Showing 39001 words to 42000 words out of 86608 words
ɗakin Fatima don ɗauko mata hijab su tafi asibiti.
"Na san ba haka kika so ba ko? To mu zuba da ni dake ɗan halak ka fasa, in makirci ne ke jiya kika soma amma Fauza kam ta jima a ajin don ina ga har ta gama ma ta fita da sakamako me kyau"
Jin motsin kaman yana dawowa ne yasa tayi saurin karasawa tana ɗagota tace
"I'm so sorry ya fati"
Hijab ɗinta ya miƙawa Fauza ta saka mata, sakawar ma na mugunta ta mata don seda ta karɓa da kanta ta karasa a hankali.
"Karki ci abincin nan, ki nemi wani ki ci bari na kaita asibiti.."
Kanta kasa tana zub da hawaye ta ɗan ɗaga, har ya kama Fatima a jikinshi sun nufi stairs ya ɗan dakata tare da waigowa kaman ya zamar mishi dole yace
"kukan nan kuma ya isa haka"
Yana kai nan suka fara sauƙa.
Wani kalar dariya Fauxa tayi tace
"gobe zaki maimaita abunda kika min munafuka kawai"
Dining taje ta samu abincin shin ma be gama ci ba ya tashi, ta kara akai ta ci tayi Nak ta tattare wurin kan ta zo ta fara kimtsa parlorn da ba wani datti sbd rashin mutane dayawa a gidan.
Bayan ta gama ta koma ɗaki tayi kwanciyarta cikin kewan jaddanta kan bacci ya sure ta.
Chan cikin baccin ta taji ana taɓa gefen hannun kujeran da tayi matashi dashi, yadda ta saba yiwa jadda in bacci be ishe ta ba ta tura baki ta mike cikin kunkuni tana kaikaya idanu haka tayi, a hankali ta buɗe idanun nata se suka faɗa cikin nashi, yana tsaye hannunshi ɗaya a aljihu ɗaya na riƙe da Wayanshi, har kaman ze mata faɗan kwanciya bisa kujera se ya fasa.
"Riƙe Jaddah ke son Magana dake"
Ya faɗa yana miƙa mata wayan.
Da sauri ta karɓa
"Jaddah na!"
Tayi maganan tana karya wuya se hawaye..
"Haba Fauza, ke da nake miki kallon jaruma ashe ke ɗin raguwa ce kukan ma menene to? Yayyun naki suna miki wani abu ne?"
Yadda ya kakkafeta da idanu yana jiran jin me zata cewa jaddan yasa tace
"babu komai Jaddah kawai nayi kewanku ne"
Tace
"nima anan hankalina da tunanina duk yana wurinki Fauziyya fatan babu komai ko? In akwai wani abu ki gayamin"
Tace
"ba komai, ina mammi ya kafafunta? Allah sarki yanzu wa ze dinga mata Adu'a oho"
Ta faɗa cikin alhini.
Murmushi Jaddah tayi tace
"tana yiwa kanta amma na san tayi kewanki itama, fadyaa zasu taho ranar Laraba me kike so a kawo miki?"
Zata yi magana ya zare Wayanshi ya sa a kunne tare da Juyawa ya nufi fita yana cewa
"Zaku ƙarar min da credit, me zata buƙata kuwa yarinyar da ta zo jiya in ba ke ba ma Jaddah"
Zata fara mishi nasihun da suka kashe mai jiki da niyyar da yayi a kan yarinyar yayi saurin kashe wayan, daga Jaddah, Babanshi da mammi duk in sun kira ko ya kira su maganan ɗaya ne kar ya sa yarinyar nan kuka kanwarshi ce wacce ko ba aure shi me share mata hawaye ne, hakanan bata da kowa a Abuja in ya cuceta don ba idanunsu Allah na gani kuma ze saka mata.
