Showing 57001 words to 60000 words out of 86608 words

Chapter 20 - DIDDIGAR ƘAYA COMPLT Hausa novel

21 Aug 2024

18463

too young"
Shi karan kanshi da ya faɗa ɗin he's not so sure of his self bare Faisal me sauraro.

"Maganan gaskiya shine ka fito ka raba musu kwana ko da bazaku kwana tare ba ya zamana ran kwanan ta bakwa tare da Fatima ta hakan ne zaka iya kwasar girkin tunda kana so"
Shi ba fa hakan ne baze iya ba yanzu yadda ze fuskanci Fauza ne yace ta cigaba da girki bayan a fuskanta ya jefe ta da mugun kalamai yana cewa ba ze iya cin jagwagwalonta b.....

Gigitaccen Ƙara da yaji da Hasbunallahu wani'imal wakeel shi ya saka shi saurin miƙewa daga jinginen da yake..

Muryarshi na rawa yace "Fauziyya..!"
Da gudu shi da Faisal suka yi inda suka ji ƙaran tana kokarin cire hijab ɗinta yayinda wani dake daga gefe yake kokarin kai hannu da taimaka mata, cikin zafin nama Faizan ya damki hannun nashi ya cillar kan ya fusgota kaman yadda take a rude haka shima ta ruɗa shi.

Fahimtar ƙadangare ne ya sa ya sure ta gabaɗaya yayi wurin motan shi yana sanyata ya zare hijab ɗin gabaɗaya ta haukace da kuka da kiran sunan Allah daidai ƙadangaren ya zo kan bayan wuyanta se ya tsaya Chak a wurin ko motsi baya yi.

"Yaaaya.. Don Allah ka cire min wayyo kafafunshi na shiga min fata, da zafi sossai ka cire min don Allah"
Yadda take kuka take abu kaman shafan aljanu yasa ya matse ta bisa kirjinshi yasa hannu da nufin fusge ƙadangaren sede duk iya gwada karfinshi ƙadangaren nan ya ƙi ko motsi, hankali tashe yake kallon ƙadangaren wani irin tashi tsikar jikinshi yayi da sauri ya fiddo waya ya fara kiran Baba prof.

Cikin hanzari ya mishi bayanin abunda ke faruwa gashi Fauza ta dena motsi, Baba prof yayi salati ya sallamar kan yace
"ku yi sauri ku je wurin prof ghali na tabbatar ze yi duk abunda ya dace yanzu yanzu Faizan karka ɓata lokaci bari na kirashi"

Kofan motar ya tura ya kira Faisal tare da cila mai key don yanzu ba ze iya tuki ba gabaɗayanshi ya sauya idanunshi har sun sanja kala, Afnan da husna da har sun fara hawaye ne suka shiga gaba. A take ya ja mutane suna ta mamakin wannan abu da Allah ya kiyaye haka students suka watse.

A hannu ya ɗauke ta zuwa wurin malam ɗin, already Baba Prof ya kirashi ya mishi bayani, a jikinshi ya sanya ta Tare da kwashe gashinta da ya baje Malam ghali na kallon kadangaren yace
"la haula wala quwwata illa billah..."
Da sauri ya janyo ruwan zamzam da wasu Adu'o'i ke ciki ya tashi ya shiga dakinshi mintuna biyu ya fito da wani Allon karfe ruwan ya zuba a Allon kan ya saka ya buge ƙadangaren yana ambaton sunan Allah.

A take ƙadangaren ya fice fit daga jikinta ya faɗi ƙasa ya fara kokarin guduwa wannan ruwa malam ya diba ya fara zuba mai nan ya fara wani kalar birgima da mutsu mustu ba'a ɗauki lokaci ba ya zama baƙi kirin ya tamushe kaman wadda wuta ya babbake.

Faizan na ta patting kumatunta yana cewa
"Ke Fauza buɗe idanunki kiga an cire... Fauza! Fauziyya..!!"

Malam yace
"bazata tashi ba Faizan kwantar da ita"

"malam me yasa bazata tashi ba? Don Allah kayi wani abu"
Yadda yake maganan kaɗai zaka san ba karamin ruɗe wa yayi ba, me hakan ke nufi? Yau da baya school ɗinsu fa? Haka zata shiga wannan hali ita kaɗai?

