Showing 84001 words to 86608 words out of 86608 words
ba bata wani ci me yawa.
Duk yadda ya so tafiyarsu tare haka ya hakura ya barta sbd ya san yanzu tana bukatar babba kusa da ita, sede suna manne a waya.
Watanta ɗaya da sati biyu a gida ranar ta tashi da nakuda me tsanani, yana kwance tun dare yake ta juye juye bayan mafarkin ta da yayi, ya kirata bata yi picking ba.
Hankalinshi gabaɗaya ya tafi yola, haka dae da yaga baccin ba ze yiwu ba ya tashi ya fara nafilfili yana rokar mata sauka lafiya.
Bayan ya dawo sallar asuba ya danna kiran Jaddah, ta ɗaga daga yadda yaji muryarta ya rikice yana tambayar lafiya? Ta sanar mishi Fauza ke labor.
Hmm Allah ne kadai ya kaishi Airport lafiya don ma akwai available flight karfe takwas haka yayi ta safa da marwa a Airport ɗin hankalinshi duk a tashe.
Har ya isa yola ya isa asibitin bata haihu ba, kuma wai ta kwana a haka, ai be jira wani jawabi ba ya banka kofar ya shige, duk ta galabaita kaman jira nakudar ya sake taso mata.
A jikinshi ya sanyata yana mata Adu'a, wani riƙo da ta mishi seda ya runtse idanu be buɗe ba se da kukan jariri ya cika kunnuwanshi, Alhamdulillah! Yake ta nanatawa yana mata sannu a lokaci ɗaya yana shafa kanta.
Wani Sabon nakuda ne ya sake tasar mata, ba bata lokaci ta sake sulbiyo wani babyn.
Shikam Sam hankalinshi na kanta irin wahalar da ta sha se zufa take yi yana share mata.
Mika mishi yaran aka yi bayan an tsaftace su. Ya rungumesu hawaye na zubar mishi..
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!!"
Lallai Allah me kyauta da ƙari shine yau rungume da ɗan shi ba ma guda ɗaya ba har biyu, wani irin godiya ze yiwa ubangiji? Fitowa yayi dasu su Jaddah kowa farin ciki a take Fa'iza da tun asuba ta iso asibitin ta ɗaukesu hoto ta turawa su ya fadila kowa murna mata ne Duka kaman babansu yayi khaki ya tofar har hasken fatar.
Wani irin so da kauna da Faizan yayi ta nuna mata a asibitin sede ita ta ji kunya shi kam ko a gyalenshi, Kwananta ɗaya aka sallameta, Faizan ya kusa cika parlorn Jaddah da saye saye, duk.abunda aka ce ya dace me jego ta ci se ya je ya sayo, kan saniya har uku ya kawo ga manyan bindi yace ayi ta mata psoup tana sha.
Ranar suna yara suka ci sunan Jaddah da mammi, fa'iza ce ta musu inkiyar Arwa da marwa, me jego ta samu kyaututtuka masu dumbin yawa, ta shiga ta fita a wanka da ado kam masha Allah, shima angon karni ba'a barshi a baya ba suka dinga chanza dressing ana daukar su hotuna take suka baza ko ina latest parents of the month ba, kyautar tsaleliyar mota me rai da motsi Faizan yayi mata da wani set ɗin gold me tsada tukuicin kyautar da ta mishi.
Sanye da doguwar hijabi har ƙasa ta shigo gidan, idan ba ka mata farin sani ba bazaka gane ta ba, tayi baƙi sossai ta rame kaman ba Fatima ba, kai tsaye inda aka yi decorating don taron sunan ta karasa, a gaban Fauziyya kawai ta zube tare da kama kafafunta ta fashe da wani irin kuka da ya ja hankalin mutane masu yawa.
Faizan yayi saurin mikewa yana kallonta, Fauza ta ganeta tayi saurin tare shi ganin ze taɓa ta don rabata da jikinta.
"Fatima???"
Kowa sunan ya maimaita yana kallonta da mamakin yadda ta koma
"Don darajar Allah ku yafemana Fauziyya, ke da Ammi da mammi ku dubi Allah ku yafe mana ko zamu ga da kyau, Don Allah ku yafewa Auntyna ta tafi tana rokar gafararku sede babu halin zuwa nan ɗin..."
"Ta rasu??"
Fa'iza tayi tambayar idanunta duka waje
Kuka me ciwo Fatima ta cigaba da yi wadda ya saka su jin tausayinta.
"Ta rasu Fa'iza, ta ce don Allah in ce kuma ku yafe mata, ku rokar mata Allah gafara, ta kamu da cutar dajin kwakwalwa ba tare da mun sani ba aka mata allura, tayi jinya me tsawo wadda kan ta rasu seda kamannin fuskanta ya sauya, fatar fuskanta da naman haka suke zazzagowa suna zub....."
