Showing 30001 words to 33000 words out of 56004 words

Chapter 11 - GIDAN AUNTY BOOK 2- END BY MSS LEE

miss lee   

28 Jun 2024

11256

kad ai tunanin shigowar king take amma shiru , a fili kuwa da asabe tayi abu sai ta tafa mata , sai  karfe 80:20am Suka kammala asabe sai faman nuna mata ydda ake jere tayi , ita kuwa sai bin motsin kowa take so take taga fitowar Ammey amma har yanxu shiru. Suna tsaye wasu  yan mata kyawawa suka shigo falon ko wannansu sanye cikin material gabaki d ayansu babu Wanda be hadu ba acikinsu, Hutu da kud i duk ya nuna a jikinsu. Da Sauri asabe ta gaishesu, tahee ta durkusa daniyar gaishesu taji ta farkon ta furta  gaskiya ilham baki da mutunci ki duba kiga da sassafe kinsa duk mun wani shirya  , da Sauri tahee ta d ago ta kalleta , cikin Sauri kuma ta bisu da kallo ilham ? Sumayya? Firdausi? , Dagaske kunake gani? Duk wad annan tanbayoyin kanta take yiwa su, firdausi da ta kula da kallan da tahee take musune yasata sakin murmushi  ya sunanki? cewar fiddy,  kwallar da take  ko karin zubo mata tayi saurin tare wa cikin washe baki ta furta  sunana kande  , atare gabaki d aya yan matan uku suka kalleta , haka kawai suka ji burgesu kodan wani abu da ya ta ba faruwa da bazasu manta dashi ba .  Ammey fa? , da Sauri tahee ta juya wajan asabe , cike da girmamawa ta furta  har ynxu bata fito ba  . Okay cewar ilham, cike da girmamawa suka bar wajan har yanxu taheee tana tunanin me ya hanasa zuwa part d in , ta bata da asabe tayi ne yasata tashiga taitayinta , su ilham basu wani dad e ba suka bar part d in sai alokacin Ammey ta fito fuskarta duk a kunbure , dariya ce ta so  kwace wa tahee amma ta danneta ganin yadda le ben Ammey ya kunbura, ganin yadda suke sunkuyar da Kai Ammey cike da kuluwa ta furta Menene kuke sunkuyar da kai, d agowa sukai a tare suka kalli Ammey ganin babu ha kwara biyu a bakinta yasa gabaki d ayan su fashewa da dariya .


