Showing 54001 words to 57000 words out of 86608 words

Chapter 19 - DIDDIGAR ƘAYA COMPLT Hausa novel

21 Aug 2024

18464

waya ba'a yi mintuna biyar ba se gata a ladabce ta gaishesu yana kallonta yace

"yauwa Afnan ga ƙawa nayi miki Dukda dae da hafsa ne kawancen asalin amma a nan kawar ki ce, ku je ki nuna mata wurare sannan Naga kuna da lectures 9-10 duk ku shiga tare kin ji?"

Tana murmushi tace
"Toh Yaya, Aunty mu je"

Murmushi Fauza tayi kan ta miƙe tsaye se ta kalli Faizan da nufin neman izinin tafiya, murmushi me kyau da ya tafi da imaninta ya sakar mata kan yace
"a kula, ina jiranki anan"

Kai ta gyaɗa itama ta ɗan yi mishi murmushi kan ta bi bayan Afnan dake Kallonsu da burgewa tana amsa bye bye ɗin husna.

"Kan uba! Kai fa ɗan iska ne Faizan so kake ka hana yarinya karatu da wannan narke narken?"

Harara ya zabga mishi yace
"ka manta ɗan guguwa ne.."
Dariya suka yi a tare, Faisal yace
"Masha Allah amma Amaryar ka na da hankali gata sweet sixteen shiyasa mana ka makale a gida ka kasa fita outside countries tunda aka kawo maka ita, Haba ai biri yayi kama da mutum"

Duka Faizan ya kai mai yana cewa
"ba da aljani ba?"
Dariya sossai faisal yake mai, daga karshe suka saki hiran Fauza suka kama wani, don sun san Faizan mutum ne da baya so ko a junansu ne suke kawo maganganun iyalansu in har ya zamana sirrinsu ne, ya sha gayamusu girman sirri dake tsakanin miji da mata da kuma tanadin Allah ga me fallasawa walau miji walau matar, lokutta dayawa in sun zauna daga sun fara in ya dakatar dasu zasu fara mishi tsiyar social ustaz ko young sheikh ya hana dole a hanu.

A ɓangaren Fauza kuwa taji daaɗin makarantar fiye da yadda ta zata, Afnan na da hankali ga saurin sabo nan da nan suka saba, a tare suka ɗan yiyyi signings da bata yi a course form ba suka kuma shiga lectures, basu dayawa don haka ba wani surutu kuma for the first time Fauza ta natsu a class har ta saurari malami ba zagi, faɗa ko neman tsokana.

Bayan sun tashi ta same shi a office ɗin kaman yadda ya faɗa suka nufi gida.
"Amm Faahim ya ƙira Visa ɗin husna ya fito zata bisu"

Da sauri ta kalleshi idanunta na cika da hawaye sede bata ce komai ba, ya fahimci kewan husna zata yi to amma ba yadda suka iya dole ne zata koma wurin iyayenta, har suka dawo gida jikin ta a mace, juicy pasta bolognaise tayi musu sharp sharp suka ci yayi daaɗi kuwa sossai, har ya kasa shiru yace

"Ni kam Fauza duk wa ya koya miki abubuwa masu daaɗi haka?"
Murmushi tayi zata yi magana husna ta ɗauki pillown kujera taje bayanshi tana kare mishi tace
"haka fa mommy ke yiwa Daddy idan yana cin abinci yana santi, wai kunnenshi na motsi..."

Duk dariya suka saka Fauza ta kasa tsayar da nata har ya shagala da kallonta for the first time he admits it she's so cute and beautiful, da kyar ta tsagaita dariyar ganin irin kallon da yake mata tayi gyaran murya tare da cewa
"Na koya wasu wurin friends ɗina though idan na biya wurin koyan kullum se na sha duka amma haka nake zuwa bcs shine abinda ke sani farin ciki time ɗin, se kuma da nayi waya nayi classes masu yawa online"

Kallon tausayi ya mata yace
"then me yake hana ki faɗin ga inda kika je a time ɗin? Me yasa ba zaki ce a saka ki a catering school ba?"

