Showing 36001 words to 39000 words out of 86608 words

Chapter 13 - DIDDIGAR ƘAYA COMPLT Hausa novel

21 Aug 2024

18459

ɗin kujeru akwai TV akwai kuma fridge a ɗakin, daga dan lungu window kuma akwai coffee table ɗaya da kujerun shi guda biyu masu kyau se karamin kofa da ze sadaka da madaidaicin balcony ɗinta wadda be wuce na tsayuwar mutum ɗaya ba an tare shi da wani black and gold glass.

Kofan bayi kuma na daga kudu, duk yadda Fatima take Tunanin tsaruwar ɗakinta se taga na Fauza ya fi nata don ko ba'a faɗa mata kudin kayan nan ba ta san ba laga laga bane Dukda natan ma masu kyau ne amma na Fauza sun fi nata, ash ne da gold ɗakin haka labulayen gold da light ash, dressing mirror ɗin yayi mata sossai kaman ta ɗauke, idanunta kafe kan show glass na zamani wadda aka cika shi makil da wasu hadaddun turaruka wuta take rayawa a zuciyarta; lallai an nuna mata wariyar launi a nan wurin, an nuna mata kuma Fauxa ce yar gida kuma er gata.

Da kyar tayiwa su yaya fadilan sannu ta ajiye abubuwan hannunta, daidai lokacin me aiki na shigo da saura tace
"ya fadeela ku ci abinci, bari na ɗan sha magani don har yanzu cikina ciwo yake"

Cikin tausayawa suka mata sannu ko kallonta Fauza bata yi ba har ta fice.

"Fauziyya ya kamata fa a ce zuwa yanzu duk wani baƙin halinki kin baro shi chan yola kin nemi natsuwa da salama kin ɗaurawa ranki, daga Fatima har Faizan yayyunki ne suna da ikon hukunta ki da duk iskancin da zaki yi, kina ƴar fitsitsiyarki har kin san kishiya na ciwo ko sannu bazaki ce mata ba?"

Faɗa sossai take mata wadda wacce ake wan ta lumshe idanunta kawai tana tunanin yadda zamanta ze kasance a gidan, ko sauraron ya kakar dake faɗan ba yi take ba.

Bayan ta gama suka ci abinci wadda Fauziyya bata ci ba, bayi yaya kaka ta shiga don yin alwala yayinda ya fadeela ta ɗago Fauzan ta zaunar da ita.

"Fauza kar mu fara haka dake mana? Kin manta kin ce zaki zauna lafiya dasu bazaki neme su rigima ba in har ba su suka neme ki ba?"

Tace
"ban manta ba, amma dae kin san tun da ba magana nake mata ba me don ta ce cikinta na ciwo zan buɗe baki in ce mata sannu bayan bata kasa dani ba? Yaya fadila don Allah ku Rabu dani in ji da abunda ya dameni, matar nan kuma ta ci darajar Jaddah wallahi"

Tana kai nan ta koma ta kwanta abunta, girgiza kai ya fadila tayi tace
"kina da aiki wallahi, amma ba komai duk sadda kika so zaman lafiya da samun kwanciyar hankali se ki neme ni"

Daidai lokacin ya kaka ta fito, Ya fadeela ma ta shiga suka zo suka gabatar da sallah, suka ɗan kara kakkabe mata ɗakin don akwai injin shara a ciki, kuma ya fadila daman su dashi suke anfani a lokacin ne ma ta mike zaune tana kallon yadda ya fadeelan ke operating, bayan sun gama suka kara gyara mata wardrobe ɗinta da rabin shi glass ne ita kanta bata taɓa ganin ɗakin da ya burge ta irin natan ba, ta kuma sanyawa baba da jadda albarka don sun zuba kudi ba kaɗan ba a kayan nan, abunda kuwa yafi burge ta shine lefe don yadda take son gayu haka ya fadeela ta zaɓa mata isashun kayan gayu da ado.

Sun gama kenan sun kara sa turaren wuta a burner ya shigo da sallama, kwanciya tayi tare da juya baya, be ma san tana yi ba don ko inda take be kalla ba, akan kujeran ɗakin ya zauna ya gaishe da ya kaka tare da mata ban gajiya, ya kuma tambayi ko akwai wani abunda suke so, suka ce babu yanzu ma shirin tafiya suke.

