Showing 42001 words to 45000 words out of 86608 words

Chapter 15 - DIDDIGAR ƘAYA COMPLT Hausa novel

21 Aug 2024

18449

ya sani wasu be sani ba, daga yanayin hotunanshi zaka san yana da zafin kai don kusan duk babu wadda yake cikakken dariya banda na fuskan wayan.

A kan wani ta tsaya wadda aka dauke shi be sani ba shima da uniform ɗinne hannayenshi rike da abun tuka jirgin kunnenshi sanye da headphones ɗinsu ya ɗan wai go kaman ze yi magana ne aka ɗauka ba karamin kyau yayi ba.

Scrolling tayi ta wuce se taga hotonshi da Fatima, Fatiman ce ta ɗauka kwance a jikinshi kaman a wani wurin shakatawa ne, se wasu a bakin ruwa wadda ba tantama Legos ne don ta san chan ne kaɗai za'a samu beach haka, yana sanye da kananun kaya tana sanye da wasu hoodies orange, baki ta taɓe zata wuce se wayan ya ɗauki ringing.

'My number' ta ga an saka, to wani number kuma? Har wayan ya kusa katsewa kan tayi kundunbala ta ɗaga
"Fauziyya... Ina ta kiran Fatima bana samunta ki fita ki kama mata aiki su Faahim zasu kawo mana yini da yaran nima Ina dawowa nan ba da jimawa ba"

Kusan rikicewa tayi da sauri kuma tace
"Toh"
Kashe wayan yayi ba tare da ya sake furta komai ba.

Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke...a fili ta maimaita sunan nata
"Fauziyya.."
Sai de bata ji ya mata kaman yadda shi ya kira ɗin ba don har faɗar mata da gaba yayi.

Tuna su Ya fadyaa ne zasu zo yasa tayi saurin mikewa ta fito parlorn saman babu motsin Fatima don haka kasa tayi, ba wai tana tsoron Fatima ne yasa bata shiga kitchen ɗin saman ba, kawai tana tsayuwa ne limits ɗinta gudun fitina da tadawa iyayenta hankali, Allah kaɗai ya san yadda zuciyarta yayi haske da taji yadda suke farin cikin da jinta ba kaman da da a duk sadda za'a kira sunanta se gabansu ya fadi ba.

Abinci ta fara Haɗawa me rai da lafiya, Allah ya sa ma komai za'a kawo gidan a gyare ake kawo shi kuma cooker ɗin me kai har shidda ne a take ta Haɗa pineapple rice kamshinshi duk ya cika kitchen ɗin, bayan ta gama ta yi mishi pepper chicken, tayi grilling fish manya guda biyu se ta Haɗa zobo, karfe sha ɗaya da rabi lokacin kuma har lokacin bata ji motsin Fatima ba.

A dining na sama ta shirya su kan ta shiga ɗakinta tayi wanka, ta sanya wani material lace riga da skirt yayi mata kyau sossai ta fita shar da ita, lip gloss kawai ta shafa ta ɗaura dankwali harda sarka da abubuwan hannu ta saka.

Daidai lokacin take jin shigowar mota, farin ciki sossai ne ya ratsa ta yau zata kalli mutane, mutane su kalleta ko da basu wani yi shiri da ya fadyaa ba sbd rashin jinta yayarta ce uwa ɗaya uba ɗaya tana son ta kuma har ranta kaman yadda take jin sauran en uwanta

"oyoyo"
Ta faɗa tana rungume ya fadyaa, ya fadyaa ma na murmushi tace
"oyoyo Fauzan jadda, masha Allah.. Kin ganki kuwa?"

Da gudu yaranta biyu Asma'u(husna) da Sameer suka zo suka rungumeta suna mata oyoyo, cikin jin daaɗi ta tarbesu, tana cewa ya Faahim
"sannu da zuwa yaya Faahim"

Yace
"uhm karki yi ya Faizan ya jiki ni yanzu ƙani nake, Aunty Fauxan Jaddah yauwa sannunki"

Dariya duk suka yi ta musu iso ciki dukkansu biyu kallonta suke yadda ta sauya, a parlorn sama suka baje suka fara Gaisawa ta kawo musu ruwa da fruits.

"Ina Fatima ne naji gidan shiru"
Fadyaa ta tambaya.