Malam ghali yace
"wato wannan ƙadangaren ɗan aike ne, a yadda ka ganshin kila ta ambaci Allah a sadda ya nufi hawa jikinta da bata ambata ba ƙara kawai ta tsaya yi da yanzu ganinshi ma wahala ze mana don jikinta ze shiga, ko ya lahanta mata abubuwan ciki ta mutu ko kuma yayi mata illar da warakarshi se rabba"

"waye ze mata hakan? Waye yake neman illatar da lafiyar ta haka? Me ta musu?"
Kaman ze yi kuka yayi maganan.

Malam yace
"wannan mu barwa Allah, yanzu mu tsaya kan lafiyanta"

Ruwan Adu'a malam ɗin ya bashi yace ya shafe ta dashi, bayan yayi ya saka shi saka mata a baki, nan ya bashi za'afaran da habba da suke dauke da Adu'a yace ya shafa mata, fuska, hannaye, gashin kanta da kafafunta nan take yayi.

Ya zauna yayi shiru yana kallonta cikin jiran malam ya gama Adu'ar da yake yi, yana gamawa kuwa ya watsa mata se ta ja numfashi a kuma ruɗe tayi hanzarin mikewa tana mutsu mustu..

"Yayaaa ka ciremin... Wayyo zafi, Hasbunallahu wani'imal wakeel... Wayyo Jaddah..."
Duk bata san tana wannan sambatu ba kamata yayi ya rungume a hankali ya sauke hannunshi bisa bayanta ya zagaye kan ya da matse ta a jikin shi cikin rarrashi yace

"shhhh ƙanwata, yi shiru an cire baya jikinki... Shhh"
Lub tayi.

Malam yace
"ku je a duba jikin nata in ya so ko maganin asibiti se a sake bata watakila yana da dafi, amma ga wannan ta dinga anfani dasu zamu yi magana da Mahaifin naka"

Prof ghali babban malami ne don tsohon professor ne na musulunci abokin Baba prof ne, kuma dama chan Faizan kan leƙa ya gaida shi idan ya samu time.

Zamewa tayi daga jikinshi kanta a ƙasa, haka suka miƙe suka fito, hijab ɗinta ya sanya mata yana kallon bayan wuyan nata da shape ɗin ƙadangaren har yanzu yake kwance yayi baƙi sidik...

"Me ke shirin faruwa ne?"
Yayi maganan yana sake kallon hannunta da ta gimtse a cikin nashi har yanzu yana iya jin yadda jikinta ke rawa ta ciki....

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤



25

Ko da suka isa asibitin Jafar ne ya duba raunin aka yi mata allura, ganin ko tsorata bata yi ba kaman yadda ta saba ba ya san har lokacin bata dawo daidai gabaɗaya ba, haka dae Jafar ya dawo dasu gida yana kallon yadda gabaɗaya Faizan ɗin Damuwa me yawa ya nuna a fuskanshi.

"Ka tafi da motar na ga kaman hadari ko gobe se ka ba driver ɗinka ya dawo dashi"
Cewar Faizan bayan sun sauƙa yana rike da hannunta, Afnan tayi mata Allah ya kiyaye kan suka fice daga gidan.

Haurawa suka yi zuwa ɗakinta, cikin kulawa yace
"bari na Haɗa miki ruwa ki watsa se ki sha magani ko?"

Girgiza kai tayi idanunta tab da hawaye ta sake riƙe hannunshi da yake Shirin zarewa cikin nata.
Fuskanshi cike da tausayinta yace
"babu abunda ze sake faruwa yanzu kin ji? Sake ni kiga"

Nan ma girgiza kai tayi se hawayen ya gangaro, babu yadda ya iya illa ya sa hannunshi ɗayan ya share mata kan ya ce ta tashi su tafi, a tare suka shiga bayin ya Haɗa mata ruwan ya zare mata hijab ɗin se ta ɗan ja baya amma bata sake shi ba, yace chan ƙasa
"Toh yanzu kiyi wankan bari na fita"

Cikin wani irin murya a shagwaɓe cike da sangarta tace
"uhm uhm ni de don Allah karka fita ka barni ka Juya bayanka kawai"

Babu yadda ya iya ya matsa daga bakin kofa ya juya mata baya, sharp sharp ta watsa ruwan tana ta kalle kalle, tana gamawa ta janyo towel ta ɗaura tana kokarin jan hijab ɗinta ta saka Bon ɗin da ta kama gashinta dashi sakwa sakwa ya kunce zuban gashin ya haɗu da ruwan dake jikinta yayi mugun firgitata ta kwalla ƙara, a hanzarce ya waigo kan yayi wani yunkuri ta faɗa jikinshi yayi saurin taro ta, yana cewa

"menene kuma?"
Siririn kuka ta saki tana cewa ya taimaka ya duba mata bayanta motsi taji kaman ƙadangaren ne ya dawo.

