Showing 3001 words to 6000 words out of 86608 words
ta kura idanu se taga kaman jini ne ke gangara daga jikin Fatimar alamu wannan cikin ma da ya kwallafawa rai ya tafi.
Baki ta taɓe tana jin burbushin farin ciki a zuciyarta, ko yaya shima ya shiga cikin baƙin ciki kaman yadda take ciki, tana shirin Juyawa ta koma taji wata daga cikin en uwansu na cewa
"khaihh na tausayawa yarinyar nan, kishiya ba karamar abu bace a wannan zamani bare ma irin kishiyar da kuka tashi tare matsayin ya da kanwa, iyayenku mata kuma suna auren miji guda"
Ɗayar wacce ƴar uwar Mahaifiyar Fatiman ce tace
"wannan kam son zuciya ne karara daga gani ai cusa mishi Amaryar aka yi don yadda take ta bore ya nuna komai, Allah sarki Fatima ciki na kusan biyar kenan shima be zauna ba sanadiyar wannan kadararren auren!"
Juyawa tayi ta koma tana mamakin kanta, for the first time kenan da aka yiwa Fauxa Abu ta ɗauke kai ta wuce, lallai abunda ya dameta ya dameta.
A kan gadon Jaddah ta sake yin masauki tare da tsunduma komar Tunaninta da ta san babu ranar gamawa, ɗagowa tayi jin alamun shigowar mutum.
"Ya Fadeelah!"
Ta kira sunan kawai kan ta maida idanunta ƙasa, babbar yayarta ce itace babba mace a ɗakin su, bata da wani shaƙuwa ko kusanci da kowa a gidan bayan Jaddah da Fa'iza wacce ta san a yanzu ko giyar wake fa'iza ta sha bazata zo kusa da ita ba.
karasowa Fadeelah tayi ta zauna gefenta tare da rike hannunta tace
"Fauxa! Kin ga yadda kika koma kuwa? Wannan anya fauxa ce kuwa? Wannan Fauzan da na sani bata taɓa zama na minti biyu shiru ba tare da ta nemi maganar wani ko faɗar wani ba? Fauxa nata ne..!"
Ɗago kai tayi tana dan ɓata fuska tace
"A'a yaya Fadeelah banda ɗan banza"
Dariya Fadeelah ta saki ita kuma fauza ta ɗan yi murmushi duk sun tuna sadda suke tare kirarinta kenan 'Fauxa kowa naki banda ɗan banza' ta kan faɗi hakan da proud musamman idan Fatima na kusa se gashi kaddarar Allah ya Haɗa su zama inuwa ɗaya a matsayin kishiyoyi.
"Bazaki tambayeni yaushe na zo ba? Ko ina yara?"
Ɗago idanu ta sake yi ta kalleta cikin gajiyawa tace
"Yaya stop been nice please ba haka muke ba"
Rike hannunta tayi tace
"I know, yanzu ina so mu fi haka.. Fauziyya ke yarinya ce har yanzu gashi Allah ya jarabceki da auren wadda kika ɗauka a matsayin Maƙiyi gabaɗaya rayuwarki ya kuma Haɗa ki da wacce tun shigowarta gidan nan matsayin agola baku taɓa kaunar juna ba a matsayin kishiya, ba Yola Zaku zauna ba bare ace akwai idanun Jaddah ko Ammi da mammi Abuja Zaku inda daga ku se ku you really need a guardian, please Fauxa ki girma and let me be a good sister I've supposed to be tun farko"
Hawaye masu zafi ne suka saukar mata tana kallon Fadeelah tace
"Ya Fadeelah kema kin yarda in hakura in zauna da Maƙiyina bayan kin san cewa duk mun tsani juna? Hakanan matarshi ko na minti biyu shiri be taɓa shiga tsakaninmu ba? Yaya Fadeelah wallahi wallahi ban taɓa aikata zina ba, meyasa kowa ze min wannan shedar alhali duk sharrin Faizan ne?"
