Showing 33001 words to 36000 words out of 86608 words

Chapter 12 - DIDDIGAR ƘAYA COMPLT Hausa novel

21 Aug 2024

18443

ni na janyo don na san halin Fauxa na Haɗata da wata yarinyar makota a nan farkon layin ganin kullum tana wahalan samun abun hawa, to wai Fauziyyar sau biyu bata rubuta paper ba tana fita wani ke rubuta mata a madadinta, to ranan sai bata dawo da wuri ba shine yarinyar ta fara zagin ta har ta kai kaina se fauziyyar ta fasa mata baki a mota kaman yadda driver ya bada nashi bayanin, to bayan nan ne suka haɗu da ƙawayen ta wai zasu dake ta shine tayi musu dukan kawo wuƙa iyayensu kuma suka kawo min hukuma sun kuma aibata ni sun yi min kazafi wadda na Barsu da Allah zasu bada shedar shi ranar gobe"

Shiru parlorn ya ɗauka kan Jaddah da ta zabga tagumi tace
"yau na shiga uku da yarinyar nan, to ina take zuwa? Da wa take fita kuma?"

Baba prof ya kalli babanta da yayi shiru hawaye na shirin zuba mishi yace
"kar ka yi mata kuka Sulaiman, da ni da kai duk ɗaya ne haka yaranmu don an zo kamani a madadin mahaifin Fauziyya ba'a yi kuskure ba, a yinin yau na yanke hukunci akan Fauziyya wadda nake so duk ku sheda, bana bukatar shawarar kowa bayan na mahaifiyata, na yanke nan da watanni biyu zan ɗaurawa Fauziyya Aure da Faizan..."

Ɗib haka parlorn ya ɗau shiru, Faizan dae yi yayi kaman be ji ba don ya san kila karan jirgi ya fara taɓa mishi kunnen shiyasa ba ya ji da kyau, ko a imagination baze taɓa kawo wannan hadi ba bare a zahirin gaskiya.

Mammi tace
"Allah ya sanya Alkhairi, wannan haɗi shine daidai"

Baba Alhj yace
"A'a yaya, ya zaka fara wannan kwamachalar? Taya zaka fara Haɗa nitsaste kaman Faizan da fits...."

"Akul Sulaiman, in dae ba kana so ka nuna min bani na haifi Fauziyya bane babu ruwanka naka idanu, Faizan na ba Fauziyya kuma ya riga ya zauna.."

Ba don kar ace yayi rashin kunya ba da se ya tambayi baba wai wani Faizan ne yake referring to, kanshi gabaɗaya ya dau hayaƙi in kuwa baba yayi hakan ba karamin cutar shi yayi ba, me ze yi da sauran wasu? Me ze yi da ƴar giya?

Jaddah sossai ta nuna amincewarta da shawaran a haka suka tsayar kan su Faraj suka yi ta ba baba hakuri yace ba shi zasu ba wa ba Fauza zasu ba kuma biyar da Faizan ya kashe a asibiti su tabbatar sun biya shi, a haka aka watse aka bar Faizan a zaune a wurin.

Seda baba ya kula da Sam kaman baya hayyacinshi ne ya tashi yaje ya ɗibo ruwa masu sanyi ya kawo mishi
"karɓi ka sha!"

Ya kalli kofin kan ya ɗaga ya kalli baba da rinannun idanunshi yace
"na koshi"

Baba yace
"karɓi mana ai ruwa rayuwa ne"

Karɓa yayi ya kafa kai ya shanye tas kan ya ɗago ya sake kallon baban, murmushi shimfiɗe a fuskanshi yace
"karka ɗaga hankalinka Faizan, a yadda na sanka da natsuwa, kawaici da hangen nesa kaman mahaifiyarka ina so ka cigaba a haka, na zaɓa ma Fauziyya Kaine sbd Kai ne Allah ya sha nuna min a duk istikhara na, da kai hankalina ya fi kwanciya, na san bazaka taɓa tozarta abinda na baka ba"

Faizan yayi shiru kaman ruwa ya cinye shi
"baba fa watana kwata kwata uku ne da aure"

Yace
"na sani, Fatima da mahaifiyarta masu fahimta ne na san zasu fahimta"

"baba mahaifiyarta bata taɓa ƙaunata ba, ko gaisuwata bata taɓa buɗe baki ta amsa ba"

Yace
"na sani wannan duk ba wani abu bane ba lallai kowa ya so ka a duniya ba, daga kan Annabawa har Sahabai zuwa malamai babu wadda bashi da maƙiya"

Yace
"Baba Fauziyya da Fatima basu taɓa shiri ba taya zan iya haɗe kansu su zamar min tsintsiya madaurinki daya kaman yadda ka zamarwa iyalan ka?"