Se lokacin Fauza tayi saurin ɗagowa
"Ya fadeela yau Zaku tafi wai?"

Se a lokacin ya kalleta babu ɗan kwali kanta gashinta ya sha kananun kitso irin na kanuri yiri yiri ya zuba a bayan wuyan ta wasu ta baya wasu sun sauƙa a kirjinta, doguwar riganta na Holland babba ya tattare daga sharabarta sbd irin kwanciyar da tayi.

Tsaki ya kaka ta ja tace
"yo to dama zama zamu yi? Yau zamu koma tunda mun kawo ki fatan dae Allah ya baku zaman lafiya"

Rau Rau tayi da idanu tana jiran jin amsar yaya fadeela, shi kuwa tun kallon farko da ya mata ya ɗauke kanshi, ya fadeela tace
"zamu tafi Fauxa, haka kowacce mace take hakuri a duk randa aka kawo ta ɗakinta amma ba gaki ga fadyaa ba zaku ke haduwa nima kan in koma Australia zan zo kin ji?"

Kanta ta mayar kasa tana jin kewan gidansu na shiganta, duk yadda ta so tayi dauriya a sadda suka fito tayi musu rakiya kasawa tayi ta fashe da kuka tare da rungume ya fadeela, barin ta yanzu zasu yi da wannan munafukar da kuma azzalumi? Yanzu kenan kowa baya son ta? A haka zata zauna dasu su biyun su kasheta a banza?

Ya fadeela ne ta kalleshi tace
"Ya Faizan se fa ka tayamu riƙeta"

Haɗe fuska yayi yace
"ke! Ban fa son hauka me haka? Se kace wacce za'a bari a gidan yankan kai?"

A zuciyar ta tace
"kaman ka sani wallahi babu maraba"

Ganin bazata sake fadeelan ba yasa ya taka ya sanya hannu ya zarota daga jikinta suka shiga mota driver ya ja suka fice daga gidan, suna fita ya saketa ba tare da ya ce mata ci kanki ba ya juya ya koma, don Fatima bata fito ba wai ta sha magani kuma bacci me nauyi yake sakata shine suka ce kar a tasheta ai tayi kokari ma.

Ta jima tsaye a wurin tana share fuska kan ta juya ta nufi steps na parlorn tana dan kallon black rumfa da aka yiwa mashigar yayi kyau sossai ba kaman normal da ta saba gani ba, koda ta turo parlorn ta shigo babu kowa.

Stairs ta nufa ta fara hawa se a lokacin ta lura da dining area na parlorn kasan da daga saman stairs kana hango shi daga sama, akwai washing hand base da console a wurin shima, se kofa wadda babu tantama na kitchen ne, ba laifi gidan ya mata kyau ya burge ta.

Parlorn saman ma ba kowa se kawai ta shige ɗakinta ta maida kofa, bata kwanta kaman ɗazu ba ta hau kalle kalle da taɓe taɓe kaman ba itace ke kuka yanzu ba, babu abunda bata duba ta taɓa ba, duk da yadda take zabga kamshin humra da turaruka haka tayi ta sake fesa na kan mirror ɗinta wai tana jin kamshin su, bayan ta gama tsab ta wuce bayi nan ma tayi ta dube dubenta, ba laifi bayin ya tsaru ta kan yi mamakin toilets na hotels da suke zuwa musamman irin su transcorp sede wannan ya ci uban waenchan haɗuwa.. Ita bata san ma akwai kayan bayi ruwan gold ba se anan ɗin kusan komai ruwan gold ne Fararen kaɗan ne.

Bayan ta gama tayo fitsari dama bata sallah, ta ma yi mamakin wannan period nata be zo mata da ciwon da ya saba ba ko don sbd tashin hankalin da ta shiga ne oho.

Fitowa tayi ta cire Rigan jikinta don ya ishe ta ta duba leggings da vest ta saka abunta ta zauna ta ci tayi Nak kan ta hau gado tayi ɗaiɗai ta fara bacci.
(Su Fauza an samu duniya)

Chan cikin baccin ta me daaɗi taji ana buga kafafunta, bata da nauyin bacci hakan yasa ta mike zaune tana ɓata fuska hasken bulb da ɗakin ya dauka ya tabbatar mata da dare har ya shiga bata sani ba tana baccin da ta kwana biyu bata yi ba.

