Showing 12001 words to 15000 words out of 86608 words
kwana biyu bata huce ba hakan yasa shirin su da fa'izan yake yawan ja baya.
Sashen Jaddah suka shiga tana zaune tana jan chasbi Fauxa ta zube kan kujera tace
"Jaddah wainar fulawa nake son ci na manja da yaji me tafarnuwa"
Jaddah tace
"se ki ci ai, ni kam ban yi tunanin akwai fulawa a gidan nan ba"
Fa'iza tace
"kash! Ya kenan Fauxa gashi namu ma babu ya kare"
Mikewa Fauxa tayi tace
"mu je wurin Mammi mu yi, dama wlh tun jiya ban je na gaisheta da ciwon kafan nan nata da ya tashi ba"
Ficewa suka yi Jaddah bata ce komai ba har suka fice, ko da suka isa a ɗaki suka sameta kwance a ƙasa an shimfiɗa mata bargo me taushi da pillows, ƴar yayarta da zata ɗan girme su da take hannun ta tun bayan auren farida ita ke taimaka mata tunda bata karatu.
Sashukan nan basu da maraba da sashen su Fauxa, se na kitchen da akwai cikin kowanni sashe saɓanin nasu, se kuma na yawan ɗakuna wadda nan kofa biyu ke fuskantan biyu, na Mammi ne na farko wadda babban parlor ne sossai da kitchen da ɗakuna biyu, hakan ne kuma a kowanni ɗaki, sannan akwai kitchen na waje da kowacce me girki a sashen take girki ranan girkin ta, tsakar gidansu bishiyar cashew ce me ni'imtacciyar inuwa.
"Fauxa yau ke ce a sashen namu? Lallai za'a yi ruwa da kankara"
Fauxa na murmushi ta zube kasa tace
"sannu Mammi ina yini? Ya kafa?"
Mammi tace
"Alhamdulillah Fauxa da sauki sossai har ɗazu ma na taka zuwa toilet"
Fauxa tace
"Allah ubangiji ya ƙara sauki"
Da Ameen ta amsa, fai'za ma ta gaisheta.
Fauxa tace
"Mammikina da fulawa? Wainar fulawa nake son yi bamu da fulawa haka Jaddah ma"
Ta karashe tana karya wuya
Mammi tace
"Ah Kice abunda ya kawo ki kenan ba zuwa na musamman da kike cewa ba"
Tana dariya tace
"Allah ba haka bane dama nayi niyyar zuwa"
Mammi tace
"ba za'a rasa fulawan nan ba ku duba a kitchen na cikin nan se kuyi, dama akwai yaji da Zuwaira(kanwar ta) ta kawo min ma jiya da alama ze yi daaɗi"
Cikin jin daaɗi Fauxa ta mike, fa'iza ta bi bayanta suka yi kitchen.
Anan suka kwaɓa suka fara suya se suka fara na manja sbd yadda Fauxa ta hanata sakat Seda suka yi me yawa se suka koma man gyaɗa sbd shi fa'iza ke so, suna cikin yi se Fa'iza tace
"ni bani manjan ma in yi mixing kaɗan yadda ze bada wani dandano me armashi"
Fauxa tace
"Wallahi bazan bayar ba ka jimin wayau, kowa ya ci da plain abunda yake so"
Musu suka fara, fa'iza ta kai hannu da niyyar fusgan manjan Fauxa ta ɓalle da gudu daidai kofar kitchen ɗin taji taci wani uban karo da wani broad chest me yanayi da rock, gabaɗaya manjan ya zube a jikin kayan mutumin.
A hankali na kai idanuna bisa mutumin da aka kwararawa manjan Masha Allah, kyakyawar matashi ne me tsawo sossai a kamannin fuska zaka iya cewa kaman an tsaga kara da Fauxa, banbancin nasu kaɗan ne shi ɗin fari ne Kal saɓanin Fauxa, haka idanunshi wasu irin Ash ne me walƙiya..