Yace
"kai ɗin jarumin namiji ne wannan me sauƙi ne a gareka, ina me tabbatar maka zaka yi alfahari da wannan haɗi watarana, ka je ka kwanta karka yawaita tunani instead ka raya daren idan ba zaɓin Allah ba ce se ka ga Allah ya musanya mata da alkhairi in kuma ka ga an ɗaura to kaddarar ku a sarƙe take da juna tun fil azaal"

Mikewa yayi yace
"Na gode, se da safe"
A ladabce kan ya juya ya fice.

Wannan dare haka ya zamarwa Faizan daren tashin hankali don ya kwana yana rokon Allah akan wannan abunda baba ke shirin tinkarar rayuwarshi dashi, duk mazan gidan a rasa wadda za'a lakabawa wannan fitananniyar yarinyar se shi? Yayi nadamar zuwa yola a ranar ya fi sau dubu kila da be zo ba baba be ganshi ba da wani ya zaɓa ya baiwa ba shi ba.

Jadda da mammi dae sun kwana cikin farin ciki yayinda baba Alhj ya kwana yiwa wan shi Adu'a ya tabbatar ba don shi ba da lamarin Fauza yanzu ya kaishi ƙasa, Ammi ya kira ya mata bayani tashi ɗaya ta nuna Allah ya kasheta wallahi baza ta kara Haɗa zuri'a da Mammi ba an yi mata fin karfi a lokacin fadyaa yanzu kam babu wadda ya isa, har gwara faahim sau dubu da Faizan a gareta.

Baba be kula ta ba ya yi kwanciyar shi don in yace ze biye mata se Amarya ta ji kuma yana so ya sanar da ita ta yadda zata fahimta babu cin fuska ko son kai a wannan tafiyar.

Washegari zaliha ta tashi daga baccin da ta koma bayan sallar asuba bata samu Fauza ba, neman duniya da nurses suka mata bata cikin asibitin ko da Baba prof da jadda da kuma Aunty Amarya suka iso ana kan nemanta ne.

Alamu dae sun nuna fita tayi sede ina zata da rauni a jiki?

Ita kuwa tana tashi ta mike zaune tana kallon inda suka bare mata a fatarta da take matukar tattali, ranta yayi baƙi kirin da irin wannan tozarci da yayyun nata suka mata, ta tabbata duk gidan maƙiyanta ne banda mammi da jadda da Amminta, lallai abunda suke gudu se ta sake yi in basu kasheta ba ba su cika mugaye ba.

Dira tayi daga kan gadon ko hijab ɗin da ta dauka ganin yadda ya fashe yasa ta cillar, takalmin zaliha ta saka ta fice, abun hawa ta tare se gidansu sakina, ta sa me gadi yaje ya karbi kudin ya kawo mai, sossai hankalin sakina ya tashi da ganinta haka.

Anan tayi wanka ta sauya kaya tayi kwanciyar ta bayan ta ci abinci, duk yadda sakina ta so tayi magana kasawa tayi da ta matsa se ta kawo kuka ta sa, hakan yasa zaliha bare wasu tabs tace
"sa wannan a ƙasan harshen ki duka biyu ki barshi ya narke da kin yi bacci kin tashi bacin ranki ze kau"

Sawa kuwa tayi ta kwanta, a haka tayi bacci har sha biyun rana kan ta farka abu kam ya fi karfin jininta ga shi ta bata overdose ne, tana tashi ta gayawa sakina duk abunda ya faru ta kuma ce tana so ta kunsa musu bakin cikin da zasu saka wuyan ta gabas su yanka, wayan sakina tayi anfani dashi ta kira Zubair luckily ya koma da yau abunda yake so da ta bashi.