Kallon Fatima da ta tashetan take yi tana jira taji me zata ce sede shiru tayi tana sake kallon Fauxan zuciyarta na hautsinewa da wani zazzafar kishin yarinyar ta ko ina.

"Lafiya zaki wani tasheni ina baccina kuma ki tsaya kina kare min kallo kaman yau kika saba ganina?"

Haɗe rai Fatima tayi tace
"kul ki soma min rashin kunya daga shigowanki gidana, idan baki sani ba ya kamata ki sani da ba yanzu bane, a da ina kallonki ne kawai a matsayin shashasha wacce bata san me ke mata ciwo ba shiyasa nake kyaleki kike abunda kike so, amma a yanzu da kika amsa sunan kishiyata yanzu ne zaki sake yanke rago ki tabbatarwa da duniya cewa Fatima munafuka ce duk na baya wasa ne"

Murmushi Fauza ta saki tace
"kishiya? Mtseww ke kika san wannan, in baki sani ba ya kamata a ce na saka wannan a bayan tosheshen kwakwalwarki, ban shigo gidan nan da niyyar komai ba don daga ke har mijin naki ba kwa gabana, amma daga sadda kika bari na harzuƙa zan nuna miki cewa kin riga kin bar kari tun ran tubani, zan zame miki kadangariyar bakin tulu se kin yi nadamar fara auren mijin kaddarana. Don haka ki kiyayeni"

Yunkurawa Fauza tayi zata miƙe daidai lokacin da aka turo kofa hakan ya sa Fatima yin baya baya zata faɗi cikin zafin nama yayi hanzarin isowa ya tarota yana aikawa Fauza dake tsaye tsakiyar gadon bata kai ga Sauƙar da tayi niyya ba wani irin dead look.

*Yanzu wasan ya soma*

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤


17

*Assalamu Alaikum warahmatullah barkanmu da warhaka, fatan duk muna cikin ƙoshin lafiya? Alhamdulillah na gode sossai da adu'o'inku gareni Allah ya saka da alkhairi🥰 jiki yayi sauƙi se a ɗaura daga inda aka tsaya in shaa Allah.*

A hankali ta samu wuri ta zauna akan kujeran parlorn saman chan nesa da inda suke, dukda zuciyarta a tsinke yake don har Ga Allah Faizan na daga cikin waenda take jin shakkarsu don tana tsorace dashi ne tun tana ƴar ƙaramarta, matarshi kawai ya kama suka fita daga ɗakin nata bayan ya ce ta same su a parlor.

Ya ɗan yi shiru kan yace
"Fauziyya kike ko?"

Kai ta ɗago tana Kallonshi wai ita yake tambaya sunanta? Bata amsa ba seda yace
"wai ba da ke nake magana ba? Kin san Allah ki rufawa kanki asiri ki zauna lafiya da mu tun muna sheda juna, ba zan lamunci rashin kunyarki da fitsaranki ba, ba a kaina kaɗai ba har da matata"

Kallon Fatima yayi yace
"Daga yau ki sallami Baaba ta dinga tsabtace gidan nan tana girka muku abunda Zaku ci da ke da ita, ba zan iya cin jagwagwalonta ba don haka ke zaki kula da nawa abincina da gyaran ɗakina"

Fatima na murmushi tace
"in shaa Allahu habeeby"

Ya sake kallon Fauziyya yace
"Daga ni har Fatima akwai wadda kika fi shekaru?"

Girgiza kai tayi yace a ɗan zafafe
"baki da baki ne?"

A hankali tace
"A'a"

Yace
"madalla! Saboda haka duk safe ke zaki gaisheta, karki kuskura in sake ganin abunda ya faru yau ya faru don bazaki ji da daaɗi ba Fauziyya, matata ta fi karfin wulakantarwanki, Abu na ƙarshe shine babu wani zancen rabon kwana don zaki zauna ne a matsayin ƙanwarmu.."

