Showing 18001 words to 21000 words out of 86608 words
jigida" kawai se Aunty Amarya ta saki kuka. Baba Alhj da shigowar shi gidan kenan ya tarar da faɗan da Aunty Amarya ke yi kuma yana kallon lokacin da take gungunin sede gudun kar ya ce ze buge ta yanzu ya karya ta yasa ya shige parlornshi kawai.
Aunty Amarya tace
"tashi ki tafi bana son aikin, in har aikin da zaki sani magana ne, nayi maganan kuma ki zage ni don baki dauke ni da daraja ba tunda ba ni na haife ki ba jeki karki sake sakamin hannu a aiki"
Mikewa kuwa tayi ta fito ko a jikinta, ta zo wucewa ta gaban Fatima suka Haɗa ido a saman labbanta tace "munafuka" tana ball da bucket ɗin wankin har ruwan ya kwararare.
"Fauziyya!"
Baba Alhj ya kirata cikin wani irin kaushin murya.
Se Fatima ta fara kuka mikewa tayi ta wuce ta gaban Fauziyya ta duƙa a gaban Baba Alhj tace cikin sanyin murya
"Baba Don Allah ina so kayi min izini ina so in koma wurin mahaifina haka..."
Cikin tausayinta yace
"Babu inda zaki koma Fatima, nima mahaifinki ne in akwai wacce tafi cancanta da ta bar min gida Fauziyya ce!"
A razane Fauziyya ta ɗago ta kalleshi, Ammi ma da ta fito se idanu ta zuba mishi yana kallon Fauziyya yace
"Eh kin ji abunda na faɗa! Na gaji bazaki kasheni tun kwana na be kare ba, ke kaɗai ranki guda kin zama sheɗaniy...."
"A'uzubillahi Sule!"
Jadda da ta shigo bikon ƴar gidanta sbd ta ƙi shiga wurinta tun jiyan nan ta faɗa tana karasowa ta kama Fauxiya da ta zama speechless tana kallon mahaifinta.
"Ƴarka na cikin ka kake kira sheɗaniya Sule? Wani irin baki ne wannan? Me tayi maka da zafi haka?"
Kanshi a ƙasa yace
"Mama na gaji da halayyar Fauziyya, dubi goshin uwarta Sumayya yadda tayi mata jiya, babu wadda ze faɗa magana Fauziyya bata bashi amsa ba, ta sakawa yarinyar nan karan zuƙa tana mata gadara da gidan uba! Ita ɗin ai ba daga Bishiya ta faɗo ba, gwara Fatima sau dubu don bata sa uban ta da uwarta zub da hawaye ba... Wallahi wallahi Mama Fauziyya ta gama sane min cikin yarana har raina na gaji da komai nata"
Ammi kuka ta fashe dashi tace
"ba kinji ba Fauziyya? Wallahi ki guji duniya, uban da ya haife ki ma yace ya gaji dake to wa ze iya zama dake? Da wannan halayyar naki Fauziyya gwara ki sa wuƙa ki mana yankan rago mu huta da zafin zuciya kullum a kanki"
"Ruqayya! Sulaiman!! Ya isheni haka, tunda mutuncina da ganin idanuna be sa kun kasa amayo da kalaman bakinku ba, ni kuwa ba zan tsaya in cigaba da saurara ba, karku manta yaranmu kaman kiwo suke a garemu Allah ya kan jarabceka ta hanyoyi daban daban maybe ita ɗin itace jarabawar taku, idan kuka yi hakuri a matsayinku na iyaye kuka kai zuciyarku nesa kuka cigaba da mata adu'a har zuwa sadda Zaku Rabu lafiya kila ku samu rabauta ta sanadiyar ta, yanzu da duk kuke aika mata da kalamai marasa daaɗi ta karasa lalacewa kuma haka Zaku ɓata lahirarku saboda se Allah ya tambayeku, abunda ya saura ku ce shine kawai ta fita ta bar muku gida tunda har ka fara attempting to zan tafi da ita sashena ku zuba ruwa a ƙasa ku sha"
Tana kai nan ta janyo hannun Fauza da take tsaye kaman icce suka fice.
DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin
09039206763
Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰
Karku sake a baku labari.
🖤Gureenjoh🖤
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Shafi Na Tara*
*PAID BOOK*
ƊANƊANO
**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA🥰❤️**
Ƙurawa kanta idanu tayi a Door size mirror na ɗakin tana jin sukar kalaman iyayenta a kanta, lallai kam basu faɗi abunda ze gyara mata rayuwa ba se ma wadda ze ɓata saboda hango abubuwan da zata ke yi musamman wadda a da gudun ɓacin ran nasu yasa ta danne burinta take rayuwa yadda ta taso ta gani Dukda baya cikin tsarinta, kallon kanta take da kyau tare da lumshe idanu tana tuna maganar sakina.
"Ke yadda kike da kyaun nan da sura wallahi kika fara ɗaukar wanka kika zama ƴar gayu ba karamin rububi maza zasu yi a kanki ba, kin san kuwa irin baiwar da kike dashi na fusgan hankalin mata ma ba maza kaɗai ba? Babe ki waye pls ki dena kunshe kanki cikin hijab"
Ajiyar zuciya ta sauke tana tuna amsar rahama.
"Ke wallahi abunda Sakinah ta faɗi gaskiya ne baki ganin yadda duk muke rayuwa cikin wayewa da aji da izza? Don Allah hakan baya burgeki? Amma ku kullum gidanku hijab hijab Ina ka fito karatu ina zaka karatu, babu babban waya, babu samari babu hangout da su party, wallahi kuna cikin duhu"
Ba kalaman nasu bane ke tunzura ta sede illa irin tsarin rayuwar da take so ɗin kenan se ya haɗu da maganganun su yake tasiri a hankali a ranta sede yanzu kalaman iyayenta ya hauhawa su kaman tashin farashin man fetur, a yanzu take jin zata fara nunawa su baba prof ba irin rayuwar su take so ba, ko da zasu yanka ta su fige tane.
Rahama da sakina ƴan ajinsu ne waenda suka shigo third term na SS1 ɗinsu asali a Abti suke sede rashin jinsu, da yawace yawace yasa iyayen Rahama suka cire ta suka dawo da ita Elkenemy ganin makarantar musulunci ne kila ta shiryu sede ba tare da sun sani ba sakina ma ta uzzuruwa iyayenta suka sake dawowa suka jone a ajin su Fauxa, tunda suka ganta suke admiring kyaunta da kalar idanunta suka fara nuna mata yadda zata ja hankali tare da tada hankalin maza a tiktok sede bata mai da hankali ba, iya kaci taji wakoki da wayoyinsu tayi ta kallon mata masu class a Instagram waenda har ga Allah suke burge ta.
Tana matukar son gayu da class sede su gidansu ko ba hijab baka isa fita ba, a daren ta fara tsara yadda zata sauya rayuwarta zuwa ra'ayin kanta ba ra'ayin wasu ba, sallamar Faazila ya sa ta ɗago idanunta da suka sauya ta zuba mata, birkicewa yarinyar tayi don ta san sarai yanzu se Adda Fauxa ta mammake ta yadda take a harzuke ɗin nan.
"Me??? Kin zo kin wani yi min kerere kina kallona?"
Baya ta ja tace
"Mammi ce tace in kira ki"
Dauke idanunta tayi ba tare da ta amsa ba ta juya ta dauki hijab ɗinta ta saka tare da fitowa zuwa sashen Mammi, tana shirin shiga ɗakin Fatima na shirin fitowa da gayya ta bangaje ta har Seda tayi baya tana kallonta sede ko kallo bata ishi Fauxa ba ta wuce zuwa wurin Mammi tana daidaita fuskanta Gaisawa suka yi Mammi tace
"Fauxa zo don Allah kiyi min tofi a kafan nan"
A ladabce tace
"to Mammi"
A gabanta ta duƙa ta fara se Fatima ta shigo da bowl na fruits a hannunta ta ajiyewa Mammi ɗin tana cewa
"Mammi Adu'a ce ake yi?"
