Showing 78001 words to 81000 words out of 86608 words

Chapter 27 - DIDDIGAR ƘAYA COMPLT Hausa novel

21 Aug 2024

18456

wani cotton blue shiffon shirt da straight skirt baƙi se ta ɗaura black dan kwali a kanta, se kamshin khumras na sabon gyaran da Jaddah ke mata take zubawa, fitowa tayi ta shiga kitchen ta samu zaliha na yin kosai da koko, baki ta taɓe ta warware gyalen da ta ɗaura a kanta se ta yafa ta fice daga sashen.

Har ta nufi sashensu se ta juya ta nufi na mammi don tun shekaranjiya rabon da su haɗu ta aiko mata da kifi dafaffe ma da rana bata je godiya ba kuma kila abunda ta dafa se ya fi na jaddar nan daaɗi.

Da sallama ta shiga parlorn, Mammi na zaune tana karyawa itama maraba tayi mata fuskanta cike da fara'ar ganin surukar tata, zama tayi suka gaisa sossai kan mammi ta mata umarni ta isa akwai abincin a dining ta ci abin ta.
Tsam ta mike tayi dining ɗin ta diba kuwa me ɗan yawa ta fara ci a hankali.

Sam bata san mammi har ta gama ta mike ba ma, fitinannen kamshinshi da ya cika wurin ne ya sakata saurin ɗagowa se suka Haɗa idanu, da sauri ta ɗauke kanta ta mayar kan abincin ta da idanu ya bi abincin na seconds kan ya samu wuri ya zauna ya miƙe kafafunshi ya zuba mata idanu yana kallo.

Kasa cigaba da cin abincin tayi, se kawai ta miƙe da niyyar barin wurin kafa ya sa mata tayi gaba zata faɗi yayi hanzarin janyo hannunta se gata bisa kirjinshi, rungumeta yayi da kyau a cikin kunnenta ya raɗa..

"Ke kam baki san haƙuri bane Fauza? Pls kiyi hakuri mu koma gidan mu hakanan wallahi na miki alkawari ba zan ƙara yi miki komai ba idan har ba da yardar ki ba, am so sorry bisa duk abunda suka faru ki yafewa mijinki kin ji?"

Bata ce komai ba se kokarin tashi da take, ya kara matse ta cike da masifa ta fincike bata ce komai ba ta juya zata fita, she's killing him da wannan shirun wallahi..
"I'm hungry ki sama min wani abu please"

Bata juya ba ta fice, sashensu taje suka gaisa da mammi kan ta koma sashen Jaddah, Jaddah na zaune a parlor ta mika mata wani cup da wani haɗi ciki karɓa tayi sbd yadda yaji madara da zuma ta zauna ta shanye tass ta ajiye kofin, Jaddah tace
"Fauza ki shiga kitchen ki sama ma mai gidanki wani abu duk abunda aka yi a sashukan biyu ba ci yake ba shima"

Baki ta tura tace
"me zaliha ke yi Jaddah?"

Jaddah ta mata dakuwa tana cewa
"zaki ci ƙaniyarki fa Fauziyya wai aka gayamiki zuba miki idanu da aka yi tsoron ki ake? Ki zauna kina Jawa mijinki aji mijin ma irin Faizan dake da matukar wahalar samu, wata macen na kyalla idanu ta kwace shi tsab ki zo kina min kuka wlh se na lahira ya fiki jin daaɗi, a kanki aka fara samun irin wanchan matsalar a da da se an dauko mu a ka a kaiwa miji a kullo kofa, to karki kiyaye ni kiga.."

Bakinta kaman ze taɓa gini ta miƙe ta wuce fuu zuwa kitchen girkin take sede ba da wani armashi ba, da gangan sbd ta san be son yaji kwata kwata tayi girkin da zallar attarugu ta saka a plate ta ɗaura a tray bayan ta rufe ta ɗauko ta fito ta ajiyewa Jaddah

"To wa ze kai mishi? Kin dae san Zaliha ta wuce kasuwa"

Sake ɗauka tayi Jaddah na kallonta har ta fice kan ta taɓe baki tace
"Zaku ji dashi dukkanku biyu wlh"
Don shi ya zo ya roki Jaddah da ta saka ta yi mishi girki please Allah yayi kewar taste ɗin abincin ta.

