Showing 72001 words to 75000 words out of 86608 words

Chapter 25 - DIDDIGAR ƘAYA COMPLT Hausa novel

21 Aug 2024

18442

sbd tausayin halin da take ciki wadda ba zan iya nunawa ba, Fauziyya..."

Ammin ta kira sunanta, ɗagowa tayi har bata iya kallonta da kyau sbd kuka ta amsa..
"Ki yafe mana iyayen ki Fauziyya don Allah ki yafe mana mun kasa baki kariya kaman na kowa su iyaye, tun kan ki zo duniya muka yi saken da aka cutar dake barin ma ni mahaifiyarki, ki yafemin don Allah"

Kai take gyaɗawa tana kuka, Baba Alhj ma dake kuka sossai yace
"Fauziyya nima ki yafe min irin kalamai da tsana da na ɗaura miki, ki yafe mana don Allah kwarai bamu kasance iyaye na kwarai a gareki ba.."

Girgiza kai tayi cikin muryarta da baya fita tace
"Na yafe muku wallahi Ammi, ban taɓa rikeku ba, ko na riƙe ɗin Jaddah da ta zame min uwa kuma uba ta kan nusar dani har in yafe muku, tabbas ban samu gatan iyaye ba saide na samu gatar kakata wadda har Abada bazata taɓa fita cikin mutanen da suka fi kowanne daraja a rayuwata ba... Mammi kiyi hakuri da irin amsar da na bayar"

Mammi tace
"Fauza nima na ji ne kawai Amma ban amince ba, ko kin manta a duk sadda kika taimakamin na kan yi bacci cikin kwanciyar hankali? Wannan kaɗai ya isa shaidar cewa ba don cutar dani kike yi ba"

Su ya Farhan ma yafiyar ta suka nema duk ta amsa da ta yafe musu, se a lokacin Faizan ya iya ɗaga kai ya kalleta zuciyarshi kaman ze fashe da tausayi da kuma ƙaunar ta, lallai ta ga rayuwa kuma daga yanzu yayi alkawari wa kanshi cewa har Abada baze taɓa judging mutum by cover ba, Fauza yarinya ce amma kafin Allah, ba don Allah na tare da ita ba da yanzu babu ita.

Hannu ta mika ta rike na fa'iza dake wani irin kuka ta kasa kallon ko mamanta da Fatima da suma suke kukan tace
"Ni kam ba zan iya neman yafiyar ki ba twin sister, na san bazaki taɓa yafe mini ba, ina ma ina ma... Ina ma zan iya chanza Aunty daga mahaifiyata in dauki mammi ko Ammi, ina ma bawa na da damar ɗauke ranshi da kanshi... Aunty kin cuceni, kin cuci kannena, kin cuci mahaifina, kin yi min illar da Har Abada baze taɓa mantuwa a raina ba... Wallahi na tsaneki, na tsani ganin mummunar fuskarki, meyasa kika haife ni meyasa aaa"

Ta karashe tare da kurma ihu faɗuwa tayi, numfashinta na barazanar ɗaukewa, Faraj ne yayi hanzarin ɗaukar ta, Farhan ya rufa mishi baya suka yi asibiti don zata iya mutuwa a yadda taken nan. Allah sarki shiyasa wani lokaci in zaka yi abu kake duba bayanka, me zaka barwa ƴaƴan ka?

Fatima ce ta rarrafo tana kuka har da majina ta riƙe kafafun Faizan..
"Wallahi wallahi abubuwa dayawa ban sani ba se yanzu, na rantse da Allah ban taɓa bin ta ko rakata wurin wani mushiriki ba, wallahi soyayyar da nake maka daga cikin zuciyata take don Allah karka barni, wallahi kana Rabuwa dani babu abunda ze hana ni mutuwa ka taimakeni karka bari na mutu Ya faizannn Don Allah.."
Yadda take kuka seda kowa yaji a ranshi kwarai ita kam ta so Faizan..

Shi kuwa idanunshi da suka rine gabaɗaya suka sauya ya ɗaga ya zubawa Fauza ko kallon wurinsu bata yi ba, tana dae kwance a kan kafadan Jaddah hannunta na riƙe da nata har lokacin kuma hawaye kan zuba a idanunta ta sa hannu ta goge....