Fauxa na barewa husna lemon ɓawo tace
"nima fa tun safe bamu haɗu ba kilan tana ɗaki kila kuma ta tafi school"

Bayan ta bata ta dubi ya fadyaa tace
"ya fadyaa tun fa wanchan sati Jaddah tace min zaku dawo shine baku zo ba har se yau"

Ya Faahim yace
"ba gashi mun zo ɗin ba dae, Ya Faizan ya ce ya shiga wurin Faisal ko?"

Tace
"eh ya de ce gashinan zuwa"

Kallon juna Faahim da fadyaa suka yi suna gulma, yadda ake zaton jin hayaƙi a gidan Faizan ba haka ba, ashe igiyar aure na natsar da mutum?

"Kinga muna ta shirin tafiya ne zan ga Dr shi kuma ya Faahim ze yi wani course to har yanzu visa ɗin husna ne bamu samu ba gashi ma lokaci na ta tafiya"
Cewar Fadyaa

"ai na ce miki mu hakura mu barta wurin su mammi kin ce za'a kara mata dawainiya ga rashin lafiya"
Cewar Ya Faahim

Fauza tace
"to don Allah ni ku bar min ita kan ku je ku dawo Allah zata debi min kewa dama zaman kaɗaici ya isheni"

Zaro idanu fadyaa tayi tace
"Fauza rufa min asiri da mijinki..."

"Me mijinta yayi ne?"
Faizan ya faɗi yana shigowa cikin parlorn, duk ɗago idanu suka yi suna Kallonshi...

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤


19

"Ayya don Allah yaaaya su bar mana ita anan pls!"
Yadda tayi maganar yasa dole ya kafeta da idanu yana kallonta, ta wani narke fuska se yaji wani abu ya mitsini zuciyarsa, ya lumshe idanunsa ya buɗe.

"Da nan ɗin da wurinsu duk ɗaya ne tunda mu ma iyayenta ne"
Ya faɗa yana zama, da kallo ta bishi babu laifi ta fahimci guy ɗin ta ko ina ya haɗu, komai nasa me kyau ne, kuma ko wani irin sutura ya sa ta kan zauna daidai da tsarin hallitarsa, ɗauke kai tayi ganin ze kalleta ta dubi husna tace

"zamu zauna ko husna?"
Kai yarinyar da bata wuce six years ba ta gyaɗa tana dariya.

Su fadyaa ma fuskansu cike da murmushi Alhamdulillah ko gobe ne yanzu kam zasu iya tafiyar su, Gaisawa suka yi da Yayan nasu, kiran sallahn azahar ya sa mazan suka fice sallah yayinda su kuma suka shige ɗakinta bayan sun yi sallah fadyaa ta dube ta tace

"Fauza ba wani matsala ko?"

Fauxa ta ɗan yi kasa da kai kan ta ɗago tace
"ya fadyaa dama can kin san ni da Fatima Bama shiri to dae har yanzu bata sauya zani ba, ta ɓangaren shi kam ba wani matsala, matsala ta ɗaya ne"

"Uhm"
Fadyaa ta faɗa jin ta ɗan yi shiru

"me yasa nake jin Ammi ta sauya min daga wacce na sani? Meyasa bata so na zauna lafiya a gidan nan kaman yadda kowa ke buri? Duk yadda zan duba na kasa fahimtarta Ya fadyaa"

Shiru fadyaa tayi na mintuna har saida Fauza ta sake kiran sunanta ganin fuskanta ya bayyana damuwa tace
"Fauza babu abunda zan iya ce miki saide kiyi haƙuri da ita, uwa ta wuce gaban wasa amma ina me tabbatar miki ni kaina tun daga randa na amsa auren ya Faahim Ammi bata sake sakarmin fuska kaman yadda take yiwa su Fadeela ba, ban sake jin daaɗinta a matsayin uwa ba, ban sani ba ko tsanar da take yiwa Mammi da ahalinta ne ya shafemu ko yaya"

Ajiyar zuciya Fauza ta sauke gaskiya halayyar Amminta na ɗazu ya dameta, jin motsin mazan yasa suka miƙe suka fito.

Yana kallonta yace
"Fatima fa?"