Da sallama ta tura ɗakinshi fitowanshi daga wanka kenan se lokacin ta tuna haduwar da suka yi a sashen Mammi da kananun kayan shan iska ne wando three quarter me taushi da kuma riga marar nauyi, ɗaure yake da towel iya kugu, saurin ɗauke kai tayi ta karasa gaban center table ta ajiye tray ɗin zata juya..

Sam baya so ta fice da sauri yace
"serve me please"

Dawowa tayi ta buɗe plate ɗin kawai ta sanya mishi spoon don ba'a wani coolar ta saka ba, ta wuce frigde ta dibo ruwa ta zo ta ajiye mishi daidai lokacin ya zauna ba tare da ya damu ya saka kaya ba Dukda Acn da yayi yawa a ɗakin zafi yake ji kasancewar damina kilan a samu ruwa zuwa jimawa don zafin yayi yawa.

Se ta tsinci kanta da kasa tafiya ta tsaya tana kallon abincin gabanta na faɗuwa, don ta san yadda yaji yake wahalar dashi.

"Yaaa...ya"
Da sauri ya ɗaga kai ya kalleta tace
"Karka ci"
Ta matso tana shirin ɗauke plate ɗin ya riƙe hannun ya kalleta sossai kan ya kalli abincin se ya lumshe idanu kan ya kai baki, wani irin radadin yajin da ya ziyarci kwanyarshi ne ya saka shi saurin kallonta ita kuma ta runtse idanu tana jin wani tashin hankali na bijiro mata.

"Idan har wannan shine hukunci na precious pearl na karɓa, zan ci har se kin ji hukuncin ya miki daidai da muradinki"
Yana kai nan ya cigaba da ci abunshi Dukda yadda yake jin kaman harshen shi ze tsinke, idanunshi a take suka rine jijiyoyinshi suka tattashi, a hannunta take jin yadda jikinshi ya ɗauki rawa don Allah yayi shi yaji ba abunshi ba gashi yana da masifaffen ulcer..

Ze kai cokali na uku tari ya sarƙe shi, numfashin shi na fita babu daaɗi hakan kuma ya sake diba ze ci da sauri ta buge spoon ɗin tana zub da hawaye...
Kokarin ɗaukar spoon ɗin yake tayi saurin jan gabaɗaya table ɗin ta maye gurbin table ɗin gwiwowinta a ƙasa ta ɗauko ruwa ta mika mishi a rikice tana cewa ya sha yana ture hannunta.

Tuna yadda suke tafe cikin ruwa ya yafa mata designer suede ɗinshi yana kare mata ruwa shi kuma ruwan na dukanshi amma kaman be damu ba har zuwa cikin gida tayi, ta kuma tuna yadda ya kula da ita a sadda bata da lafiya Dukda a lokacin ranshi a ɓace yake da ita, ta tuna yadda a duk sadda take neman taimako shine mutum na farko dake kawo mata ɗauki he's her life savior, meyasa don ya mata laifi cikin rashin sani zata azabtar dashi ta wannan hanya, shin shi kaɗai ne yayi mata irin wannan zargi cikin rashin sani? Meyasa bata hukunta kowa ba se shi...

Faɗawa jikinshi tayi tana kuka tana cewa wlh ta hakura ta yafe mai yayi haƙuri, kankameta yayi idanunshi a runtse ganin har lokacin ruwan yaki ya dawo dashi daidai kawai tayi saurin haɗe bakinsu, kaman jira yake ya cabke yana jin his life depend on that yana saketa yaji ze ji, sanyin tongue ɗinta na ratsa dukkan sassan jikinshi a hankali ya fara dawowa hayyacinshi...

****

Kwano me ɗauke da tuwon datsan masara da wani bakin miyan kuka banda daddawa da gishiri babu abunda ke ciki da aka dangwalar musu ya saka Fatima rushewa da kuka tana kallon Aunty da fuskanta ke a kumbure sbd ciwon kai da ya matsanta mata tunda aka yi wannan hatsari tana cewa
"Wallahi na gaji Aunty, na gaji da wannan cimar dube ni fa, dubi yadda jikina ya fara komawa tsabar yunwa da talauci, ni dae Allah ki san yadda zaki yi dani ki kwatanta min inda zan je na samu maganin damuwata..."

