Showing 69001 words to 72000 words out of 86608 words

Chapter 24 - DIDDIGAR ƘAYA COMPLT Hausa novel

21 Aug 2024

18457

hannunta kawai ya cillata kan gadon ɗakin.

Yunkurin miƙewa take ya bita ya danne, a zafafe ya fara zare mata hijab yana faɗin maganganu da suka saka ta sakar mishi jiki ta Daena fighting kuma, tabbas zata ɗauki mummunan mataki kan wannan abu amma ba yanzu ba, se ya tabbatar ita ɗin ba shashasha bace, lusara, wacce bata san me take yi ba da zata rabe kanta a titi, se ya tabbatar ita ɗin daban take da sauran mata anan ne zata ɗauki matakin da ya dace da rayuwarsu..

A zafafe yake komai tun tana hawaye har ta soma kuka a hankali, daga karshe cikin kuka ta rike hannunshi tana bashi hakuri akan kar ya je mata a haka amma inaaa yayi nisa sossai, kan ta kara furta wani kalma ya haɗe bakinshi da nata yana bata wani irin zazzafar sumba, bakin da ya jima yana tsone mishi idanu...

Saida yayi matukar nisa a tirbar da ya ɗauka kan ya fahimci wani abu da ya so gigita rayuwarshi, saide ba ze iya dakatar da kanshi a wannan yanayi ba, ba ze iya katange kanshi daga gareta ba..

Ƙara me ƙarfi da ta kwala shi ya saka shi kankameta kaman zasu shige cikin juna a take dukkaninsu jikinsu ya ɗauki wani irin mugun rawa, daga ita har shi hawaye suke zubarwa... Ya je mata ne a yadda be yi zato ba se gashi ta shayar dashi ruwan mamaki da baya Tunanin har Abada ze kau daga idanu, zuciya da gangar jikinshi..


Bayan lokaci me tsawo ya mirgina gefe tare da janyo ta ya rungume da karfi kaman wani ze kwace ta
"I'm sorry..! I'm so sorry"
Abunda kawai yake iya maimaitawa kenan hawaye na zuba a idanunshi..

Ita kam Sam bata san inda kanta yake ba, ba karamin wahala tasha ba, babu inda baya mata ciwo da radadi a jikinta, amma Dukda haka tayi juriya me yawa..

Sallah da yaji ake yi a masallaci na magrib ya sa ya zameta ta kwanta, bayi ya shiga ya watsa ruwa da wuri wuri, zuciyarshi cike da emotions da baze iya tantancewa ba, hawayen tausayi da kaunar ta kuwa sun kasa tsayawa a idanunshi, yarinyar nan ta sha wahala for nothing.... He never thought that. meyasa a sadda take kokarin kare kanta a sannan su kuma suka saka mata wani irin kyara da tsana?

Fita yayi yayi masallaci, duk sallar da yake ɗin ba cikakken natsuwa yake ba..
Ana idarwa ya mike ya fito se ga Farida da be san zuwanta gidan ba ta nufosu da gudu..

"Yaaaya Mammi... Mammi"
Da gudu shi da Farhan suka yi sashen Baba prof ma ya rufa musu baya da sauri ganin yadda duk faridar ta gigice.

Yanayin da suka samu mammi se ya ruɗa su, da sauri suka kama ta suka fito da nufin shiga mota a kaita asibiti... Daidai lokacin da wani irin hayaniya da basu taɓa riska ba a gidan ya ɓarke da buge buge kaman faɗa, ko kan ɗaya daga cikinsu yayi wani yunkuri Aunty da Ammi sun iso tsakiyar harabar gidan ana cin uwar sabada....

Faizan cigaba da kokarin saka mahaifiyarshi mota yayi don be da lokacin su se ta rike hannunshi tace a sanyaye..
"Ku fara sassauta wannan bala'i da ya taso kan mu tafi asibitin Faizan"

Gabaɗaya ilahirin ahalin gidan suna tsaye cirko cirko an rasa wadda ze raba se baba Alhj ne ya daka musu mummunan tsawa tare da rufe su da wani irin faɗa
"Me wannan? Me kuke yin nan a gaban ƴaƴa da jikoki? Wani irin bala'i ne wannan? Shamsiyya!! Ruqayya!!!"

