Showing 51001 words to 54000 words out of 86608 words
murmushi yana girgiza kai, shi duk labarinta da ake bashi be ga ko ɗaya ba banda sanyin hali da tsoro kaman farar kura.
Fita suka yi da Jafar zuwa masallaci suka yi sallar magrib, bayan sun dawo suka shiga wurin Fatima sun samu ta farka, dukkansu biyu da kyar ta amsa musu gaisuwar su, babu wadda ya sake magana sbd ganin yanayinta se Faizan ne ya bata umarnin tashi su wuce, haka ta mike yace taje mota ta jira shi gashinan zuwa.
Ita kuwa tana zuwa motan ta buɗe baya ta shiga a dole tana fushi da shi na goyon bayan Fauza da yayi, yana isa office na Jafar ya samu ma har baccin wahala ya ɗauke ta.
Haka ya sa hannu ya ɗauke ta, ta gyara kanta kan kafadanshi ta cigaba da baccin ta, husna ta biyo bayansu Jafar da ya rakosu ganin Fatima a baya ya sa hannu ya buɗe mai gaba ya sanyata.
Ashar Fatima ta lailayo ta buga, da sauri ta sauko tace
"Ya Faizan wai me kake nufi dani ne?"
Yana gyara Fauza yace
"kaman ya kuma Fatima? Duk maganan da zamu yi yanzu ki bari mu je gida pls"
Tace
"in bari mu je gida? Na rasa cikina sbd wannan karuwar...."
"Shutt uppp Fatima!!"
Ya daka mata tsawar da har saida Fauza ta tsorata tare da watsakewa daga baccin da ya cika mata idanu.
Itama cikin kukan baƙin ciki tace
"ba zan yi shiru ba yaya, ba zan yi shiru kayi ta zaluntata ba... Ta ɓarar min da ciki baka ce mata komai ba, asibitin ma ka zo ka ajiyeni kayi tafiyarka wurinta, ni da ya kamata ka ɗauko ka kawo mota baka ɗauko ni ba ka je ka dauko ta a hannu sbd tayi bacci, ni gani ƴar iska marar gata... To Alhamdulillah na gode Allah da baka sameni a watse kaman kofar taxi b......"
Mari yake shirin sauke mata sbd yadda ranshi ya ke tafarfasa Jafar yayi saurin riƙe shi.
Ita dae Fauza bata ko motsa ba banda idanu da take binsu dashi, sbd yadda idanun Fatiman ya rufe bata yi shiru ba tace
"ka barshi ya mareni Jafar, ya mareni tunda ni ce karamar dangarshi me daaɗin hawa, ba se ka mareni zaka nunawa duniya cewa ni ɗin ba jininka bace, ba se ka mareni zan san cewa kana fifita wanchan karuwar ƴar shaye sha...."
Marin da bata sha ɗazun ɗin ba shi ta sha yanzu saida ta kusa kaiwa ƙasa, hannun da ya nuna ta da shi har yana rawa yace
"Ki kiyaye ni Fatima, ki kiyayi ganin ɓacin raina kuma ki rufe min baki ki shiga motar nan mu tafi...!"
Jafar yace
"Haba Faizan in ita ta rasa hankalinta tana faɗar abubuwan da basu dace ba kai be kamata ka biye mata ba, ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi har ita ta sauko kan ka nuna mata rashin kyautawar abunda tayi ɗin, zafin kishi ne kawai ke dawainiya da ita da kuma na rashi da tayi ka san dae se ta fi ka jin zafin hakan"
Kallonshi Faizan yayi yace
"zafin kishi? In zafin kishin ne se aka ce a rashin hankali yake zuwa?"
Juyawa yayi kanta yace
"I can tolerate anything but don't u dare cross ur boundaries... Ki wuce ki shiga mota mu tafi I won't repeat myself"
Yana kai nan ya buɗe motar ya saka husna da har ta fara kuka, kan ya juya ga Jafar yace
"zamu yi magana"
Daga haka ya zagaye ya shiga motar, ya tayar idanunshi na zube kan hanya, saida yayi kaman mintuna uku da tayarwa har yana shirin jan motan yayi gaba kan Fatima dake kuka ta shiga, ita dae Fauza sannu bata ce musu ba ya tsaya restaurant ya musu takeaway kan suka kofanufi gida.