Ko kaɗan bashi da rama wani irin tsayayyen namiji ne da yake da jikin every woman dream, daga ka ganshi zaka san cewa ma'abocin workouts ne, yana da dogon hanci sak irin nata da lips wadda suke iri daya da nata kaman an shafa musu cherries yadda suke kyalli, yana da gashin saje gyararre me kyau wadda har zuwa gemu amma be cika yawa ba, a gyare tsab baƙi sidiƙ se shining yake yi wadda ya kara fitar da ainihin kalar farin fatar shi, daga yatsunshi na hannu zuwa na kafa dogaye ne a gyare suke tsab gwanin burgewa, yana da wani irin kwarjini da farin jini sede fa ma'abocin tsare gida ne, Miskilin bugawa a jarida ne sannan yana da murɗaɗɗen hali da zama dashi se ka shirya.
Sanye yake da Fararen kaya Kal Kal Jean da shirt designers kafafunshi sanye da Dior lufas masu kyau, kamshinshi a take ya baza lungu da sako na kitchen ɗin, kyawawan idanunshi na kafe kan inda manja ya zube a Rigan nashi kan a hankali cikin tsantsar natsuwa ya ɗago birkitattun idanunsa dake cike da kwarjini irin na cikakkun maza ya zuba mata.
Wani irin faɗuwar gaba ne ya risketa ga tsoro da ya kusa sumar da ita, cikin da na sanin fara sha'awar wainar fulawa da ta yi a yau ta fara ja da baya, wannan baƙin azzalumin yanzu se ya mata abunda se ta gwammaci kiɗa da karatu, ita kanta fa'iza dake tsaye jikin gas a take ta saukar da pan ɗin sede ta kasa kashe gas ɗin se rawan tsoro jikinta ya ɗauka.
Kokari yake yayi controlling ɓacin ranshi sede ganin ko sannu bare yi haƙuri ta kasa ce mai yasa ya ɗaga kafafunshi ya fara takawa zuwa gareta, a duniya ya tsani ganin yarinyar halayen ta, neman tsokananta, rashin jinta, rashin kunyarta duk ya tsana bata yi mishi don babu fuskan yi ɗin sede ya kan tsinkaya tana yiwa wasu, sannu be taɓa Haɗa su ba tana karama in har zata zo kusa dashi se ya mata mugunta tun tana zuwa har ta dena hakan ya dasa mata tsoron shi, Sam baya zama a inda take sbd hakan itama ta koyi kin zama a inda yake, idan kana son ganin ɓacin ranshi ka ce suna kama yanzu se ku samu matsala, ya kan yi mamakin yadda kowa a gidan complain ɗinshi baya wuce Fauziyya har iyayensu maza, shi yana ganin iskancinta wuri ya samu bata sami me saita ta bane, hakan ya sa ya buga Mata tambarin annoba don shi da annoba yake kiranta.
Ganin da gaske nufanta yake ga fuskanshi babu ɗigon rahama yasa tayi kokarin gudu, taku ɗaya yayi ya saka mata ƙafa hantsilawa tayi zata faɗi, garin neman abunda zata dafe don gujewa kaiwa ƙasa ta ɗaura hannunta na dama bisa kan gas ɗin da yake kunne, ba wutan bane karafunan da suka riga suka jima da ɗaukan zafi sossai ne suka aika mata da wani irin raɗaɗin azaba zuwa kwakwalwanta har bata san sadda ta saki wani ƙaran azaba ba tana rike hannun.
Wani mugun murmushi da ko haƙorin shi be bayyana ba ya saki kan ya juya ya fice daga kitchen ɗin, da gudu Fa'iza ta kashe gas ɗin kan tayi kanta ta kama hannunta a tsorace tana kallon fuskanta yadda hawaye ke ambaliya kaɗai zaka gani ka san tana cikin wani hali ga zufa dake aikin tsatsafo mata.
"Sannu Fauxa! Sannu"
Mammi ce jin ihun Fauxa yasa ta lallaɓa ta fito a hankali ta nufe su tana cewa
"Subhanallah me ya same ta? Konewa tayi?"
Cikin kuka Fauza tace
"mammi wannan azzalumin ne ya saka min hannu akan karafunan gas, Wayyoooo hannuna!"