Daga ita har shi jikinsu rawa ya ɗauka, zuciyarshi na bugawa da karfi karfi jin yadda take kara mannewa jikinshi hannunshi na cikin wet gashinta yana shafa bayan wuyanta zuwa bayanta, ya salaaaam ya ambata cikin ranshi jin yadda take kokarin kunce mai notikan kai gabaɗaya.

Janyeta yayi suka fito daidai nan Fatima ta buɗe kofan ta shigo tare da nufo ciki gabaɗaya ai se idanunta suka mata mugun gani, baƙin kishi ne ya taso ya Rufeta idanunta har rawa suke yi..
"Me...me me zan gani haka? Me wannan?"

Be tankata ba yana rike da fauza har zuwa dressing mirror saide bata zauna ba ta kara mannewa a jikinshi fuskanta cikin kirjinshi tana sauke numfashin dake gigitashi ba tare da ta san me take aikata mishi ba.

"Zauna"
Ya faɗa calmly.
Zama tayi ya juya ga Fatima dake tsaye yace

"Next time pls ki nemi izinin me wuri kan ki shigar mata, and bata da lafiya find something da zata ci don bazata bari na fita nema mata abinci ba"
Har kaman zata lailayo Ashar ta maka se kuma ta fasa ta ficeee fuuu

Sama sama ya shafa mata mai, kan suka tafi tare ya buɗe wardrobe ɗinta ya duba mata riga marar nauyi ta sanya, bayi suka koma suka yo alwala a tare daidai lokacin da ruwa ya tsuge sossai kaman da bakin ƙwarya Dukda daminar bata wani shiga sossai ba especially a ta north ɗin nan amma Abuja ba laifi suna samu akai akai tun last week.

Shi ya ja su sallar magrib bayan sun idar ya bata Alqur'ani ta karanta, cikin tattausan muryarta ta fara karantawa wadda ya taimaka sossai wurin ƙara natsar da ita, se a sannan ya mike yaje ya duba Fatima ta kusa gama girkin ya sakata tayiwa husna wanka duka ranta a cunkushe, tunani kawai take me ya faru tsakanin fauza da Faizan da har yake riritata haka?

Shi kuwa wanka yayi ya sake alwalan isha ya fito sanye da dogon wando da jallabiya, hannunshi waya ne yana magana da Baba prof da yake ta jimamin wannan abu, nema yayi da ya bata wayan shima kuma dama daidai lokacin yake isa wurinta se ya zauna daga gabanta ya miƙa mata wayan.

Tana sawa a kunnenta ta fara hawaye cikin rawar murya suka gaisa da baban yake rarrashinta karta damu babu wani abu ta rike adu'o'in da ya bata sossai kuma ze kara mata wani, rikici ta sanya mishi akan ita kam zata dawo wurin jaddar ta tana jin tsoro.

Da kyar ya shawo kanta zata zauna Abuja ɗin kan ya ba wa babanta wayan shima dae ya mata sannu da Allah ya kiyaye gaba haka jadda da mammi ma, bayan ta sauke wayan se ta miƙa mai ƙin ƙarba yayi.

Idanunta da suka yi laushi yau ɗin gabaɗaya ta ɗaga se suka faɗa cikin nashi da ya kara lumshesu yana kallonta, a hankali tace
"Yaaaya ga wayan"

Ya rasa yadda take kiran nata yaayan da yake jinshi har cikin ɓargonshi ba ƙarya, a hankali yace
"ba zan karɓa ba" chan ƙasa

Kara marairaicewa tayi tace
"Meyasa to?"