Fadeelah ta sake rike hannunta tace
"Fauziyya kiyi Adu'a kinji? Ki sasaautawa ranki ki ɗauka cewa wannan aure shine alkhairinki kuma aljannarki karki manta abunda babba ya hango yaro fa baze hangonshi ba ko da kuwa ya hau dutse, yanzu iyayenmu duka fushi suke daku especially ma ke da kike da taurin zuciya, Fatima ta zama abar tausayi tunda tana chan kwance ta rasa cikin da ta kwallafawa rai"
Tace
"ya fadeela duk cikin munafurcinta ne, ni a duniya Ban taɓa ganin munafuki irin Fatima ba!"
Dafe kai Fadeela tayi, Fauza ta kau da kanta, Fadyaa ce ta shigo itama suka haɗu Suka yi ta nusar da ita, ɗan banzar taurin kai ne da ita kaman arnan fari, ga kafiyar tsiya da kyar suka samu tayi wanka ta ci wani abu, Fadyaa ta fice ta barsu da fadeela tana ta kokarin cigaba da bata shawarwari.
Walimar da za'a yi ranan har an yi niyyar fasawa Baba prof yace ayi tunda an yi gayyata, duk a Tunanin Faizan za'a fasa auren nan a gobe ganin abunda ya faru kuma har a yammacin da aka yi waliman Da seda mammi ta sa baki kan Amaryar ta fito Fatima na kwance a asibiti, Bayan ta farka tayi ta mishi kuka likitoci suka tabbatar mishi da jininta yayi mugun hawa duk abunda ya ɗaga mata hankali haka yayi kokarin kau dashi.
Da takardar ya dawo gida a Tunanin hakan ze zame mishi wata madafa wurin gujewa wannan kadararren aure sede hasashen shi be zama gaskiya ba, a washegarin da safe jama'a masu tarin yawa daga mabanbanta garuruwa ciki harda sarakuna da ƴan siyasa tare da manyan malaman ƙasa suka shaida auren
"FAIZAN IBRAHIM KAKA DA AMARYARSA FAUZIYYA SULAIMAN KAKA" kan sadaki dubu ɗari uku lakadan ba ajalan ba.
Sanarwan yayi daidai da tsayuwar bugun zuƙata masu yawa sede waenda suka bayyana a fili mutum uku ne, Chak numfashin Fauza ya ɗauke ta yanke jiki ta faɗi dama tun safiyar ranar kuka take, Faizan dake zaune kaman mutum mutumi yaji wani duhu ya rufeshi tsana da kyamar auren na ƙara lulluɓe shi.
Fatima da take daga cikin mota dawowar su kenan daga asibiti da mahaifiyarta ta fashe da wani matsanancin kuka me taɓa zuciya, lallai An zalunce ta kuma an ci amanar ta an nuna mata ita ɗin ba jinin GIDAN F ba ce, har Abada bazata manta wannan ba kuma tabbas an taɓa wutsiyar damisar da take bacci cikin matsanancin yunwa...
DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰
Karku sake a baku labari.
🖤Gureenjoh🖤
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya... Paid*
*Shafi Na Biyu*
*PAID BOOK*
ƊANƊANO
**Wannan shafi gabaɗayanta sadaukarwa ce gareki sister zainab Salis, hausawa suka ce yaba kyauta tukuici na ji daaɗi sossai da wannan kyauta Allah ya saka da alkhairi🥰❤️**
Ba'a samu kan Fauza ba har Seda aka nemi doctor da kyar ta farfado, in ka ganta bazaka ce Fauzan Jaddah ba ce gabaɗaya ta firgice wadda hakan ya taɓa zuciyar Jaddah da Baba prof sossai.
Ya sani auren dole a musulunce haramun ne, sede yana da tabbacin gata ya musu wadda har abada ba zasu mance ba, watarana kuma in sun tuna zasu yi alfahari dashi su mishi Adu'a idan har be riski lokacin da rai ba, sannan sunan gidanshi ya riga ya fara ɓaci ta silar Fauziyya har hawaye ya zubar saboda wani da ya tare shi ya faɗa mishi magana marar daaɗin ji akan ɗiyar ƙanin nashi, sannan ya san halin Fauziyya ba me chanzuwa da sauki bane muddin bata gamu da abunda ya girgiza mata kwakwalwa ba, ko ta shiryu samun mijin da zata samu farin ciki da kaunar en uwanshi ze yi matukar wahala hankalinsu baze taɓa kwanciya da tayi ta musu yawon makaranta alhali sun san da cewa ga hanyar da ta ɗauka ba.
