Showing 81001 words to 84000 words out of 86608 words

Chapter 28 - DIDDIGAR ƘAYA COMPLT Hausa novel

21 Aug 2024

18454

haɗu da Afnan suka yi ta murnan ganin juna nan da nan ta hau ɗaura mata abunda ya wuce ta a makarantar.

Se yamma lis ta dawo gidan ta ɗan samarwa kanta abun ci kan ta watsa ruwa tana shirin sa kaya se taji wayanta na ringing, dubawa tayi se ta saki murmushi ganin shine ke kiranta, ɗagawa tayi nan fa suka fara hira, jin ta sake sossai ya saka shi ce mata ta kunna data.

Kunnawa tayi se ga video Call Sam ta mance ma towel ne jikinta tayi picking, daga chan ya kura mata idanu yana kallo she's morethan beautiful ya ayyana hakan a ranshi.

"Ka ci abinci yaya?"
Ya karkata kai kaman ɗan yaro yace
"wa ze bani precious?"

Puppy face tayi tace
"Toh ka je ka saya mana yaya?"

Yace
"ni uhm uhm se an chanza min wannan sunan kan zan ci abinci yau"

Dariya sossai ta saki yana ta kallonta yana murmushi, tace
"tohm faɗamin wani suna kake so?"

Yace
"ko ma wani iri ni dae a chanza min yayan nan"

Tana dariyar abunda zata faɗa tace
"Toh Uncle? Ko mai gida?"

Dariya ya saki yana cewa
"kuttt lallai yarinyar nan Allah karki sake na kama ki, me wani uncle?"

Tace
"tohm am sorry mi carazon suna dae se ka gaji dasu in shaa Allah, now please go and eat"

Yace
"yes my queen, take care of yourself zamu yi magana anjima right?"

Kai ta gyaɗa, yana kallonta yace
"I love you...u are the story that I never want to end"

Tayi murmushi kawai tare da hanging up, ajiyar zuciya ya sauke yana shafa kanshi he hopes ta so shi watarana.

Haka rayuwa ta cigaba, don seda yayi kusan 2weeks be dawo Abuja ba, tana fama da karatu ita kuma a gefe ɗaya yana kasheta da soyayyarsa me tsayawa a rai, zasu yi voice call, su yi chat su yi video call duka, dukda har yanzu in ze mata kalamai na so da kauna ta kan yi murmushi ne kawai ba tare da ta bashi amsa ba amma in ta hira da shagwaɓa ne haka zata saki jiki tayi ta zuba mai, kusan duk abunda ya faru a rana haka da dare se ta bashi labari.

Shi kuwa ta bangarenshi ko da awa ɗaya baya iya yi idan har be ji daga gareta ba.

"Kin yi sallah? Kin ci abinci? Kar fa ki fita ba hijab, ya lectures kun gama? Ki tabbatar kin yi Adu'a kan ki yi bacci baby, Allah ya miki albarka"
Kusan sune kalamai mafi tsada a gareta wadda ba'a kai dare be yi mata waennan tambayoyi na kulawa ba, wani lokacin in tace suna da CA haka sede ta ga text ɗinshi

"kin yi karatu? Kiyi karatu bana so wanna CA ya wahalar min da ke"

Misalta irin yadda yake kula da ita Dukda distance dake tsakaninsu ɓata baki ne, ta gefe ɗaya matar Faisal ta haihu ya saka driver ya kaita suna da sha tara na arziki don seda ta biya shopping abunda yayi ta bata mamaki sadda ta dawo daga sunan kasa hakuri tayi ta koma ɗakin nashi inda ya ce ta ɗauki kuɗi ɗazu ta je shopping.

Wayan ta ɗauko tana Juyawa a hannunta wannan wayanta ne wadda ta taɓa bari a motarshi, to me yake yi dashi? Ta tambayi kanta Kunnawa tayi se taga akwai chaji alamu ana yawan yin chargynshi dubawa tayi babu sim, mayarwa tayi ta ajiye bayan ta kashe ta mike ta bar ɗakin, hirarrakin matan abokanshi ke dawo mata har ta isa ɗaki.

