Showing 63001 words to 66000 words out of 86608 words
shiga ɗakinshi da kyar ta iya barin wa gobe ta ga abunda hali ze yi, wlh Allah ya gani ba da wani niyya mummuna ta kira sakina ba kuma ita yanzu Zubair baya cikin rayuwar ta don har ta mance dashi ma.
Haka dae tayi wanka ta zo ta kwanta ko abinci bata nema ba zuciyar ta fal tunani, washegari da safe bayan ta idar da sallah tana zaune tana azkar taji alamun tashin mota, da sauri ta miƙe taje jikin window se ta hangi motar shi na fita, ajiyar zuciya ta sauke ta dawo ta zauna da gaske fushi yayi? Ta tambayi kanta don ba zata Iya tuna sadda ya fita be gayamata ba tunda suka ɗan fara shiri.
Gari yayi haske taje tayi wanka ta zo ta shirya cikin jalbab ɗinta dogo har ƙasa don tana da lectures, fitowa tayi bayan ta sha cereal ta zuba chocolates masu yawa a jakan bayanta, Fatima ta gani zaune tana karyawa.
Kaman ba zata mata magana ba se kuma tace
"mun tashi lafiya?"
Ko kallonta Fatima bata yi ba, zama tayi tana jiran ta ko don ta san tana jiran ta ne ita kuwa ta fara jan lokaci, ganin zata ɓata mata lokaci har a shiga lectures yasa ta miƙe ta fice.
Mai gadi ya gaida ta yana buɗe mata gate ta taka da kafa har ta samu taxi ta ɗauki shata ta wuce school.
Se karfe huɗu ta dawo gidan nan ma da taxi don bata ga Fatima ba, Seda tayi sallah ta zo ta shiga kitchen ta fara girki sanin itace yau da girkin, tuwo tayi mishi na doya da miyar ɗanyen kifi bayan ta gama taje tayi wanka tare da sallar magrib ta shirya cikin kananun kaya, ba karamin kyau tayi ba tayi isha kan ta fito ta zauna a parlorn saman Dukda bata ji motsin shi ba.
Se a lokacin Fatima ta shigo basu tankawa juna ba, ita dae Fatima ganinta yasa ta san bata san mijin da ake yiwa kwainanen baya ma ƙasar ba, dariya ta sheke dashi tana cewa
"lallai kuwa za'a yi jiran gawon shanu"
Tana kai nan tayi wucewarta ciki, ganin har karfe tara be shigo ba yasa tayi Tunanin ko baya ƙasar, ranta dae ba daaɗi kaman yadda tun safe yake har Afnan take tambayarta tace babu komai, yau gabaɗaya abu mai nauyi be shiga cikinta ba, tuwon ta dibi ɗan kaɗan ta ci kan ta tattara taje ta adana a frigde daga nan ta haura tayi shirin kwanciya ta kwanta.
Washegari bata yi breakfast ba miyan kifin ta yi microwaving ta ci da bread, yau ma bata jira Fatima ba tayi ficewarta yau ma dae haka ta kashe ranar da tunani, lectures ɗin ma bata wani fahimta..
A kwana na ukun har kuka tayi, ta rasa gabaɗaya me ke damunta da fushin shi, da a gidansu ne da yanzu in duka ne an daketa an wuce wurin amma shi ba duka ba zagi kawai ya ɓace mata ba tare da ta san inda yayi ba alhali yana fushi da ita.
Hadari ne sossai ya haɗe garin har ana iska, Afnan ta riga ta wuce ita kuma tana tsaye tana neman taxi da sauri ta sanya hannu ganin motar Fatima amma ko bata tsaya ba tayi wucewarta kuma ta tabbatar ta ganta ba bata ganta ba, da kyar ta samu wani taxi Dukda ya tsula mata kuɗi bata damu ba ta shige da sauri sbd ita bata son ruwa ya taɓa ta, ko yaya ya jiƙata se tayi mugun zazzaɓi.
***
Karfe shidda ya iso gidan yayi parking motan shi da dama Airport ya kan bari yayi tafiyar shi, Gaisawa suka yi da gate man kan ya wuce ciki yana kallon motar Fatima dake nuna alamun bata jima da shigowa ba.