Yana zama kan kujera se ga call na baba prof suka gaisa kan ya ce
"na manta ne ban maka maganan karatun yarinyar nan ba, ka san ko bare na aurarwa ɗiyata akwai sharadin yin karatu to akan Fauziyya ma ba zai sauya zani ba, idan Neco ɗinta ya fito zaka nema mata university of Abuja su cigaba da zuwa da yayarta"
Idanunshi na kan TV ya ɗan fesar da iska yana shafa kai yace
"Baba ba za'a bar maganan makarantar yarinyar nan mu ga kamun ludayin ba tukun? Ba wai ina nufin ba zata yi bane sede ina tsoron komawarta halin da ta shiga a baya ne wadda yanzu se ya fi zunubi da da, tunda yanzu tana da aure"
"in shaa Allahu yanzu bani da shakka akan Fauziyya zata maida hankali tayi abunda ake so, mu cigaba da Adu'a dae kar mu gajiya sannan ka riƙe ta amana kaman yadda ba zaka cutar da farida ba karka cutar da ita Faizan"
Ajiyar zuciya me nauyi ya saki yana sake shafa kanshi Fatima ta fito ta zauna kusa dashi tana cewa
"ya aka yi ne?"
Ya ce
"Fauziyya...! Kowa ya tashi amana amana duk sun ɗaure ni da jijiyoyin jikina wallahi"
Bakinta ta taɓe kan tace
"amma yaya ka san yarinyar nan da gangan ta so cutar dani ɗazu? Ai ko bata san ina da BP ba ta iya girki me yasa bata yi me kyau ba?"
Yace
"Meyasa ne kike son dawo da abunda ya riga ya wuce Fatima? Yarinyar nan ta baki haƙuri ba shikenan ba? Kina ji dae ina faɗa miki yadda ake bani amanarta kina so ne in yi ta jan matsala tsakaninmu har iyayemu su yi fushi damu?"
Girgiza kai tayi ranta na zafi, wai ina duk tsanar da yake cewa yana yiwa Fauziyyan? Duk a kwana ɗaya baya bata wani wuta wuta kaman ma lallaɓata yake akan wani dalili? Idan ta bar zaman nan ya cigaba a haka akwai matsala dole zata nemi wani hanyar wargaza tsakaninsu.
Da sauri ta miƙe ta ɗauki wayanta dake kan table ta nufi ɗakinta don neman shawarar abin yi...
DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰
Karku sake a baku labari.
🖤Gureenjoh🖤
DƘ
18
Bata san me ya hau kan Fatiman ba ta dena shiga mata sabga girki ma idan ita zatayi bazata ci ba, se ta koma dafa nata ita kaɗai ita Fatiman nayi musu su biyu.
Tsakanin ta da shi kowani asuba ze tasheta sallah, anan take gaishe shi ba zasu sake haɗuwa ba se wani asuban sbd bata fita a sadda taji motsin su a parlor, babu ruwanshi da komai nata tunda bata rasa ci da sha ba don be katangeta ta harkar abinci ba kullum kawo abubuwa ake a loda a fridge se abunda taga daman dafawa.
Iyakaci ta ci ta sha ta kwanta, a sati biyu da suka yi tayi wani irin kara girma fatanta ya sake yin fresh sbd zama wuri ɗaya, kaɗaici duk ya dameta gashi bata da waya bare ta ji mutanen gida.
Yau bata nemi abinci ba sbd wani series da ake yi a Star life da ya ɗauke mata hankali bata kula da lokaci ba kawai taga magrib yayi ko da tayi sallah bata tashi ba har tayi isha kan ta mike ta ninke hijab ɗin ta ajiye, sanye take da wani half gown wadda iyakanshi kaurinta purple ya zauna mata das a jiki, gyale ne yake dashi se ta mishi ɗaurin da ya fitar da jelar gashinta yana reto, ɗan kunne fashion purple ne a kunnenta haka ta buɗe kofan ta ta fito.
Dasu ta ci karo yana zaune hannunshi da remote Fatima kuma na kwance a kan cinyar shi cikinta gwanda ne a bowl da ta yanka kanana tana ci a hankali, jin motsin ta yasa duk suka ɗaga idanu suka zuba mata kowa da abunda yake saƙawa a ranshi..
Kaman bazata yi magana ba se tace
"Sannunku"
Be amsa ba ya maida kai TV haka Fatima ma bata amsa ba, a wuya yarinyar ta tsaya mata barin ma yadda take kara murjewa tana kyau kaman ka sure ta, ba don umarnin da aka bata na ta ɗauke kai a kanta zuwa ɗan wani lokaci ba da bata barta tana morewa zamanta gidan ba.