Haka ta diro ko mayafi taƙi sakawa kaman ba ɗiyar musulmi ba ta nufi fita, Sakina da kyar ta shawo kanta akan driver ya maida ta.

A farkon layinsu tace ya ajiye ta don tana so kowa ya kalleta yadda su Farhan zasu kara jin haushi, aikuwa kaman ta kimta daidai.

Farhan, Faizan, Faraj, Baba Alhj baba prof da polisawa ne tsaye ana batun yadda za'a samo ta shi Faizan kaman dole ce kawai aka mai na shiga case ɗin zuciyarshi na bashi wurin watsewarta tayi don mashayi daga ranshi ya ɓaci abun shaye shayenshi yake nema ya rage zafi.

Yana cikin wannan tunani ya ɗan kalli hanya har ya ɗauke idanu yayi saurin sake mayarwa ya zuba mata su yana kallo, tun daga nesa zaka san a make take mankas, so yake ya janye hankalin baba Alhj sede yana juyowa yaga duk suma sun zuba mata idanu, ga bandage a jikinta ta sa wani riga da da kadan ya sauka kaurinta, hannunta duk a bayyane gashin kanta a Parke cikin loose bon, Baba Alhj ne ya tafi ze fadi, Baba prof yayi saurin tare shi yace

"Menene haka Sulaiman? A kanka aka fara jarrabawa? Kana so se ka ɗaurawa yarinyar nan abunda ya fi wannan?"

Su Farhan yayiwa kallon duk wa ya janyo? Ba ku ba? Kan ya saki baba Alhj ya fara tattaki zuwa gareta.

Maganganu take maras kan gado tana faɗin laifin babanta ne da yayi mata baki kullum yake kiranta fitsararriya gashi fitsara ta bita, ba su Farhan sun ce zasu mata abunda bazata kara marmarin rayuwar banza ba? To gashi ta kara su sakata gabas su yanke yanzu yanzu zuwa tayi don su gani, Kaman Faizan ze yi kuka don tausayin kanshi yanzu da abunda Babanshi ze Haɗa shi kenan?

Har ɗakinta ya kaita a sashen Jaddah tare da taimakon ta ta shimfiɗar da ita se bacci, duk idanu suka zuba mata.

Jaddah tace cikin karfafa mishi gwiwa
"Adu'ar mu baze taɓa faɗi ba professor, ka kwantar da hankalinka abunda kake shirin yi in shaa Allah shi ze zama silar warakar komai, Allah maji roko ne me jin ƙai ka fini sanin cewa baya taɓa juyar da Adu'a sai de in ya musanya da abunda ya fi alkhairi, ya kuma amsa ta hanyar da tafi kowacce daidai, sadaqa maganin masifa ne, haka kuma Qur'ani waraka ce, Adu'a kuma takobin mumini ne duk bamu daina akan Fauza ba kaga kenan muna da yakinin Allah ze karɓa ko ba daɗe ko ba jima"

Yace
"hakane mama, bana kokonto akan Hukuncin Allah sede a duk sadda zan ɗaga idanu na kalli yarinyar nan jikina yana bani wani abu na daban mama, gani nake ana zaluntarta amma ban san ta ya ba, tausayinta ke ratsa zuciyana har na kan zubar mata da hawayen tausayawa in na kalleta, ba ni kaɗai ba sau ba Adadi Aisha ta min magana makamancin haka akan yarinyar nan"

"komai ze tafi daidai professor in shaa Allah auren da ka Haɗa ze zama sanadiyar warwarewar duk wasu al'amuran ɓoye"

Mikewa yayi ya fita bayan ya tofe ta da wasu Adu'o'i, ko da ya dawo ya nemi Faizan ya rasa don barin garin yayi.

Satin shi uku da komawa Fatima ta sake ɓarin cikin wata guda.

Wannan karon har gida ta zo sbd yadda duk ta ɗaga mai hankali, ta kasa fahimtar komai na Allah ne.