Idanunta ta kaɗa wadda yaji har tsakiyar kwanyarshi tana ɗaga kafada tace
"Taurin kai irin na Fauza"

Kallonta kawai yake yana mamakin ita kuma wannan haka Allah ya yi ta ko kuwa? Tattare wurin da ta fara ne yasa ya ɗauke idanunshi kanta.

A haka suka kwashe kwana bakwai curr kullum ita zata yi musu breakfast ya sauke ta makaranta ya wuce inda zashi wani lokacin kuma ya tsaya wurin Faisal in an tashi ya maida ta ko karfe nawa zata kai baze ci abinci ba ze jira har ta gama su koma ta sama musu abunda zasu ci.

Be taɓa zaton rayuwa da ita in a shade ze zama haka ba, yarinyar tana da tsafta, kunya ga iya girki har ba'a magana, sau dayawa yana mamakin ina wannan kunyar nata yaje har take yawon hotels da shaye shaye, lokuta dayawa idan ya tuna hakan halin da rayuwarshi ke shiga baya mishi daaɗi hakan yasa yake ta kokarin rufe baabin ganinta da yayi a hotels da kuma irin shaye shaye da tayi.

Ranar Sunday bayan ya karya yake sanar mata ze je yola amma gobe da yamma ze dawo, kaman zata yi kuka haka tayi mishi Dukda tana tsoron kwana haka baya nan amma da sauƙi tunda ga husna, Seda ya tabbatar babu abunda suke bukata kan ya wuce bayan ya bata Wayanshi da take yawan anfani dashi ɗin nan.

***

"Na fahimce ki yanzu Fatima, an samu matsala ne girma da daraja irin na aure ya kunce ɗauri masu yawa akan Fauziyya ɗin hakan ne yasa kika ga halinta gabaɗaya kaman sake mata shi aka yi, sannan gidanta akwai kariya sossai amma jikinta da sauƙin kariyar, mijinki ze zo ku koma kawai ki zuba idanu kiyi kallo kaman yadda kika bar gidan haka itama zata bari ba na kwana bakwai ba ita kam na har Abada"
Aunty ta sauke Ayar cikin cin alwashi.

Murmushi Fatima ta saki tace
"yauwa Auntyna maganin kuka na"

Ko da ya iso se dare suka zauna da Baba Prof ya gayamusu duk abunda ya faru, kai tsaye Fatima ta Musa wadda ya saka baba prof kallonta cikin mamaki don tabbas ze iya cewa fauza bata yi karya ba kan yayi magana ma baba Alhj yace..
"Ko ni da ban shaku da fauza ba na san wannan ɗabi'ar tata na rashin ƙarya, ta kan faɗi gaskiya ko hakan ze ja mata dukan mutawa ne".
Da sauri Fatima ta kalleshi har zata ce kenan ita ɗin an mata shedar karya kenan Aunty tayi saurin cewa

"ai duk maida magana bata taso ba, na yiwa Fatima faɗa sossai akan shiga harkar Fauza tunda an samu tana zaune lafiya karta dinga shiga harkar ta idan har ba mutunci ne ze Haɗa su ba, kuma in shaa Allahu ta ɗauka"

Baba prof yace
"masha Allah, to yayi"
Faɗa ya ɗan mata akan yadda Faizan ya mayar mai yadda take maida mishi magani ya nuna mata girman miji da matsayinshi kan ya sallame su akan gobe zasu wuce.

Faizan wurin mammi ya kusa cinye daren suna hira tsakanin uwa da ɗa, amma fa kusan duk hiran na Fauza ne ita ke mishi yana ji, ta bashi labarin yadda Fauza ke kula da ita da cimarta in bata da lafiya har ta faɗa mai Adu'ar da Fauzan ke mata in kafanta ya tashi yanzu bata nan ne sede tayi da kanta Dukda bata tausan kafan yadda ya kamata.

Tana bashi labarin tana kula dashi da a da ne da yanzu duk wani fara'arshi ya kau kilan ma da ya bar mata wurin amma yanzu har murmushi ya kan yi, se dare sossai ya miƙe yayi mata se da safe, har ranta ta ji daaɗin fahimtar da tayi akwai haske a lamarinsu.

Yana isa ɗaki a kan three seater ya kwanta ya fiddo ainihin Wayanshi ya fara neman layin shi dake wurin Fauza ɗin.