Duk wannan be sa sun dakata ba, Ammi tace
"Na jima da sanin ke ɗin makirar ɓoye ce, Algunguma, munafuka ban tabbatar ba se yau.... Ashe ke ce kike ta kokarin kashe min yarinya? Ashe kece kike ta kokarin haukatata ta bi duniya to wallahi baki isa ba... Na fi karfinki saka idanunki cikin nawa ki gani da kyau"

Aunty ma shewa tayi
"Ahayye nanaye... Wai kura ashe ze ce da kare maye? Duma har yana da bakin raɗan maɗaci karki ɗauka ban san ke kike ɓarar da cikin Fatima ba sbd karta haihu da Faizan.... Karki ɗauka Cewar Ban san ke da Ƴar ki Fauziyya kune silar duk wani wahala da Uwar Faizan take ba.... Ko ba ke ce kika harbe mata kafa ba? Ko ba Fauziyya ke saka mata maganin da yake karya duk wani Magani da aka bata take sha ba...????"

Rassssssss haka gaban kowa ke wani irin dokawa suna kallon sabon abunda basu taɓa zato ko tsammani ba...
"WHAT.....!!!"

Faizan yayi exclaiming da karfi gabaɗaya alakanta komai da Fauziyya da aka yi shi ya gigitashi...

Waige Waige yake se chan ya hange ta tsaye tana kuka me taɓa zuciya, da sauri ya karasa gangar ta yace
"Wai da gaske? Da....gaske..ke ke kike sakawa mammi ma...ga...ni?"

Kai ta gyaɗa tana cewa
"Eh nice Amma......"

Wani irin gigitaccen tsawa ya daka mata, har tana shirin faɗuwa.... Haƙorin shi ya sa ya danne lip ɗinshi hawaye ya fara tsere bisa idanunshi, da sauri ya waiga ya nufi mammi...


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤


30

**Wannan shafi sadaukarwa ce gareki Aunty hajjo *Autar Manya* Alkhairin Allah ya cimmiki a duk inda kike ina godiya kwarai🥰❤️**

"innalillahi wainna ilahi rajiun....! Allahumma ajjirni fi musibatin wa akhlifnee khairan min ha.."
Abunda Ammi take iya maimaitawa kenan jin numfashinta na seizing da gudu Farhan yaje ya riƙeta yana aikawa da Aunty wani irin kallo na kaskanci.

"Mammi don Allah mu tafi in kaiki asibiti"
Cewar Faizan, ta girgiza kai tace
"kaima bazaka iya driving a yanayin kan nan ba Faizan, kaima kana bukatar ganin likita a wannan yanayi da kake ciki... Ka yi ta maimaita sunan Allah."

Baya so ne yayi breaking don iyakacin jarumtar hana kanshi faɗuwa yanayi, maganan ya dake shi ne fiye da yadda yake zato ko tsammani... Baba Prof dake rike da kafadan ɗan uwanshi yana ɗan bubbugawa ganin irin yanayin da ya shiga yace

"Duka wannan magana ba na nan bane, mu je parlor bana so in kara jin wani yace tak a cikinku"
Ya bada umarnin tare da janye baba Alhj suka nufi parlornshi.

A hankali hankali kowa ke binshi ciki Fatima na ta kuka cike da baƙin ciki yau kam kila se buzunsu kilan aurenta ya mutu kenan, ya zatayi da soyayyar Faizan?

Jaddah ce ta taka ta nufi Fauza dake tsaye kanta ƙasa tana kuka a hankali, abubuwa dayawa ne suka haɗe mata da kananun shekaru, Zuciyarta, gangar jikinta da kwakwalwarta duka babu wadda yake aiki bisa daidai.

Meyasa Faizan ke min haka? Meyasa a koyaushe fahimtar shi a gareni gurguwa ce? Bata da amsa, kuma a yanzu bata buƙatar sani.

Jaddah da ta riƙeta ta ɗaga kai ta kalla se kawai ta sake rushewa da kuka, jadda ta tsorata ainun da kallon yanayin Fauza ɗin fuskanta ya kumbura sossai kaman wacce ta kwana biyu tana kuka.