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤



31

Tsatsareta yayi da idanunsan nan masu kaifi yana so yaga yanayinta da maganan Fatiman saide ko inda suke bata kalla ba bare ta bashi damar karantar ta, maida idanun yayi kan Fatima yana me kallonta cikin kyamata da tsana yace
"kiyi haƙuri ba zan iya cigaba da zama dake ba, I never loved you. Sannan ko ba don haka ba, ba zan taɓa Haɗa wata macen da Fauza ba she had enough in her life so maganar baƙar kishiya babu shi har Abada, na sawwake miki igiyoyi biyu bisa uku dake kanki"

Ihun kuka take kurmawa tana rokon su baba da su sa baki, babu wadda ya motsa sbd babu wadda ya taɓa kawo Fatima zata iya aikatawa Fauza abunda ta aikata, zama da munafuki me fuska biyu ba karamin hatsari bane don babu abunda bazata iya aikatawa ba.

"Shamsiyya na sake ki saki biyu, ki je ke da Allah zaki girbi duk wani abunda kika shuka, sannan na baki nan da awanni 24 ki gama duk wata ganawar da zaki yi da yaranki ki tattare duk abunda kike buƙata ki bar min gida har abada kuma bana so in sake ganin kafafunki cikinshi"
Ita kam bata yi kuka ba, se wani murmushi da take yi, lallai duk wani ƙarya tata ta ƙare saide bata karaya ba, a ganinta don ka yi farautar Burin rayuwarka ba wani abu bane, mikewa kawai tayi da nufin ɗaga kafa tayi tafiya se kafa yace be san zance ba, ihu ta kurma jin wani azababben ciwon ya tsarga mata a gabaɗaya kafofin nata, "Kaikayi koma kan mashekiya" ta furta tana kallon Mammi da wani irin hanzari.

Se yanzu ta tuna boka ya ce mata duk ranar da aka san itace da hannu kan ciwon na mammi tsab ze dawo mata, se lokacin ta fara kuka jin yadda kasusuwanta ke tauna, haka wai dama Aishar ke ji? Ta tambayi kanta tana kara kure mammi da itama take kallonta da mixed emotions da kallo.

Fatima take kira ta taimaka mata su fice, Fatima na kuka kaman ranta ze fita ta kamata suka fita ba wai don wani abu ba se dae tana Tunanin kila mahaifiyartata ta sama musu mafita don ta saba sama mata mafita, ita wlh bazata taɓa iya hakura da Faizan ba.

Yunkurawa Fauza tayi da niyar miƙewa sbd Baba prof ya sallamesu bayan nasiha da yayi musu me ratsa jiki, duk sauran matan jikinsu yayi matukar sanyi, ganin kowa na shirin fita ne yasa itama ta yunkura saide bata kai ga miƙewa ba ta koma ta zauna tana runtse idanunta da suka kankance don azabar zafin da ya ratsa ta.

Tsab yana hankalce da ita, wani irin tausayinta ne ya tsirga mishi, abunda ta guda kenan amma ta lura kusan kowa ya harbo jirgin duk kunyar Faizan be ji ko dar ba se ma murmushi da ya ɗan saki yana jin daaɗin yadda kowa ya kamata ya san Fauza ɗin ba ƴar iska bace kaman yadda aka mata tambari.

Ammi bata kula ta ba sbd ta san zata samu duk kular da ya dace a wurin Jaddah ko mammi, yayinda ita kuwa ta ma kasa hada idanunta da mammin kwata kwata.

Ji yake kaman yaje ya ɗauke ta chadak ya kaita har sashen na Jaddah, ya san tana wahalar tafiyan ba laifi ta wahala sossai, hannunshi ya cusa cikin kwwantanccen gashin kashi ya shafa yana sakin murmushi sanin se sun kwashi daru da ita alamar ta ya nuna ba karamin fushi take dashi ba.