"Fatima gwara dake kina iya cin abincin dube ni, babu abunda ke shiga cikina, bakya tausayina? Dubi yadda fuskata ta kumbure baki maganan muje asibiti a duba ni se wani maganan Faizan chan..."
Aunty ta faɗa a wahalce

"ni duk babu ruwana da wannan, ko ki nema min mafita ko in koma gidan mahaifina nima in barki ki fama da naki iyayen... Ba zan iya ba wallahi"

Da kyar Aunty ta sakata amincewa zasu je su ga likita, suka shirya da kafa suka je wani asibitin gomnati, sun sha wulakanci kam su da suna zuwa asibiti za'a karɓe su hannu bibbiyu se gashi cleaner ma na asibitin na zagin su, test aka bata bayan sun yi, tashin hankalin da ya ziyarcesu a sadda suka ji sakamakon result ɗin Allah ne kaɗai ya sani.

Ciwon daji ashe take dashi gashi an mata allurai a sadda tayi hatsari shine mafarin hauhawar ciwon. Tashin hankali wacce ba'a sanya mishi rana...

***

Jin yana shirin zarcewa wani babin ya sakata janye jikinta idanunta a ƙasa, hannunta dake cikin nashi take shirin zamewa yayi saurin sake gimtsewa a hankali ya buɗe idanunshi da suka birkice yace
"Fauzaaaa...!"

Ya kira sunan murya a sarƙe, bata iya ta kalleshi ba ta amsa a hankali, yace
"kin yafewa yayanki? Kin huce?"

Shiru tayi kan ta ɗaga kai a hankali, mikewa yayi ya taka ɗaya ya haɗe kirjinshi da bayanta ya sanya hannu ya zagaye kirjinta a kunnenta ya raɗa mata
"thank you wifey! Thank you so much... I LOVE YOU"

Shiru suka yi a haka na sama da mintuna biyar kan a hankali ya saketa, bata iya Kallonshi ba ta fice da sauri tana jinshi yana cewa ta shirya gobe da safe zasu wuce..

DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰

Karku sake a baku labari.


🖤Gureenjoh🖤

https://chat.whatsapp.com/BjpWJdHnjtpKNK4iCeqNwh



34

Washegari

Kaman yadda ya faɗa da safe ya fito a shirye, sashen Ammi ya fara zuwa suka gaisa sbd weekend ne su baba ma suna gida, ya jima sossai anan kan ya musu sallama ya nufi sashen iyayenshi suma duk ya musu sallama akan zasu wuce yau, duk Kallonshi suke da mamaki saide basu ce komai ba se farin ciki dake shimfide bisa fuskokinsu aka ce tsakanin mata da miji se Allah to shine suke kallo.

Daga nan sashen Jaddah ya wuce, a parlor ya sameta suka gaisa tace
"Ba dae tafiya ba? Na ganka shirye tsab kaman sabon ango"

Tsadaddiyar Murmushi yayi yana kallon jikinshi don be ga wani sabon shiga da ba sabonshi bane, sanye yake da wani ɗanyen bowel sky blue an mishi dinkin boda ya zauna mishi sossai, hula zanna a kanshi ya murza ta da kyau se agogo da wayoyinshi dake a hannunshi banda kamshinshi dake baza parlorn babu abunda kake ji.

"Kika sani ko zan mai dake ɗakinki a yau ɗin?"
Ya bata amsa cike da tsokana, haɓa ta rike tace
"zancen kake nema ai ni na jima da raba gari da kai bana auren nan, ina ni ina zama da miskilin miji ka fi mahaukaci ban haushi? Barni in lallaɓa da su Fahad yauwa...!"

Yana murmushi yace
"ni fito mun da matata mu wuce"

"wai ina Zaku wuce?"

"Dama daga ina muka fito Jaddah? Na kula na zauna jiran ki se mun yi missing flight"
Tsam ya mike ya nufi ɗakin Fauza da kallo baki sake Jaddah ta bishi kan ta fara gyaɗa kai tana jiran ganin ikon Allah.

