Showing 27001 words to 30000 words out of 56004 words

Chapter 10 - GIDAN AUNTY BOOK 2- END BY MSS LEE

miss lee   

28 Jun 2024

11258

part din Ammey bata sani ba sai da hajiyar ta jijjigata  ke Menene sai faman kiran ki nake Amma gabaki d aya hankalin ki baya jikinki? Amaimakon tahee taji haushi maganar ta sai ta Washe mata hakwaranta da suka sawa abu, da farko idan ka kalla sai ka d auka hakwaranta haka suke dar harwani baki baki sukai kamar na kod ewa, tuba nake hajiya,arabu gidan nagani kamar Aljanna  tsaki hajiyar ta saki kafun tace fito ajiyar zuciya Tahee ta sauke kamar cikakkiyar na kauyiya tafara kici niyar yadda zata bud e motar harsaida hajiya tazo bud e mata tana Jan tsaki ,bin ta abaya tahee ta soma tanayi tana  kara bin part d insa da kallo kamar anan ne Zata gansa . Lokacin da zasu shiga part d in Ammey sai datayi addu o in neman tsari tukunna tasaka kafarta da Bismillah, Ammey na zaune kan kujera kafa d aya da sauri ta tashi tsaye sabida yadda ta jiya zuciyar ta , ta tsinke ga wani bugawa da take yi sosai da sosai , kallan kallo suka tsaya yi ita da tahee da taji kamar taje ta sha keta mutu , tsanarta na  kara shiga cikin zuciyarta Amma gudun kar agano yasa ya wajance da kallan falon tana zazzare idanuwa kamar yadda  yan aiki sukeyi, ajiyar zuciya Ammey tasaki dukda lokaci d aya taji jikinta ya mutu tana bu katar Hutu shiyasa cike da fara a tace wa hajiya su shigo ciki, Tahee a  kasa ta zauna tana  kara bin Ammeey da kudi ya  kara zauna mata da kallo , muryar hajiyace ta dawo da ita hankalinta lokacin da taji tana gaishe da Ammey , itama tahee cike da sokwanci da bar kwanci ta gaishe da Ammeey tana bud e mata hakwaranta ba ka ke , da Sauri kuma Ammeey ta kawar da kanta sabida yadda taga bakin tahee , a fakaice tahee ta danna wani abu a wuyanta lokacin da zata agaishe da Ammeey, cikin ikon Allah kuwa sai ga muryarta ta canza kamar ba ita ba , Ammey bata jira jin dogon zance ba bayan sunan tahee da ta tanbaya, yanxu ma tahee washe mata baki tayi kafuntace  ai aradu hajiya sunana kande kina ganina a  kauyan mu nafi kowa cin gasar  kyau,  girgiza kai Ammeey kawai tayi hakanan taji batasan hayaniya musamman kanta da taji ya fara sara mata , sama ta hau shaf shaf kafin ta sauko da wata jaka a hannunta tana mi kawa hajiya  zaki iya barin ta anan , duk yadda ake ciki nan da kwana biyu zan sanar dake , idan ta cancanci zama dani shiknn, idan ina bu katar wata kuma zan sanar dake  cike da girmamawa hajiyar tayiwa Ammey Godiya bayan shatara ta arzikin da ta bata, falon yayi saura daga tahee sai Ammeey dake bin tahee da kallan  kurinla. Kikace sunanki kande ? Yanxu ma tahee hakwaran ta washe duk da ydda taji zuciyarta tana tafarfasa kamar gawashi ganin Ammey a gabanta . Eh hajiya sunana kande , kuma a radu hajiya kome zaki sani a gidan nan zan miki indea zaki dunga bani abincin ku na birni , wani lallausan makirin murmushi Ammey ta saki tana  kara bin fuskar tahee da kallo, wayarta ta d aga kafun tace ina jiran ki yanxu  , basu  kara mintuna biyar ba tahee sai faman barkwancin ta take mata, Asabe ce ta Fito daga wata  kofa kamar kullum shigarta na  yar aiki ne a jikinta,nuna mata tahee Ammeey tayi  kikai ta dakin can na  kasa ita kadai banaso a had ata da kowa sannan ai mata abunda ya kamata zanje na huta kafin anjima , cike da girmamawa asabe ta amsa da toh Ammeey , itama tahee har da dur kusawa wajan godewa Ammeey.
Bin d akin da aka kawo ta tahee tayi , katifa ce kawai a d akin sai wardrobe da gaban mudubi , koda asabe zata fita ynxu ma sai da ta gode mata, maida kallanta tahee tayi kan gaban mudubin d akin tana  karewa fuskarta kallo, duk Wanda ya ganta tabbas zai d auka yar  kauyece musamman yadda jikinta yake da bakin wahala, guntun murmushi ta saki  idan kinsan wata ai baki san wata ba  cewar tahee cikin zuciyar ta , dawowar asabe ne yasa tayi saurin  karasawa ta kar bar mata kayan cike da girmamawa  ga wannan abincin Ammey tace a baki kici ki huta zuwa anjima kafun ta nemeki, amma gaskiya gaskiya kin cika mai sa a sabida ni banta ba ganin hajiya ta saka wani a wannan d akin ba .hajiya na da kirki kiyi mata duk abunda tace ko kinsamu  karin albashi  ,cewar asabe , tahee kuwa sakin baki tayi tana kallan asabe kafun cikin mamaki ta furta  Dagaske kike ? Gaskiya hajiya nada kirki, kuma ko me tasani zanyi mata  , itama asabe washe mata baki tayi kasantuwar ta da shegen surutu gaskiya dai ya kamata,kinga yanxu shirye shiryen biki ake sai kisamu ko atanfa da Jan baki kishiga sabida Kema ki fito cas dake , yanxun kama tahee batacewa asabe komai ba sai hakwaranta data Washe har ta bar d akin  tabbas befi wata biyu bikin sis Ilham ba kamar ydda yazama Kema zaki fara irga ranar tonuwan asirinki cewar tahee cikin zuciyarta.  Dakin ta  karewa kallo kafun ta kalli tray d in abincin da aka kawo mata , har zata  kici kuma sai wata zuciyar tace karta zauna da yunwa karba fuskanci wani abu, saida ta zauna tayi addu o in neman tsari da yanxu bata gajiya da yunsu cikin Bismillah ta zauna taji lafiyayyan abincin da aka dafa tunda tasan aikin asabe ne , kunun ayar da ta gani ne yasata binshi da ido kafin cikin Sauri ta d aukesa ta juye a sink gabaki d aya ta dawo da medium abun kunun, katifar da aka ajje mata ba , amaimakon ta kwanta akai sai ta samu gefe tayi kwanciyarta bayan ta kulle d akin, bata jima ba bacci  barawo ya d auketa.

