Showing 60001 words to 63000 words out of 86608 words

Chapter 21 - DIDDIGAR ƘAYA COMPLT Hausa novel

21 Aug 2024

18445

za'a yi walƙiya... Karku yi gangancin tarar aradu da ka don tabbas kuka tara se kun samu, ni ɗin kafin Allah ce!"

Tana kai nan ta nufi ɗakin Fatiman ta tado husna suka yi ɗakinta har lokacin Fatiman na tsaye tana juya maganan, kenan Fauza ta san suna da mission akan ahalin prof? Ta yaya? Kuma a ina ta sani? Da sauri ta nufi ɗakinta don kiran Aunty hankalinta a tashe.

Fauza kam bayan tayiwa husna wanka ta zuba musu abincin da already ta hauro dashi suka fara ci, har sun yi nisa don har husna tana cewa ta koshi ya tura kofan ya shigo.

A tsakiyar center rug ya samesu suna ta cin abinci, har a ranshi yaji sanyi ganin har ta iya yin girki kenan ta ji sauƙi, zama yayi husna na gaidashi.. Daidai lokacin ta gama itama ta fara tattare wurin ganin bata mishi tayi ba kuma ranshi ya riga ya biya yace

"Ni baza'a bani breakfast ɗin bane?"
Ɗago kai tayi ta kalleshi kan ta kauda don bazata iya faɗar abunda take son faɗa ba matukar tana kallon cikin idanunshi tace

"Ni? Wani jagwalgwalon zan baka?"
Kallon mamaki yake aika mata magana take shirin gaya mai ko me?

Yace
"Eh jagwalgwalon dae zan ci"

Tace
"ai wannan ba zaka iya ci ba, na tabbatar matarka da ta kware a girki ta tanadar maka hadadde ma kuwa"

Kallon husna yayi yace
"je parlor ki kalli cartoon"
Da gudu ta tashi ta fice.

Yace
"Me kike nufi ne kam?"
Ganin ta mike tana shirin tattare kwanukanta tace
"Yaaya pls me yasa kake so se na fito na faɗa kai tsaye? Toh ina nufin ba zan iya baka ba gaskiya don jagwalgwale ne kaje wurin matarka ta baka me daaɗi.. Ko ba haka kace ba?"

Tayi maganan tana kallon gefe...
Mikewa yayi ganin da gaske take yayi saurin riƙe hannunta yana cewa
"Toh yanzu zan cigaba da cin jagwalgwalon don raba muku girki zan yi kwana bibbiyu yadda addini ya tsara"

Kai tsaye tace
"ni kam ba zan yi ba"
Ta karashe da murguda baƙi idanunshi gabaɗaya ya waro yace
"ni kike yiwa rashin kunya da murgude murgude?"
Me makon yaji haushi ma dariya take bashi ala dole fushi take yi.

Tana kunkuni tace
"ni dae ba zan yi ba bana so ai tun farko ba'a nuna ana so ba se yanzu! Ni de babu wani girkin da zan karɓa"
Hannu ya kai ya dalli bakinta

"ni kike yiwa kunkuni?"
Haba ai se ta sakar mai kukan shagwaɓa har da bubbuga kafafu wai zafi...

"Yaa ilahil alameeen"
Ya furta akan lip ɗinshi kawai yana kallonta, yarinyar nan bazata kashe shi ba.

Ganin kaman yayi fushi yasa ta dangwalar da abincin tana tura baki ta zuba mai, ba tare da ya kalleta ba yace
"ɗauke kayan ki ba zan ci ba"

Da sauri ta fara kokarin ɗaukewa yayi hanzarin rike hannunta suka zubawa juna idanu....

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤




26


"Wai da gaske ɗaukewar zaki yi?"
Ya faɗa a marairaice, se ta saki ta tsuguna ta zuba mai tare da miƙa mai.

Karɓa yayi yana cewa
"thank you"
Tana shirin magana Wayanshi ya ɗauki ringing, dubawa yayi se yaga Faisal suka gaisa yake tambayar shi me jiki, Seda ya kalleta kan ya amsa da da sauki, faɗa mishi yayi matansu zasu zo su duba ta.