=ؖ?=ؖ?GIDAN AUNTY =ؖ?=ؖ?
07041879581
Mss Lee


BOOK 2

Page biyu na had e muku na jiya da na yau & . =?O?
Page 14&15

Ita kanta tahee bata san lokacin da dariya ya kwace mata ba musamman yadda ta hango wawulon Ammey ,daka musu tsawa Ammey tayi rai a  bace , sai a lokacin suka kula da abunda Suka ai kata , gabaki d ayansu shiga taitayinsu sukayi ganin yadda ranta ya  baci, wata dariyarce ta so kama taheee amma take  ko karin danne ta gudun kar Ammeey ta  kara zuciya, cikin muryar fad a ta  kara daka musu tsawa  ku  bace mun dagani , bashiri kuwa suka bar Wajan , tahee na shiga d aki ta  kara fashewa da dariya ita kadai idan ta tunano bakin Ammeey sai ta  kara fashewa da dariya , knocking d in dakin asabe tayi kafun ta shigo ciki kai tsaye, Allah ya te mako tahee bata cire face d in ta ba , abincin ta asabe ta mi ka mata itama idan ka kalleta zaka san da fara a a kan fuskarta, lokaci d aya kuma tahee da asabe suka  kara fashewa da dariya sai da sukayi me Isarsu tukunna asabe ta bar d akin,breakfast d inta tahee taci hankali kwance tana tunanin shirin da zata yi nagaba kar Ammey ta gano ta . 12 : 10 asabe ta  kara zuwa kiran tahee , yanxu ma abincin rana suka fara shirye shiryen yi fuskar kowa da annashuwa musamman tahee da take yi da biyu, har lokacin kuma tun da Ammey ta shige d akinta bata kuma fitowaba hatta breakfast kai mata a Kai. Yanxu ma lafiyayyen lunch suka yi kusan rabin aikin asabe ce ke yi,sabida kallan tahee da take a bata waye ba bata san yadda ake abincin  yan gayuba , suna Kammala girkin asabe ta zubawa Ammeey cikin babban tray bayn ta zuba komai da komai cikin warmer, mi kawa tahee jug d in juice tayi ita kuma ta d auki tray d in  Abincin Ammey ne tace na kai mata d akinta ni kuma sun mun yawa shiyasa zaki rakani kinji , toh Kawai tahee tace mata dan ko ita da Ammeey ta kawo ta bata ta ba shiga d akin ba sai ynxu da zata shiga , bakinta d auke da addua  kasa  kasa ta biyo bayan asabe lokacin data bud e mata kofar d akin, Ammeey dake kishingid e kan gado ce ta d ago azabure , cikin firgita da tsoro gabaki d aya ta Amma ta da hakwaranta da Suka jire , jikinta har mazari yake da ya bawa tahee mamaki, wani tsawa ta daka musu da Suka ji har saman kansu  Me ya kawo ku d akina na rawa asabe ta nuna tray d in hannunta , a rarrabe ta furta  da daman abincin ki ne muka kawo miki ganin baki fito ba&  bata  karasa ba Ammeey ta kwashe fuskarta da mari sakin jug d in hannunta tahee taji jiki na rawa zata soma bawa ammey hakuri ta nuna musu kofa  kafun ranku ya  baci banasan ganin d aya daga cikin ku anan , ku  bace mun dagani cike da Tsoro tahee ta nuna jug d in da ya fashe  hajiya bari na fara kwashe abun tangaran nan  , bata kai karshe ba Ammey ta  kara daka musu tsawa  nace ku fita ko? Bashiri gabaki d ayansu suka bar d akin, tahee harda janyo mata  kofa, tana ganin  bacewarsu ta zu be  kasa tana dafa kanta  nashiga uku meyake shirin faruwa dani?   ko karin danna zobanta take amma ciwan bakinta ya hanata dan tasan abunda zai biyo baya , tana tsugunne a wajan kamar wani aljani ya bayyana a d akin, inda Ammey take ya nufa shima gabaki d ayansu a firgice  me kike shirin aikatawa? Tonuwar asirin mu kike so ko kuma me?kinfi kowa sanin  ka  idojin bokanya, kara na biyu da kika  kara  bata mana shiri, bazan lamunta ba  , na fad a miki bazan lamunta ba, idan kika  karayin kuskuran akaro na uku to tabbas jininki ya zama salwantaccen, yana kai  karshen maganar sa yayi wurgi da ita saida kanta ya bugu, shima gabaki d aya hankalinsa a tashe ya  kara  bace wa daga cikin d akin. Cikin d aga murya da fita hayyaci Ammey ta soma magana  bazeyu ba tabbas Kema kande lokacin aikin ki yayi , shirina bazai  baci ba, daga rana irin ta yau , aikin da ke kanki zai fara  ita kad ai sai surutai take yi .