Har Seda ya kusa katsewa kan ta ɗaga
"Assalamu Alaikum warahmatullah"
Ta faɗa ƙasa ƙasa wadda a take muryar ya saukar mishi da kasala yaji gaɓoɓinshi a gajiye.

Shima chan kasa ya amsa ta kan ya ɗora da
"kin yi bacci ne?"

Tace
"uhm na soma kenan, ka isa lafiya? Ya ka same su?"

Ya ɗan yi shiru kan yace
"lafiya ƙalau duk suna lafiya, mammi na ta missing ɗinki"

Tana murmushi tace
"Allah sarki mammina nima nayi kewarta sossai"

Yace a ƙasan maƙoshi
"ɗan mammi fa?"

Dariya me sauti tayi tace
"Husna na ta tambayar ka, gidan shiru mu kaɗai shiyasa ma muka kwanta da wuri"

Shima basarwa yayi kaman yadda ya fahimci ta basar da tambayar shi yace
"in Shaa Allah gobe warhaka muna nan Kice mata kar ta damu sannan ki ce mata nayi missing ɗinku"
Yana kai nan ya yanke wayan....

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤




24

kaman kuwa yadda ya ce ɗin karfe biyar daidai a bakin kofan gate ɗin gidan ya musu kaman kuwa sun Haɗa baki da wadda ya tuƙo motar Fatima ɗin tun asuba don suna parking shima yayi horn aka buɗe mai ya shigar, hana shi tafiya Faizan yayi yace ya shiga ya ci abinci in ya so ya sama mai wuri ya kwana se gobe ya wuce da sassafe ta tasha.

Godiya sossai mutumin yayi kan suka shiga ciki a tare, parlorn ƙasan ya sha gyara se kamshin turarukan wuta masu sanyi yake zubawa, murmushi ya saki sanin aikinta ne don kamshin a wurinta ya saba ji irin wannan kam, ji yake kaman yana ɗakin mammi ko jadda sbd natsuwa da ya saukar mai.

Kujera yayiwa drivern izinin zama shi kuma ya nufi sama don tuni Fatima ta jima da wucewa..

"Yaaa salaam!" Ya furta a ranshi a sadda idanunshi suka faɗa kanta, itama dakatawa tayi tana sakin murmushi da ya Karasa saukar mai da gajiya, da gudu husna taje tayi hugging nashi hakan ya dawo dashi daga wata duniyar da ya tafi, ɗauke kai yayi saide idanunshi basu koshi da kallonta ba.

Tayi kyau sossai cikin wani material silk da aka yi mata doguwar riga fitted ya fitar da duk wani siffanta ta saka jewelries fashion gyale baƙi a ɗaure bisa kanta, tana murmushi tace
"sannu da dawowa yaya"

Sam wlh babu wadda yake kallo a parlorn bayan ita be san Fatima na parlorn ba har lokacin seda yaji ta ja wani wawan tsaki ta wuce ɗakinta tare da doko kofa.

Duk kallon kofan suka yi kan suka kalli juna yace
"yauwa ƙanwata! Pls zamu samu abinci? Akwai baƙo a parlor yayi tafiya me nisa"

Tace
"kwarai kuwa baza'a rasa abinci ba, bari na duba mishi"

Kallonta yake ya ga ko zata fita a haka saide ga mamakin shi ta shiga ɗaki ta dau hijab ta saka kan ta fito ta nufi ƙasa, fuskanshi kaman gonar auduga ya bita da kallo har ta ɓace mishi.

Hira suke yi da husna tana mai rigimar ina tsarabarta har ta dawo ɗauke da jug da cup ɗinshi me kyau bisa tray, a gefenshi ta tsuguna ta tsiyaya mishi tare da miƙa mai.

Hannu ya sa yana karɓa sanyin abun na aika mishi da zakuwar son ɗanɗanawa Dukda be san me bane, kurbi daya yayi ya lumshe idanu yace
"wannan kuma me sunanshi ƙanwata?"

Husna tace
"laaa uncle kunun aya ne baka sani ba?"