Kuka ne ya kwace mata, fa'iza ma nayi.
Fauza seda ta zub da hawaye jin irin wahalar da Aunty ta sha kan mutuwa lallai wadda yace ruwan wani baze tafasa ba nashi ko zafi baze yi ba, yanzu wa gari ya waya? Arziki, kuɗi babu abunda baya jawowa.. Allah ya tsarremu da son zuciya.
Sun ce sun yafe sauran ita da ubangijinta, Fatima tayi ta godiya ko da Baba prof ya tambayi ina take zaune ita nan ta gaya musu ai Aunty ɓoye iyayenta tayi suna fama da baƙar rayuwa, kilan da ta taimaka musu sun zama wasu abu kan barinta gidan Sulaiman ɗin da sun iya sun Haɗa mata kudin aikin da ya gagara har ta mutu da azabar ciwon cancer.
Ta sheda musu itama zata koma gidan nata mahaifin dama Aunty ne taki sam ta bari su wani shaku sbd burinta a gidan prof ɗin..
Kyauta me yawa suka mata, Faizan dae be ce komai ba, se Kallonshi take da yaranshi rungume kirjinshi tana jin yadda azabar sonshi ke huda zuciyarta sede ya ta iya ba komai kake so kake samu ba.
***
Yau suke gama wanka, ita da su faazila suka fita zagayen arba'in sun zazzaga wuraren en uwa da abokan arziki, sun zo ta wurin gidansu Sakina tayi parking motar ta sauka tana tambayar me gadi mutanen gidan.
Yace ai iyayen sakina sun rasu se ita kaɗai da masu aiki, itama ta tafi islamiyya ne.
"Islamiyya"
Fauza ta maimaita.
Bata gama rufe baki ba se ga Sakina ta taho ita da wani a gefenta kanta ƙasa hannunta rungume da Alqur'ani.
Ɗaga kan da zata yi se taga Fauza da sauri suka rungume juna sakina na fashewa da kuka sossai, Gaisawa suka yi da mutumin nan kan ta cewa su Faazila su karasa ciki.
Sakina ta cika musu gaba da abun motsa baki kan ta zauna tana ta kallon su Arwa yaran bul bul gwanin sha'awa kaman yaran labarawa.
"Sakina ina rahama?"
Ta tambaya, Sakina na kuka tace
"Fauzaa na ji tsoron Allah naji tsoron rayuwa, na rasa iyayena a hatsarin jirgin ruwa hakan me makon ya saka min natsuwa Dukda kaɗaici da rashin wani dangi yasa na sake samun duniya yadda na so nake yi, Fauziyya mun tafi Gombe kusan mu shidda muna dawowa muka haɗu da wani mummunan hatsari, da idanu na na ga mutuwa Fauziyya, kowa ya mutu a gabana har rahama... Tun daga sannan tsoron Allah ya saukarmin na fara tuba.
Kaɗaici ya min yawa, se masu aikin gidanmu da da nake wulakantawa suka zama en uwana, su suka sa na shiga islamiyya yanzu haka wadda kuka gaisa dashi malami na ne kuma shi zan aura"
Ajiyar zuciya me nauyi Fauza ta sauki, Sakina ta nemi yafiyar ta bisa hanyar da suka jefa ta a baya, tace ta yafe kuma in shaa Allah auren ya tashi zata halarta.
kaman kar su Rabu bayan sun yi exchanging numbers Fauza ta wuce gida, sati ɗaya bayan nan ya zo ya ɗaukesu da wata da Jaddah ta sama mata me taya ta renon yara suka wuce Abuja.
Maternity leave ɗinta ya riga ya kare so makaranta kawai ta koma, tana kuma kula da yaranta da mijinta a gefe guda.
***
Bayan tsawon lokaci.
Cikin bacci yaji barinta jikinshi ya zata ma bayi zata shiga se yaga ta nufi kofa ta buɗe ta fice.
Mikewa yayi yabi bayanta, ƙasa gabaɗaya ta sauƙa a dining ta zauna bayan ta ɗauko ruwa ta zare bowl ta Haɗa cornflakes ta fara sha.
Daga saman stairs ya tsaya yana kallonta da mamaki karfe biyun dare?
Zuwa yayi ya zauna gefenta tare da d'aura hannunshi d'aya kan ha'barshi zuwa bakinshi ya karkace sossai yana kallonta ba tare da ta sani ba.