Ruwan zafi sossai da wasu magunguna Jaddah ta Haɗa mata akan ta shiga ta zauna, idan ya huce ta sake saka wani tayi kaman sau uku kan tayi wanka ta fito, duk yadda ta so shigar kasawa tayi tana kuka tana yarfa hannu, Seda Jaddah ta tsaya a kanta sossai kan ta iya shiga duk yadda Jaddah ta so ta dubata ko taji ciwo kiyawa tayi, haka aka yi wankan amma ta sha wahala kuma ita kam bata ji sauƙi ba, banda Allah ya saka mata babu abunda take kira.

Bayan tayi wankan ta sha magani tare da rama sallolin da ake binta ta kwanta saide fa zazzaɓi me zafi ya rufeta har tana fita hayyacinta ba arziki Jaddah ta kira Faizan da shima ya sake wanka kenan bini bini se ya saki murmushi ya ɗan cije leɓe, ganin kiran Jaddah yasa da hanzari ya zura jallabiya me taushi Ash ya fice.

A hannu ya ɗauko ta Jaddah na gaba ta buɗe mishi motar ya sanyata tana ta mishi faɗa, shi dae be ce komai ba ya zagaye ya shiga ya ja da gudu se asibiti, likita namiji suka samu kai tsaye yace a nemo mace don matsalar ba na namiji bane kuma baze iya hakura wani ya duba mishi mata ba.

Haka ko aka nemo Dr mace, ko da ta duba ta taji ciwo kuma wurin yayi tsami dole tana bukatar ɗinki, haka ko aka yi tana kuka don ta sha baƙar wahala, bayan an gama aka sake mata allurai sbd zazzaɓin tuni wahalallen bacci ya ɗauke ta.

Zuwa suka yi suka duba Fa'iza da har lokacin itama bata farfado ba, dama Jaddah ta tura musu zaliha ta taya su kwana, se kuma ga Fauza ma.

Jaddah ce ta kwana da fauzar yayinda mazan suka wuce gida.

Da misalin karfe goma na safiyar washegari ya fito a shirye tsab cikin wata farar ƴar uban sun yadi da aka yiwa ɗinkin zamani kwata kwata da kaɗan ya sauka cinyar shi, fuskanshin nan cike da haiba da wani irin annuri Dukda ba sake take ba, ya saka wata takalmin fata me surkin ja da brown se ya ɗaura jar jaddara a kanshi, sajenshi nan a gyare lub lub haka gashin kanshi dake sheki, agogonshi Iwatch ne wadda kallo ɗaya zaka mata ka san diamond ce sbd walwalinta, hannunshi cushe a aljihu ya nufi sashin mahaifiyar tashi yana taku cikin salon tafiyarsa na ingarman namiji me cike da kwalisa.

Har cikin ɗakinta ya sameta ya ɗan rungumeta ganinta tsaye tana gyara kan dressing mirror ɗin ta, a hankali yace
"Alhamdulillah Mammi lafiya ta samu Allah shine abin godiya"

Tace
"kwarai kuwa Son, ji nake kaman ban taɓa wani ciwo ba"

Yace
"Good morning mom"

Ta amsa cikin kulawa, sannan ta ɗaura da
"akwai abinci basket biyu a kitchen ka fita dashi ina zuwa mu wuce asibitin"

Fita yayi yana murmushi ya zaku iya zakuwa wurin son ganin kyakyawar fuskar ta da idanuntan nan masu kyau da ɗauke hankali.

A mota ya saka baskets ɗin yana tsaye yana jiran mammi se kuwa gata, daga nesa yake ayyana kyaun mahaifiyarshi da iya shigar ta Dukda hijab ne jikinta amma kallo ɗaya zaka mata ka san wannan ɗin ƴar gayu da ado ce, zobunan gwal guda biyu se walwali suke a hannunta na hagu, na damar na riƙe da jaka.

Da kanshi ya buɗe mata gidan gaba ta shiga ya zagaye ya shiga ya ja suka fice, tun asuba iyayensu mazan suka je asibitin suka dawo, da kyar baba prof ya lallaɓa fa'iza ta bar kuka me cin rai da take, ya mata nasihu sossai haka babanta, Fauza kam da kyar ta iya gaida su kunya kaman ta tsaga ƙasa ta shige.

Sun so su dawo tare da Jaddah tace bata san zance ba se Mammi ta zo Farhan da yake ta zirga zirgan asibitin se ya maida ta.