Yace
"Husna uncle be saba shan me daaɗi da kaurin wannan bane but it's so so giving wlh"

Dariya suka saka mishi, Fauza tace
"Yaaya ya su mammi da Jaddah? Baba prof da Baba Alhj da kowa da kowa dake gidan kowa na nan ƙalau?"
Ta faɗa a marairaice.

Yace
"kowa na lafiya, duk sun gaida ke"
Sossai tayi kewan su.

Bayan ya gama sha ya mike yana ce mata bari ya kai bakon nan masauki, ze yi magrib kan ya shigo. Seda ya gama faɗa kuma se yaji wani iri sbd ba sabawa yayi ba.

Tace
"Allah ya tsare a dawo lafiya"

Seda ya leƙa ya gayawa Fatima da ta amsa da kyar kan ya juya ya fice.

Fitowa Fatima tayi tana kallon Fauza dake kwashe abubuwan da ya sha kunun ayan tace
"mtseww ba girin girin ba dae tayi mai..."

Fauza bata yi niyyar tanka ta ba ta sake cewa
"cushe ba farin jini"

Dariya Fauza ta saki sossai kan tace
"Eyyaaa ai Alhamdulillah tunda ni umarnin iyaye nake bi kuma seda aka ɗaura na zama tashi kan nake cushen wata fa da ta gina komai a ƙarya?"

Matsowa tayi tace
"karki ga kaman kin ci galaba a kaina last week sbd cikina da kika ɓarar wlh yanzu se in nuna miki na riga ki shan iskar duniya"

Fauza ta mata kallon sama da ƙasa kan tace
"ko? Allah sarki abunda kuma aka koyar dake kenan? Iya shi kenan ko har da barbaɗe? Kin San Allah in da nayi niyyar shayar dake bakin ciki marar misaltuwa da nayi tuntuni ki kiyaye ni... Kaman yadda nake faɗa ki tsaya matsayarki sannan Haɗa jiki dake ai zubda aji ne, Allah sarki yayana bana so kayi tsiya, don kin san Haɗa ƙashi da kishiya miji yake janyowa tsiya.. Kuma komai lalacewar masa Fatima ai ta fi karfin kashin shanu"

Tana kai nan ta wuce ɗakinta don husna tuni ta shige, a daskare Fatima take tana bin bayanta da kallo, lallai yarinyar nan ta gama raina ta, ya tana mata kallon biri ita kuma tana mata na Ayaba? Ashe dama Fauzan kura ce lulluɓe da fatar akuya? Waye yake hure mata kunne ta mamaye min gida? Ihu ta kurma kan ta nufi ɗaki tana ji kaman ta sa wa gidan wuta kowa ya huta.

Bayan ya dawo ta gabatar mai da abinci Dukda bata yi niyya ba amma ganin yau suka dawo yasa ta bashi, amma gobe kam matarshi da ta iya girki ita zata cigaba da sama mai abunda ze ci dama taimako tayi.

Tuwon alkama ne da miyar kuka ya ji ma shanu naman kazan nan yayi raga raga a ciki, ya ci sossai kuwa kan ya kira su duka parlor, nan yayi musu faɗa sossai akan rikici tsakaninsu ya kuma gargadesu da kar ya kara ji bare gani, daga karshe ya ɗaura da
"Fatima tunda kina da mota Zaku dinga tafiya school da fauza har muga yadda za'a yi"

Tace
"Toh Yaya in shaa Allah"

Fauza da bata so ba kuma har a fuskanta ya nuna ya kalla se tace
"in shaa Allah, mun gode"

Daga haka ta mike tayi ɗakinta da kallo ya bita har ta shige, sadda Fatima bata nan kusan a parlorn suke kashe lokacinsu amma yanzu tana so ta komawa halin farko da ta fara zama a gidan.

Mikewa yayi ya bi bayanta, husna na kallo ya nufi wurinta don tana tsaye ne gaban wardrobe kuma in ba husna ta taso ta zo wurin ba ba ganinsu zata yi ba.

Dab da ita ya tsaya har tana jin kamshin shi na cika mata ciki, yace
"Bakya so ne?"

Ta ɗago tace
"me fa?"