Kwafa ta ja a ranta tana cewa
'Fauza kema maganin ki'
Daga haka ta nufi ƙasa abunta, kitchen ta je ta fara Haɗa macoroni salad ɗan daidai na cikinta, bayan ta gama tayi smoothie na ayaba da madara ta zuba a cup, kyuiyar haurawa taji dashi don se ta sake fito da kwanukan bata iya bari a ɗakinta don haka dining kawai ta karasa ta zauna ta fara cin abincinta.
Da ma ze yiwu da ta ce a dawo mata da kayan ɗakinta ɗakin ƙasan tana rayuwanta hankali kwance, da kyar ta gama ɗan abincin taje ta dauraye plate da cup ɗin ta mayar ta kara kimtsa kitchen ɗin don tsabtar gidan banda dakunan masu gidan har yau bata dena ba.
Haurawa ta nufi yi yanayin da ta iske su ne yasa tayi saurin ɗauke kanta ta nufi ɗakinta Dukda sun riga sun Haɗa idanu dashi, janyewa yayi wadda hakan ya sa Fatima Juyawa se ta ganta tana kokarin shiga ɗakinta, tana ji Fatima na tsaki sede bata juyo ba Dukda kuwa so take tayi waya da su jadda kaman me.
Haka dae ta kwanta tana ta juye juyen kewa kan bacci ya sure ta, washegari da asuba da ya shigo ɗakin ya jima tsaye yana kallon yadda ta kwanta ɗin a matukar takure irin kaman mutum na kaɗaici haka, se ta ɗan bashi tausayi bubbuga gefen pillown yayi tayi miƙa wadda ya saka shi saurin ɗauke idanu daga kanta kan ta miƙe zaune bakinta na motsin Adu'a kaman yadda ta saba tana gamawa tace
"Ina kwana"
Ya amsa
"lafiya"
Ɗan tsayawa yayi be fita kaman yadda ya saba ba yana tunawa da Fa'iza ta zo gidan basa barin ta tayi mintuna arba'in ɗaki dole zasu zauna da ita su yi hira a ci abinci ayi kallo duka, amma in ba jiya ba ya manta rabon da ya ganta tana tafiya zata kitchen ko wani abu Sam basa haduwa se a ɗakinta in ya zo da asuba ba dole ta takure wuri guda ba!
"Kina da wani matsala ne?"
Ya tambaya.
"A'a amma don Allah ina so zan yi waya da su Jaddah yau sati biyu kenan rabon da in ji muryarta"
Ta karashe tana Kallonshi da idanun baccin ta waenda suka kara girma da haske ba kaman na normal wasu mutanen ba da in sun tashi idanunsu yayi ja.
Wayanshi ɗaya ya fitar daga aljihunshi fara sol design ne da bata taɓa gani ba don ba iPhone bane ba kuma dangin su tekno bane.
"Yanzu yayi sassafe da ƙira, anjima se ki ƙira su"
Hannu tasa garin saurin karɓa hannayensu suka shafi na juna, duk ɗaga kai suka yi suna kallon junansu kan ya ɗauke nashi yana furta
"saura ki kira waenda basu dace ba ki ga ikon Allah"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Baki ta karkace tana tuna su waye ne basu dace ba? Kwafa tayi su sakina ne kilan yake nufi, ajiye wayan tayi taje tayi alwala ta zo tayi sallah.
Bayan ta idar ta koma ta kwanta se seven ta tashi ta fara gyaran ɗakinta tana gamawa taje tayi wanka ta shirya cikin wani Hot red top da black wando ta ɗaura black ɗan kwali, bakinta ta sanyawa red lipstick se tayi wani irin kyau, kwalli ta zana a idanunta kan ta ɗauko wayan ta zo kan kujera ta zauna.
Sliding tayi se wani hotonshi hadadde ya bayyana, sanye yake da kayan aikinshi cikakke yayi wani irin kyau gashin kanshi na sheki yana dariya ne tsaye a matakalar jirgi aka ɗauke shi, kurawa hoton idanu tayi na mintuna masu yawa kan ta sauke ajiyar zuciya tana shiga call logs.
Bata san da me yayi saving number ɗin jadda ba se kawai ta shigar da numbobin tunda tana dasu a kai.