Tace
"bari na duba ta"

Karasawa kofan ta tayi tayi sallama shiru tayi knocking sau biyu shiru, juyowa tayi ta kalleshi shima ita yake kallo kan ta murɗa kofan da nufin shiga sede a rufe yake ruff da makulli.

"Baki faɗa mata sakona bane?"

Tace
"ban ji motsinta bane shiyasa"

Wayanshi ya fiddo yana shirin kiran Fatiman yayinda ita kuma tayi dining ta fara kwaso abincin tana kawo su tsakiyar parlor, gabanshi ne ya faɗi kardae ita ce ta kwaba musu abunda zasu ci? Ai da bari ma tayi ya saya a waje tunda bata samu Fatima ba da jagwalgwalontan nan. Amma kuma ina Fatima ta tafi ba tare da ta sanar dashi ba?.

Jin wayan na shiga ya sa ya tashi ya wuce ɗakin shi don kar su ji tambayar da ze yiwa Fatiman sanin ba girman shi bane taya za'a yi mace ta fita babu izinin miji?

Ita kuwa bayan ta gama ta kwaso plates da spoons da forks haɗe da tissue ta kawo, babban warmer me ɗauke da pineapple rice ɗin ta buɗe a take kamshi ya cika su nan ta ɗauki plate zata fara serving kawai taji hannunsa mai azabar sanyi da taushi cikin nata.

A razane ta ɗago se suka Haɗa idanu ya kauda kai yana zare serving spoon ɗin yace
"kama wani let me help with this"

Janyewa tayi tana jinta wani iri, basarwa yayi ya fara serving yana kawowa Faahim Hirar aikinshi da kusan akan zancen jirgi ne tunda shi Sojan sama ne.

Miƙewa tayi ta sauka kasa ta samo silver tray me Adon gold ta fidda zobon da ta yi ta ɗaura a kai ta jera cups ɗin jug ɗin a gefen tray ɗin kan ta dawo ta ajiye musu fadyaa na mata sannu.

Kifin ta yaye wa foil paper da ta Naɗesu dashi, shi kuma yana sanyawa kowa pepper chicken ɗin, fadyaa na kallon su da burgewa don ba karamin kyau suka mata a taren ba.

Bismillah yayi duk suka sauko, zuciyarshi dae a tsinke kar su sha kunya ya ɗibo abincin a spoon ya kai bakinshi.

Lumshe idanu yayi se ya buɗe a kanta maganganun su da su Faisal ɗazu a office ɗin Jafar ne ya dawo mishi.

Bayan ya sauke wayanshi a sadda ya faɗa mata su fadyaa na zuwa Faisal yayi dariya yana cewa
"kaga mijin mata biyu cikin wata biyar ba... Kai fa kana morewa ba'a fita a angonci ba an sake dulmiyawa sabuwa dalll me sirrin ne?"

Tsaki yayi yana furta
"kanku ake ji"

Jafar yace
"kaima za'a ji naka ne a sadda ka shiga hannun Fauza"

Wani dariya yayi na baka da hankali yana dawo da kwakwalwar shi baya wurin Tunanin suffar ta da har za'a ji kanshi, a ganin da ya mata na ɗakinshi, da ganin da yayi mata randa aka kawo ta ya san kwarai tana da cikakkiyar siffa da sura, abunda kuma ke kashe shi ba ƙarya sune idanunta waenda baya jurar kallon cikinsu ba tare da yaji wani yanayi da be san menene ba, ba karya yarinya ce me cikakkiyar suffa da daradaran idanu, hotonta rungume da Zubair a elevator ne ya dawo mishi wadda ya saka shi saurin kau da Tunaninta yana sakin tsiririn tsaki.

"Ya dae angon mata biyu? Yaushe ne za'a gayyacemu cin abinci ne kaga dae tun kawo Fatima kake mana haka haka, matar Faisal har ta haihu muna gari ɗaya baka bar matarka ta zo ba"
Cewar Jafar

"sannan ka manta Fatima tana rashin lafiya ne? Bari na zo na tafi kar baƙin mu su zo bana nan, amma karku damu kanku in shaa Allah nan kusa zan gayyaceku cin abincin ku maida kwalamarku Mayu kawai..."
Yana kai nan ya nufi kofa

Dariya suke yi Faisal yace
"eh mun ji, wlh ko me zaka faɗa se mun zo mun kwashi gara ah to"

Yana murmushin zancen ya karasa mota ya shiga ya dawo gidan.