Yanzu ɗin ma zagayawa yayi ya buɗe ya ɗauke ta, ko Fatiman be kalla ba ya nufi ciki, a kan gadonta ya ajiye ta har ya juya ze fice tayi saurin riƙe hannunshi wadda dukkansu saida suka ji har cikin ƙashinsu.
Fuskanshi ya juyo ya kalleta cikin sanyin murya tace
"I'm sorry...! Ban san hakan ze faru ba da ban biye mata ba, pls kayi hak'uri"
Ta karashe tana duƙar da kanta ƙasa.
Zama yayi yana ɗan murza hannunta dake cikin nashi Ɗayan kuma ya ɗaura a kan kumatunta da har yanzu yake kumbure ya ɗan shafa dukkansu suka lumshe idanu, wani sanyi ya ji a ranshi wadda be san na menene ba, ɗago idanunta tayi ta kalleshi dasu daidai shima ya buɗe nashi dake lumshe.
Chan ƙasan maƙoshi yace
"it's not ur fault, haka Allah ya tsara cikin ba me zama bane... Amma me ya Haɗa ku?"
Tiryan Tiryan ta bashi labarin abunda ya faru bata ɓoye komai ba, yadda suke kallon juna a cikin idanu kuma ta bashi labarin ba rawar murya ko wani kame kame ya san cewa babu ƙarya a cikin labarin nata, murmushi ya saki kawai da nufin tsokanarta yace
"Eyye ashe ƴar gurguwa kunnuwanta na ji da kyau tunda har ta ji sadda loudspeaker ke sanar da cewa ita ɗin ta zama matar Faizan"
Da sauri ta zare hannunta tare da kare fuskanta tana murmushi shima yana murmushi yace
"Haba ƴar gurguwa kunya kuma?"
Baki ta turo tana cewa
"ni Allah ni ba gurguwa bace"
Yana miƙewa tsaye yace
"Toh Ladi chogal"
Ihu ta sake tana kukan shagwaɓa ya fice abunshi yana dariyar shagwaɓar tata.
Se bayan ya fita ta saki murmushi ashe ya Faizan haka yake?.
Abincin da ya sayo ya koma ya ɗauko, a plate ya juye takeaway biyu da ruwa ya sa kan tray ya ɗauka ya kaiwa Fauza ɗin, yanzu kam be ce mata komai ba ya ajiye mata ya baiwa husna nata kan ya juya ya fita.
Na Fatima ya ɗauka ya nufi ɗakinta dashi Dukda yadda yake jin ɓacin rai na abunda ta mishi ɗin amma be fasa zuwa ba.
Tana zaune tana kuka ya shiga ɗakin, abincin ya ajiye mata kan ya juya shima yaje ya ci nashi, an riga an yi isha so ɗakinshi kawai ya shiga ya watsa ruwa yayi sallah, bayan ya idar ya mike yaje ya duba maganin Fauza ya nufi ɗakinta dashi.
Samu yayi tana sallah daga zaune, toilet ɗinta ya shiga yana yabawa tsaftarta don bayin ta ba zaka ce ana anfani dashi ba ya samu roba ya tare ruwan zafi ya samu Towel ya fito.
Husna tayi bacci ya ɗauke ta ya ɗaura ta kan gado ya sauya mata kaya daidai lokacin ita kuma ta idar.
Da taimakon shi ta koma bakin gado, ya janyo stool ya zauna tare da ɗaukan kafan ya ɗaura kan cinyar shi.
Ruwan da zafi sossai haka yayi ta danna mata tana raki tana yarfa Hannu, da muzurai da komai aka gama dannar ya bata magani ta sha, yace
"dube ta..!"
Baki ta turo kayan bacci yaje ya ɗauko mata ya ajiye mata gefenta kan ya dube ta yace
"akwai wani abu kuma?"
Kai ta girgiza yace
"tohm se da safe Allah ya qara sauƙi"
Tace
"thank you"
Ya juya ya fice ta bishi da kallo har ya maido mata da kofan ya rufe.
Maganin Fatima ya ɗauka ya nufi ɗakinta.