Bakinta yake kallo kan yace
"seems like baki ji daaɗin zancen tafiya school da Zaku ke yi da Fatima ba, for now it's my only option don in aiki ya min yawa ba zan dinga iya kaiki ina ɗauko ki ba and I hate it so much in ga matata tana hawa motar haya ko bolt ne kuwa"

Juyawa tayi tana kokarin buɗe wardrobe ɗin tace
"ba komai, na fahimta"

Har yanzu ranshi be bashi ta gamsu da hakan ba, ya rasa me yasa ya matsu kuma yake so ta fahimce shi ba don cin fuska bane yayi hakan, amma dae haka ya hakura ya fita kar ya janyowa kanshi raini a faɗar shi fa kenan.

Washegari da safe ya fito tsab a shirye saide ganin Fatima tsaye a dining yasa ya san yau kam ze yi missing girkin Fauza, zama yayi tayi serving ɗinshi kaɗan ya ci ya miƙe yana duba agogo yace
"zan ɗan fita wani meeting ba zan dawo yanzu ba ku kula pls"

Daidai ya nufi cikin parlorn Fauza ta fito rike da hannun husna shirye cikin hijab dogo tayi kyau sossai, tace
"Ina kwana yaya?"

Yace
"lafiya ƙalau ƙanwata"

Shiru duk suka yi ya ɗan tsaya kan yace
"Na fita"

Tace
"Allah ya tsare ya kiyaye"
Dama abunda yake son ji kenan se yayi murmushi ya nufi gangarawa.

Dama sun sha cereals yau a ɗaki don bata yi wani girki ba, zaman jiran Fatima tayi seda ta ga dama kan ta fito suka sauka zuwa motanta, gaba ta tura husna ta buɗe baya ta zauna.

Tak be Haɗa su ba har suka isa makarantar, Fauza tayi dept ɗinta suka haɗu da Afnan suka yi lecture hall, Afnan ƙanwar matar Faisal ce Dukda basu haɗu da matar ta Faisal ba amma Afnan na yabon halinta hakan ya kwadaitar mata da son zama dasu ko zata rage kaɗaici barin ma in husna ta koma.

Ko da aka tashi saida ta jira Fatima har ranta ya soma ɓaci kan ta zo suka yi gida, abinci marar nauyi ta Haɗa musu suka zauna suka ci da husna kan suka haura sama abin su.

Ko da ya dawo ma abincin Fatima ya samu haka dae ya ci yana Tunanin kwaɓar da yayi da yadda ze gyarota.

Washegari ma hakan ce ta kasance..
Suna zaune a ƙasan bishiya ita da Afnan da husna wurin akwai students haka dake kai kawo duba wani handout take yayinda Afnan ke kara mata bayani don an yi farkon lectures ɗin bata nan.

Wani shirgegen ƙadangare taga yana saukowa daga bishiyar ita ba wai tana tsoron su chan chan bane amma bata so su zo kusa da ita ganin ya tsaya yana ta gyaɗa kai gashi marar kyaun gani yasa ta ɗan ɗaga hannu tayi shhh, ai kaman ta ce mishi ya zo yayi wani irin tahowa da gudu ta kafafunta kan ta miƙe tsaye ya shige mata hijab ƙara ta saki tana ambaton Hasbunallahu wani'imal wakeel....!

***

Tsaye yake gefen Faisal yace
"kwaɓa nayi faisal kuma duk tunanina na rasa yadda zan warware shi wlh"

Faisal yace
"Toh kai ɗin ma kenan bare mu? Wani irin kwaɓa ne haka da ya dameka?"

Shafa kanshi yayi yana jan iska tare da fesarwa yace
"ka gane ko? Yarinyar nan ne a sadda ta zo na ɗauka tayi kankanta da ɗawainiyar gida kuma bazata iya wani aikin a zo a gani ba bare har ta iya girkin da zan iya ci, to my biggest surprise abubuwan da ta iya ko chef da yayi ten years in profession be iya ba, ta kula da cikina tsawon lokacin da Fatima bata nan yanzu kuma Fatima ta dawo se ta sakar mata"

Faisal ya kwashe da dariya yana cewa
"kana raina yaran yanzu my guy... Dama baka raba musu kwana bane?"

Girgiza kai yayi yace
"she's

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login