Kallon Fatima yayi yace
"ko kina da abun cewa?"

Tace
"ya Faizan na ga baka ja kunnenta akan shan kayan maye da kuma bin maza ba!"

Wani irin kallo Fauziyyan tayi mata kan ta maida idanunta kanshi jin mai ze ce, se taga ya kauda kai da alama ita yake kallo ganin zata kalleshi ya kawar da nashi idanun, bazata ce ga expression ɗinshi ba amma da saisaitacciyar murya ya furta..

"Gate ban amince ki taka ba tare da izini na ba Fauziyya"
Abunda ya faɗa kenan ya sallameta, ta mike ta wuce ɗakinta ba tare da ta tanka musu ba.

Fatima tace
"Abunda zaka ce kaɗai kenan?"

Ya ɗan miƙe tsaye kan ya ce
"me zan ce to? Babu wadda ta sani anan garin da ze shigo har gidan nan ya ruɗe ta, hakanan tun da ta sanya kafarta cikin gidan nan na yiwa gateman kasheɗin bayan ni da ke kar ya bar kowa ya fita daga gidan nan ko ya shigo idan har ba da sanina ba"

Ganin ze wuce room nashi tayi saurin mikewa
"amma fa kai da kanka ka ce ka ganta a nan garin kenan ai baka san ko akwai wasu bad friends ɗinta a nan ba..."

Ya dakata tare da juyowa ya kalleta na seconds kan ya juya kawai ya wuce ɗakin shi, zama tayi kan kujeran dabas tana sake sake, ta so ya gayawa Fauziyya maganan da ze hana ta bacci wlh akan shaye shaye da yawace yawace da take yi amma ba komai da ita take zancen.

Itama mikewa tayi ta wuce ɗakinta don shiryawa ta dawo turaka.

Samun wuri tayi kan kujera ta zauna tare da ɗaga throw pillow ta ɗaura kan cinyar ta ta zabga tagumi, wai haka zata yi wannan zaman? In aiki ne be dameta ba don horon da ta sha kwanakin nan a gidansu na aiki ba kaɗan bane har ma ta saba, amma bata da waya ba abokin hira, shiru haka ze yiwu kenan? Chan ƙasan ranta kuma maganan Fatima ba ƙaramin kuna yayi mata ba amma ba komai zata yi lokacinta.

TV ta kunna ta rage daren da kalle kalle daaɗi sossai ta ji da ta ga ba wa'azu zuƙa bane, se karfe sha ɗaya ta kwanta don ma ita ba gwanar ci ba ce da dole se ta fita ta nemi abinda zata ci.

Buga kofan ta da aka yi da karfi shi ya tasheta a ɗan firgice, dalll haka aka kunna mata bulbs ɗin ɗakin duka Fararen waenda suke da matukar haske, da sauri ta sanya hannu ta rufe idanunta, duniya ta tsani a kunna mata wuta daga tashi daga bacci.

"Malama tashi ki sama min abunda zan ci karfe bakwai nake da lectures"

Dukda yadda ranta yayi mugun ɓaci bata tanka ba, haka kuma bata ɗaga idanu ta kalleta ba.

"Da ke fa nake magana malama!"

Har lokacin bata yi magana ba tana calming kanta ne, bayan ta gama Adu'ar tashi daga bacci ta sauka kawai ta shige toilet bata ce komai ba.

Se hakan ya kular da Fatiman, a fili ta furta
"kammm ni zaki mannawa hauka? Wato ga mahaukaciya tana magana?"
Kwafa tayi ta fito ta je ta zauna a parlorn saman ta ɗaura ɗaya kan ɗaya tana girgizawa, time ta dibar mata in bata fito ba kuma wlh se ta kai karata wurinshi.

Ita kuwa Fauziyya watsa ruwa tayi ta fito ta ɗan shafa mai da turare kadan ta saka cotton bubu ta fito, a kan kujera ta wuceta ta nufi hanyar kitchen ba tare da ta ko kalleta bane.

"Ke! Ina zaki je? Ba'a shiga min kitchen kije na ƙasa wannan ɗin abincin mijina kaɗai nake dafawa a ciki gudun barbaɗe"

Juyawa kawai tayi ta nufi ƙasa ba tare da tace komai ba.