"Zaki iya tarban baƙi kuwa?"
Ya faɗa bayan ya sauke wayan.

Kai ta gyaɗa tace
"Sossai ma, ni da nake so in ga mutane mutane su ganni.."

Yace
"families ɗin Faisal da Jafar ne wai zasu zo"

Tace
"Tohm Allah ya kawo su lafiya"

Ya amsa da 'Ameen'

Bayan ya gama ci yaje ya shirya ya zo ya tambayeta ko akwai abunda zata buƙata ta amsa da babu kan ya duba Fatima ya faɗa mata tare da umarnin ta fito suyi aikin bibbiyu sbd sauƙaƙawa, ta dae amsa yana fita ta kwanta abin ta ta fara bacci.

Girki me rai da motsi Fauza tayi musu, dukda bata yi yayi yawa ba saide tayi varieties ta tsara shi kuwa yayi kyau sossai, ita da husna suka dinga jigilar kaiwa sama, bayan ta gama ta je tayi wanka.

Bata shafa mai ba se ta shafa magungunan nan da prof ghali ya bata ta shirya cikin lace riga da skirt ne da dinkin yayi matukar amsarta, ga colourn lace ɗin blue da onions se ya haske fatarta, ɗan kwalin irin hular nan ne so gyara parking ɗinta kawai tayi ta sanya ta nemi jewelries da suka yi matching ta saka.

Tana cikin shirya husna ya turo kofanta da sallama, ta amsa tare da ɗagowa.

Gabaɗaya idanunshi ya sake a kanta yana karewa halittar Allah kallo, tambayar kanshi ya fara wai me yake ji a kan yarinyar nan ne takamamme? Ko ta ina ta cike mishi zuciya da Tunaninta, idan ya fita yana marmarin ya dawo ya ga shigarta da kwalliyarta, hancinshi ya shaki sassanyar turarukanta masu saukar da natsuwa, bakinshi a ko yaushe yana marmarin tasting abincin ta...

"Yaaaya sannu da dawowa"
Abunda kenan ya dawo dashi daga duniyar da ya tafi.

Kasa riƙe compliment ɗin yayi yace
"Masha Allah kin yi kyau"

Tana murmushi tace
"thank you"

Yana kallon husna yace
"Na gama shirye shiryen tafiyar husna fa jibi ne da misalin karfe 5 na yamma jirgin su ze tashi"

Da sauri ta kalleshi kaman zata yi kuka tace
"Wai dama da wuri ne?"

Kai ya gyaɗa yanayinta gabaɗaya se ya sauya, yace
"Ki bar musu nasu ke ki haifi naki tunda dae kayan aro baya rufa asiri"

Yi tayi kaman bata ji ba, se ma tace
"kaman sallama ko?"

Fita yayi ta bi bayanshi aiko iyalan abokanshin ne da su kansu kasancewar Saturday ne, Fauza kaman ta san su kuwa tayi musu tarba na mutunci bata bar matan anan ba ta ja su ɗakin ta bayan sun gaisa da mazan suka mata sannu da jiki.

Yaran Faisal biyu mace da namiji matarshi hafsat da ciki, se na Jafar uku matarshi firdausi tana goyon na huɗu.

Ruwa ta gabatar musu da fruits suka sake Gaisawa sossai hafsa ke gayamata yadda Afnan ke kai mata labarinta nan suka ɓarke da hira kaman sun jima da haɗuwa, mikewa tayi ta fita musamman ta je ɗakin Fatima ta shaida mata da zuwan baƙin amma bata ko tanka ta ba.

Su ɗin sun riga sun jima suna son zuwa gidan Faizan ɗin saide Allah be yi ba ko da suka ji ya ƙara aure ma su suna team uwargidaye ne abun mamaki se suka ga Amarya ke ta ina za'a saka ina za'a aje dasu.

Abincin ta gabatar musu bayan sun yi sallah suka ci suka yi nak suna cewa ita da bata da lafiya ta iya yin girki haka, tana ta murmushi kawai.