Duk zaune suke a babban parlorn nashi, in ka cire yara daga kan Fa'iza dake sa'ar Fauziyya zuwa kan auta Faazila babu wadda babu a wurin kuma tsab ya ɗauke su duka har ya bar fili me yawa saboda girman parlorn na Baba prof.
Gyaran murya yayi kan ya fara nasiha me ratsa jiki akan bin umarnin iyaye da kuma kyautata musu, daga nan ya ɗaura da haƙuri da irin girmansa har a wurin Mahalicci, bayan ya gama ya kira sunan Fatima.
Ɗago rinannun idanunta da suka haɗu da fuskanta suka kumbure tayi ta kalleshi kan ta maida kanta ƙasa tana bitar karatun da ba'a jima da fara ɗaura mata ba tace
"Na'am Baba"
Yace
"ke zan fara ba haƙuri Fatima, na san mun miki ba daidai ba kina zaman zamanki mun saka mijinki aure, amma ki sani mu ɗin ma bamu isa hakan ta kasance ba idan ba da yardar Allah da sahalewarsa ba, Ke da Fauziyya ƴan uwa ne waenda kuka tashi gida ɗaya ɗaki guda kusan gabaɗaya rayuwarku tare kuka yi shi, babu halin juna da baku sani ba hakan yasa nake jan kunnen ki da ki cigaba da rike Fauziyya a matsayin ƙanwarki, kiyi haƙuri da duk wasu halayen ta kaman yadda na san ki na kuma shede ki me dumbin haƙuri da kauda kai, to ki ƙara akan hakan, Allah ya zaunar daku lafiya ya baku zuri'a dayyaba"
Kanta ƙasa hawayenta da ta kasa rikewa na ɗiga akan shinfidadden jan carpet da ya cike parlorn tass tace
"in shaa Allahu Baba, ai Fauziyya ƙanwata ce kaman yadda ba zan iya cutar da Fa'iza ba haka ba zan taɓa iya cutar da Fauziyya ba, Zaku sameni me hakuri akan hakan Allah ya bamu zaman lafiya"
Kowa a parlorn seda ya sa mata albarka, Fauziyya wani irin baƙin ciki ya zo mata wuya, a duniya in akwai abunda ta tsana ya biyo bayan munafurci wallahi ita bata taɓa yiwa Fatima kallon ba munafuka ba, komai nata na munafurci ne, sunanta da Baba prof ya kira ne ya katse mata bitar wasiƙar jaki.
Ta ɗago fuskanta da yayi mugun chanzawa ta kalleshi.
Yace
"Fauziyya ba wai Bama son ki bane muka nace da lallai se an ɗaura wannan aure, ina so ki san gata ne wadda ba kowa ke samun irin wannan ba, Fauziyya ke ce shaye shaye kece club club da hotels hotels babu wani zuri'a da zasu zauna dake ba tare da sun wulakanta ki ba..."
Katse shi tayi saboda yadda zuciyarta ke matukar ƙuna idan aka jefeta da waennan kalamai masu daci wadda ta san ba laifin kowa bane illa nata.
Hawaye na gangaro mata ta miƙe tsaye tace
"Duk nan kuna zargi na ne da zina da kuma kuma shaye shaye, lallai idan har kuna zargina ku dangi na waenda na ɗauka bani da ya su a duniya to babu wadda ze yarda dani kuma!"
Katseta babanta yayi yace
"Me yasa baki da kunya ne ni kam a rayuwarki Fauziyya? Kin zauna kin rufewa mutane baki ko se na zo nan nayi fata fata dake?"
Baba prof ne ya dakatar dashi ya san she's too young for all this duk tauna tsakuwar da suke don kawai aya taji tsoro ne.
Yace
"kina nufin ki ce duk wasu videos da hotuna naki da aka turo mana ƙarya ne? Ko kuma ganinki sau biyu da Faizan yayi a mabanbanta hotels da mutanen banza cikin shigan banza da buguwa suma ƙarya ne? Ko ganinki da idanuna da nayi shima karya na miki? Ko kuma biyo cikin layin nan da kika yi a buge shima karya ne?"