A hankali Mammi tace
"FAIZAN!" Don shi kaɗai Fauxa ke cewa Azzalumi.
Da sauri Mammi ta cewa Fauxa
"ɗauko akamu yi sauri gashi a chan in saka mata kar ya tashi"
A hankali ta karasa gareta ta ɗaga ta tare da riƙe hannun har ya tashi gabaɗaya tafin na hannunta yayi wani kalar bororo, wani irin tausayinta ne ya rufe Maa sbd ta san zafin wuta ba daaɗi amma se ta saɓawa Faizan, ashe kaddarar ƙone wa ya kawo ta sashen nata da ta jima tana mita akan rashin zuwan nata, da kuwa ta san Faizan ma ze zo yau da bata ma bari sun yi wainar anan ba, wani irin abu ne haka?
Akamun fa'iza ta kawo ta kwaɓa ta saka mata har lokacin kuka take, tayi tayi ta ci wainar da saura kaɗan ma su kammala ta ƙi tace ta koshi, cikin rashin jin daaɗi Mammi ke bin ta da ido har ta fice se ta saka fa'iza juye wainar a flask ta bita dashi su je su ci a gida don ta tabbatar ko sashen Jaddah Fauxa bazata kara zuwa ba se an tabbatar mata da baya gari.
Haka kuwa aka yi da fa'iza ta kawo mata ma ƙin ci tayi, Allah ya isa kuwa ta ja mishi yayi cikin kwando, gashi Ammin ta bata nan ta tafi kauyensu jiya uncle ɗinta ya rasu, da magrib ma da kyar ta samu tayi alwala ta tako zata fito zuwa masallaci kenan ta tsaya Chak jin muryar dake tashi a speaker na masallacin, tsaki ta ja ta koma ɗaki nan tayi sallah har isha bata fita ba, a Cewar ta bazata bi sallar azzalumi ba don Allah ba karba ze yi ba. bayan tayi isha ne ta kunna speaker ɗinta iya daidai jin kunnen ta ta saka waƙa abunta anan mood ɗinta ya fara dawowa daidai.
Tana ji su fai'za na cin abinci bata fita ba, idanunta a lumshe take jin Fatima na fesawa fa'iza ita duk yadda take jin karatu bata taɓa jin me natsuwa da kwantar da hankali irin na Ya Faizan ba, fa'iza na dariya tace mata
"zaki ce haka ne ma tunda kina son shi"
Fatima ta ce
"ban gane ina son shi ba? Ko de muna son juna?"
Fa'iza tace
"ai ko makaho ya shafa ya san ke ce kike mahaukacin son ya Faizan shi ba take yake ba, ba ta yadda za'a yi yana son ki ne ke karan kanki kan ya miki magana ɗaya se kinyi hamsin, sannan ya tafi yayi wata da watanni ko a wayan Jaddah baze ce a baki ku gaisa ba idan ma yana jin kunyar Mammi kenan, ni wlh bana son miki kasancewa da ya Faizan ina so ki samu me son ki inda zaki ji...."
Tsawa ta daka mata
"dakata fa'iza! Don ina maganan soyayyata dake ba shi yake nufin ki gayamin duk wani banzan maganan da ze fito daga bakin ki ba idan ma ba kitsa miki aka yi ba don baki da wannan wayaun, to henceforth as from today kika kara min irin wannan maganan wlh se nayi mummunan saɓa miki ni ba sa'ar ki bace"
Fa'iza tace
"Ya Fati daga faɗar gaskiya?"
"Bana son gaskiyar ki riƙeta"
Daidai lokacin Fakiha ta shigo da gudu tana shelan ya Faizan ya ce a je a karɓi tsaraba yana sashen Jaddah.
Da sauri duk suka tashi suka fice daga tsakar gidan.
Taɓe baki Fauxa tayi, Fatima na neman magananta ta tabbatar harda shagube a zancen nata, amma ba ta ita take ba yanzu ta samu ta warke shine damuwanta kuma wlh akan Fatima zata rama abunda ya mata tunda shi azzalumin ya fi karfinta.