Yini sur suka yi amma Fatima bata leko ba se gab zasu tafi ta fito suka gaisa kawai ta koma, Hafsat da Firdausi wayayyun mata ne kuma sun fahimci kishi irin na Fatima a take suka dau yi mata lecture da yadda zata karkatar da hankalin miji kanta ita kaɗai, kaman yadda Burin kowacce macece ace ta zama tauraruwa a gidan mijinta kuma sarauniyar birnin zuciyarsa.

Ta Haɗa su da turarukan wuta kuwa ta zubawa yaran snacks masu yawa da Faizan ya saya musu suka yi ta murna, har mota suka raka su suka tafi.

Juyowa Faizan yayi yana kallonta fuskanshi cike da murmushi na burgewa da jinjina yace
"Allah ya miki albarka"

Murmushi tayi tace
"Ameen"

A tare suka koma be zauna ba shi ya taya ta suka tattare gidan tsab, tana tsaye kitchen tana shirin wanke wanke kenan taji kamshinsa ya bule kitchen ɗin waigawa tayi se ta ganshi tsaye sanye da red riga marar hannu ta shan iska da ya bayyana damatsanshi da suke a murɗe se three quarter milk, hannayenshi zube a aljihun yana kallonta.

Maida kanta kawai tayi ga dauraye kwanukan kan ta zuba ruwan sabulu se ta nufi drawer don ɗauko lemon fresh da ta ɗaura shi chan sama sbd husna dake yawan son wasa dashi.

Hannunta ta miƙar har tana ɗagel don ɗauko wa kawai taji hannun mutum bisa nata, da sauri ta waigo se fuskanta ya kusan dukan kirjinshi sbd kusantota da yayi sossai, idanu suka zubawa juna na seconds kan yayi gyaran murya yana cewa
"Amm jikinki ba wani matsala ba?"

Fuskanshi na kusan kan nata sbd tsawo sossai da ya fita hakan ya sa ta kasa magana se da ya ɗan matsa baya kan ta saukar da kanta ƙasa tace
"Ai na warke"

Wani dogon tsaki da suka ji yasa duk suka kalli kofa, Fatima ce tsaye tana Kallonsu hawaye ne ke zuba a idanunta ta fara cewa
"Wallahi Allah se ya saka min, Allah baze taɓa barinki ba Fauziyya kaman yadda kika yi min kema Allah ya miki, kin zo kin sameni gidana ina zaune lafiya da mijina kika shiga tsakaninmu kika juye hankalinshi gabaɗaya to Wallahi ban yafe miki ba"

"Kai kuma" ta nuna shi.

"Allah kaima se ya bi min hakki na, watana biyar a gidanka ka kara aure, a wata biyar da nayi ban taɓa yin sati ɗaya cikakke da kai ba kana chan gobe kana nan amma tun zuwan Fauziyya gidan nan baka taɓa fita daga Kasar nan ba, kai ka ce min baka iya komai a harkar kitchen ba, zan iya rantsuwa baka taɓa shiga kitchen da sunan aiki ba amma yau gashi nan kana taya ta... A haka kake cewa kana min adalci Toh wlh ban yafe ba idan ina da hakki Allah ya bi min..."

Yadda take kuka duk suka tsaya suna kallo, kan Fauza ta taɓe baki ta nufi gaban kayan wanke wankenta ta fara wankewa, shi kuwa a natse ya isa gabanta ya sa hannu ya riƙe nata ya fusge ta suka fice be tsaya ko ina ba se Ɗakinta ya daka mata tsawa

"wai me yake damunki ne Fatima?? Me yasa bakya so kiga an zauna lafiya? Meyasa kika kasa sakawa zuciyarki salama? Kullum ƙorafi an yi miki kaza an yi miki kaza? Yanzu da zan yi baƙi ban taka har ɗakinki na faɗa miki ba amma me kika musu? Babu. da babu Fauziyya haka zan kunyata? Ke baki san zuru ba? To karki yarda ki kai ni bango ba zan lamunci wannan ba, ki sani na raba muku kwana jiya da yau kwanan ta ne gobe ke zaki ci gaba, kaman yadda bata sa miki ido a naki ba karki saka mata a nata bana son fitina... Kin gane ko?"