"Mu je Fauza"
Ta faɗa tana kokarin jan ta suyi parlorn Baba ɗin saide ta kasa taka kafar ta sbd azabar zafin dake ratsa ta, wani kukan ta sake saki..

"Lafiya me ya sameki?"
Kasa magana tayi se kuka.

"Jaddah su baba, ba hijab jikina"
Se a lokacin Jaddah ta lura ko dankwali babu a kanta gashinta a tufke kuma wlh ta nemi hijab ɗin nata ne bata gani ba gashi ta gigice jin hayaniyar da gidan ya ɗauka sossai.

"A ina kika bar hijabin?"
Kanta a ƙasa ta nuna sashen en mazan.

Ajiyar zuciya Jaddah ta sauke kan ta nufi ɗakin Faizan ɗin don duba mata hijabin.

Abunda ta ci karo dashi shi yayi mugun razana ta, cikin wani irin tsantsar mamaki take karewa beddings ɗin kallo, se kuma hawaye ya fara zarya a idanunta, Juyawa tayi tana kallon bayanta kaman zata ga Fauza a wurin a hankali ta furta
"Allah sarki baiwar Allah!"

Lallai Allah Allah ne, in ba shi ba waye ze iya wanke Fauza daga wannan zargi da aka yi ta mata aka ta shiga hakkinta akan abunda bata aikata ba a idanun dumbin jama'ar gidan nan?
Bedsheets ɗin ta yaye, chan lungun gadon ta samo hijab ɗinta ta fito.

Saida ta kai Bedsheets ɗin toilet ɗinta kan ta dawo ta sanyawa Fauza da har yanzu ke kuka hijab ɗin tare da rungumota
"kiyi hakuri kin ji? Kiyi hakuri Allah ya miki albarka.. Lallai kina cikin masu hakuri Fauziyya sannu.. Ki daure mu karasa na san mu suke jira a parlorn"

Da ƙyar take iya taka kafar da take ji kaman tana takawa ne bisa ƙayoyi, duk taku ɗaya kuwa ita kaɗai ta san zafin dake ratsa ta har cikin kwakwalwarta.

Ilai kuwa sun samu parlorn tsit se kukan Ammi ke tashi, kana jin kukan zaka san na dana sani ne me yawa, ashe hassada ka iya jaza maka bala'in da baka san hawarshi ba bare Sauƙar shi?

Duk da kallo suka bi Jaddah da fauza ɗin kowa na mamakin me ya sameta haka ita kam fuskanta a ɓoye jikin Jaddah ji take kowa ya kalleta ya san me ya faru, shi kam be iya ya ɗaga kai ba har suka zauna.

Bismillah baba prof yayi ya fara da Adu'a kan ya fara da jan hankali akan wannan abu da ya faru a gidan nashi yau wadda ba'a taɓa samun hatsaniya haka ba, ga dae Mammi a sadda aka fitar da ita kaman zata mutu amma yanzu kuma Alhamdulillah da kanta take zaune.

Ammi ya kalla yace
"Ruqayya ke ce babba, don haka dake zan soma, me yake faruwa? Me Shamsiyya ke nufi da kalaman ta? Ko jikina duka kunnuwa ne ba zan taɓa aminta Cewar Fauza zata iya cutar da Aisha ba abunda kuma ba ze yiwu ba kenan so ina so ku faɗa min gaskiya me ke wakana a tsakanin ku?"

Ammi cikin kuka tace
"Wallahi Yaya(prof) ban taɓa sanin cewa za'a iya anfani da ƙi da kuma hassadar da nake yiwa mahaifiyar Faizan a nemi lawye ni ba, lallai duk wadda ya ɗauki hassada abun yi to yayi gaggawar tuba ya kuma kori sheɗan... Ba kowa bane ze nuna yana son ka a fili kuma har a zuciyarsa ta kasance haka, haka kuma ba kowa bane ze nuna tsanarka a fili ya kasance kuma har cikin zuciyarshi haka ɗin ne ba. Zan fara da neman gafararku ku yafemin don Allah"

Duk kai kowa ya gyaɗa kwarai haka magananta hassada mugun ciwo ne, amma ba wannan tukuna suke son ji ba.