Gidan ya shiga yana jin wani kewa chan ƙasan ranshi da duk yadda yayi kokarin dannewa ya ƙi dannuwa, lumshe idanu yayi ya buɗe a sadda ya shaki sassanyar turaren wutan da ta kan yi anfani dashi wa gidan, a natse ya haura yana jin yadda aka tsuge da ruwan kaman da bakin ƙwarya.
Ɗakin Fatima ya fara shiga tana ganinshi cikin farin ciki ta tare shi tana mishi sannu da dawowa, ya amsa fuskanshi a sake kan yace bari ya duba Fauza se yaje yayi wanka.
Tace
"Ai ina ga bata dawo ba fa..."
"Bata dawo ba?" Ya watsa mata tambayar cikin mamaki.
Kanta ta mayar ƙasa tace
"eh bata dawo ba don ban ji shigowarta ba"
Yace
"ban gane ba, ina ce tare kuke tafiya ku dawo? Ya aka yi ke kike gida ita bata nan? Me ze ajiye ta a waje har an yi magrib?"
Tace
"ni dae wlh ban sani ba, abunda na sani dae tunda ka tafi bata sake tsayawa mun tafi tare ba taxi take fita ta hau haka dashi take dawowa Dukda nayi kokarin jan hankalinta akan baka son ɗabi'ar shine ma musababbin da yasa ka saya min mota amma taki saurare"
Be tanka ba sbd yadda ya sake jin sabon ɓacin rai na rufe shi a kanta, duk yadda yake kokari akan yarinyar nan me yasa take so ta fara bashi matsala? Sau nawa ya gayamata baya so matarshi ta hau taxi? Ɗakinta ya wuce kamshin ta na tashi a ɗakin wadda ya dawo mishi da sabon kewanta kaman yadda ya kashe kwanaki biyun cikin kewar nata ko abincin kirki bai iya ci.
A balcony ɗinta ya tsaya dake shine ke facing gate, ya rasa hukuncin da ya kamata ya ɗauka a kanta, sheɗan ke ta wassafa mishi kila tana chan da Zubair tunda har ta fara ambatarshi, hangar taxi yayi ya sauke ta, ba lema hannunta hakan yasa cikin hanzari ta iso gate ɗin ta fara bugawa saide gate man ɗin kaman baya kusa don baya jinta, ta kai mintuna biyu tsaye cikin ruwan tana knocking da ƙarfi sede ƙaran ruwa ya hana gate man ɗin ji, ya so ya kyale ta ruwan yayi ta jiƙata se kuma ya ga baze iya ba.
Da sauri ya juya ya nufi fita ganin ta juya itama ta bar gate ɗin da sauri sauri, da hanzari ya buɗe gate ɗin ya fara duba ta, chan ya hangota tana tafiya tana dube dube ko zata samu inda zata fake kan ruwan ya tsagaita..
Sam bata san da isowar mutum ba se ji tayi an ɗaura mata wani suede me kauri wadda a take ta dena jin Sauƙar ruwan jikinta, a hankali ta ɗaga kai se suka Haɗa idanu ruwan na zuba a jikinshi sossai.
"Yaa..."
Be bata daman magana ba ya riƙo hannunta suka juya suka yi gida, a kofan ɗakinta ya saketa ba tare da ya bi ta kan suede ɗinshi ba ya shige dakinshi.
Ta ɗan jima tsaye a wurin kan ta shige ta cire suede din ta ajiye ta wuce toilet ta cire kayanta da ya jike gabaɗaya ta hada ruwa me zafi sossai tayi wanka, a ɗakin ta Haɗa tea me kauri da zafi ta sha jin jikinta ya fara rawa alamar zazzaɓi.
Da kyar ta iya gabatar da sallah kan ta hau gado ta ja bargo ta shige tana rawar dari.
Yayi wanka shima ya sauya kaya ya fito ya duba Fatima yace ta sama mai wani abu marar nauyi don yana jin yunwa, ranta fal farin ciki sanin yayi fushi da fauza ne tunda girkin ta ne amma ya saka ita tayi mishi.