Chan da yunwa ya fara damunta don ko abincin rana bata ci ba ta sa a zuciyarta zata ci wainar fulawa yasa ta mike ta fito a hankali ta nufi kitchen, ja tayi ta tsaya jin kuka na tashi a hankali....
DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin
09039206763
Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what'sapp.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰
Karku sake a baku labari.
🖤Gureenjoh🖤
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Shafi Na Bakwa*
*PAID BOOK*
ƊANƊANO
**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI AUNTY HALILLOS GWANATA KUMA MALAMATA🥰❤️**
"Aunty wallahi son shi ze kasheni! Kin Reneni ne da soyayyar shi hakan ya bani karfin gwiwar kwallafa rai a kan samunshi sede gashi har yanzu shi bana gabanshi, yanzu har fa su fa'iza sun san nice me cusa kai a gareshi shi ba ta ni yake ba! Aunty kinga wulakancin da ya min a gaban su Fa'iza da kannenshi maza?"
Ta karasa tana me kara rushewa da kuka.
Aunty tayi saurin sa mata hannu a baki tace
"Haba Fatima! Me yasa ke kam kullum rashin haƙurinki kara gaba yake? Na faɗa miki na kara jadadda miki idan har Faizan be aureki ba to wallahi ba ze auri wata ba, wannan alqawarin da na daukar wa kaina ne tun kan in shigo gidan nan, tufka nake ana warwarewa amma ba matsala ki kwantar da hankali na miki alqawari Faizan ba ze bar garin nan ba tare da an tsayar da magana tsakanin ku ba!"
Wani wawan tsaki Fauxa ta ja kan ta juya ta fice daga gidan gabaɗaya, a chan gefe da sashensu inda aka yi wasu kujeru haka masu kyau na tayoyi ta zauna, tana me kallon qonannan hannunta, murmushi ta saki na jin daaɗin ba ita ba aikin gida har se ta warke, makaranta ma in ta je ba rubutu ai kuwa za'a sha neman tsokana.
Bata san iya adadin lokutan da ta ɗauka a wurin ba, chan ta hangosa yana tahowa cikin tafiyar nan tasa me cike da natsuwa kaman saraki, sanye da wasu kananun kayan still farin Jean da navy blue shirt a ko yaushe Adonshi da shigar shi masu kyau ne da salo irin na burgewa.
Maganan Fatima ne ya faɗo mata bata san sadda ta kwashe da wani irin dariya ba har da hawaye, wai amma Fatima tayi asara ta taɓe duniya da lahira fisabilillahi ta rasa abun so se wannan? Dariya take tayi tana sakewa wai fa har da kuka Fatima ke yi sbd shi? Ta kara kwashewa da dariya tace
"Taabbb Allah ka rabani da aikin wahala"
Har ya wuce tana babbaka dariyar ta kaman sabon kamu inda Allah ya taimake ta ba Kallonshi take ba don ta san in har ya san dashi take yadda ba kowan nan se na lahira ya fi ta jin daaɗi, ji fa yadda yake tafiya, ita wallahi tafiyar da yake yi ko ita mace bazata yi irin shi ba, dariyarta tasha daidai sashensu na samari ta ga ya ɗan tsaya ya waigo, daidai itama ta ɗago ta kalle shi se suka Haɗa idanu, kallon kanki ya taɓu ya watsa mata.
Ko seconds biyu be yi ba ya juya ya karasa shigewa sashen, mikewa tayi tana share hawayen dariyarta kaman wacce duniya ta yiwa daaɗi ta wuce sashen Jaddah, tana shiga ta narke tana tafiya kaman marar lafiya.
Jaddah tace
"zo ki karbi tsarabar ki na wurin Faizan"
Haɗe rai tayi, Fa'iza tace
"ke kinga rikicin da aka kwasa da ya Faizan kan Jaddah ta kwasar miki chocolates ɗin nan karfi da yaji? wlh ki gode mata ta san yadda kike son chocolates shiyasa, ga su da daaɗi kaman zasu tsige kunne"
Kallon chocolates ɗin tayi masu tsada ne sossai, daga gani ma maybe ba a nan Nijeria ya sayo su ba sede tunda daga hannunshi ya fito basu ba ta sha'awa ba, kau da kai tayi tace
"Jaddah da baki wahalar da kanki ba don ni kam ba sha zan yi ba"
Jaddah ta saki baki zata yi magana kenan Fauxa ta fara kukan hannunta na zugi, da sauri Jaddah ta karɓe hannun tana salati tace
"Faozia garin yaya? Me ya sameki haka?"