3:40 tahee ta farka da Sauri ta mike tanufi toilet shaf shaf tayi abunda zatayi tayo alwala, kafin ta d auko face d inta da abun bakin ta shash shafa a cikinta , sallar asahar ta rama , Daidai lokacin da ake kiran la asar shima , tana idarwa ta bud e  kofar takin kamar wata  barauniya ta fito daga cikin dakin tana bin ko ina da kallo,  kina bu katar wani abune ? , cewar asabe da take  ko karin kiranta, cikin waske wa tahee ta soma kinkina  dama dama na d auka akwai aikin da zanyi ne sabida zama waje d ayan danayi duk jikina ciwo yake na saba da Noma da ayyukan gida shiyasa nake neman hanya  , Washe mata hakwara asabe tayi  Allah sarki Aushe baki da  kiwa kinga kuwa duk abunda hajiya tace miki kiyi toh shiknn zaku shirya da ita sosai nake fad a miki yanxu ma catai na kiraki , ina  kara jadda da miki kiyiwa hajiya biyayya tana da kirki matarnan, cikin gamsuwa tahee take d aga mata kai har suka  karaso cikin falon ita kuma asabe ta juna , cikin girmamawa cike da  kauyancin tahee ta soma yiwa Ammeey karari, Ammey kuwa sai faman sakin murmushi take kafun ya kalli Tahee da mugun kallan nan nata  kikace kome aka saki zaki iyayi? Da Sauri tahee ta jinjina mata kai  Aradu hajiya kome kika sani zanyi miki , yanxun ma wani murmushi Ammeey ta saki kafun ta ciro wasu Abu a cikin jakar gefanta da wasu ma kudan kudi ta fun ta nuna tahee  idan kika bi abunda nace toh tabbas zaki samu ninkin su ba masu ba  . Sai ta nuna wasu wani abu Aroba  yanxu idan nace ki zubawa wani wannan fiya fiyan zan baki 50k zakiyi , waro idanuwanta da aka sawa  kwayar iho tahee tayi , da farko Ammeey ta d auka ihu zatayi ne sai kuma tafa sa banin hakan  Haba hajiya yo ai wannan me sau kine , dubu hansin ba ? Idan akai mun kayan d aki nida iluna ai sai nafi kowa gata , Nidai kome kika sani hajiya zanyi miki dan saida a kaimun fad a a gida akan duk inda kud i suke innemo , yanxu ma murmushi Ammeey ta saki tana raya wani abu acikin zuciyar  yanxu nice shugabanki, duk abunda nasaki shi zakiyi , idan kika kuskura kika sa bamun sai dai in wata bake ba , sannan maganar ta tsaya tsakanina dake idan kika kuskura najita abakin wani toh tabbas daga lokacin bazaki  kara magana ba  cikin tashin hankali tahee ta zaro idanuwanta tana had e hannayenta biyu  tuba nake hajiya aiko me kika sani shi zanyi miki ni babu ruwana da kowa umarnin ki kawai zan bi  , wata yar iskar dariya Ammeey ta saki ita kad ai tasan me take rayawa cikin zuciyarta , kafin ta danna wani abu? Babu jimawa asabe ta  kara fitowa  kinuna mata yadda ayyukan suke , da tsare tsaran komai bana san kuskure , insha Allahu hajiya ai duk abunda kika ce shi za ayi , kafun tayi wa tahee alamar ta taso, cike da  kauyanci tanayi tana  kara kallan falon haka suka bar falon . Duk abunda take akan idan Ammeey shiyasa ta d auko wata kanta memiyar wayarta , wata number ta saka , ba a jima ba a ka d auka , bata jira jin maganar me wayar ba ta soma magana cike da  kosawa  tabbas muna gab da cika burinmu dan nasamo wacce zatayi mana komai namu kawai umarnine  , banji me aka ce mata ba sai  kara sakin wata dariya da tayi kafun ta kashe kiran , jinta take yau sakayau ga wani farin ciki da ya cikata ganin burinta yana  ko karin cika cikin sau ki.