Tahee kuwa ranta fess suka ci gaba da ayyukansu bayn sunyi sallah, har yanxu idanunta na kan kofar da yah moh ya sanar da ita akai amma har ynxu shiru Ammey bata shiga ciki ba . Sai wajan yamma Ammey ta fito daga cikin dakin , daka kalli fuskarta kamar hadarin kaji, har lokcin le banta daya kumbura be saceba,  kande , kande  , Ammey ta dunga kwalawa tahee kira , jiki na rawa tahee ta zo ta zube mata , kare mata kallo Ammey tayi ganin yadda jikinta yake rawa , kafun ta mi kawa tahee wata  yar  karamar jaka , da Sauri kuwa tahee ta karba  zaki ga bangarori da yawa , ki irga na ukun ciki daga hagu , idan kinga  yan mata a falon kice kina neman dada sai kibata, karkiyi kuskure fa  , ba kin hakwaranta tahee ta bud e mata  insha Allahu hajiya bazanyi ba  , kamar sa kai Ammeey tayi daga ganin hakwaran tahee. Da Sauri tahee ta nufi kofar fita , da kyar ta iya bud e kofar acewarta wahala ne da kofar  yan gayu tana fita har zata nufi part din dada ki tsaye sai ta fara irgawa kamar tanasan cinkar part d in, sai da tayi almost 5 minutes tana  karewa ko wane part kallo kafun ta nufi part d in dada wani irin sanyi da iska me kamar hadari yana busata. Tana shiga kuwa ta tarar da su ilham sai baman za ban kaya suke , da sallama tahee tashigo palour gabaki d aya kallanta sukai lokaci d aya kuma suka amsa mata sallamarta.jakar ta mi ka musu cike da barkwanci ta furta  wai hajiya ce tace a bawa dadu(dada) ,gabaki d ayansu kwashewa sukai da dariya kafun ilham ta furta  dada ko? , washe baki tahee tayi  kwaran kwatse haka tace , sunan yan gayun ne nakasa fad a shiyasa  , yanxun ma wani saban dariya suka saki , Daidai lokacin da dada take Fito wa daga cikin d akin, binta da kallo tahee tayi  itama ta  kara tsufa, farin gashin kanta ya Fito sosai  , cike da girmamawa tahee ta tsugunna ta gaishe ta lokacin da taji hawaye ya sakko mata a ido , da Sauri ta goge gudun kar wani ya gani a gidan , itama dada ba yabo ba fallasa ta amsa mata kafun ilham ta mikawa dada jakar da tahee ta shigo dashi  Allah sarki , kilishi bata gajiya da d awainiya , toh Allah yayi albarka  , gabaki d ayansu amsawa sukai da Ameen banda tahee . Zata tafi ilham ta tsayar da ita ,  kande bari na d an aikeki part d in ummey ki kai mata wannan , tsayawa kallan bakinta da ta furta ummey tayi , zumudi nasan fito mata Amma tana  kara dannewa, ta mi ka hannu daniyar kar ba taji sallama a bayanta,da Sauri ta juya batasan lokacin da bakinta ya furta  you!? , tsayawa kallansu su ilham sukai , tahee sam ta manta suna wajan sai tayi saurin wayancewa da  You You!! Nayi daidai ? , yar dariya sukai tare da kawar da shashancin tahee, ajiyar zuciya Tahee tayi tana  kara bin Mimi da tashigo cikin shigar  yar aiki itama a fakaice , Yawwa shikenan tunda kinzo , ita kande ta koma wajan aikinta inyaso ke sai ki kai wa ummey kayannan  , kar ban kayan Mimi tayi tana cewa toh , dariya duk ya cika mata ciki wato haka tace musu sunanta kande , ita kanta tahee saratu da aka kira Mimi sai da yaso bata dariya Amma tana dannewa , a fakaice ta yadda babu Wanda zai gansu Mimi ta d aga mata gira d aya da Sauri tahee ta d auke idanuwanta tana musu sallama, ita kad ai a ranta take magana  yarinyar nan so take asirin mu ya Toni take mun signal ko ? Zan kamata , amma Yaushe ta zo gidan nan itama ? da wannan tunanin tahee ta koma part d in Ammey. Yanxu ma Ammey bata falon shiyasa kai tsaye ta nufi makwancinta, kan  karamin karfe d in Wajan sai kayanta datayi fulo dasu har yanxu ta ki yadda ta hau kan katifar sabida hakanan kawai bata yadda da katifarba. Da daddare ma asabe ce ta kawo mata abinci tunda babu wani aiki da zasuyi, ita kad ai tana tsaya yadda zatayi magana Ammey. Part d in king ne ya fad o mata arai,  kana ina nayi kewarka sosai !!!!!! Plx kana ina  , duk da acikin zuciya tayi magana dole ka gane kad ai cin da take ji aranta , sosai yau take missing d insa so badly, so take kawai tajita a jikinta, bata san lokacin da ta rungume jikinta ba tana lumshe ido gabaki d aya tsananin kewarsa shida junior d inta ne ya cika mata cikin zuciya . Bata san lokaci ya ja ba saida ta kalli agogo taga  karfe 9, da Sauri ta Tashi tayi sallahr isha i tare da kulli  kofar da lock , sai da ta zauna tayi addu o in neman tsari sosai kafun ta soma akaratun alkurani a hankali a hankali, a haka bacci ya d auketa tana karatun.

Karfe 2:30am na safe tahee ta soma jin wani irin bugun  kofa a d akin ta, tun anayi a hankali har aka somayi da  karfi kamar za a  balla  kofar d akin, a rud e tahee ta soma karanto duk adduar data zo bakinta ,  karar abubuwa da jijjigar kofar da ake ne ya  kara tsoratar da ita amma duk da hakan sunan Allah ne a bakinta . Kamar  kiftawar ido aka koma side d in window shima a haukace aka dunga bubbuga windows din kamar za a  balla ga wasu irin kuka da suke tashi ta ko ina, side d in kofar aka koma shima nan d in bubbbuga wa akeyi had e da kuru ruwa , mintuna kad an kuma ya koma window , haka y dunga yi tsawan lokaci, sai wajan 3:10 kafun abun ya lafa , har yanxu tahee addua ce a bakinta daman tasan za  a rina , Ammey bazata ta ba barin ta Haka ba . Gabaki d aya tsoran komawa baccin take , saida bacci  barawo ya kwasheta.