Ai jin tambayan Jaddah yasa ta kara narkewa tana fashewa da kuka, she's so fragile in tana abu kaman little baby, Fai'za tace cikin damuwa.
"Jaddah ita da ya Faizan ne"
Nan ta bata labarin abunda ya faru tsakaninsu, Jaddah tayi ta masifa ta kuwa ci alwashin se ta saɓa mishi wani irin mugunta da bakin hali ne wannan?
A kan cinyar Jaddah ta kwanta tana jin daaɗin yadda Jaddah ke ta zuba mitan abunda ya farun, ta kara da
"mutum ne se baƙin miskilanci yanzun nan yasa yarinyar da yake ikirarin buduruwarshi ce kuka amma ko a kwalan riganshi"
Kau da maganan Fauxa tayi don be shafe ta ba, anan ta kwana ma yau..
Washegari Monday ko aiki ɗaya bata yi ba da taje school ma babu abunda ta rubuta se surutu da neman magana, a ranar Ammi ta dawo itama Seda tayi faɗan hannun nata sede baba Alhj be ce komai ba.
Bayan 2days ta ɗan samu sauki ta cigaba da aikinta, zuciyarta kuwa na kiyasta mata yadda zata rama abunda ya mata sbd ta sha wahalan qunan sossai.
Yau tana kwance bisa kujerar Jaddah tana danna ƴar karamar wayar jaddahn sbd ita ba kaunar kallon tashoshin wa'azuzzuka da shi kaɗai suke dashi gabaɗaya gidan take ba, jaddah ta fito rike da tray tana kallonta tace
"Fauziyya don Allah miƙawa Faizan abincin nan kinga yaran duka suna wurin Ibrahim(baba prof)"
Haɗe rai tayi tace
"Jaddah eyyah ki jira su in sun dawo su kai mishi"
Jaddah ma rai ta ɓata tace
"zan saɓa miki wlh Fauziyya, ki wuce ki tashi ki kai in dodonki ne se ya cinye ki, in kuma baza ki je bane ki gayamin"
Hawaye ne ya cika idanunta, ita ba mikewa take son yi ba don ko da yaran suka je wurin baba prof da be ganta ba seda ya aiko fakiha tace mata tace tayi bacci idan kuwa bata ce haka ba se ta kirɓa ta in aka dawo sake kiranta, gashi yanzu Jaddah zata saka ta kaiwa wannan azzalumin abinci.
Mikewa tayi ta ɗauki tray ɗin da Jaddahn ta dangwalar ta fito, shiru tayi tana tunani, in ta taɓa ji da kyau Jaddah ta taɓa maganan rashin son yajinshi sbd muguwar ulcer ɗinshi ko yaya ya ci yaji se ya kwanta, murmushi ta saki taje kan kujerun tayunsu ta ajiye tray ɗin da gudu ta koma gidansu taje ta fara binciken drawer ɗinta akwai wani yaji me zafi da ta daka ranar girkin Amminta sbd an yi mata dole daka yajin shinkafa da waken, kowa da wahala yaci yajin sauran ne ta kulle ta boye a sif ɗinta.
Da gudu ta dawo ta buɗe miyan kubewa danyen ta juye duka, cokalin da ta biya ta ɗauko a kitchen ta saka ta juya kan ta ajiye shi a wurin, ta dauki abincin ta nufi sashensu, a gaban site ɗin ta kalli Haɗaddiyar beymach ɗinshi baƙi siɗik se ɗaukar ido yake da yayi parking a wurin, baki ta taɓe ta isa kan motar da sbd yanayin kyaunta mutum kan iya finshi tsawo ta ɗaura