Kitchen ta shiga ta sama mai abinci yana zaune a parlor yana kallon Tvc news ta shigo ta ajiye mai, kallon kofan Fauza yayi kan ya maida kan abincinshi ya fara ci yana Tunanin me ya hanata fitowa ta nemi wani abu ta ci?
Har ya gama ci suna tare da Fatima, tana ta kokarin jan hankalinshi sede idanunshi ne kawai gareta, tana tattare kwanukan ya miƙe ya nufi ɗakin Fauza ɗin.
Kwance ya tarar da ita tana rawar ɗari sossai, yaye bargo yayi ya taɓa gefen wuyanta wani irin zafi jikinta yayi da har yayi saurin zare hannunshi, da kyar ta buɗe idanu ta kalleshi..
Harara ya zabga mata, kan yayi tsaki ya wuce toilet ɗinta towel ya samo da ruwa ya zo ya karasa yaye bargon yana ɗauke idanunshi daga kan santala santalan cinyoyinta da suka bayyana, ɗagota yayi ya fara saka Towel nan a ruwa yana shafa mata, wani irin numfashi take saukewa wadda ke rikirkitashi ganin ruwan baze Sauƙar mata da zazzaɓin ba gashi ta fara mishi kananun kukan fita hayyaci ya sa ya rufe ta da faɗa don abubuwa dayawa ne suka haɗu mai.
Sossai yake mata faɗan abubuwan da ta aika ta ɗin, harda taurin kanta take shirin dawo mai dashi to baze ɗauka ba, shi ba lusarin namiji bane da ze ke gindaya mata sharudda tana tsallakewa he could remember vividly yadda ya gayamata baya so matarshi ta hau taxi amma me ta aikata? Har tana tuna wani katon gardi ɗan shaye shaye cikin gidanshi.
A hankali ta sabule daga hannunshi da yake rike da kafadunta ta faɗa jikinshi tare da kankameshi tana kuka kawai don bazata iya magana ba.
Tsit haka maganan ya yanke mai, ya sanya hannu ya tarbeta, fuskanta take ta gogawa bisa kirjinshi alamar tana kara fita hayyacinta ne, da sauri ya kwantar da ita ya kashe wutan ɗakin tare da zare jallabiyar jikinshi, ya saura daga shi se boxer, Rigan jikinta ya cire mata don bata taimakon body contact kan da safe su tafi asibiti.
In a romantic way ya sanya lallausar hannunshi ya ɗagota a hankali ya kwanta kan yayi mata masauki a faffaɗar kirjinshi, a tare suka sauke nannauyar ajiyar zuciya, mannewa ta sake yi ta shige jikinshi kaman zata tsaga shi ta shiga ciki sbd sanyi da taji jikin nashi na dashi wadda hakan ya bashi daman sake kanainayeta ya cusa fuskanci tsakanin wuyanta yana sauke numfashi me nauyi, cikin wani irin salo yake shafa mata sajen nashi a hankali hankali cikin wuyanta, siririn ƙara ta sake tana kara kankameshi jin ya saka babban ɗan yatsan kafan shi yana wasa da tafin kafafunta, duk su biyun sun haukace da wannan masifaffen body contact da suke samu, shi da yayi da niyar taimako ma ya fi azabtuwa.
Hmmm wani irin moment ne suka yi spending wadda baze Mantu ba, gabaɗaya seda ta gigitashi da albarkatun jikinta wadda duk ba cikin hayyacinta take hakan ba, ba jikinsu kaɗai ba a lokacin ze iya rantsuwa cewa numfashi ma guda ɗaya suke yi ba biyu ba, Seda suka shafe mintuna sama da talatin suna rabawa juna temperature ɗinsu kan ya mirginata, hancinshi yake gogawa da nata yana jin yadda su biyun duka numfashi ta hanci yayi musu kaɗan suna Haɗawa da baki, a hankali ya fara brushing lip ɗinshi kan nata, yana kokarin haɗe lip ɗinsu tayi wani miƙa da ya tabbatar da zazzaɓin ya sauka, yaraf ta dawo kan pillow a take wani wahalallen bacci ya sure ta, zamewa yayi ya kwanta daga gefenta yana jin yadda zazzaɓin tan ke shirin dawowa jikinshi.