Girgiza kai tayi in confused tace
"bani da masaniya akan wasu pictures da videos, shi kuma da ya ganni duk a wuraren na yarda ni ya gani amma na rantse da wanda raina yake hannunsa ban taɓa aikata zina ba, tun da nayi wayo na san menene zina kuma na kyamaceshi wallahi ban san duk yadda abubuwan suka zama haka ba..."
"FAUZIYYA!"
Yayanta Farhan ya kirata yace cikin jin zafinta
"Ki dena rantsuwa akan ƙarya zaki cutar da kanki da kanki!"
Shesheka ta ja me karfi tana ciccilla idanunta cikin parlorn, chan cikin sif ɗin baba prof ta hangi Alqur'ani izu sittin da gudu taje ta ɗauka tare da ɗaurawa akai
a razane duk suka miƙe suna kallonta har Faizan da duk jijiyoyin jikinshi suka miƙe saboda wani irin tafasa da zuciyarshi ke yi, ji yake kaman in ya kamata da musu da rantsuwar nan ze iya kashe ta.
"Na rantse da wanda ya saukar da wannan littafi ban taɓa aikata zina ba kuma ban taɓa ɗaga abun maye da hannuna cikin hayyacina na sha ba, ban san meke faruwa dani ba amma wallahi ko a mafarki ban taɓa aikata zina...."
Kwace Alqur'anin da aka yi a hannunta ya sakata saurin ɗagowa se suka Haɗa idanu, yana shirin sauke mata zazzafar mari mahaifiyarshi tayi Charab ta riƙe hannunshi a kausashe tace
"A kul Faizan! ban yarda ba ban amince ba, ko a bayan idanunmu ka daga hannu da sunan dukan Fauziyya ban yafe maka ba duniya da lahira!"
A razane yake kallon mahaifiyar tashi kan yayi wani magana mahaifinta ya bata mari daya, Farhan ya ƙara mata har Seda bakinta ya fashe.
Da sauri Amminta ta miƙe ta nufi kofa tana kuka, Baba prof ne ya dakatar da ita
"Ruƙayya!"
Tsayawa tayi tana jin yadda kukan ɗiyarta ke ratsa parlorn.
"Dawo ki zauna"
Mikewa ya yi da kanshi ya nufi Fauziyya ya riƙe hannunta suka dawo dab dashi a ƙasa ta zauna kanta ƙasa tana cigaba da kuka.
Kallon su yayi ɗaya bayan ɗaya kan ya sauke ajiyar zuciya yace
"Farhan ban yarda ba ko da bakin wasa ka sake ɗaga hannunka akan Fauziyya, bana so ka sake mata kallo a matsayin ƙanwarka ita ɗin matar yayanka ce a halin yanzu"
Hannunshi na kan ta yana shafawa ya ɗaga ya kalli Faizan da da kallo guda zaka san ranshi be taɓa sosuwa irin na ranar ba, ko ɗagowa baya yi yadda mamminshi ke fifita wannan yarinyar fiye da farin cikinshi hakan na matukar ƙona ranshi, idan ya kalli matarshi da halin da ta shiga duk saboda ita se yaji ina ma ze iya kawar da ita a duniya ko ze huta.
Ɗauke kai baba prof yayi shima kwarai ya san an shiga hakkin shi sede ya za'ayi shine babba dole shine Juji.
"Fauziyya ki sani yanzu bakin alƙalami ya riga ya bushe, duk wannan bashi da anfani sannan Qur'ani ya wuce wasa babban hatsari ne amfani dashi wurin rantsuwa se idan har babu yadda za'a yi ne.... Ki yi haƙuri ki rungumi sabuwar rayuwar ki"
Kai ta gyaɗa tace
"shi ke nan Baba"
Shafa kanta yayi yace
"Allah ya miki albarka"
Babanta yace
"Ni kam ba zan ce kiyi hakuri ba, in kin ga dama kar kiyi abunda nake so ki sani shine daga ranar da kika kashe aurenki karki neme hanyar gidan nan, kije chan wurin abokanan watsewarki ku cigaba na yafe ki har Abada, in har kina son Adu'a da farin cikina gareki shi ne ki zauna da Faizan ba tare da wani matasala ba, ko a labari na ji ranar da kika saɓawa umarninshi Fauziyya ban yafe ba, tun rayuwarki baki taɓa saka ni farin ciki ba kullum da fargabar abunda ze fito daga gareki nake kwana nake tashi, sau ɗaya dae zaki yi kokarin proving Cewar ke ɗin ɗiyata ce har ki min biyayya!"