"Jaddah na"
Ta faɗa bayan an ɗaga wayan ko sallama bata yi ba.
Jidda da ita ma muryarta ya bayyana jin daaɗin ta da jin muryar Fauzan tace
"Na'am Fauza ta ya kike? Ya gidanki?"
Shagwabewa tayi tana cewa
"shine ko kewata baki yi ba ko Jaddah"
Jaddah tace
"na isa ban yi kewar baki abun magana ba? Ai ba karamin kewanki nayi ba babu me sakani magana da shari'a, babu me nemo faɗa in tare, babu wacce kullum ke sakani kumbiya kumbiya idan professor ya aiko nemanta"
Dariya Fauxa tayi tana jin tayi missing old life ɗinta, rayuwa fa kenan! Waye ze yarda yanzu Fauxa tayi sati biyu bata nemi faɗa ba, ai da a da ɗinta ne ko Fatima bata nemeta ba wallahi ita se tayi yadda tayi ta nemeta faɗa, amma gani take yanzu ta wuce level ɗin sede in an nemeta a samu.
"Jaddah to meyasa bakya nemana?"
Ta faɗa tana tura baki.
"Kullum sede wannan me katon kan yace min baya gida ko kin yi bacci..."
Hannunta ɗaya ta ɗan sa baki tare da zaro idanu tace
"khaihh Jaddah Ya Faizan ɗinne me katon kai? Wlh kanshi daidai ne"
Salati Jaddah ta ɗauka muryarta cike da farin ciki da dariya tace
"innalillahi.. Fauziyya yau ke kike karbawa Faizan faɗa? Azzalumin?"
Da sauri ta katse wayan kunyar duniya na kamata, me ya kaita? Wlh ta ma rasa ya aka yi tayi wannan subutar bakin, ai se ta shiga bakin duniya in dae Jaddah ce.
Jaddah kuwa a ɓangarenta har sujada tayi na jin daaɗi, ko basu zama kaman yadda take so ba alamu sun nuna lamuransu akwai haske, da Faizan na cutar da ita ta tabbatar ita ce ma zata fara kawo sukarshi yau wace rana!
Sake kiran layin tayi da kyar Fauziyya ta ɗauka..
"Eyyaa Jaddah kewa!"
Ta fara kawo maganan dake ranta.
"Ina jin kaɗaici da kewa sossai, babu inda nake zuwa babu wadda ke zuwa guna banda waya bare in dinga jin muryarku, jadda ko Ya fadyaa da kika ce zasu zo basu zo ba har yau"
Jaddah tace
"haka aure dama ya gada barin ma a wuri me nisa, kiyi hakuri zan mishi magana ko wayan ne se ya saya miki ai ba wani matsala kuma bayan wannan ko?"
Kai ta gyaɗa tace
"babu"
"Ina Fatima kwana biyu itama bamu gaisa ba"
Tace
"Ina ga ta tafi school"
Hira sossai suka yi jadda tayi ta faɗa mata abubuwan da suke faruwa a gidan, wadda ya mata ta dara wadda be mata ba ta tofa albarkacin bakinta wani kuma tayi Kwafa, barin ma su ya Farhan kam.
Da kyar suka yi sallama don har katin Jaddah ya kare ta sake kira da wayan Faizan ɗin.
Bayan ta sauke wayan fuskanta cike da annashuwa ta shigar da layin Mammi.
"FIRST LOVE"
Sunan da taga yayi saving kenan da emojis ɗin heart, murmushi ta saki tana tuna nata uwar wadda basu taɓa magana ba tunda ta zo.
Bayan mammi ta ɗauka suka gaisa take tambayarta kafanta tace
"Fauziyya kafafun nan se godiyar Allah amma kam da abunda yake nema"
Fauziyya bata gane zancen ba tayi mata Adu'ar samun lafiya, bugan cikinta mammi tayi tayi don taji ko Faizan ɗin na mata wani abu sai de ko ɗaya bata kawo wani laifinshi ba don be matan ba, shakuwa ne dama chan babu tsakaninsu, zaluntarta da ya kan yi in ta mishi abu kuma ya daina tunda bata mishi koman ba.
Daga karshe da dabarun zama da miji da kuma nasihu mammi tayi ta mata kuma tana ɗauka wannan karo kam har tana mamakin kanta.
