Ya faɗa cikin alwashi.

"Oh haka kace?"
Tayi maganan tana Kallonshi.

Yace
"eh don ban ga maraba ta da mugun yayankin nan ba, shi yayi min cune ina tare da drugs da gomnatin Nigeria ta hana Anfani dasu ya kuma san idan har an kama ka kisa ne amma ya cuna ni ina dawowa daga Russia aka kamani, ba don connections ba da se wani ba ni ba Fauziyya duk a haka kika zaɓe shi over ni?"

Tana shirin magana kenan idanunta suka faɗa cikin nashi, wani mummunan faɗuwar gaba ne ya riske ta har bata san ta matse hannun fa'iza dake cikin nata ba, tsaye yake sanye da kananun kaya riga da wando daga gani ka san sun ci kuɗi hannayenshi zube a aljihu ya tsaresu da firgitattun idanunshin nan masu rikitar da ita yana kallo..

Ɓacin rai take hanga shimfide a fuskanshi me tsanani, yaushe ya zo? Ta jefawa kanta tambayar da bata san amsar shi ba, da sauri ta zagaye Zubair ta nufe shi da nufin yi mishi bayani ba abunda yake tunani bane, tana isa kawai ya sanya hannu ya fincike hannunta suka yi gida.

Jan ta yake ba tare da ya damu da saurin da yake ɗin yayi mata yawa ba. Basu zame ko ina ba se room ɗinshi da karfi ya jefa ta kan kujera yana kallonta zuciyarshi kaman ya Faso kirjinshi ya fito sbd yadda yake hawa da sauƙa na bacin rai...

***

Tun da ta bar garin Abuja yaji garin ya zamar mishi kaman Ƙango, baya jin daaɗin rayuwa, baya iya cikakken farin ciki, 24/7 da tunaninta yake kwana yake tashi, gabaɗaya Fatima ta kasa gane kanshi don ba wani abincin kirki yake ci ba, ko yaushe kuma yana ɗakin Fauza a kwance.

Shi karan kanshi be san Son ta yayi mishi mummunar illah ba seda suka nesanta da juna, ita yake so ta fahimci darajar shi hakan yasa ya ƙi kiranta ko da a waya ne ba tare da haƙarshi ta cimma ruwa ba sbd rana tsaka kawai ya cewa Fatima ta shirya su tafi yola su dan kwana biyu se su dawo gabaɗaya, ya azabtu kwarai da Tsananin kewan girkin ta, shayin ta, rashin kunyar ta in tayi niyya wadda babu abunda ke mai kyau daga gareta irin shi, shagwaɓarta, ƙamshin ta, shigar ta da ma lallausar fatanta... Daren karshe da suka yi spending gabaɗaya ya kasa fita daga kwakwalwarshi.

Ita Fatima ta zama abin kallo ne kawai illa iyaka abun ya ishe ta ta shige ɗaki ta sha kukanta, ta kira Aunty tana mata kuka akan yadda tunda Fauza ta bar gidan irin yadda suke dashi kaman an chanza shi, Auntyn ta tabbatar mata da ta kara hakuri na lokaci kaɗan ne komai ze sauya karta damu.

Hakan yasa ta cire damuwar a ranta kawai kuma wai ta shirya su je yola in zasu dawo su dawo tare gabaɗaya, me yake nufi?

Karfe 3 daidai na yamma jirgin su ya sauka a international Airport na Yola, Farhan da Faraj ne suka je suka ɗauko su, tun daga nesa kuma ya hangesu ita da Fa'iza a sadda suke tafiya.. Da idanu ya bi ta har motar su ta karya kwanan gidan nasu.

Hakan yasa be shiga ciki ba ya samu kan mota ya zauna jiran ta, yana so yaga expression ɗinta a sadda zata ganshi, yana so yaga tayi kewar shi ne kaman yadda yayi mahaukacin kewar ta? Yana so yaga idanuntan nan da yayi kewarsu fiye da komai, ganin sun ɗan jima yasa ya dira ya fita wajen gate a chan nesa ya hangesu da wani guy, be ma gane Zubair bane seda ya matsu dab dasu...

***

"Ashe Abun naki hauka ya koma ban sani ba Fauziyya?? Da Aurena a kanki kike kula wani gardi? Me wanchan Yaron yake dashi da ya fi ni Fauziyya??? Eyee?"
Ya daka mata tsawa yana kallon yadda take ta murza hannunta da ya rike hawaye na zuba a idanunta.

Fuskan nan a murtuke jajazir yace cikin dakakkiyar muryarshi da ya Haɗu da bacin rai..
"How could you? Oh da kin gayamin abunda kike buƙata da na banbance miki tsakanin Aya da tsakuwa... Da na nuna miki cewa wadda kika saba dashi fank....."

"Don't...!"
Itama tayi ihu cikin kuka tace
"Karka fara jefana da wannan kalma, karka bari na tsaneka ya Faizan.."
Kuka sossai take tana jin zafi sossai na yadda yake kokarin kawo abunda ba shine ba cikin rayuwar aurenta..

"Shut up!! Just shut the fucking up! Babu abunda zaki ce in yarda dashi.. Babu Fauziyya..."
Zata yi magana da niyyar kare kanta ya riƙo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login