Har yanzu tana kuka, zama yayi bakin gadon yace
"Fatima!"
Yadda ya kirata ɗin dole ya sa ta ɗaga idanu, yace tashi zaune.
Mikewa tayi ta zauna, yace
"menene matsalarki? Me yasa kike ganin an miki rashin adalci?"
Kallon tambaya ta ma kake ta mishi, kan ta ɗauke idanunta bata ce komai ba, shima ɗauke nashi yayi yace
"Ki tashi ki ci abinci ki sha magani"
Yana kai nan ya ajiye mata maganin ya tashi ya fice abunshi don ta ƙi magana.
Ya gaji ainun so yana kwanciya bacci ya sureshi, da asuba yana dawowa daga sallah kenan ya hangi ɓacewar mota kaman kuma ta Fatima, me gadinshi ya tambaya ya tabbatar mishi da yanzun nan Fatima ta fice.
Be ce komai ba ya haura yaje yayi kwanciyar shi don yau bai da wani aiki, be tashi ba se karfe goma da rabi.
Wanka yayi ya shirya cikin kananun kaya ya fito, zaune ya same su suna kallon wani animation, zama shima yayi ta dube shi tace
"Ina kwana?"
Ya amsa da lafiya yana kallon kafafunta yace
"ya jikin?"
Ta amsa da
"Alhamdulillah"
Duk shiru suka yi, ta san Fatima bata nan don itama ta hangi fitanta ta window kuma bata ji alamun dawowarta ba, ta barshi da yunwa kuma be dace ba tunda sun yi girki kuma ya saura.
Miƙewa tayi tana ɗan ɗingisa kafafunta ta nufi ƙasa da kallo ya bita har ta ɓace mai, sanye take da blue Indian gown da ya zauna mata sossai a jiki, be kai ƙasa ba se wandon shi da ake hangar adonshi daga gwiwar kafanta, yana da tsagu me tsayi daga gefe da gefe, ta ɗaura gyalen ɗaurin turban a kanta, ba karamin kyau tayi ba barin ma da ta gyara fuskanta ta saka lip gloss, bata jima ba ta dawo.
A gabanshi ta ajiye tray ɗin da ta hauro dashi ɗin.
Wani fancy bowl ta zuba kifi da yafi yanayi da soup don yayi kauri ta ɗaura kan plate ɗinshi, a idanu kaɗai abun sha'awa ne gwanin kyau bare a baki, akwai kuma warmer a gefen plates ɗin ta buɗe ta ɗaga miyan ta ajiye gefe doya da ta soya da kwai ne ya ji kwai ta zuba a plate ɗin kan ta matsar mai, ta sake miƙewa ta fice chan se gata da wani karamin tray wadda shayin shi da ta saba dafa mai ne ciki, ta zo ta ajiye mai ganin ya fara cin abincin ta tsiyaya mai da kanta.
Idanunshi na kanta yana kiyasta abubuwa masu yawa a ranshi yace
"thank you"
Ta miƙe tana ɗan murmushi bata zauna a parlorn ba se ta nufi ɗaki.
"Fauza!"
Ya kirata yadda kowa ke kiranta, da sauri ta juyo yace
"kin sha magani?"
Kai ta gyaɗa mai yace
"to dawo ki zauna"
Dawowa tayi ba musu ta zauna a parlorn.
Bayan ya gama cin abincin da kanshi ya tattare kwananukan amma kitchen ɗin sama ya ajiye, a tare suka yi spending time me yawa Dukda babu me magana cikinsu banda husna da ta ishe Fauza da surutu sede ta amsa da eh ko a'a, azahar da aka kira ya saka su duk mikewa.
Ya fita be dawo gidan ba se yamma lis.