Bacci me nauyi ne ya kwasheta yayinda shi kuwa yace be san zance ba, janyo ta ya sake yi jikinshi ya rufa musu bargo sbd jikinshi wani irin rawa yake yi... Ya fi awa kwance cikin wannan yanayi Ganin in yana cigaba da barin ta haka a jikinshi komai ze iya faruwa ya sa ya miƙe dafe da marar shi ya fice a ɗakin.
Kitchen ya shiga ya matsa lemon tsami a lipton ya kwankwade tunda yau ba kwanan Fatima bane bare ya rage wani abun, tunda yake be taɓa jin irin wannan sha'awa ba se yau, ɗakinshi ya shige ya zube rub da ciki bisa gadon shi yana juye juye.
Ita kuwa bacci tayi sossai, chan wuraren karfe uku na dare taji kaman ana kiran sunanta, cikin gigin bacci ta buɗe idanunta se taga ɗakin gabaɗaya ya sauya mata ya koma wani irin Ƙango me cike da abubuwan razanarwa, a firgice ta miƙe sede bata iya ambaton komai ba kaman ɗaure mata baki aka yi ko numfashi da kyar take iya ja amma bakinta ya ƙi furta komai.
Wasu irin abubuwa taga suna motsi daga jikin ginin ɗakin, sanyi taji me yawa a jikinta waigawar da zata yi taga wani irin hallita da bata taɓa sanin akwai irin shi ba baƙi sidik, me munin gani da razanarwa, ƙara ta saki wadda taji muryar yayi amsa kuwwa iya ɗakin, da sauri ta sauƙa jikinta na rawa ta nemi riga ta saka ta suri hijab ɗin sallarta ta saka, jakan da ta dawo dashi jiya ta zara ta fice da sauri daga ɗakin.
Parlorn kasa taje chan lungun dining ta makale ta takure Kaman wacce ta rasa gata, jikinta wani irin karkarwa yake gabaɗaya bazata ce ta san me take yi ba, banda tsanar gidan da tsananin tsoronshi babu abunda take ji.
Tana nan har aka kira sallar asuba fuskanta har ya kumbura da kuka, kaman wuta ake rura mata a gidan haka take ji, tana ji ya sauko da nufin tafiya masallaci, da sauri ta miƙe ta bi bayanshi yana fita itama ta fice daga gidan ko waiwaye babu....
**Ayi comment in takarkare in baku na dare😎**
DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰
Karku sake a baku labari.
🖤Gureenjoh🖤
DƘ
28
Saboda rashin baccin da be samu ba jiya ya sa ko azkar da kyar ya iya yi ya mike ya dawo gidan, ɗakinshi yayi direct ya kwanta ba shi ya tashi ba se wuraren karfe goma sha ɗaya, wasai haka ya ji shi Adu'a yayi kan ya sauƙa ya wuce toilet ya watsa ruwa har a lokacin ze iya cewa yana jin tsadaddiyar jikinta cikin nashi, yana jin duk wani moment da suka yi spending a jiyan cikin ƙashi da ɓargonshi.
Haka ya gama wankan ya fito ya shirya cikin kananun kaya, fitowa yayi yana baza kamshinshi me natsuwa da kwantar da hankali, ɗakin Fatima ya fara dubawa bata nan da alama ta tafi school, ɗakin Fauza ya nufa haka kawai ya tsinci kanshi da sakin murmushi.
A hankali ya tura kofan saide turus ya tsaya ganin kaman an yi wasan kura a ɗakin, komai kaca kaca a wargaje abinda ba ɗabi'arta ba.
Sunanta ya fara kira yana shiga ciki ciki sede bata kan gadon, bayin tura ya shiga nan ma bata nan.
Saukowa yayi kasa ya je wurin Peter yake tambayar shi ya ga fitan Fauza ko tare suka fita da Fatima?
Yace a'a Fatima ita kaɗai ta fita kuma shi yana kofan tun asuba be ga fitan ta ba, hankalinshi ya fara tashi da sauri ya koma saman ya fara kwala kiran sunanta saide babu ita ba alamar ta.