Kallonshi kawai take kaman bakonta tunda ta shiga gidan yau ne rana na farko da ya zage ya rufe ido yake ta mata faɗa Dukda ita har lokacin bata ga laifinta ba, son shi da take kawai yayi yawa shine laifinta, irin attention da yake ba Fauza da take so kawai shine laifinta?
Kuka take yi sossai tana jin kaman tayi hauka.

Lallai Mahaifiyarta bata kyauta mata ba da ta kwadaitar da ita Faizan tun bata gama sanin menene so ba, son shi yayi mata zurfi wadda bazata iya Daena ƙorafi ba in har akan wata macece.

Fita kawai yayi ya kyale ta.

Be koma kitchen ɗin ba se yayi ɗakinshi kawai, Fatima na da matsala abubuwa dayawa da tayi tayi a farkon aurensu se yanzu yake ganin rashin dacewarshi ko dama sbd ita kadai ce kuma he was new in the system yasa be gani ba amma yanzu duk asalin halayyar ta kishi ke hankaɗosu.

Har dare ma be sake haduwa da kowaccensu ba, se da ya dawo isha ne ya shiga ɗakin Fauza itama ganin ranshi har lokacin ba'a sake ba yasa bata ce komai ba ta gabatar mai da abinci da tea ɗinshi.

Yana Ci ya dube ta yace
"gobe zan koma wurin Fatima pls idan tayi kwana biyu ki cigaba da naki and ki dinga ajiye mana a dining zamu ke haɗuwa muna ci mu duka that should be the policy"

Tace
"Toh"

Yace
"jibi da safe zamu tafi yiwa Husna shopping"

Ta amsa
"Allah ubangiji ya kaimu"

Ya so ya kawo maganar waya don Jafar ya kirashi wai matarshi na son layin Fauza don sun manta basu yi exchanging ba se kuma ya fasa don har yanzu be jin ze iya saya mata waya tukuna.

Ranar dae kam kowa ɗakinshi ya kwana, tayi kwanciyarta da husna.

Sunday ma ya ɗan yi short tafiya kwata kwata basu haɗu ba se dare shima abinci ya ci wadda Fatima ne ta karɓa tunda yamma ya riga ya shiga, saida ya tabbatar basu da wani matsala kan ya wuce room ɗinshi Fatima ta bi bayanshi Fauza kam ko a jikinta ta kama husna suka yi ɗakinta.

Washegari Fatiman ce tayi breakfast itama tayi wanka ta shirya cikin Atampha dinkin bubu, sanye da kaftan dinkin zamani ruwan ƙasa ya fito, ya haɗu har ya gaji.

Itama Fauza Abaya ta saka milk and brown tayi kyau sossai barin ma ɗan face ɗinta da ya fita a Tarhan da tayi, ta gaishe shi kan ta gaida Fatima a dakile ta amsa, baki Fauza ta taɓe tare da serving husna tayi serving kanta tunda Fatima tayi serving mijinta ne kaɗai.

Quitly suka ci abincin Dukda ita kam Fauza kaɗan taci ta miƙe ta koma parlor tana jiran shi.

Kallon Fatima yayi yace
"Am kin kuwa san yau da yamma husna zata bi iyayenta?"

Kai ta girgiza tace
"ban sani ba tunda babu wadda ya faɗa min"

Kallonta yayi kaman ze yi magana se kuma kawai ya fasa, ya lura harshen Fatima ba a kame yake ba Sam bata san yadda zata ke mai magana ba.

Mikewa yayi yana goge bakinshi da tissue hannunshi rike da husna suka fito parlorn yace
"mu je ko?"

Mikewa Fauza tayi Fatima tayi saurin cewa
"Ina zaku? Ko ka manta kana cikin girki na ne?"

Yace
"don ina cikin girkin ki se aka ce ba zan fita da fauza ba? Ko ke kika ajiyeni da dole se kin san duk inda zani?"