"Ɗazu bayan na idar da sallah, se na duba ban ga redio na ba se na tuna ashe Shamsiyya ta ara da rana taji wani program a ABC don nata ya ɗan samu matsala har ta ba Farhan ma ya kai mata gyara.. Kaman Allah ne ya turani ina zuwa na samu tana yiwa Fatima faɗa akan tana kokarin ɓata mata aiki da tun kan ta shigo gidan nan take ginawa, na so shiga se kuma jin ta ambaci sunana a farkon fari yasa na dakata.. Ga abunda take cewa in na mata ƙarya kar Allah ubangiji yayi min gafara...

'Fatima kin san abubuwan da na aikata kuwa? Toh buɗe kunnen ki ki jini ina ga baki sani bane yasa kike min wasa da aiki, tun farkon fari Professor na so aure se kuma ya fi karfina da naje aka duba min se aka tabbatar min da Cewar babu aurenmu da professor har duniya ta nade sede ya hangi aurena da Sulaiman har da zuri'a, tun a lokacin na sa ya bincika min matar Sulaiman wato ni kenan(Ammi ta nuna kanta) tashin farko ya faɗa min cewa tana da halin saurin fushi sannan kuma ta kan ji haushin mammi ganin kaman ta fita a komai a gidan har miji, kai natse na mishi umarni da ya kulle zuciyarta, ni kuma zan koma in kashe aurena in dumfari gidan se na tabbatar duk wasu arziki nasu ya kasance cikin tafin hannuna.

Kai tsaye ya samu nasara sbd shaidan dama ya riga ya darsawa Ammin hassada a ranta, Zuciyarta ya zama baya jin komai ƴaƴan da na haifa ma ban damu dasu ba bare miji da surakai..."

Kuka ne yaci karfin Ammi tana tuna yadda take wasarere da rayuwar ƴaƴanta barin ma Fauza da ta fi bukatarta da kowa, Amma ta kan gode Allah dayake ba azzalumin bawa bane ya baiwa Fauza Jaddah da mammi da kuma baba prof.

Auntyn ce ta ɗan sosa kanta kan tace
"Ai baki faɗi komai ba ruqayya, wannan kaɗan ne daga cikin kaidi na.. Bayan na sa an rufe zuciyarki ana kuma anfani da kwakwalwarki se na zo na aure miki miji, tashin farko na fara kokarin cusa Fatima ga Faizan don na san ta hakan ne kawai zan samu abunda nake so, se bokana yace min idan dae har Mahaifiyarshi na da cikakken lafiya burina baze cika ba don ita ɗin a tsaye take a cikin gidanta kan mijinta da yaranta.

Dukda ya tabbatar min da cewa ko an nakasta kafafun nata zata iya cigaba da nemawa yaranta kariya wurin rabba se na ce ya saka mata ciwo me tsanani wadda baze bar ta natsuwar lafiyar nema musu sauƙin ba, kwatsam se muka samu ciki ni da Ruqayya, da na koma ya duba min se ya tabbatar min yarinyar cikin Ruqayya masifa ce ga rayuwata don itace zata yi silar tabarbarewar duka aiki na in ban yi wasa ba, kai tsaye na nemi a ɓarar da ita ta bi rariya yace in bada kwanaki, duk wani hanya da ze bi don zub da cikin babu nasara ko da ya faɗamin nima ban zauna ba, hatta da maganin zubar da ciki na saka overdose na bata a kunu sede cikin nan ya ƙi barewa abun ba daaɗi wai mahaukaci ya ci kashi, duk inda muka buga cikin nan yaki ya lalace se ya kawo shawarar a dasawa mahaifanta tsanar ta musamman uba, suyi ta mata mugun fata ita kuma tun daga cikin za'a sa mata taurin kai na bugawa a jarida yadda zata gallabi kowa..

Hakanan destiny ɗinta a sarƙe yake da Faizan shima za'a saka mishi tsanar ta kaman yadda itama baza'a bari ta so shi ba ko na minti guda, duk a aikin mun manta da Jaddah, Baba prof da mammi a tsanar na Fauza saide mutanen duniya da iyayenta yadda za'a yi ta mata baki ta bi duniya... Hakan kuwa ta kasance don haka ta ta cimma ruwa sbd tunda Fauziyya ta fara wayau kowa ke kuka da ita.