Mammi tace
"eh wlh jiya da ta min baki ji yadda na ji daaɗin kafafun ba"
A fakaice Fatima ta aika mata da wani kalar kallo tare da taɓe baki, ina Fauxa ta ma san tana yi, wai harara a duhu, bayan ta gama mata ta fice don bata jin magana in kuma ta zauna inuwa daya da Fatima karshe se Mammi ta raba faɗa.
Washegari a class bayan an tashi break ta kalli rahama tace
"am interested in ur way of life taya nima zan fara?"
Rahama da sakina suka yi wani ihu tare da tafawa suka ce
"welcome to the club babe"
Sakinah tace
"dama akwai wasu Zafafan dinkunan da zamu yi har ma mun yi placing order ɗin materials ɗin amma tunda zaki yi bari na sa dake"
Fauxa tace
"amma fa bani da kuɗi kun san gidanmu ba wani bada kudi ake banza banza ba"
Rahama tace
"don't mind dear! anything for you precious "
Sakina tace
"bare ma kwana biyu zaki fara rike wasu makudan kuɗin da se kin ji tsoro just chill babe"
Aiko gwada ta suka yi suka turawa tailor ɗin su, nan suka fara nuna mata mahaukatan dinkunan tana kallo cike da yabawa..
Iyaye ya kamata mu san cewa duk fushin ka da yaro ba kowacce kalma ya kamata ka furtawa ɗa cikin fushi ba domin baka san irin influence da zaka yiwa yaro ba idan har Allah ya amsa.
MAFARI
Dukda rashin son karatun Fauxa ta kasance mace mai son karance karance, hakan yasa bata rabo da littafi ko na turanci ne, babu kalar abunda bata karantawa hakan yasa abubuwa dayawa tana da masaniyar already aikata shi a fili ne kawai bata yi ba.
Wani irin kalar Juyawa rayuwar Fauxa yayi cikin lokaci kankani, idan tayi dressing se ka dauka ba Fauxan gidan baba prof bace, Fallin balaga ya buɗe rashin M ɗin ta se abunda ya karu ga rashin daukar raini, se neman tsokananta da yayi sauƙi sede fa ba shi ya hana kana ce mata Kule ta ce maka chass ba.
Abunda take yi shine tunda yanzu Sam Sam ba cika zuwa part ɗinsu tayi ba se idan zata gaida Ammi don baba Alhj ma ta manta rabon da su haɗu tunda ya ce baya kaunar ganin fuskanta ta gwammaci ta dinga wasan buya dashi.
Idan an tafi school daga an tashi break zata yi bribing gate man sbd su Rahama ma ba cika zuwa suke ba se once or twice in a week, zasu ɗauke ta a gate su tafi gidansu rahama inda wasu abubuwanta suke a nan zasu yi dressing ɗinsu na class su fice yawo, samari kuwa kaman kuda a kan Fauxa hakan yasa ta juya wannan ta waina wanchan ga yadda take sha musu kamshi kaman ƴar shugaban kasa, ɓarin kudi suke mata ba na wasa ba har ta mallaki iPhone 13pro na kanta kuma har gida take zuwa da abunta.
Ta chanza mayukanta gabaɗaya zuwa wasu organic masu tsananin tsada, na kafa daban na gashi daban na fuska kala kala, in ta wuce ka se ka jima kana jin kamshin designers perfumes na jikinta.