Ammi ta ɗago tana Kallonshi
"me yasa ne Sulaiman? Me yasa kullum ka buɗi baki alkhairi baya fita in har dae akan Fauziyya ne? Duk wannan hali da ta shiga da wadda take ciki baka taɓa tausayinta ba! Ni kam wlh ban yarda a zalunce ta ta ja baki tayi shiru ba!"
Kallonta kawai jadda ke yi, wani lokacin hankalin Ruƙayya na bata mamaki ganin idanunta tana ga yadda Aisha da Prof ke ture yaronsu ba wai don basa sonshi ba se don ganin sun samawa Fauziyyan ƙima da daraja a idanun Faizan ɗin sun kuma hana shi cutar da ita saboda rashin ƙaunarta da baya yi tun tale tale, amma ji inda ta dosa ita, babu wadda ya fi dacewa yayi magana a nan na rashin adalci irin Fatima da mahaifiyarta amma they sat patiently suna sauraron baba prof ɗin.
"Ruƙayya...."
Ɗaga mishi hannu baba prof yayi, kan ya dubi Faizan
"Faizan ga amanata na baka, ka san girman amana ka kuma san hukuncin duk wadda ya ci amana, in ka cutar da ita ina rokon Allah ya saka mata, Allah yayi muku albarka ya baku zaman lafiya, an riga an yi mata jerenta so mutum biyu ne kawai zasu raka ta su dawo"
Mammi tace
"Toh ka ji, nima Amana na baka Fauziyya in ka ci ma kanka! Ka riga kayi karatu babu abunda baka sani ba, ina fata zaka wanzar da adalci a tsakaninsu su biyun"
Jadda da hawaye suka zubo mata da kewar fauzin nata tace
"Fauziyya kiyi haƙuri! Kiyi hakuri!! Ki ƙara haƙuri!!! Ina tabbatar miki zaki ci ribar wannan haƙuri.. Faizan ga ƙanwarka nima na damka maka amanarta, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyaba, Fatima kiyi hakuri kin ji? Haka Allah ya tsara"
Kuka sossai duk su biyun suke kowa da abunda yake saƙawa cikin zuciyarsa, Fauziyya ta ƙudiri aniyar zama ɗiya ta gari for the first time ko don saboda Mammi da Baba prof, ko don babanta yayi alfahari da ita sau ɗaya dae a rayuwarta, bata taɓa saka shi farin ciki ba kap rayuwarta se bakin ciki har hawan jini yake dashi sanadiyarta, zata yi hakuri har taga yadda Allah ze yi da ita a wannan gida da yafi kabari ko wuta a gareta....
Kowa yana ta kara yi mata nasiha har suka fito a yammacin zasu tafi Abuja inda nan ne gidanshi kuma anan suke zama da Fatima, bata taɓa Tunanin zata yi wani kukan rabuwa da gidan da tafi tsana ba se yanzu da take ji yafi mata sau dubu akan inda za'a kaita a kuma barta chan bata san kowa ba se maƙiyanta, kuka sossai take yi da kyar aka cire ta ɗaga jikin jadda se ta koma na Amminta, daga nan tayi kan mammi ta sha kuka kam, daga karshe ma fa'iza da kullum se sun yi faɗa ta rungume tana kuka sossai, Fatima tuni tana mota.
Cikin sassarfa ya fito daga sashensu ba tare da ya kalli ko sashen inda suke ba ya nufi mota sanye da wasu ɗanyen boyel me taushi da tsada farare sol, hulanshi light ash da fari tangaran ya zauna mishi sossai haka takalmin shi half cover ce me ainihin kyau da tsada ta bayyana Fararen digadiginshi da kaman baya taka kasa.
Baba prof da ya bishi da kallo yana murmushin yadda duk yayi kicin