Fitowa yayi ya shiga mota ya ja da matsiyacin gudu se makarantar su, Afnan yake ta nema ko ze gansu tare sede be ganta ba, wurin Faisal yaje yace ya kira mishi Afnan ko suna tare da fauza? Kiranta yayi tace tun jiya da suka rabu basu haɗu ba, yau basu da lecture ma da safen.
Tun Faizan na ɗauka wasa sede hankalinshi yayi matukar tashi ganin da gaske bata nan ɗin, Faisal ne ya tuka shi suka je police station suka yi reporting, polisawan sun tabbatar saide in da kafafunta ta fice da sakacin me gadi in ba haka ba da shiga aka yi aka ɗauke ta se an gane bare da yace har tsakiyar dare ma suna tare.
"Iyayen ku na nan garin ne?"
Dpo ɗin ya tambaya.
Faisal ne ya amsa da
"A'a suna Adamawa"
"to ko gida dae ta tafi?"
Dpo ya faɗa.
Faizan da ranshi ya soma ɓaci yace a tsawace
"Me aka mata ɗin da zata tafi gida ba tare da sanina ba? Ni fa mijinta ne!!!"
Ya faɗa cikin hargowa, Kafadanshi Faisal ya dafa yace
"Calm down please Faizan ka natsu, ban san ka da hayaniya haka ba.."
Yace
"Kar in yi hayaniya Faisal? Matata fa na nema na rasa na kawo musu report kuma me makon su yi aikinsu sun tsaya suna faɗan wasu abubuwan da baze yiwu ba, ana tafiya gida haka kawai ne a aure?"
Dpo ɗin yace
"I'm so sorry, ka natsu please ka san komai na iya faruwa ne shiyasa muke maka waennan tambayoyi kila ka mata wani abin ɓacin rai da ze sa ta bar gidan ta tafi gida ba tare da saninka ba, amma tunda kace ba hakan bane yanzu zamu fita mu fara bincike ka kwantar da hankalinka komai ze tafi daidai"
Fitowa suka yi sbd azahar da ake ta kira suka tsaya suka yi sallah, Faisal ya dube shi yadda gabaɗaya kamananninshi ya sauya jijiyoyinshi suka tashi suka yi raɗa raɗa yace
"Faizan ko zamu kira su baba?"
Kai ya girgiza yace
"Ko gidan ta tafi in dae a mota ne zuwa yanzu be ci a ce ta isa ba... Amma me na mata da zata tafi gida?"
Ya faɗa cikin sanyin murya.
Dafa kafadanshi Faisal yayi ya bubbuga alamun rarrashi kan suka miƙe suka fito se ga Jafar shima suka haɗu suka fara yawon nemanta da polisawa, a Airport babu jirgin yola da ya tashi a ranar ma gabaɗaya ya gayamusu amma basu yarda ba seda suka je suka gama binciken su kan suka nufi tasha...
***
Ita kuwa Fauza bazata ce ga takamammen Tunanin da take yi ba, Sam kaman makuwa tayi ne ko yaya haka dae ta miƙi hanya ta tafi sossai Dukda wani irin sanyi da ake zabgawa na asuba, bakin wani masallaci ta zauna ana sallar asuba limamin na karatu cikin Suratul baqara ayoyin ƙarshe, a hankali take jin natsuwa na zuwa mata, itama ta karɓa taci gaba da binshi har ya kai karshe yayi ruku'u.
Da sauri ta miƙe ta shiga ciki ta samu ruwa tayi alwala kan ta gabatar da sallar itama nan fa ta ji bakinta ya iya fara ambaton Allah amma zuciyarta har lokacin baƙi kirin babu abunda ta tsana irin Abuja da gidan Faizan.
Fita tayi daga masallacin ta tafi ta tari taxi yana tsayuwa tace
"Park zaka kaini"
Yace ta shiga, tashar Jabi ya kaita.
Ta biya shi sbd akwai kuɗi a jakan, taje ta shiga mota nan da nan motar yola ya cika suka ɗauki