Shi kam ya ma tafi chan wata ƙasa ne hakan yasa dole ba yadda ya iya ya barta ta koma gidan, a gidan bayan mutane shiddan nan har yanzu babu wadda ya san da maganan auren na Fauza da Faizan, a fakaice Jaddah ke mata gyara ba tare da ta sani ba, asalin gyaran shuwa Arab take mata.

Dayake yanzu ko parlorn Jaddah baba be yarda ta wuce ba necon tan ma karasa mata ake yi yasa bata fita rana, skin ɗinta ya kara wani irin kyau da sheki tayi fresh tayi kiba abunta, nasihohi take sha har ta gaji da jinsu amma tayiwa baba alkawarin bazata sake shan kayan Maye ba har abada.

Yanzu wayanta bashi da anfani don tayi ta neman Zubair bata samu se kawai ta jefa shi kasan akwati.

Ko da Fatima ta zo ma sannu be hada su ba har tayi kwana bakwai ranan ne baba ya kirata yayi mata nasihu masu yawa kan ya faɗa mata auren Faizan da Fauziyya da ya hada, ba karamin girgiza tayi da wannan zance ba, tsanar da ta yiwa Fauziyya me yawa ne matuka gashi zata aure mata masoyi ta zama suna shearing komai nashi, abunda ba zata iya amincewa dashi ba kenan.

Ta dawo wurin mamanta hankali tashe cikin matsanancin kuka, Fauza ya sa aka kira mai itama ya faɗa mata, abinka da shiririta irin na fauza dariya kawai tayi ta fito abunta bata taɓa dauka serious bane seda abu ya karato dangi suka fara zuwa nan ne musababbin tashin hankalinta ya fara...
Ko da ta nemi halaka kanta kawai kiran sakina tayi tace ga abunda zata sayo mata ba tare da ita sakinar ta san ita zata sha ba, ta sayo ta bi ribibin en buki ta bata...

DAWOWA LABARI

"FAUZIYYA!!!"
ya fadila ta faɗa tana jijjiga ta da karfi, firgigit tayi tare da ɗago kai se taga babu kowa a jirgin se su uku.

"Me haka? Me yayi zafi da zaki ɓata a tunani haka? Kin san tun yaushe muke tsaye akanki?".

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤


16

A natse suke saukowa jirgin, Ya fadila na riƙe da hannunta da kallo ɗaya ka mata zaka san cewa wannan ɗin amarya ce, don kwalliyarta na ban mamaki, ba fa na fuska ba lafayarta kaɗai ka kalla ze tabbatar mata da ita ɗin Amaryar babban gida ce.

Hannunta dake riƙe da jakanta ya bayyana lallenta me kyaun gani, chan jikin mota Faizan da Fatima ke tsaye suna jiran su har yanzu mita take mishi

"habeeby ka san halin Fauza, wlh tsoro nake ta tarwatsa mana gida muna zaman lafiyanmu, ba wai ina ja da shawaran Baba bane amma raba mana gida shi ya fi alkhairi"

Ya ɗan kalleta sbd tausayin da take bashi don ya san fitinar Fauza babu wadda ze shaƙa dayawa irin Fatima duk yadda kuwa yayi, yace mata cikin natsuwar shi
"Na sani Fatima, amma ba mun gama maganan gida ba? Baba be lamunce min raba gida ba tunda tun tasowarku a tare kuka taso da Fauza kowaccenku kuma ba baƙuwar ɗaya ba ce, na san baki da fitina kiyi hakuri ku zauna tare har ku samu fahimta"

Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗauke idanunta daga kanshi, se suka sauka kan su Fauza dake tahowa yadda take tafiya kaman ƴar sarki dole ya fusgi hankalin jama'a ga kyau tayi, abunda ta san zata nunawa Fauxa hasken fata ne kaɗai ko tsawo Fauza ta ɗara ta Dukda ta fi ta shekaru, dama kuma Hausawa sun ce tsawo rabin kyau, da sauri ta maida kallonta kan Faizan se taga su yake kallo shima.

A take ranta yayi baƙi kirin, ta tabbatar ba don Fauza bata son Faizan ba da se ta saka mata hawan jini in ta gane tana mutuwar kishin shi, hannunshi ta kama ta rike wadda ya saka shi ɗauke lumsassun idanunshi daga kan su Fauzan ya maida shi kanta.