Aka ce akuyar ɗaure in ta samu sake Habaaa, har Sakina da half rayuwarta outside tayi wani lokacin ta kan mutu da kalar gayun Fauxa sede a gida har yanzu babu wadda yayi noticing ana getting to five months.
Sau ɗaya fa'iza ta taɓa mata maganan rashin zamanta aji se da ta ja mata katoton layi tayi mata fata fata wadda har ta Haɗa da mahaifiyarta hakan yasa fa'iza dauke kai daga rayuwar ƴar uwar tata.
Se dab za'a tashi school take dawowa su koma tare da ƴan gida, wayanta kuwa kullum a ɓoye yake kasancewar ɗakin da take a sashen Jaddah ita kaɗai ce, yanzu damuwanta yadda zata fara fitan dare sbd ana kawo mata cikas sossai da ganin ƙarancin wayewarta sbd rashin zuwa night parties ɗin nan.
Zama tayi ta tsara yadda zata ke fita abunta bayan isha zuwa asuba, randa ta fara gwada luck ɗin ta Dukda yadda take a tsorace kuma cikin bugawar zuciya haka ta saka dogon hijab ɗinta bayan ta yi wanka ta gama duk shafe shafenta, fuskanta da ba ko Digon powder se wani ɗaukar hankali yake sbd kyaun da ta kara na musamman, wurin Jaddah ta je tace
"Jaddah yau wurin Mammi zan kwana"
Jaddah tace
"yau kuma ni aka yiwa Hijira kenan, to se da safe"
Tana murmushi tace
"Allah ya bamu alkhairi"
Sashen Mammi tayi ta gaisheta, tace
"Mammi bari na tofa miki Adu'ar nan"
Kasancewar kullum kaman ka'ida duk dare ta kan je ta tofa mata adu'o'in hakanan kan su wuce school kuma Alhamdulillah sossai Mammi take jin daaɗin kafan kaunar Fauxa sbd Allah na ninkuwa a zuciyarta, kuma duk wadda ya san Mammi se ya ji zancen Fauxa a bakinta sbd irin gudumawar da Fauxa ke bayarwa idan Mammi ɗin ba lafiya.
Seda ta shafa mata adu'ar kan ta mike ta nufo hanyar gate, Allah ya taimake ta daidai lokacin baba prof yake baiwa Lawal kuɗi ya amso mishi credit, a jikin flowers ta buya har Seda ya wuce ciki daga masallacin da shi se lokacin yake fitowa, Lawal kuwa yayi waje ta fito da sauri ta fice gabanta na dukan uku uku.
Wayanta ta fidda ta kira su Rahama suka zo da driver ɗinsu da shine yake yawo dasu dama suka wuce suna ihun ganinta at this time around.
Shiri suka yi suka wuce birthday party ɗin wani saurayin Rahama, wuri ne na manyan yara waenda iyayensu suke da kumbar susa, ado ne kala kala zaka gani da kalar dinkunan rashin kamun kai, kuɗi kuwa ba'a maganan adadin da aka zube don wannan party din musamman.
Fauxa ta ja hankalin matasa masu daloli dayawa a wurin kuma kowa so yake ta kula shi, sede fa in tana cikin ji da izzarta ko su Rahama shakkar mata magana suke, Fauxa ta riga ta zama hatsabibiya Dukda bata rabin abunda suke, su suna ɗan taɓa kayan maye hakanan su kan yi soyayyar shan minti sede ko ɗaya Fauxa bata yarda da wannan ba.
A nan wurin suka yi till down, gab asuba ta sa wani ya ɗauke ta suka nufi gida, Seda ta bari an shiga sallah kan ta shige da sauri, alwala ta ɗaura kawai ta nufi masallaci dayake ta chanza dressing ɗinta zuwa yadda ta fita, Jaddah dauka tayi ta makara a wurin Mammi tunda Mammi ba koyaushe take samun zuwa masallaci ba.