Mun kawar da hankalin baba prof kan Faizan ta yadda duk haɗe Haden auren da yake yi be bi ta kan Faizan ba, Ganin kissa ta bazata saka Faizan ya kula Fatima ba yasa na koma ma bokana da kukan damuwata, nan da nan ya ce ze yi aikin karkato hankalinshi dama already kaman yadda akwai tsana me girma tsakanin shi da fauza haka tsakanin mahaifiyar Fauza dashi, ita kuma ta fara jin haushin shi ne sbd abubuwan da yake yiwa fauziyya amma dayake bata da damar nunawa sbd akwai aiki a kanta se ya zamana ta fara tsanar shi a ranta wadda mu kuma muka kara rura wutar.

Fatima ta tashi ne da tsananin son Faizan sbd shine nake kwadaitar mata a kullum as miji, ita tayi ta matsawa nayi ta shiga da fita har aka ɗaura aurensu suka tattara suka tafi, burina na lalacewar rayuwar Fauza ya cika na kuma san ko a kafa aka ɗaurawa Faizan ita se ya kunce ya yasar, sbd ta zama itace yawace yawace, shaye shaye da Zin....."

Faizan da Jaddah suka Haɗa baki cikin kunan rai suka ce
"Fauza bata yi zina ba.."
Hawaye ne ke zubarwa Jaddah kaman yadda Fauza ke kuka marar sauti tana jin ita kuma yadda aka yi da rayuwarta tun tana cikin cikin mahaifiyarta.

Cigaba Da bayani tayi..
"Kwatsam Professor ya shammaceni aka ɗaura auren Faizan da fauza duk wata hanya da zan bi wurin ganin na wargaza auren hakan be yiwu ba, na ba Fatima baki akan duk yadda zamu yi mu lalata auren se mun yi, bani da masaniyar cewa igiyar aure da girman darajarshi ya warware wasu abubuwa nawa masu dumbin yawa akan Fauza ciki har da rashin ji da saurin faɗa, rashin kunya da kuma shaye shaye, se da na koma wurin bokana yake faɗamin, Fatima taki kwantar da hankali tayi tayiwa Fauza abubuwa wadda a hankali ya kawo kusanci tsakanin Fauxa da Faizan se kuma ta dawo ta haukacemin, gashi Allah da ya fi ni dabara se ya hana cikin Fatiman zama bare in saka ran mallakar burina.

Komawa nayi nace ko ta karfi ko ta tsiya a fitar da fauza daga gidan Faizan, ko kasheta ne ayi, shine aka tura mata ƙadangare da nufin kasheta amma Allah ya bata kariya, aka sake nufin haukatata sbd ranar ne muka samu dama ta kwanta da zazzaɓi bata iya tayi Adu'ar bacci ba shi kuma Faizan ya mance be yi mata ba, a son mu ne fitan tan nan ta bi duniya amma se Allah ya sake kare ta ta kawo kanta gida. Wannan shine abubuwan da na aikata ni shamsiyya...."

Salati kowa yake yi, wasu na ta kuka barin ma fa'iza da ta fi wayo cikin yaranta kaman zata hadiye ranta, Farhan ne dake kusa da ita ya iya miƙa hannu yana lallashin yarinyar, Allah sarki uwar su bata duba kananun yara har uku da take dasu ba kwata kwata babu wacce ta kai secondary, ta aikata irin waennan abubuwa har gwara su kuma da Fatima da ta ɗaura a Keken ɓera wadda ya dire su a tashar dana sani.

"Fauziyya me yasa kika amsa Faizan cewa kina shafawa Aisha magani?"
Baba prof yayi mata tambayar, tana cikin ciwo bazata iya magana ba, abubuwa sun mata yawa kuma sun haɗe mata, Aunty da Fatima sun cutar da ita mafi munin cuta kuma bazata taɓa yafe musu ba har duniya ta tashi.

Kirjinta ciwo yake mata, gabadaya ji take kaman zata mutu.

Ammi ce tace
"Kwarai tana shafa mata magani da wani Adu'a wadda ni na bata, maganin kuma wurin kawu na Wadda yake bada magungunan gargajiya na musulunci nake karbar mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login