Dankali ta fere me yawa ta zuba gishiri tuli guda kan ta soye shi yayi kararau ta juye a warmers ta ɗauka ta je ta ajiye kan dining kan ta wuce ta haura.

Har zata wuce ɗakinta Fatima ta ce
"Fauziyya..!"

Juyawa tayi ta nufi dining ɗin saman, ganinshi a ciki yasa ta ce
"Ina kwana"

Kaman yadda yayi mata umarni
"lfy"
Shine abunda ya amsa da kan ya cigaba da cin abincinshi.

Kallon kiran me kika min kawai take yiwa Fatiman, ita kuma se tayi shiru na seconds kan tace
"tunda ni ba zaki gaisheni ba, ina kwana? Fatan kin tashi lafiya?"

Wani irin kallo Fauza ke mata na kina kure haƙurina, ɗaga idanu yayi ya kalleta se tacewa Fatiman
"Ina kwana"

Fatima tace
"lafiya ƙalau ya kwanan bakunta?"
Bata amsa ba hakan ya sa Fatima cewa
"yauwa kin gama abincin ba?"

Kaɗan ya saura zuciyar Fauza ya zo wuya tace
"uhm"

"yana ina to?"

"Kasa"

"ka ji ki, ai anan ne muke karyawa, je ki ɗauko mana"
Seda ta lumshe idanu ta buɗe kan ta juya ta nufi sauka, shi karan kanshi da kallon mamaki ya bita a sanin halinta bazata bi umarnin Fatima kai tsaye haka shiru ba, ko ta fara sauyawa ne... Kafadan shi yayi shrugging kan ya cigaba da cin abincin shi.

Bata jima ba se gata da food flask ta zo ta ajiye kan dining ɗin ta juya zata tafi
"ke bazaki ci bane Fauza?"

Juyawa tayi ta kalleta kawai kan ta juya ta wuce ciki.

Tana shiga ta faɗa kan kujera tana ji kaman ta fashe da kuka sbd yadda ranta yayi mugun ɓaci gashi bata fitar da abunda ke ciki ba, ita kuma haka take in har bata rama abunda aka mata ba ranta yayi ta zafi kenan da kuna.

Kakari taji me ƙarfi se kuma taji ana kiran
"ke! Ke!!"

Ta san ita kaɗai yake kira da ke hakan be sa ta amsa ba, tana kwance kan three seater taji ya turo kofan ya shigo.

"Ke! Bakya ji ina kiranki ne? Ko yadda kwakwalwanki yake a toshe haka kunnuwanki?"

Miƙewa zaune tayi tare da fara kunkuni
"to ai ni sunana ba ke ba...."
Ɗallin bakinta da taji an yi ne ya sakata sakin ƙara tana dafe bakin sbd azabar zafin da ya ratsa ta, hawaye ne ya cika idanunta ta ɗago tana Kallonshi.

Kau da kai yayi yace
"kashe min mata zaki yi? Wani irin jagwalgwalon girki ne kika yin nan? Baki san tana da BP bata cin gishiri bane? Tashi ki wuce mu je"

Mikewa tayi ya sako ta gaba suka fito, Fatima na kwance kan kujera sama sama take numfashi sbd yadda take jin kaman zata mutu, murmushi me kyau ta saki ganinta hakan sarai ta ji yadda ake ta maganan jininta na hawa sossai sbd damuwar da ta sawa kanta na ɓarin da take tayi hakan yasa aka hanata cin gishiri, da gangan tayi labtawar da ko loma ɗaya tayi se ta ji a jikinta.

Da sauri itama ta karasa gabanta ta duka tana cewa
"Ya fati sannu! Me ya sameki haka?"

Harara ta zabga mata kan ta cigaba da numfashin ta hannunta dafe da kai.

Rufeta da faɗa yayi sossai kaman ze daketa, raurau tayi bayan ya gama idanunta na zub da hawaye tace
"Yaya Don Allah kayi haƙuri, ni ban iya bane, ban kuma san tana da hawan jini ba... Jiya jiya fa na zo"

Lumshe idanunshi yayi se ya sauke ajiyar zuciya kawai ya wuce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login