Tayi nisa wurin shan cornflakes d'inta sbd yunwar da take ji d'aga kan da zatayi kawai ta ganshi bazata hakan ya mugun Bata tsoro tayi Baya luuuu zata fad'i daga ita har kujeran yayi azamar tarbota tare da kurawa firgitattun idanunta ido, a hankali ya mayar kan lips d'inta da suke d'an bud'e kad'an sbd tsorata.
Daidaitata yayi yana cewa
"Easy precious ni ne"
Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke ta shagwaɓe tace
"Abban twins ka tsorata ni wlh"
Yace
"sorrie! Ina mamakin yadda daaɗin cornflakes ya sa kika kasa jin zuwana ma gabaɗaya"
Cigaba da shan kayanta tayi ba tare da tace komai ba, ya jira ta gama kan suka koma seda suka leƙa yaransu da yanzu suke shekara da wata shidda babu abunda basa ci babu kuma inda basa zuwa kan suka koma ɗaki.
Da asuba kan tayi sallah seda ta sake shan cornflakes shi dae be ce komai ba, suna breakfast ita cornflakes take sha.
"Anya lafiya Fauza?"
Tace
"me ka gani?"
Yace
"shan cornflakes ɗin nan haka kawai nake jin ba ƙalau ba"
Gabanta ne ya faɗi, ita dama ta ɗauko Ammi ne in tana shayarwa bata period to haka itama bata taɓa yi ba tun samun cikin su, goyo me tsafta ake cewa ko, to amma kwata kwata en biyu yaushe suka girma? Gashi karatun ta ya ɗauko gangara yanzu duk bata da wani lokaci na kanta.
Bata ce komai ba, bayan ta sallami su twins ta fito da niyar wucewa school ta biya asibiti, abunda take tsoro ne ya tabbata ciki take dashi na tsawon sati biyar.
Kasa zuwa school ɗin tayi ta komo gida ta shige ɗaki ta fara kuka, yana tsaye balcony ɗinshi ya ga shigowar motan ta shiru shiru ya dauka mantuwa tayi sede be ga fitar ta ba ya sa ya fita ya nufi ɗakinta.
Hankalinshi ya tashi ganin tana kuka ya hau lallaɓata da kyar ta ce mishi wai wani ciki ne da ita.
Da tsantsar mamaki yake kallonta
"saboda kina da ciki shine kike kuka Fauziyya?"
"Yaya ka kuwa san wahalar renon ciki da nakudar? Kwata kwata yaushe na haifi twins? Ga school ni dae wlh ba zan iya b...."
"Kul Fauziyya!!"
Ya daka mata tsawa.
"Karki kuskura wlh karki fara kawo koma menene yake ranki ki binne shi, ciki ne ya riga ya shiga don haka se kin haife shi"
Yana kai nan ya miƙe ya fice yana banko mata kofar.
Sossai tayi kuka kan bacci ya ɗauke ta.
Gabaɗaya ranar ta fita harkar su twins ɗin da baban ko fita daga ɗakinta ta ƙi yi, tana ji yadda suke kiran
"mommy! Mommy!!"
Bata ko kula su ba seda daddyn nasu ya fita daga nashi ɗakin ya ɗaukesu yayi nashi dasu.
Wasa wasa seda suka kwana uku a haka, bata shiga harkarsu banda kuncin rai da ta sawa kanta ko makarantar bata zuwa, bata taɓa kai hannu jikin yaran ba amma a tsakanin seda ta make Arwa wadda ya sake saka matsala tsaninsu seda yayi kaman itama ze daketa.
Jafar yake faɗawa matsalar tashi don basu taɓa samun damuwa haka ba, wlh ko bacci baya iya yi tunda suka raba makwanci, Jafar ya kirata a waya ya mata nasiha sede be wani shige ta ba.
Da Faizan ya gaji ya kira baba Alhj ya faɗa mishi, aiko kaman ze bar yola ya zo Abuja ya daka ta don faɗa seda baba prof ne ya dakatar dasu ya kirata ya mata nasiha sossai da kuma nuna mata kyauta ce daga Allah wasu na nema ido rufe basu samu ba, kan ta sassauto be bar Faizan ɗin ba ma ya mishi faɗa shima ya nuna mishi Fauza har yanzu yarinya ce, kwata kwata yanzu ne take shirin yin 19 ga albarkan yara Allah ya bata idan be bita da lallami ba kenan ba anfanin tarin shekarun da ya bata.