Dukda bata sa musu baki ba sede ta ɗauki abubuwa masu yawa ciki, wadda dole zata yi anfani da wasu, ita ɗin idan ta duba se taga kaman tana cikin masifa da tsinuwar mala'iku tunda dae gashi ta hanashi abunda ake kira da auren gabaɗaya sbd wani laifi da yayi mata da har ta mance ma, dukda ba haushinshi take ji ba tsoro take ji, tsoron abun ya riga ya mata tasiri, bayan haka shi matafiyi ne yana shiga wurare daban daban yana ganin mata kala kala in ya faɗa halaka sbd ita fa?

Tuna cabin crew na ranan tayi da irin shigar su se taji hankalinta ya tashi, yanzu fa da su yake yawo duk inda zashi, kuka ta fashe dashi tana jin zafin kishi na huda kirjinta.

Kaman kuwa yaji a jikinshi se ga video Call daga gareshi, ɗagawa tayi bayan ta share hawayenta.

Idanu ya zuba mata na seconds kan ya miƙe zaune yana jefar da pillown hannunshi yace
"what happened? Meyasa kika yi kuka?"

Kawai se ta sake sakar mishi kukan.
"OMG darling please! Menene? Me ya faru?"

Ganin tana shirin ɗaga mai hankali ne ya saka ta tsagaita kukan tace cikin wata kalar murya.
"I miss you 😩 please ka dawo haka..!"

Ajiyar zuciya ya sauke shima cikin kasalalliyar murya yace
"kukan duk na kewata ne pretty?"

Kai ta gyaɗa tana sake matso hawaye..
"Ya rabb! I wanna hug you so tide right now...but you are too far I also miss you so bad dear.. amma me aka tanadar min da ake so in dawo?"

Yayi maganan yana kwanciya kan pillow ta saki murmushi tace
"Duk abunda kake so"

Yana dage gira yace
"really? Duk abunda nake so? U promised? Zaki bani vitamin K, H da L?"

"Me kuma hakan mi carazon?(My heart in Spanish).

"Lalala baki san vitamin K,H da L ba?"
Ya faɗa harda kama baki.

Ta gyaɗa kai yace
"tohm lemme educate you, vitamin K stands for kiss, H stands for Hug and L stands for love.. Zaki bani?"

Kai ta gyaɗa tace
"everything..!"

"Kar fa ki sa in kamo hanya yanzu?"
Dariya ta saki yana murmushi yace
"soon zaki ganni kinji? Don't cry again please"

Kai ta gyaɗa mai, nan ta sake suka fara labarin gidan suna da kyaun babyn, jin ya kamo zancen saura nata ne yasa ta sallameshi ta gudu.

Washegari a gajiye ta dawo daga school ko abinci bata iya yi ba ta sha tea bayan tayi wanka ta saka light black shirt da iyakarshi cinyarta tare da zubewa kan gado bayan ta yi sallar isha.

Har bacci ya fara shirin daukarta kawai taji tsayuwar mota, da sauri ta miƙe tana leƙa window se ta hangeshi ya fito sanye da kananun kaya baƙaƙe wadda suka mugun amsar farar fatar shi yayi fresh yayi wani irin kyau, da mamaki take Kallonshi har ya ɓace da alama ciki yayi shine ko ya gayamata yana zuwa?

A take farin ciki ya cika fuskar ta, da ɗan gudunta ta buɗe kofa zata nufi sauƙa se suka yi kicibus a parlorn saman, fadawa jikinshi tayi tana murnan ganinshi shima ya rungumeta tsamm yana shakar kamshin ta me daaɗi, daga haka ya nemi zarce mata nan fa tsoro ya bayyana kiri kiri a fuskar ta, janyewa tayi ya tsaya yana kallonta.

"Mu je kayi wanka bari na samo maka abunda zaka ci"
Tana shirin wucewa ya dawo da ita jikinshi yace
"ke kin ƙoshi?"

Kai ta gyaɗa yace
"fine"
Yana faɗar haka ya ɗauke ta chadak se ɗakinshi, tana ta zillewa haka ya ribaceta duk da irin tsoratar da tayi ya lallaɓata kuma ya bita a hankali ya cika ta da soyayyarsa me tsayawa a rai, tayi ta mishi raki da shagwaɓa... Wannan dare na daga cikin daren da bazasu taɓa mancewa dashi ba.