Ba se Fauxa ta samu abun yi ba, se ta kwana waje sau biyu ko sau uku a sati wadda hakan ya kara mata buɗewar idanu ba na wasa ba.
****
"Malam kwana biyar ne kawai Don Allah ka yarje mana ka taimaka ka Haɗa wannan plan din, in ba Fauxa ba zamu taɓa jin daaɗin wannan party ɗin ba"
Kallon Fauxa da tunda suka shigo bata ce komai ba yayi, yarinyar tana burgeshi tashen balaga ke dibar ta gashi Allah ya zuba mata sanyin kyau, ya jima yana bibiyarta tana wulakanta shi...
"Albashinka na wata nawa kake so?"
Ta watso mishi tambayar, wani fitinanniyar kallo ya watsa mata kasa kasa yace
"just one night stand please Fauxa na jima da ƙishirwanki"
Wani banzan kallo da ya kara kunna shi kanta ta mishi tace
"am not that kind in baka sani ba ma ya kamata ka sani just say your price!"
Rahama tace
"Sir please just say your price Fauxa ba irin waennan cheap matayen bane...."
"Before the count of three say your price or you loose the opportunity! And I must leave to Abuja"
Dukkansu uku kallonta suke da tsantsar mamaki, barin ma malamin wata iriyar yarinyace wannan? Me take nufi? Ba de hatsabibancin nata take shirin sauke mishi ba!
Be hankara ba ya ji ta ce "3"
Tana murmushi ta danna play a wayanta se ga muryarshi yana faɗin just one night stand please Fauxa wlh na jima da ƙishirwanki...
A razane yake kallonta zufa na yanko masa rahama da sakina suka saki murmushi lallai Fauxa ta ci lakabin da ake mata na
"Hadari malafar duniya, punkasau babban girki, biri da gatari ajalin mai gona, jan ƙasa na bayan ɗaki kowa ya ganki ya tuna Allah. Kadangaren bakin tulu; a barki ki ɓata ruwa a taɓa ki kuma a fasa tulu. Ba a banza ba, biri ke shan duka a rani, kowacce ze hadiye gatari zamu riƙe masa Kota....."
Wannan kirari ne da babu wadda be san Fauxa dashi ba kuma har yanzu idan ana son ganin fara'arta cikakke to ka yi mata wannan kirarin shiyasa yawancin ƴan korensu da hakan suke cin kuɗin ta.
Cikin dage gira tace
"zaka rubuta mana takarda da sunan zuwa excursion na kwana biyar kuma mu uku kaɗai aka zaɓa daga makaranta. Sannan ka sani ka yi wa kanka don ko biyar ba zaka samu ba! Ka yi abinda na ce kan a tashi or else..."
Daga haka ta miƙe ta kaɗa mishi idanu ta juya ta fice suka bi bayanta suna murmushin irin zufan da yake Haɗawa....
DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
09039206763
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰
Karku sake a baku labari.
🖤Gureenjoh🖤
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Shafi Na Goma*
*PAID BOOK*
*LAST FREE PAGES*
Babu yadda wannan malami da ya shiga tasku ya iya haka ya rubuta don tabbas ya san ƙaramin aikinta ne playing wannan audio wa school authorities daga nan kuma ya san aikinshi gabaɗaya ya rasa, time da ta bashi na cika ta zo ta karɓa tana yi mishi murmushin wulakanci irin nata.
Aiko tana isa gida Momma ta kaiwa don ta san daga momma ta amince to Baba Prof ma ya amince ta ci sa'a kuwa babu wadda ya hanata tafiyan suka shirya suka wuce akan ma Gombe ne bayan flight aka biya musu zuwa Abuja.
Karfe biyar na yamma suka sauka a birnin tarayya Abuja Motoci har biyu suka zo ɗaukar su Dukda duka duka su ukun ne kuma mota ɗaya suka shiga ɗaya na take musu baya, babban masaukin baƙin da har gomnoni da kusoshin