Boyeyyen ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda take ta ba husna abinci a baki suna hira da dariya da yarinyar, ta bashi tsananin mamaki guda biyu a yau

Na farko be taɓa kawo zata girka abincin da ya kai wannan daaɗi ba don ze iya rantsuwa bayan abincin mammi be taɓa cin abinci me daaɗin wannan ba, se kuma abu na biyu yadda ta tarbi su Faahim be taɓa zaton tana son mutane har ta ja su a jiki haka ba duba da yadda duk inda ta zauna se an samu hatsaniya da ita, kannenta karan kansu ba son zama kusa da ita suke ba don masifa da saurin hannu amma ji ta yadda take yi da su fadyaa ko don ta kwana biyu bata ga mutane bane?

Har suka gama cin abincin suka cika cikinsu da zobo be Daena mamaki ba, tattare kayan suke ita da fadyaa da ta mike tana taya ta suka yi kasa suka Barsu su biyu, don yaran sun biyo bayansu, wanke wanke Fauza ke yi fadyaa na daurayewa suna ƴar hira tsakaninsu.

Sun gama suna shirin haurawa saman kenan se ga Fatima, sake fuska tayi tace
"ya fadyaa kune a gidan ashe?"

Fadyaa tace
"eh wlh Fatima mun zo kin fita"

"eh na ɗan je na ga doctor na ne, Alhamdulillah kuma da sakamako me kyau na dawo"

Fadyaa na murmushi tace
"masha Allah, Allah ya jishe mu alkhairi"

Dukda ta so Fadyan ta tambayeta menene don ciki ne da ita na sati biyu kachal amma har ta bazawa mutane tana faɗin a taya ta da Adu'a, wai ko Adu'a ne ba'a yiwa cikin yasa baya zama ga saurin conceiving da take dashi.

Duk haurowa suka yi kanzil be Haɗa su da fauza ba, ta gaida Faahim ta shiga cikin su ganin Faizan be nuna komai a fuska kaman yadda ya Rufeta da faɗa a waya ba.

Har suka yi la'asar a gidan still Fauza taje ta dafo musu shayi sak irin wadda mammi kan yi mishi itama kuma wurin jadda ta koya don Baba prof na matukar so kaman yadda shima yake so, be taɓa sanin ta iya something like this ba, ya sha shayin sossai don kusan abunda yake matukar kewa kenan a duk sadda aka ce yayi nisa da yola.

Se dab magrib suka rako su zasu wuce Dukda Fauza ta so su zauna se dare amma akwai inda Faahim ze je kuma ze iya kai dare sossai shiyasa ba zae Barsu yaje ya dawo ba, husna kam kin bin su tayi Fauza na murmushi tace
"yauwa ƴar gidana, ya fadyaa ku hado driver kawai da kayanta pls"

Duk dariya suka yi ganin yadda take ta murna daga ita har husnan, sallama suka yi musu suk fice da nufin za'a aiko mata da kayanta.

Tun a parlorn kasan Faizan ya dubi Fatima yace
"Ashe kina fita daga gidan nan ba tare da izini na ba? A iya sanina baki da lectures yau kuma na barki kina bacci"

"Yaya kayi hakuri wlh bayan fitan ka ne amai da juya ya matsa min nayi ta kiran ka kuma ban sameka ba shine na tafi ganin likita"
Ta faɗa a marairaice.

"Amma ya kamata ko Fauziyya ki sanarwa da zaki fita ba wai kawai ki fita kiyi tafiyar ki ba"

Ta Yi saurin cewa
"da ka dawo bata gaya maka ba? Na fa ce mata in ka dawo ta taimaka ta faɗa maka wallahi"

Fauza da tayi nisa a kan stairs ta dakata tare da juyowa da mamakin rantsuwar da Fatiman ke yi a kan karya, ganin kallon tuhumar da yake aika mata yasa tace
"kayi hakuri mancewa nayi"

Daga haka bata tsaya ba tayi wucewarta, a ɗakinta suka yi sallah da husna nan suka shiririce a kallo tana kuma sauraran surutun husna don husna akwai aikin surutu.