Sossai ya buɗe musu wani sabon baabin soyayya, har mancewa da karatu take bare ma da ya ɗan kwana biyu be sake tafiya ba, komai da komai tare suke yi, da yamma su fita koyon tuƙi ana yi ana shan love, a cikin kwanakin duk wadda ze gansu se sun bashi sha'awa, kana ganinsu zaka san akwai tsananin soyayya da shakuwa tsakaninsu.

Kwance take kan doguwar kujera a parlorn tana kallon wani series film yayi sallama ya shigo, da sauri ta miƙe ta tare shi suka rungume juna ya bata peck a kumatu tace
"sannu da dawowa Noor"

Yace
"yauwa my queen, je bedside ki ɗauko min 50k zan sallami driver ɗin nan tunda my queen hannu ya faɗa"

Tayi murmushi tare da Juyawa ta nufi ɗakinshi ta buɗe se ta sake cin karo da wayanta, a hannu ta ɗauko bayan ta ɗauko kuɗin Dukda ya ga wayan sede be ce komai ba ya karɓi kudin ya sauka.

Bayan ya dawo ya zauna ta kawo mishi ruwa da lemu ya sha, ta dubi wayan tace
"Yaaya a bedside ɗinka na ga wayan nan"

Yana kallonta yace
"uhmm"

Se ta rasa me zata ce, kawai se ta mike don mayarwa yayi hanzarin riƙo ta yace
"you wanna know me nake yi dashi ko?"

Kai ta gyaɗa tana Kallonshi ya janyo ta ta zauna gefen shi yace
"bude ki shiga gallery"

Ta buɗe tayi yadda yace
Hotunan ta ne masu yawa ciki kasancewar ta me yawan son ɗaukan pics, ta kalleshi ya ɗaga mata gira yace

"su nake kallo a ko da yaushe, ban san taya ba ban san yaushe ba na dae tsinci kaina tsundum cikin ƙaunarki wadda a ko yaushe bani da wani aiki se na kallon hotunanki, na kan yi chargyn wayan musamman don in kallesu, kusan babu wadda ban haddace kalar kayan, tsayuwar da kuma yanayin hoton ba... Believe me I loved you tun kan na san menene so"

Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke idanunta cike da hawaye ta rungumeshi tace
"our lives are one even though we are in two different bodies, I love you too"

Shima sake shigar da ita jikinshi yayi a hankali tace
"sweetheart! Meyasa Zubair yace ka mishi mugunta?"
Da sauri ya ɗago ta, tayi hanzarin Kallonshi gabanta na faɗuwa kar fa ya ɗauka da wata manufa ta mishi wannan tambayar..

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤



ƘARSHE

"why do you care to know?"
Ya tambaya fuskanshi ba cikakken fara'a.

Mikewa tayi tace
"am sorry"

Ɗakinshi ta shiga ta Haɗa mishi ruwan wanka ta fito tace
"ruwan wankan ka is ready"

Mikewa yayi ya wuce ta ba tare da yace komai ba ya shiga toilet ɗin yayi wanka, ko da ya fito akwai kayanshi marasa nauyi da ta fesa wa turare ta ajiye bisa gadon, dauka yayi ya saka bayan ya shafe jikinshi da mai da turarukan shi, fitowa yayi ya tsaya yana kallonta tana karasa gyara dining ɗin.

Takawa yayi ya rungumeta ta baya a kunnenta ya raɗa mata
"I just hate him tun daga sadda na ganki dashi a Abuja, wanchan ganin ya hana mini natsatsen bacci ba tare da na san dalili ba, a sadda na sake ganinku a hotel na ja mishi federal warning amma be daddara ba wai shine har da raba ki da school kina neco at that time ya zo min iya wuya, kuma na san shi dama farin sani sbd miyagun kwayoyi da yake yawan yawo dasu akan kama shi sau da dama a Airport kwana biyu a sake shi, so bayan ya dawo ya tafi Russia, that time nima Ina chan kuma ni zan tuƙo jirgin da ze dawo daga chan zuwa Nijeriya, I clearly saw him with the drugs again.. I then reported him Dukda na so hukunci me tsanani ya hau kanshi sede sun yi anfani da hanya da kuma kuɗi wurin kubutar dashi Dukda ko da ya dawo already you are mine, shiyasa ban kara bi ta kanshi ba"

Kai ta gyaɗa tace
"ga abinci"

Bata so Sam ta nuna interest ɗinta kan labarin kar ya ɗauka da wata manufa sanin yadda yake da zafin kishi a kanta, a tare suke cin abincin cikin plate guda, bayan sun gama ta tattare kwanukan.