"Tunda sun taho mu shiga motar habeeby kafafuna sun fara ciwo"

Ya juya cikin kulawa da hakkin shi yace
"so sorry, na barki a tsaye"

Motar ya buɗe mata ta shiga ya rufe, motar bayan wadda na abokin shi ne Faisal shi ya nunawa ya fadila suka shiga, shi kuma ya zagaye suka zauna da Fatima wadda hakan yayi mugun yi mata daaɗi har suka isa gida tana gayamishi abubuwan da likita yace ta dinga yi a kan ɓarin da take yawan yi.

Bayan sun sauƙa a tamfatsetsen gidan nashi dake maitama da kanshi ya musu jagora zuwa ciki Dukda ya fadila da ita aka zo jeren na Fauza, a bakin kofa Fauxa ta ja ta tsaya a hankali tayi ta karanto adu'o'in da Baba prof ya umurceta ta karanta kan ta shiga gidan, bayan ta gama tayi sallama tare da sa kafar dama se ta lumshe idanu, shikenan fa ita kuma wani sabon baabin qaddara ya buɗe mata, Allah kaɗai ya san abubuwan da zasu faru a cikin wannan gida kuma Allah shi kaɗai ya san ko gidan zaman ta ne ko ba gidan zamanta bane, ko a mafarki bata kawo auren mijin Fatima ba, ba ma wannan ba kuma wai Ya Faizan har yanzu kwakwalwanta be gama ɗauka ba bare zuciya da gangar jiki.

Tamfatsetsen parlor ne wadda ya ɗauke set ɗin kujeru har biyu, ya ƙawatu sossai masha Allah, kofofi uku ne a parlorn daga tsakiya wani hadadden staircase ne golden color wadda ya tafi a karkace har zuwa sama, dukkansu shi suka bi zuwa madaidaicin parlorn dake saman wadda na kasa ya fishi girma sede ya fi na kasa haɗuwa, dining section ɗin ma kaɗai abun kallon ne haka TV stand ɗin daga ka ganshi zaka san ba karamin kuɗi ya ci ba, console har biyu ne a parlorn ɗaya a dining section ɗaya daga tsakiyar stairs in kana haurowa, kofofi huɗu ne a saman, na farko daga dama ya fadila ta buɗe suka shige da Fauza da ya kaka.

Yayinda shi kuma ya shiga na biyun yana cewa Fatima ta duba ko me aikinta ta gama abunda su ya fadilan zasu ci, ta amsa da to tana shiga nata ɗakin wadda yake next to nashi, jakanta kawai ta ajiye ta fito, ta san shi. shi mutum ne me matukar son yaga nashi a gidan shi, yana son en uwanshi har bata san yadda aka yi ya rabu dasu yake ketare kasashe da sunan aiki ba, idan yaga nashi a gidan se abunda babu ne baya saya, ya dinga tambaya kuma ko akwai abunda kake bukata ayi maka, hakan ya sa itama dole take yi don bata son ɓata mishi Sam.

Kitchen na ƙasa ta je don ita kaɗai ke shiga na saman, ta samu me aikin nata ta gama duk wasu abunda ta faɗamata tayi a waya don haka a tare suka kwaso suka hauro sama dashi kwankwasa kofar tayi tare da buɗewa da sallama.

Su ba baƙin juna bane don haka tun tuni ma Fauza ta yaye lafayarta tana kwance a kan tamfatsetsen gadonta tana karewa tsaruwar ɗakin nata kallo, Baba prof da jadda sun yi kokari don su suka mata komai, dukda be so jadda ta sa hannu ba amma tace auren Fauxanta guda in bata fasa asusu ba na wa zata fasa kenan.

Mammi kuwa ita ta zubewa ya fadeela kuɗi akan wadda Faizan ya tura mata da umarnin Baba prof ta Haɗa mata lefe na gani na faɗa, kamshi da kyaun ɗakin kaɗai ze tabbatar maka da lallai nan ɗin na Amarya ne, akwai set

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login