Yanzu ma abincin ta kawo mai tuwon semo ne da miyan busashiyar kubewa sbd shi tayi tuwon don ta san yana so, ita kam indomie ta dafa ta ci, husna ma tuwon ta ci, se bayan magrib ya zauna cin tuwon gefen shi papers ne, bayan ya gama ya wanke hannu ya dube ta kan yace
"Dukda ban so ki fara karatu nan kusa ba saide Baba prof ya ƙi aminta da kudiri na hakan ya sa dole na shiga nemar miki admission kuma Alhamdulillah yau gashi kin samu, ina so ki san rayuwarki na da da na yanzu ba ɗaya ba, idan da kin yi abubuwa masu yawa ganin u r free yanzu kina da aure, matsayin aure kuma ya wuce duk wani matsayi da kike tunani, duk laifin da zaki aikata yanzu ki sani ba iya ke da zuri'arki ba har mijinki da ƴaƴanki wannan image ɗin baze mantu a idanunsu ba, sannan zunubinki se ya fi na da sbd kin wulakanta sunnah, in Allah ya kaimu gobe zaki je ki ƙarasa sauran abubuwan da ban karasa ba ki fara shiga aji"
Karɓan admission da ya miko mata tayi tace
"na gode Allah ya saka da alkhairi in shaa Allahu zan kiyaye"
Wayanshi ne ya ɗauki ringing ganin baba prof yasa ya ɗaga tare da sallama bayan sun gaisa baban yace
"Faizan me ya faru? Meyasa zaka bar matarka tayi yaji kuma ta kamo hanya daga Abuja zuwa yola a mota bayan ka san ba lafiya ne da ita ba?"
Yace
"Yola ta tafi kenan? Hmm baba maganan nan ba na waya bane ta zauna a gidan in Allah ya sa Fauziyya ta warke zan zo"
Baba yace
"Assha Fauziyyan ma ba lafiya?"
Yace
"Eh amma da sauƙi"
Baban yace ya bata, miƙa mata yayi a ladabce ta gaishe shi ya tambayi jiki take ce mishi ai ta warke ma bayan sun gama ya ba jadda da suke tare itama ta mata sannu tana tambayar me ke damunta, tace kwalba ta taka amma da sauƙi.
Miƙa mishi wayan tayi tana Kallonshi, kallon lafiya kike kallo na yayi mata se tayi saurin kau da kai ta miƙe.
"Gulma"
Ya faɗa yana maida kanshi ga TV🤣
DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰
Karku sake a baku labari.
🖤Gureenjoh🖤
DƘ
23
"Aunty fa wai kinga kuwa yadda ya ɗauke tan ne? Be fa hukunta ta na abunda ta aikata ba, wallahi zuciyata zata bu...."
Zazzafar mari Auntyn ta sauke mata tace
"zuciyar ta buga Fatima, nace ta buga ɗin.."
Dawowa tayi ta zauna ganganta tace
"Fatima kin san irin asarar da kike shirin ja min? Kin fa san shekaru sama da goma sha wani abu nayi ina wannan tanadi meyasa se lokaci ɗaya zaki nemi watsar min da buri? Ni da nake zaune lafiya da kowa a gidan nan alhali zuciyata dankare take da haushi da tsanarsu duka ni me ya sameni? Toh wallahi ba zan ɗauka ba, bazaki zama wawuya shashasha, lusara a gidan Faizan har ki barwa Fauza shi ba..."
Cikin kuka Fatima tace
"Aunty fa kin san makircin Fauza, da gangan yarinyar nan ta sauya gabaɗaya ni bata min rashin kunya bare shi ballantana in ce zasu samu sabani har ya sauya mata kamanni don baya daukar rashin kunya.."
Dakuwa Aunty tayi mata tace
"baya ɗauka kin sani kuma kika mishi? Fatima wallahi wallahi zan iya sauya ki idan baki yi hankali ba bazan taɓa zama ki wargaje min mafarki na ba, sarai kin san tun kan na shigo gidan nan nake da buri a cikinshi, target na ba Sulaiman bane amma saboda in yi anfani dake yasa na auri Sulaiman yanzu bayan kin girma kuma ki kasa yi min komai ba, kin san wahalan da muka sha kan Faizan ya aureki"
Fatima tana kuka tace
"Amma Aunty ai laifin ki ne, kin sanya min soyayyar faizan tun ban san target ɗinki ba, kuma mun yi yarjejeniya a aikinki ba za ki taɓa cutar da shi ba, wlh rasa shi daidai yake da na rasa rayuwata, bala'in son da ban san adadinshi ba nake mishi shiyasa kusancinsu da fauza ke kasheni... Aunty ke kika ce aure kawai za'a ɗaura ba ze shiga lamarin ta ba sbd tsanar da yake mata amma gashi nan reshe na shirin Juyawa da mujiya... Ko ki san yadda zaki yi dani ko kuma wallahi kowa ya rasa nashi Burin..."