"Are you OK"
Ya tambaya yana janyo ta jikinshi.
Kai ta gyaɗa tana ɗan murmushi yace

"menene?"
Ta girgiza kai, da yayi insisting se tace
Kawo kunnenka kaji yana mika mata ta d'an cije shi kad'an tare da Mikewa ta kwasa da gudu da gudu ya bi ta yana kokarin kamata tana zillewa.

Haka suka ta zagaye tana ta mishi dariya da gwalo daga karshe yayi nasarar kamata suka zube kan kujera yana mata jakulkuli da tambayar wa ya kama tana dariya sossai har da hawaye.

Bayan kwana biyu..

Karfe shidda ta fito lectures ta nufi motarshi ta shiga tana cewa
"washhh Allah na, hubby na gaji dayawa"

Yace yana riƙo hannunta
"sorry dear, mu je mu sayi abinci sannan mu wuce gida kiyi wanka se in miki tausa"

Murmushi ta saki, suna ƴar hira har suka isa restaurant bata shiga ba shi ya shiga ya fito daga nan suka yi gida.

Da kanshi ya ɗauko plates da spoons da ruwa ganin da gasken gaske ta gaji ɗin, don tunda ta zube kan kujera bata mike ba, Seda ya gama ajiye komai kan ta miƙe zauna buɗe ledar yayi tare da Fiddo takeaway ɗin yana buɗe psoup na kifin tayi hanzarin toshe hancin ta.

Kallonta yayi kan yayi magana ta mike da gudu tayi wurin dining sbd ɗaki ya mata nisa, a take ta fara kwara amai cikinta na murɗawa, a ruɗe ya riƙeta yana mata sannu ruwa ne kawai cikinta don tun safe da ta ci cips bata kara sha'awar komai ba, ta jigata sossai kan ya riƙo ta suka dawo tana kallon kifin ta sake fara kokarin amai cikin muryar kuka tace

"Don Allah yaya ka ɗauke kifin chan bata son gani"

Taimaka mata yayi ta zauna ya karasa ya ɗauke kifin zuwa kitchen yana mamaki.

Hannunta ya riƙe yace
"baki da lafiya ne shine baki faɗamin ba? Tun yaushe? Me ke damunki?"

Tace
"lafiya ta ƙalau kawai gajiya ce se kuma kifin nan bana son warin"

Yace
"wari kuma? Amma I thought kifi da nama na daga cikin abubuwan da kike so?"

Kai ta gyaɗa, yana ta kallonta se kuma yace
"wait..! Fauza"
Da sauri ta kalleshi, rabon da ya kirata da sunanta tun a yola, tace
"Na'am"

"when last kika ga jininki?"

Idanunta na kanshi ta tafi tunani, da sauri ta sanya hannu a kan cikinta tana cewa
"could it be possible?"

Yace
"sure, When last kika yi period?"

A hankali tace
"tun kan in bar nan in tafi yola, satin da ya kamata na fara kuka je kai da Fatima"

Ai da wuri ya tafi ya ɗauko mata hijab ya zo ya kama hannunta suka yi asibiti, bayan dogon gwaje gwaje Jafar ya musu albishir da ciki na tsawon wata uku bata taɓa sani ba se ranar, farin cikin da suka shiga baya misaltuwa barin ma shi da har Seda yayi hawaye, ze kira gida tayi saurin kwashe wayar tana shagwaɓewa.

"Eyyaaa yaya karka gayamusu don Allah"

Yace
"Meyasa bayan abun farin ciki ne ya same mu love?"

Tace
"Ai to ba zasu san abunda aka yi ba, ni dae bana so"
Dariya sossai ya saki, Fauza har yanzu taɓara irin na yara na damunta.