Wayanshi da ta gama jin nasihar mammi ta mike ta nufi ɗakinshi Shiga d'akin tayi don bashi wayanshi ta samu har bacci ya d'aukeshi, a gefen hannunshi ta zauna tare da kura mishi ido na seconds yadda lashes d'inshi suka kawata fuskanshi zuwa sajenshi da yafi komai d'auke mata hankali lumshe ido tayi ta bud'e kan pink lips d'inshi da ya d'an bud'e kad'an, murmushi me kyau ta saki he looks so damn cute kaman d'an baby, d'an buge goshinta tayi tare da mikewa da sauri bata d'aga kafanta ba taji ya rike hannunta tare da fisgo ta ta fad'a kan gadon kanta ya sauka akan hannunshi da ya Mikar cikin wani irin yanayi ya bud'e idanunshi da suke cike da bacci da tsananin kewanta ya zubasu cikin nata yana lumshewa a hankali.
Wani abu taji daga tsakiyar kanta har zuwa babban yatsanta ya tafi zirrrrr, runtse ido tayi tare da d'an juya kanta kad'an zuwa kan hannunshi hakan ya bawa gashinta daman zubowa saman fuskanta, hannunshi d'aya ya sa ya maidashi a hankali zuwa bayan kunnenta, tare da maida hannun cikin hannuta dake tsakiyarsu ya fara shafawa a hankali.
"I badly missed you hayatee...if am left alone without you how am I supposed to live?"
In a whisper tace
"I missed you more Hubby am so sorry, na yi kuskure, forgive ur wife"
Peck yayi mata a goshi kan a ƙasan maƙoshi yace
"u are pardoned, I love you"
Ta rungumeshi tana mishi raɗa a kunne
"I didn't fall in love with you because I was lonely or lost, I fell in love with you because after getting to know you, I wanted to make you a parmanent part of my lif..."
Bakinsu ya haɗe sbd kasa hakura da yayi a take suka fara nunawa juna zallar so da kauna me tarin yawa wadda baki yayi kaɗan ya misalta ko ya furta.
FIVE YEARS LATER
Da gudu suka hauro saman suna rige rige, dukkansu uku sanye da uniform na makarantar boko
"mommyyyy! Daddyyyyy we are back yeyyyyy"
Fauziyya dake daga tsaye tana serving Faizan Abinci ta haɗe fuska tamau tana gyara tsayuwar ta da ya bayyana cikin jikinta da ya soma girma tace
"Arwa, Marwa, Alaya me na faɗa muku akan sallama?"
Chak suka tsaya se suka juya sum sum suka koma da baya suka doka sallama daga karshen stairs seda ta amsa ta musu izini kan suka hauro har lokacin bata sake fuska ba.
"Sorry mommy mun manta ne"
Arwa ta faɗa tana kama kunne.
Marwa ma tace
"sorry mommy"
Alaya da taci Sunan Ammi tace
"we're sorry mammy"
Faizan yace
"my princesses are sorry daga yanzu bazaku sake shiga wuri ba sallama ba ko?"
Da sauri suka gyaɗa kai Alaya tace
"Allah mommy in mun sake punish us"
Dariya Fauza tayi wai wani punish them ko me za'a yi punishing ɗin oho,
"oya kuje Mamu ta muku wanka ku zo ku ci abinci kar kuyi lattin islamiyya"
Da gudu suka wuce ɗakin su..
Faizan ya dube ta yace
"mommy please a taimakeni da soldiers nima in samu friends"
Murmushi kawai tayi, da dare suna kallon news ake sanar da mutuwar ɗan dan majalisa wadda ya shigar da kwaya wata kasar da ba'a shiga da kwaya kwata kwata suka kama shi ya jima a prison ɗinsu kan ya mutu, Zubair ta gani rayuwa fa kenan in kana takamar kuɗi da hanya akwai inda zaka je ka zama bawa ko almajiri don a komai wani ya fi wani ne..Wai gaba da gabanta aljani ya taka wuta.
****
ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!!
ANAN NA KAWO KARSHEN WANNAN LITTAFIN NA DIDDIGAR ƘAYA ME WUYAR TSINCEWA, ABUNDA MUKA RUBUTA DAIDAI ALLAH YA BAMU LADA WADDA KUMA MUKAYI KUSKURE ALLAH UBANGIJI YA YAFE MANA. WAENDA SUKA SAYA INA MATUKAR GODIYA DA KAUNA KUMA INA ALFAHARI DA KU A DUK INDA KUKE, KU KUMA DA KUKA FITAR MIN DA LITTAFI KU KUKA SANI DA ALLAH, AKWAI FULL DOCUMENT ƊINSHI IDAN DA WANNAN PAGE KIKA FARA CIN KARO MAZA BIYA KI MALLAKI NAKI KI SHA KARATU KI KWASHI ILIMI.. ALLAH YA SADA MU A WANI LITTAFIN NA GABA🥰🥰❤️🔥
DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰
Karku sake a baku labari.
🖤Gureenjoh🖤