Tsaye take a gaban madubi sanye da zani da riga na wata Tsadaddiyar super, kanta ba dankwali tayi loose parking wadda ya fitar da wasu daga jikin gashinta ya sassakesu bisa wuyanta da fuskanta, tsayawa yayi Chak hannayenshi zube a aljihu yana kallonta cike da so da ƙauna, ji yake kaman ya tsaga kirjinshi ya sakata ya huta da azababbiyar kaunarta.

Takawa yayi a hankali ya nufe ta ganin yadda take kokawa da zip, bata ji zuwanshi ba se jin hannayenshi masu taushi tayi cikin nata, lumshe idanu tayi sbd yadda sanyinsu suka ratsa har ɓargonta ta shaki kamshi me cike da natsuwa wadda ba tantama daga gareshi ne sbd ita bata taɓa jin irin turarenshi wurin kowa ba, haka suke ne ko combination da yake na musamman ne suka bada wannan sassanyar kamshin bata sani ba.

A hankali ta buɗe idanun ta sauke su tarrr bisa kamilalliyar fuskar shi ta mirror ɗin..

"May I?"
Yayi tambayar yana nuna zip ɗin da idanu, kai ta gyaɗa tare da ɗan murmushi.

Zip ɗin yake ja mata idanunshi kafe a fatar bayantan, bayan ya gama se ya kara taku ɗaya ya haɗe gab ɗin dake tsakaninsu ya sanya hannu ya zagaye ta tare da ɗaura haɓarshi bisa kafadar ta ajiyar zuciya duk su biyun suka sauke.

"Good morning yaya"

Seda ya ɗan juya idanu kan yace
"morning but the Yaya is not accepted, bana so a bani wani sunan precious"

Murmushi kawai tayi, yace
"an gama da zip, then what?"

Ba tare da ta ce komai ba ta nuna mishi sarka dama ta saka dankunne, hannunshi kawai ya miƙa ya ɗauko gashin da suka zazzame yake ɗan tattarewa da hannunshi yana mai dasu sama kan ya fara saka mata sarkar idanunshi kan wani baƙin tawadar Allah dake ɗige daga ƙasan kunnenta, Sam bata ankara ba taji saukar peck a daidai wurin, bugun zuciyarta seda ya so tsayawa.

Sake komawa jikinta yayi yace chan ƙasan maƙoshi da idanunshi da suka fara sauyawa
"am done baby, sai me?"

Tace a hankali itama
"sauran ba lallai ka iya ba, let me finish"

Be saketa ba ta dauki wani silk black rowsleeke ta mishi ɗaurin Zahra buhari, yana ta kallonta, da idanu ta nuna mishi blue and black embroid lafayarta dake ajiye bisa gado, da kanshi yaje ya ɗauko zata karɓa yace

"let me do it for you sweetheart"

Ta ɗan wara idanu tace
"in ba kana so in je in faɗi bane Yaya bani kayana in ɗaura"

Ɗan dariyar maganar yayi yace
"Haba yarinya tsawon rayuwata tun fa da na tashi nake ganin Jaddah da mammi na ɗaurawa in har ban ɗauka yadda ake ba kenan kwakwalwar kifi gareni"

Dariya sossai ya bata wadda seda ta dara, gyara tsayuwar ta tayi tana jiran ganin ikon Allah, tsab kuwa ya ɗaura mata lafayar ya zagayeta dashi, ba karamin kyau tayi ba.

Kallon madubi tayi tana murmushi kan ta ɗaga mishi hannu alamar jinjinawa ya taɓe baki irin ba na faɗa mikin nan ba, bangles ta saka ta ɗauko black handbag da black shoe ta saka, hannunta ya riƙe yana kare mata kallo.

"Kin yi kyau kaman Fure precious pearl"

Tayi murmushi tace
"thank you yaya, and kaima ka yi kyau"

Murmushi suka sakarwa juna kan suka fito, Jaddah baki sake take Kallonsu, Fauza ta kasa ce mata komai se shine ya sallameta, har suka fice bata ce komai ba seda suka fita ta saki murmushi, lallai a gaida yaran zamani.

Daga mota ya jirata ta shiga wurin Ammi sama sama, tayi ta saka mata albarka kan ta wuce wurin mammi itama albarka ta sha, ta shiga wurin sauran matan a tsai tsaye daga nan ta yada zango wurin iyayenta a parlorn baba prof, nasiha suka mata kan suka sallameta.