Wara idanu Auntyn tayi tana kallon Fatima tace
"Fatima? Are u threatening me?"
Mikewa tayi tana share fuskan ta tace
"ba threatening ɗinki nake yi ba, ina gayamiki ne ki ɗaukar min mataki akan Fauza in ba haka ba daga ni har ke dab muke da rasa burikanmu"
Tana kai nan ta fice daga ɗakin.
***
Kaman yadda ya faɗa washegari bayan ta gama Haɗa musu abin kari ta shirya a dining taje tayi wanka, doguwar riga marar nauyi ta saka tare da sanya hijab coffee color wadda yaje mata har ƙasa, ta shirya husna ma cikin doguwar riga da baby hijab, daidai sun fito shima ya fito murmushi ya sakarwa husna wadda ya saka Fauza daskarewa a wurin tana ganin cikakken haiba da kyaun bawan Allahn nan, daga baba prof har mammi ba wadda ya bari duk seda ya bi ya zaftare musu kyau da kwarjininsu.
"Madam chogal"
Ta faɗa yana kallonta da neman tsokana, ai kuwa baki ta turo tana cewa
"Allah yaya ni ba chogal bace gashi ina tafiya da kyau"
Ta fara tafiya tana nuna mai dariya yayi yace
"ni dae idanuna chogal suka gani"
Dining suka nufa tana ta tura baki, idanunshi kafe kan lips ɗin da take ta turowan ta saka pink lipstick da yayi mata kyau sossai.
Bayan ta gama sa abincin ta tura mishi ta zubawa husna ta kuma zuba nata Dukda yadda take a takure a kuma sarge sbd yadda yake aika mata kallon ƙasa ƙasa haka ba yadda ta iya ta zauna a wurin ta fara ci, Seda suka gama suka yi hamdala kan ya saka hannu ya zari tissue ya miƙe.
Taku biyu ya iso dab da ita har suna shaƙar numfashin juna, ƙashim jikinsu na gaurayuwa, duƙowa yayi yana rarraba idanunshi tsakanin kirjinta dake bugu da sauri har yana iya kallo da kuma idanunta da suke kashe shi, da kyar ya samu ya tsayar akan lips ɗinta da yanzu suka zama abu na biyu da baya iya gajiya da kallo a jikinta, saukar hannunshi taji da tissue ɗin ya ɗan kwashe lipstick ɗin cikin wani salo da ya saka su jin yarrrrrr gabaɗayansu.
"Haka is ok"
Ya faɗa chan ƙasan maƙoshi kan ya miƙe tsaye ya juya tare da cusa hannayenshi cikin aljihu ya fara takawa don fita daga wurin.
Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kirjinta, 'oh ni fauza me ke faruwa ne kam?'
Ta tambayi kanta sede ba amsa.
Mikewa suka yi duk suka bi bayanshi, husna ta tura gaban motan ita ta shiga baya, har suka isa da shi da husna suke hiran su ita bata saka musu baki ba.
Microbiology ne course da aka bata yayinda Fatima take yin biochem kusan dept ɗinsu wuri daya ne, sauka suka yi suka nufi ciki inda office ɗin Faisal yake nan biology dept, kan su isa ta Haɗa idanu da en mata sama da biyar waenda idanunsu kan Faizan kaman zasu cinye shi danye, ɗan Kallonshi tayi taga abunda suke kallo.
Ash trouser ne a jikinshi me taushi se farar shirt wadda ya zauna mishi sossai ya fitar da siffanshi ta kakkarfan namiji, sajenshi ya kwanta lublub a kyakyawar farar fuskanshi ga fuskan cike da haiba Dukda ba murmushi yake ba amma be kama ba, taɓe baki tayi ta maida bisa hanya har suka karasa office ɗin.
Faisal ya fi Jafar wasa haka yayi ta jan ta yana tsokanarta ita kam kanta ƙasa murmushi kawai take tana kuma jin idanun gogan nata jikinta alamu ita yake kallo, wata yarinya Faisal ya kira a