WASHE GARI

Yau kam Ammey ta rigasu fitowa tunda suka fito take bun fuskokinsu da kallo kamar tana san fuskartar wani abu.har izuwa lokacin kuwa ciwan bakinta be gama sacewa ba, abun dariya facemask d in da tasaka a rabin face d inta,amma duk da haka idan tayi magana sai alamun rashin ha kori ya fito mata. Gabaki d aya yinin ranar kuwa Ammey a falo ta zauna duk yadda tahee taso had uwa da Mimi abun yaci tura kamar dama Ammey ta san plan d insu, duk yadda taso Zillewa Ammey bata , bata wannan damar ba , gabaki d aya yinin tahee bata had u da Mimi ba sai hakura tayi .

*****Haka tahee ta cigaba da zama a part d in Ammey matsayin yar aiki , ga biki da yake  kara kusantowa ,duk yadda taso ta Samu evidence akan Ammey abu ya ci tura gabaki d aya babu wan sheda da zai nuna maka Ammey tana yin wani abu , har lokacin kuma bata  kara had uwa da Mimi ba tun bayan had uwar da sukayi a part d in dada . Yau sati d aya kenan da zuwan tahee , gabaki d aya lamarin Ammey ya fara d aure mata kai , duk dare idan ta kwanta wannan buga  kofar da ake a haukace me yake tashin ta daga bacci amma Sabida kariyar ubangiji babu abunda ya sameta, tsawan sati kenan har yanxu taheee bata kwana akan katifar d akin, kome zatayi cikin taka tsan tsan take yinsa gudun kar asirinta ya tonu.

('('('('('('

Yau ya kama Monday,batasan me ke faruwa ba, sai ayyukan da Ammey ta sasu na dafe dafe da soye soye kamar za ayi wani babban taro gabaki d aya Ammey yinin ranar a tsaye take sai faman rawar kai take ga wani farinciki da ya kasa  boyuwa akan fuskarta, abinci kuwa kala kala tasa su asabe aikinyi, 6:30 ta saka su asabe zaryar kai abincin part d in Ammey , ban da wani kunun ayan da ta had a da kanta sai faman tashin  kamshi yake , tahee na tsaye tana kallan ikon Allah ganin ita ba a sata aikin komai ba , sai umarnin jiranta da Ammeey ta bata . Kiran sallar da akene yasa ta komawa d aki saida ta kulle ko ina tukunnan sannan ta cire fuskar, take kyakkyawar fuskarta tafiya kwanin burgewa gudun kar wani ya shigo ya sameta yasa ta yin alwala , tana idar da sallah ma ta mayar da face d in , sosai take kewar su junior da momy gabaki d ayansu. Kamar yadda tayi zato taba kammala sallar asabe ta kawo mata abincin Daren, ba musu kuwa ta  kar ba duk da agaban ta akai komai ,snacks din da tayi da hannunta kawai ta ydda taji shima sabida yunwar da take ji hatta leman da aka bata, bata shaba sai ma juyeshi da tayi a cikin toilet. Har lokacin Ammey bata  kara nemanta ba , sai bayan kiran sallahr isha i da ta da asabe kiranta. Tana fitowa taga Ammey ta sha uban kwalliya sai faman walwali take amma ba kin zuciyarta ya hana a ga kyaun ta sai mununta cewar tahee .  kande  cewar Ammey tana katse wa tahee tunanin da ta fad a , da Sauri tahee ta  karasa Inda tace cike da biyayya ta tsugunna , jug d in kunun ayar Ammey ta nunawa tahee ,  shi zaki d aukomun ki biyo ni dashi , da Sauri tahee ta amsa sa da to hajiya tana mamakin ne ya hana akai kunun ayar lokacin da ake kai abuncin, babu me bata amsa shiysa ta cire zancen cikin zuciyarta . Tunda suka fara nufar hanyar part d in dada haka kawai zuciyarta ta soma tsinkewa , ka  kafafuwanta da sukai sanyi kamar me shirin zubewa  kasa , duk da Haka bata karaya ba addua take karantowa a  kasan zuciyarta . Suna shiga falon saura kad an ta saki jug d in hannunta, ganin gabaki d aya ilahirin familyn suna Zaune kamar yadda suka saba , shi kad ai ne babu sai zoya da samreen da basa nan sai kuma mahma , a d ad d ai da d ad d ai ta soma bin ko wannan su da kallo kafun ta sauke idanuwanta akan ummey, hakanan ummey ta tsinci kanta da sakin wa tahee murmushi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login