"Fine my baby mama, ba zan faɗa ba"

Daga asibiti yawon neman abunda zata ci suka fara, a wani tsadadden restaurant suka yada zango a gabansu aka ajiye abun gashi yana gasa mata nama tana ci, ta ci sossai kan aka kawo mata milkshake ta jingina da jikinshi.

Kwanciya tayi jikinshi tare da kai mishi cup d'in bakinshi yayi sipping ta dawor dashi nata ta sha tana sake murmushi.

Rayuwa ta sake yi musu daaɗi sossai, a week after suka fara exams ya ɗan yi tafiya bayan ya dawo lokacin ta gama ya shirya musu tafiya, Allah ya sa cikin nata ba wani laulayi me wahalarwa, ƙasar Greece suka tafi suka baje kolin soyayyarsu a chan, sati uku suka yi a chan kan suka wuce Australia se ganinsu Ya fadeela tayi.

Sun matukar burge ta soyayyarsu ya tafi da ita ga wani kyau da kowannensu ya kara da girma alamar hankalinsu kwance yake, daga nan suka wuce wurin Ya fadyaa husna tayi ta murnan ganinsu suma kwana biyu suka musu suka tattara suka dawo sbd hutun ta ya kare.

BAYAN WATA HUƊU

A hankali take sauƙowa daga jirgin sbd yadda cikinta yayi wani mugun girma Dukda kwata kwata wata bakwai kenan, kafafunta da kyar take ɗaga su sanye da wani bubu Abaya me stones ta yafa gyalen, yana rike da jakanta a hannu daya yana rike da ita suka nufi farhan dake ta zabga murmushin ganinsu.

Se kallonta ake sbd Fauza fa ciki be hanata gayunta ba, wani lokacin in su firdausi na tsokanarta ta kan ce ciki ne fa da ita ba hauka ta soma ba, suyi ta mata dariya, shi karan kanshi ya kan yaba kokarin ta Dukda kankantar shekarunta bata taɓa gazawa a kanshi ba daga cimarshi, tsabtarshi da hakkinshi babu abunda ta dena ga karatu.

Gidan cike yake da mutane sbd yaune ake walimar Fa'iza da Faraj se Falaq da itama se yanzu lokacin yayi, a haka suka ratso mutane duk yadda take sunne kai shi kam ko a jikinshi se kara mannata da jikinshi yake har parlorn Jaddah.

Farin ciki ne ya cika ta fall ko a hira basu san da cikin ba se ganin abu kawai suka yi, daga Amminta har mammi ba karamin farin cikin ganinta haka suka yi ba hankali kwance, kar iyayenta mazan su ji labari.

Duk yadda ta ci Burin bukin se gashi ita a zaune tayi komai sbd kafafunta da suka ƙi, har aka sada su da gidajensu jama'a suka watse.

Tana kwance kan gadon Amminta hannunta waya ne tana dubawa taga saƙonshi.

Mikewa tayi zaune ta dubi Ammi tace
"Ammi akwai abinci kuwa a sashen nan?"

Ammi tace
"eh a kawo miki ne?"

"A'a Yaya za'a Haɗawa faazila ta bini dashi na tabbatar be ci komai ba"
seda ta faɗa kuma kunya ya kamata, Ammin murmushi kawai tayi tare da miƙewa ta hado ta ba faazila tuni Fauza kam ta lallaɓa ta wuce.

Tun daga kofa ya tarbeta ya ɗan rungumeta
"Sannu baby mama... Allah ya sauke ki lafiya, Allah ya miki albarka".

Kusan kalaman da ta saba ji kenan daga gareshi tunda cikinta ya fara girma
"Ameen Daddyn baby thank you"

Zama suka yi yana nuna mata wasu gadajen yara masu kyau sossai wai ta zaɓa order ɗinshi zasu zo wani sati, tace
"yanzu duk waenda muka yi ta jida a Abuja be isa ba hubby?"

Yana murmushi yace
"ko duka shagunan Abuja muka saye ni dae be min ba... Uhmm na fa ba da aikin ɗakin nan da muka yi magana"

Ɗakin Fatima ne ya sa aka fidda komai za'a gyarawa baby, tayi murmushi kawai se ga faazila da abinci, shi ya karɓa suka ci tare sbd ya Santa idan ba shi yake bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login