"Me yasa kike son barin ɗakinki ki koma gida sbd wannan abu da be taka kara ya karya ba? Baki san kowacce mace da akwai abunda take fuskanta a nata gidan aure tana zama jaruma ne tayi over coming komai ba? Na Gaza wurin kula dake ne?"
Ya karashe tambayar da wata murya da ta sakata maida kanta ƙasa kan ta girgiza tace

"A'a ka yi hakuri"
Yace
"na hakura, tashi muyi sallah"

Isha suka gabatar da kanshi ya fita ya karbo abincin don Fatima dangwalarwa tayi a dining ta wuce ɗakinta.

Kasa hakuri tayi ta kira Auntyn ta take tambayarta meyasa bata fara ganin abunda tace ba, Auntyn tace mata an samu akasi amma ba shi ze sa su karaya ba, ta cigaba da zubawa sarautar Allah ido, rayuwar Fauza a gidan kaman a tafin hannunta yake.

Husna ya ɗauka da tayi bacci a parlorn yayi ɗakin Fatima da ita, tana sauke wayan yana buɗe kofan da sauri ta gyara zamanta, a kan gado ya kwantar da ita yace

"zata kwana wurinki yau"
Juyawa yayi ya fita yana mamakin yadda Fatiman ta kasa zuwa tayiwa Fauza ko ya jiki ne, har ya taɓa handle ya dakata ya juyo fuskanshi ba yabo ba fallasa yace

"kaman na ce miki Fauza bata da lafiya ko?"
Tace
"eh ka faɗa, me zan mata bayan girkin?" Ta faɗa cikin gatse.

Yace cikin mamaki
"wai dama haka zuciyarki yake ne ko yanzu ne ya koyi sabbin ɗabi'un nan? Fatima sannu bazaki iya zuwa ki mata ba? Wai me kika ɗau kishi ne?"

"Me kuwa na ɗauke shi? Ni yaya meyasa kake min haka ne? Meyasa a ko yaushe abu ya Haɗa mu ni ce da laifi? Ni da nayi ɓari ko sannu ta min bare Allah ya kawo na mora? Gwara ni na mata girki ita ko ruwa ta kawo min? Duk baka ce komai ba se ni yanzu da ban san hawa ko Sauƙar ciwon munafurcinta ba zaka wani ce in je in gaisheta? Kayi hakuri ba zan iya ba"

Dawowa yayi ya zauna ganganta yace
"Fatima ki fahimce ni, babu wacce nake fifitawa tsakaninku illa ma ita da nake tauye ta, kina sane tunda ta zo gidan nan sati na shidda kenan nake ga ban taɓa ware kwana ɗaya tal da sunan nata ba, ban cika mata duk wani hakki na matsayin matata ba kina kallo baki taɓa ce min hakan ba daidai bane, annabi fa cewa yayi mafi darajar mace itace wacce zata taimakawa mijinta wurin bautar Allah in taga zai kauce ta dawo dashi daidai, duk na rasa wannan daga gareki..."

Hawaye ta share tace
"zaka ce haka ai tunda ta baka ka kwasa"
Ya rasa me ke damun Tunanin Fatima, mikewa yayi ya fice tunda ta ƙi fahimta tana kan rashin daidai.

Tsaye ya samu Fauza tsakiyar parlor tana ganinshi ta nufo shi yayi saurin saka hannu ya riƙe nata ganin kai tsaye jikinshi take shirin shigewa wadda illar da take mishi a yadda ya san kanshi idan be yi da gaske ba baze yi bacci ba yace
"menene?"

Tace
"Motsi nake ji a ɗakina"
Yace
"Ina kin yi azkar kuma kin karanta Alqur'ani?"
Kai ta gyaɗa yace
"to ki yi yaƙini da hakan ki saka a ranki babu wani abu da ze iya cutar dake kinji?"

Kai ta gyaɗa ya Janyeta suka yi ɗakin nata inda yace ta kwanta, zama yayi ta kwanta a kan pillow yana shafa kanta idanunta a lumshe yayinda shi kuma nashi ke kan fuskan nata yana kare mata kallo har bacci ya ɗauke ta.

Fita yayi ya tabbatar da komai daidai a gidan kan ya dawo ya rage musu wuta ya cire jallabiyar tare da kwanciya da dogon wando kawai be damu da saka kayan bacci ba, har ya lumshe idanu ya tuna magungunan ta bata shafa ba.