Da sallama suka shiga ɗakin tana kwance ne idanunta kuma biyu ba bacci take ba, har zata amsa sallamar mammin kamshin turaren shi ya cika ɗakin wadda ya tabbatar mata da tare suke da mammin hakan yasa tayi saurin rufe idanun..

Jaddah ta amsa tana mata sannu da zuwa har ƙasa ta duka ta gaida surukar tata, bayan sun gama Gaisawa ta tambayi me jiki Jaddah tace da sauƙi don har ta sha pepper soup ɗin kayan ciki da Amminta ta turo baba Alhj dashi da ruwan zafi.

"Bacci ma take"
Cewar mammi.

"Yanzu fa muke hira ina ga baccin ya fusge ta"

Shi kam da idanu yake binta, kaman ze cinye ta, fuskanta yayi fayau ya faɗa, tsab kuma ya fahimci ba bacci take ba shine bata son gani, ajiyar zuciya me sanyi ya sauke suka gaisa da Jaddah kan, Jaddah da mammi suka fita akan zasu je wurin fa'iza daga chan Jaddah zata wuce gida mammi ta dawo ɗakin.

Shi cewa yayi ba yanzu ba, zama yayi ya kishingida idanunshi a lumshe yana tuna the best moment of his life, be taɓa sanin haka mata suke ba lallai fauzar tashi ta daban ce, a kan labbanshi ya furta
"precious pearl" wato lu'u lu'u mai daraja.

Murmushi ya saki yana gyara kishingidarshi haka ma ya gode.

A hankali ta soma buɗe idanunta ta kure shi da kallo, dukda ba fuskantar ta yake ba saide tana iya hango farar fatar fuskar tashi da take cike da kwwantanccen saje da suka yi lublub, zara zaran gashin idanunshi da suka sauko sossai waenda suke taimakawa wurin maida idanunshi sexy kaman me jin bacci, gashin girarsa kaman zana mishi ita aka yi baƙi sidik, komai nashi me kyau ne da tsari.

Ganin yana motsa idanun alamar ze buɗe yasa tayi saurin janye nata tana lumshewa, murmushi me sauti ya saki a jikinshi yaji tana kare mishi kallo kuma tsab ya ganta ta ƙasan idanunshi ya barta ne ta morewa kallon nashi.

Miƙewa yayi Tsam ya nufi gaban gadon ya ja silver chair ya zauna dab ita cikin yanayin maganar shi yace
"ya dae ƴan mata? Na miki ne?"

Takaici ne ya zo mata wuya, kaman ta kurma ihu ji wani zance anan fisabilillahi.

Chan ƙasa ƙasa yace bayan ya kama hannunta ya saka cikin nashi.
"Precious pearl buɗe idanunki ki kalleni son ran ki, ni ɗin naki ne gabaɗaya, Mallakinki ne.. Ki kalleni har ki gaji babu mai miki hijabi"

Bata motsa ba kaman ma bata san yana yi ba, murmushi ya saki Sam baze yi fushi ba don ya san yayi laifi, lallaɓata ze tayi har ta sauko.

"Fauuuzaaa..!"
Ya ja sunan wadda ya saka ta jin kiran har cikin jininta, tsammmm haka tsikar jikinta suka amsa.

"Na san ban kyauta ba, na miki ba daidai ba amma wallahi ba da niyya bane so da kishin ki ne ya janyo, kiyi hakuri, kiyi min duk wani hukunci zan ɗauka amma banda shariyar nan please...ki taimaki bawan Allah Faizan kar zuciyarsa ta tsaya da aiki"

Nan ma bata buɗe idanunta ba, se baki da ta ɗan turo, red lips ɗin nata se sheki suke Dukda babu abunda ta shafa musu, caramel skin ɗin nata yabi da kallo kaman da madara take wanka tsabar shekin da fatar tata take Dukda ba fara ba ce.

Hannunshi ya kai ya zame ɗan kwalin kanta ya sanya ya fara shafa lallausar gashin kanta alamar rarrashi, ko motsi ta ƙi tayi, jin za'a shigo ne ya sanya ya miƙe ya rankwafo ya bata zazzafar peck a goshi sannan yayi pecking hannunta dake cikin nashi kan ya saki ya koma da baya ya zauna inda ya tashi.