Fauza dae bata ce musu komai ba ta kama hannun husna suka nufi ƙasa.

Yace
"yarinyar nan husna kaman yadda take ƴa a wurin mu haka kema amma ko kallon arziki da mutunci ba zan ce ya taɓa hada ki da ita ba, ina faɗa miki zata tafi yau amma me? Kina wani bada amsa cikin gatse to in miki yaya kike so?"

Yana kai nan ya nufi gangarawa abunshi.

A gaba ya samu husna ita tana zaune baya ya ja motar suka fice, shopping sossai suka yi mata tana ta basu dariya da hirarrakinta, they all enjoyed the moment Har azahar don Fauza bata da lectures kan suka biya suka ci abincin rana a yadda Fatima ta gayamai bazata dawo ba se huɗu tun jiyan yasa be ma tuna wani jira ta koma ta mai girki ya ci ba.

Daga nan suka yi gida Fauza ta haɗe mata kayan tsab.
Sam Faizan be so ta koma ita ɗaya ba amma baze iya kaita ba don akwai tafiyar da ze yi Tuesday da safe kuma ze yi 2-3 days.

Da farko ya tuna ko su je da fauza sede bata da visa, ko international passport be yi tunanin tana da shi ba, Seda suka yi la'asar kan suka fito suka tafi Airport... Suna tsaye wata cabin crew ta iso a shirye cikin irin shigar sun nan bakinta ya ji hot red lipstick se yanga take yi..

"Sir good evening"
Ya amsa fuskanshi ba yabo ba fallasa yana nuna mata husna yace
"she's my niece nd she will be flying with you guys pls take good care of her"

Ita ce shugabar crew ɗin na yau hakan ya sa yake bata amana kuma sun san shi bashi da wasa, baya shiga harkarsu idan har ba maganan aiki bane, gasu Allah ya ɗaura musu maitarshi da kwaɗayinshi, a yangance tace
"Worry not sir, we will make sure we give her all the care and attention from the boarding to departing"

Yace
"Good"

Fauza ya kalla se yaga duk fuskanta ba fara'a kaman ɗazu, ya san duk kewar Husna zata yi, dukawa tayi tana rike da hannun husna take ce mata ta gaida kowa da kowa in ta isa.

Kaman kar su Rabu haka tayi ta ɗaga musu hanu seda suka bace kan Fauza ta fara sauke hawayen da take rikewa dama bata son yin kukan ne sbd husnan.

Kawai ji tayi lallausar hannunshi ya shiga cikin nata yana matsewa a hankali alamar rarrashi.

Zare hannunta tayi suka nufi mota, har suka isa gida bata ce mishi komai ba kewan husna duk ya dameta, hakan ya sa suna isa ya je ya duba wayan nan ya bata akan ta kira su jadda.

Ɗakinta ta shiga ta kira su kuwa sun jima suna ta waya har Amminta ta kira suka gaisa saide bayan nan bata ce komai ba ta kashe wayan, tsintar kanta tayi da gwada saka layin sakina ta kira, ringing na karshe ta dauka
"Ke! Fauza ce"

Ihu sakina ta saki tana cewa tana ina ne a Abujan? Sun yi ta neman layinta shiru wannan ne sabon layinta? Tace na mijinta ne.

Rahama ce ta karɓa take ce mata Zubair ya kusa haukace musu akan ta kuma har yanzu be hakura da neman location ɗinta ba har fa cewa yake ze kai su baba court sbd an mata auren dole.

Dariya tayi tace
"Zubair kenan"

Sam bata san ya shigo ba se ji tayi ya zare Wayanshi daga hannunta yana yi mata wani irin kallo kan ya juya a fusace ya fice yana buga kofan da karfi...

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤



27

Ba karamin tashi hankalinta yayi ba ganin yadda ya fita a mugun fusace..
"Innalillahi wainna ilahi rajiun na shiga uku! Yanzu me ze yi tunani?"

Ta furta tana mikewa tsaye, bata taɓa jin buƙatuwar wani ya fahimce ta ba kab rayuwarta se yau, ta san yanzu Fatima ta riga ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login