Sauka yayi ya ɗauko ya zo ya zauna tare da zuba mata idanu na mintuna kan a hankali ya fara sakawa a hannunshi ya shafa mata a kafafu, ya sake sakawa ya shafe hannayenta dashi, daga nan se gashin kanta ya shafa mata. Sauran na hannun nashi ne yake shafa mata a fuska a hankali wadda ya saka ta ɗan buɗe idanunta dake cike da bacci tana Kallonshi.

'Tsarki ya tabbata ga Allah da ya halicci wannan idanu' baze taɓa cewa ya taɓa ganin abunda har ranshi yake mishi kyau irin idanunta ba, a hankali yake shafa kumatunta idanunsu sarke da na juna se chan ta turo baki tace

"bacci" cikin muryar da bacci ya ci karfi.

"Yi baccinki an gama"
Ya faɗa a natse kan ya miƙe ya adana magungunan ya dawo ya kwanta daga gefenta yana lumshe idanu, baya son kawo Tunanin komai a ranshi in yace ze yi tunanin wadda ya aika mata da wannan ƙadangare tabbas ze fara zato kuma ya san zunubi ne, in yace ze yi Tunaninta kuma tabbas ze iya Jawa kanshi damuwa wadda baya fata ya kasance yanzu don baze iya ɗaukar abu guda biyu ba idan abunda yake gudu ya kasance.

Haka dae yayi bacci da blank thought, asubar fari ita ta fara buɗe idanu se ta ganta kwance dab dashi kansu a kan pillow ɗaya yayinda hannunta ke kwance bisa faffaɗar kirjinshi, a hankali ta kai idanunta fuskanshi da dim haske ya bayyana haske da kwarjininshi, dukda bacci yake yi but ba karamin kyau yayi ba sajenshi dake kwance lublub gwanin sha'awa.

A hankali ta ɗago hannunta ta ɗan shafa sajen nashi tana mamakin yadda aka yi tun da chan bata taɓa ganin kyaun nashi ba se yanzu, karab taji ya riƙe hannun da take shafa mai fuskan, a hankali ya waigo yana kallon ta, kunya ne ya rufeta se tace
"Ina kwana?"

Daga haka ta zame ta sauƙa tayi toilet, murmushi ya saki kan shima ya sauƙa, zuwa yayi ya kunna Alqur'ani don da asuba sunna TV karatun Alƙur'ani mai girma suke sakawa, daga haka ya ɗauki jallabiyarshi ya fice dakinshi a chan yayi alwala ya zo ya fice masallaci.

Ko da ta idar da sallah azkar tayi tare da karatun Alƙur'ani, bayan ta gama ta miƙe ta shafa magungunanta da kanta daga kai har kafa kan ta saka riga dogo marar nauyi, tana zama a cikin kujerun ɗakin yana shigowa.

Ganinta haka ya sa ya sakar mata murmushi itama ta mayar mai tana sake cewa
"Ina kwana?"

Yace
"kin tashi lafiya? Ya jikin?"

Tace
"Alhamdulillah"

Matsowa yayi kusa da ita tare da rankwafowa yana duba bayan wuyanta inda ƙadangaren ya bar tambari sede wayam babu, ajiyar zuciya ya sauke wadda numfashin a wuyanta se da ya sakata saurin kame jikinta tana ɗauke numfashi.

Mikewa yayi yace bari ya ɗan kwanta, dakinshi ya wuce ita kuma ta mike ta fara gyaran ɗakinta daga nan ta sauka ta musu abin kari ita da husna, tana haurowa ta gamu da Fatima, abunda ya faru jiya ne ya dawo mata se tayi saurin kauda Tunanin Dukda gabaɗaya gidan babu wadda ya san ainihin su Fatima se ita amma bazata ce sune suka mata hakan ba tunda bata da shaida..

Har zata wuce se ta tsaya tare da waigo wa ta dube ta tace
"Faɗan bayan fage na lusari ne, harara a duhu kuma baze sa in chanza rawa ba kirrr nake kallonku, wai baki yi mamakin yadda nake yawan faɗin cusa kanki kika yi wurin samun ya Faizan ba? Ko kwakwalwarki a toshe yake baya tunani? Toh duk wani sirrin ku yana tafin hannuna the next time kuka sake yi min abu makamancin haka ina me tabbatar miki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login