A ranar dae ba'a samu an kawo mata kayanta ba se wani shirt nata dogo ta sanya mata ya kuwa zauna mata suka je kitchen suka dafa pasta ɗan kaɗan a ƙasan suka ci kan suka hauro sama zuwa ɗakin Fauza..

Har sun yi shirin kwanciya don tana sanye da pjamas fari me layi layin baƙi me yauƙi wando da riga ya zauna mata sossai kanta ba dankwali tana kara kakkabe musu shimfiɗa ya shigo da sallama.

"Oyoyo uncle"
Husna ta karasa ta rungume shi

"oyoyo babyn uncle"

Hannunta ya kama suka zauna ya ɗan kalli Fauza da ta gama gyara gadon ta zauna daga baki tana wasa da nails ɗinta yace
"kin ci abinci?"

Kai ta gyaɗa tace
"Aunty Fauza ta yi mana pasta me daaɗi mun ci, it was so yummy uncle kaima ka ci ka ji ko?"

Girgiza kai yayi yace
"ban ci ba baby husny amma zan ci"

"babu wata matsala ko?"
Ya jefa tambayar ga Fauza.

Kai ta girgiza tace
"babu"

Sakin hannun husna yayi yace
"OK, baby go nd sleep karki manta da Adu'a"

Tace
"ok uncle"

Da gudu taje ta hau gadon ta zauna tare da Haɗa hannayenta wai tana Adu'a, murmushi duk suka yi na wayon yarinyar.

Miƙewa yayi ya sanya hannunshi duka biyu cikin aljihu yace
"madam ina wayata?"

Tace
"oh, yi hakuri ina ta zuci zucin baka na mance"

Tahowa tayi wurin kujerun ta ɗauka a inda ya tashi ta san ya gani ko me ya hana shi ɗauka se ya sakata zuwa ɗauka ta mika mai hanu da hanu oho mishi.

Karɓa kawai yayi ya juya, kaman tace mishi saida safe amma tana tsoron dizginshi har ya fice ta rage wutan ta dawo ta hau gadon ta kwanta tare da lumshe idanu tana tuna yinin ta na yau, se kuma ta tuna bata goge hotunan da ta ɗauka ba, ajiyar zuciya ta sauke tare da taɓe baki ta gyara kwanciyarta.

Shi kuwa yana komawa ɗakinshi Fatima na shiga da shirin bacci, farin takarda ta mika mai tana murmushi, karɓa yayi ya buɗe a take shima fuskanshi ta cika da murmushi Dukda be kwallafa rai ba sanin cikinta baya zama amma shima yana son ganin gudan jininshi kaman yadda kannenshi kusan duk suke da nasu.

"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah ya sa wannan me zama ne fatee"

Tace
"in shaa Allahu Ameen"

Nan ta zauna tana gayamishi yadda Dr yace ta kula da cikin don kar a samu matsala, bayan ya gama sauraron ta ta kwanta shi kuma ya zauna tare da jingina bayanshi da gadon airpod ne a kunnenshi take ya shiga wani wuri a wayan yayi connecting ya sake komawa wani wuri ya fara duba voice recording guda biyar da ya gani.

Ba wai yana ghosting ɗinta bane, kawai natsuwarshi har yanzu be kama a kanta ba yana tsoron halinta na baya sossai shiyasa ya zame mishi dole saka idanu a duk al'amuranta.

Wayansu da jadda ya fara saurara, sossai yayi murmushi jin yadda suka drama a kanshi, yadda Fauzan ta zage take ta bada jawabi akan duk abunda jadda ta faɗa mata an yi a gidan yayi ta bashi dariya, bayan ya gama ya saurari nata da mammi, kaɗan yaji darajarta a zuciyarshi jin duk ta yadda mammi ta so taji laifinshi daga gareta ta tare.

"Ashe tana da hankali"
Fatima da ta fara bacci tace

"Na'am?"

Yace
"no yi baccinki maman baby"
Murmushi tayi kan ta sake runtse idanu cikin jin daaɗin sunan da ya kirata dashi.

Shi kuwa cigaba da sauraron Hirar ta yayi da Baba prof,, ya san tunda baba prof yace hakan dole ze fara mata shirye shiryen makarantar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login