Bayan sun gama ta kira Ammi..
"Assalamu Alaikum Ammi"
Fauza ta faɗa bayan Ammi ta ɗauki call ɗin.
"Wa'alaikumussalam warahmatullah Fauziyya ke ce?"
Shiru tayi jin muryar Ammin nata babu ɗauki sossai kaman yadda muryar jadda da mammi suka bayyana mata kewanta da suka yi tace
"ni ce Ammi, kuna lafiya? Ya baba?"
Ta amsa da
"lafiya kalau ya gidan naki? Fatan dae baki bari ana hawa kanki kaman yadda kike da?"
Meyasa kowa ke mata nasiha ta zauna lafiya da mijinta amma mahaifiyarta kuma na shirin kawo rabuwar hankalinta?
"Ammi ai babu abunda suke min, muna zaune lafiya"
"mene? Ashe dama karyar kiyayya kike yiwa Faizan ɗin kenan, na tabbatar shi kuma a wurinshi ba haka take ba don kiyayyar namiji bata taɓa gushewa, kuma bata sauyawa, kiyi tunani dae... Sannan ki sani mijinki ba ke kaɗai ba har ni ba ƙaunata yake ba ke hatta mahaifinki don gani yake mahaifinki kusan rabi da kwatar dukiyarshi na Mahaifinsu ne shiyasa yanzu yake saka idanu akan harkokin business na babanki fiye da yadda yake sakawa Faraj da ya fara kula da na babansu"
Shiru tayi cikin dan nazari kan tace
"Ammi wannan duk ba wani abu bane, kilan ba yadda kike tunani bane don na san dukkaninmu da Baba Alhj da Baba prof duk iyaye muka ɗaukesu kuma matsayin abu guda babu banbanci, sannan Ammi ai maganan yaya Faizan baya kaunarki tun da nake na san yana zuwa gaishe ki amma baki taɓa buɗe baki kin amsa ba kuma har yau har gobe kenan be tsane ki b....."
"Rufe min baki, ina nuna miki gabas kina yamma... Ke kika sani"
Tana kai nan ta kashe wayan..
Da idanu tabi wayan cikin mamakin Amminta, ta jima sossai tana nazari dayawa daga cikin ɗabi'un Ammin nata sede ta rasa a wani mataki ko matsayi zata ɗaura shi.
Baba prof ta kira shima yayi farin cikin jin tana cikin ƙoshin lafiya ya kuma yi mata albishir da result ɗinta na neco ya fito kuma yayi kyau don har yayiwa Faizan maganan yi mata registeration na jamb.
Taji daaɗi sossai tayi ta godiya da Adu'a ga baban, nasiha ya sake mata ya kuma gargadeta da Adu'a kaman yadda ya bata wani takarda da ke ɗauke da Adu'o'i masu yawa ya kuma umurceta da ta lazimcesu kuma tana yi ɗin sossai.
Bayan sun gama ta kira babanta shima ya ji daaɗin jinta lafiya ƙalau Dukda kullum a tsorace yake kar ta shukawa Faizan abunda ze zama silar tsinkewar zumuncinsu, idan har ze ga wayan Faizan se gabanshi ya faɗi da Tunanin ze ce mishi Fauza ta yi wani abun sede duk be ji ba, tun yana tsoracen yanzu har ya fara sakewa.
Nasiha shima yayi mata wadda be mata a lokacin barin ta gidan ba kuma ta ji daaɗi suka yi sallama tana ji matar nan na Mtn na cewa one minute remaining.
Sosa kai tayi bayan ta sauke tana kallon wayan yau ƙaniyarta Faizan ze ci ta ƙarar mai da katin waya.
Balcony ɗinta ta fita tana kallon harabar gidan da Gidajen unguwar da yawanci kusan irin nasu ne benaye, wayan ta sake ɗagowa ta shiga camera tare da Juyawa ya bata background ɗin unguwar Ta fara pictures style kala kala tana murmushi barin ma da taga yadda tayi kyau.
Seda ta gaji ta dawo ɗakin ta zauna a coffee chair ɗin tana kallon pictures ɗinta, tana cikin scrolling taga nata sun ƙare sun shiga na wayan, bata tsaya ba ta cigaba da scrolling yawanci hotunanshi ne wasu