Fitowa yayi musamman ya buɗe mata gidan baya ta shiga ta zauna, kan ya zagaye ya shiga shima bayan ya zauna tare da sanya hannunshi cikin nata, kan kafadar shi ta kwantar da kanta tana kallon gidan tana tuna irin rayuwar da tayi cikinshi zuwa yanzu, Farhan ne ke tuka su har zuwa Airport kan suka yi sallama.

Ko da suka isa ma be barta ta gyara gidan da yayi kura ita kaɗai ba, a tare suka yi aikin tsab suka kamalla suka yi girki marar nauyi kan kowa ya wuce yaje yayi wanka, kusan a tare suka fito ta shirya musu abincin a ƙasa suka zauna suka ci, bayan ta tattare wurin ta nufi komawa ɗaki ya sanya hannu ya dawo da ita jikinshi yana gyara kwanciyarshi yadda itama tayi lub bisa kirjinshi yace

"Babe zan yi tafiya gobe it's been a while da na ba aikina hankali hakan kuma yana so ya samar min matsala"
Ya karasa yana shafa gashin kanta.

Da sauri ta ɗago kai tana Kallonshi Rau rau tayi da idanu, ya san me take tunani ko bata furta ba, shafa kumatunta yake a hankali kan yace
"da haka kowacce mace ta saba, nan ɗin gidanki ne babu abunda ze kama ki kinji? Sannan u have to catch up with ur studies, zan samar miki driver kan na koya miki driving ɗin"

Ajiyar zuciya ta sauke tana me komawa ta kwantar da kanta, a hankali tace
"is it outside country?"

Yace
"yeah..."
Ganin zata sa mishi kuka ya saka shi kara bakinshi bisa kunnenta ya fara zuba mata kalamai da suka kusa sakata sakin murmushi ba tare da ta shiryawa hakan ba.

Da yamma likis suka fita tare yayi mata sayayya har da sabuwar waya ya saya mata me dankaren tsada tayi ta murna kuwa.

Washegari da sassafe ta tashi ta Haɗa mishi breakfast bayan ta gama taje ta watsa ruwa tana mamakin yadda be takura ta ba da ta tuna mishi da alkawarin da ya ɗauka na baze nemeta ba se in ita ta amince.

Sanye da doguwar riga orange nd black na kanti ta fito, tayi kyau sossai tana shirin knocking mai kofa ya fito sanye cikin uniform ɗinshi da yayi mugun amsarshi, kan ta motsa yayi hanzarin rungumarta yana me bata peck a kumatu yace
"Good morning my moonlight"

Tace
"morning yaya, breakfast ɗinka na dining"

Murmushi ya sakar mata yana rike hannunta suka nufi fita yace
"am already late dear, in na ce zan tsaya karyawa zan ɓata lokaci"

Hannunta ta zame tare da turbune fuska tana juya mishi baya.

"OMG baby ba dae kin yi fushi ba? Believe me zan karya a Airport I promise"

A hankali ta waigo ya kara tabbatar mata tace
"Toh ko tea bazaka sha ba?"

Yace
"uhm uhm ni me daaɗi nake so"

Dariya ta ɗan yi tace
"tea ɗin akwai me daaɗi akwai marar daaɗi ne?"

Kai ya gyaɗa mata yana murmushi

Tace
"Toh ai me daaɗin ne mu je kaji"

Matsota yayi ya manna ta da jikinshi tare da rankwafowa ya haɗe bakinsu saida yayi son ranshi kan ya ɗago yana murmushi yace
"this is sweeter, bye take care"

Yana kai nan ya juya da nufin tafiya, tayi saurin riƙe hannunshi a hankali tace
"bani minti biyu please"

Da sauri ta shiga kitchen ta Haɗa mishi abincin a box me kyau yana tsaye yana duba time ta fito, ita ta mishi rakiya har mota ta saka mishi abincin a gefen baya ta inda yake kan ta sakar mishi murmushi tana mishi Allah ya tsare, cike da farin ciki da ƙaunarta me tsanani ya tafi.

Kaman yadda ya faɗa karfe takwas se ga driver ta shirya ta wuce school sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login