A ranta take raya wannan gayen bashi da kunya, tsaki ta ja kaman ta buɗe idanu tayi ta dukanshi ko zata huce take ji.

Dr ce ta shigo, Gaisawa suka yi cikin mutunci tace
"Captain, Mrs Faizan kaka ta samu sauƙi ga takardar sallamar ta nan amma please a sahirta mata har ta warke don ta sha matukar wahala"

Wani irin smile yake saki yana shafa kanshi ba se ta faɗa ba ma ai yanzu shi da ya kara gangancin rabar ta ai se da amincewarta ɗari bisa ɗari.

"OK Dr. Thank you and in shaa Allah za'ayi yadda kika ce"
Karbar takardar yayi se ga jadda ta shigo ashe bata wuce ba, se kawai yace bari yaje ya biya bill ɗin kan sun Haɗa abunda zasu Haɗa se su wuce.

Fa'iza ma an sallameta don taji sauƙi sossai, saide har yanzu bata daena share hawaye time to time ba tana tuna irin evil mom da Allah ya bata.

Duk a tare suka fito, Fauzar na tafiya a hankali ko inda yake bata kallah ba, a maimakon ta shiga motar shi da ya buɗe mata se ta wuce ta buɗe na Farhan ta shiga gaba, Fatima na baya da zaliha.

Jaddah da mammi ne suka shiga nashi ya ja ya tafi kan Farhan ya bi bayanshi.

Dayake lafiyar motar ba ɗaya ba yasa Faizan ɗin ya tsere mishi kuma da yanayin tuƙinshi don kowa ya san yadda mutanen Abuja suke tuƙi ba kaman na sauran garuruwa ba.

A hankali Farhan ya shigar da motar cikin gidan, daga chan kofar sashen jadda suka hangi Faizan na tsaye yana amsa waya, kaman an ce ta kalli chan gefen kofar su se taga motar Aunty Fatima zaune a driving seat fuskanta a kumbure suntum ta kure Faizan da kallo.

Buɗe motar Fauza tayi ta fito, daidai fa'iza ma ta fito amma se suka yi sashen Mammi da zaliha don chan mammi tace ta je, yayinda Fauza kuwa ta nufi sashen Jaddah babu abunda take so irin tayi wanka ko zata sake jin daidai, Kure ta Fatima tayi da idanu tana jin tukukin bakin ciki yadda taga Faizan duk hankalinshi ya ɗauku kanta ita kuma tana tafiya kamar hawainiya.

Tada motar Fatima tayi a ranta tana ayyana da ta bar wa Fauza Faizan wallahi gwara ayi biyu babu, sake motar tayi tayi kan Fauzar gadan gadan, kanta na a ƙasa Sam bata lura ba, yayinda Faizan kuma idanunshi na kanta ta ɗauke mai hankali kaman an ce ya waiga se yaga Fatima tayi kanta da mota...

Wani irin hantsilar da wayan hannunshi yayi ya nufe ta da gudu yana kwala kiran sunanta a tsorace ta ɗaga kai kan ta waiwaya taji an yi sama da ita da mota, ta bugi gaban motar tare da faduwa ƙasa tana jin yadda Faizan ya sake kwala kiran sunanta idanunta suka lumshe.

Da gudu Fatima ta juya kan motar ta nufi gate, se daka tsalle gateman yayi don shima saura kiris ta take shi, Farhan da shima ihun Faizan ne ya rinjayeshi ya fito daga sashensu na en maza haka muryar tashi tayi sanadiyar fito da rabin ahalin gidan, babu wadda ze ce ya taɓa jin muryarshi haka don bashi iya ɗaga murya in yana magana kaman da kanshi yake se yau.

Ɗagota yayi ya sa akan kafar shi a rikice yana kiran sunanta ba kakkautawa yana cewa ta buɗe idanunta, saide inaa bata jinshi seda Farhan ne yace
"Ya Faizan dauko ta mu wuce asibiti"

Kan ya tuna da wani asibiti da gudu ya sabeta zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login