A bangaran tahee kuwa yadda ake anfani da komai na kitchen asabe ta koya mata shima saida asabe taci uwar kwakwa kafun tahee ta nuna mata tagane dan har yadda ake kunna gas sai da sabe ta nuna mata ya kai sau goma dan data kar bi asha na zata kunna gas sai taja baya wai wuta zai kamata, Asabe ba  karamin wuya Tasha ba kafun tahee ta fuskanci abunda ta Goya mata , duk tsarin part din Ammey sai da ta sanar da ita da inda ake shiga da inda ba a shigar mata musamman lambunta da ba a shigarsa. Cike da bin umarni kuwa tahee take furta ta gode , sai wajan 6:30 sannan suka gama , lokacin da asabe zata  kara nuna mata d akin da take dan cewa tayi ta manta hanyar, d akin da yah moh ya sanar dasu ta kalla kafun ta saki wani lallausan murmushi , har ta koma masaukinta. Shima sai data kulle  kofa tukunna tayi sallah kafun ta  kara shafa ba ki ba kin abun nan , tasan tabbas idan tace zatayi wanka ynxu zasu iya fahimtar wani abun shiyasa ta hakura da yi, bata fito ba har saida tayi sallar isha i, lokacin da Ammey ta sanar dasu tafiyarta part d in dada . Kamar tahee zata kurma ihu haka take ji ganin babu damar fita . Zagaye ta somayi cikin d akin nata, tunanin mafita akwai take yi ita kad ai , ranta har soyuwa yake idan ta kalli Ammey, tana san fita falo amma tana gudun kar Ammey ko asabe su Fito , wani  bangare na zuciyar ta kuma yana bata  kwarin baiwar fitar danji take idan bata nakasa abeey ba, bazata ji dad i ba . Shahada Kawai tayi kuwa , cikin ikon Allah kuwa babu kowa a falon, hanyar d akinsu su asabe ta kalla nan ma shiru da Sauri ta nufi kitchen tana ro kan Allah yasa kar Wanda ya fito, Daidai ta zuba man gyad a a cikin ledo kuwa ta soma jin motsi alamar ana nufo kitchen d in da Sauri ta rufe man gyad an ta shige  kar lashing dinning din, wata ce itama da kama kallanta kasan yar aikice, cikin sand a ta bud e fridge duk akan idan tahee , Ayaba da kankanar da ta gani ta  iba kafin cikin sauri ta bar kitchen d in tana waiwaye , tahee dariya ce taso  kwace mata amma ganin bata da lokaci ne yasata fitowa ita daga ma boyarta . Babu kowa a falon har yanxu da Alama Ammeey ma bata dawo ba . Bakin  kofar shigowa tahee ta nufa cikin Sauri Sauri kafun ta d iga wannan ta ydda ba Lalle hankalin mutum ya kawo wajan ba . A cikin abun flowers ta jefa ledar tare da komawa d akinta hankali kwance, dan tayi alkawari daga rana irin ta yau Ammey sai ta fara fuskantar hukunci. Gudun kar axo Tashinta yasa ta saka lock ta cikin d akin har yanxu kuma bata kwanta akan catifar ba , dan bata yarda da komai na Ammeey ba .


AMMEY
Ammey kuwa ba ita ta dawo part d inta ba sai wajan 10:30, da ka kalli fuskarta za kasan ranta a  bace yake amma kasantuwarta shu umar mata sai ta  boye hakan da murmushi akan fuskarta.har ta dawo part d in ta tana tuna maganganin bikin da aka  kara tattaunawa na ilham , ba komai ne yafi  bata matarai ba kamar yadda su momy suka zage suna yin abu gabaki d aya sun toshe ko wace hanya, tazo zata shiga cikin falonta kafarta ta hagu ta zamar da ita sai ji kake kafff , Ammey ta kife tsakiyar bakinta ya daki  kasa take jini ya fara zuba , wata gigitacciyar zafin azaba Ammey ta saka ganin yadda  kugunta ya bugu ga ha korinta da take ji kamar babu su a bakinta. Kwalla kiran sunan asabe take amma babu asabe babu labarinta , lokacin da ta fad i kuwa akunnan tahee dan itama taji  karar, ganin aikinta ya cikane yasa taje tayo alwala ta kwanta. Ammeey tun tana faman  kwalla musu kira har tayi shiru Sabida azabar zafin da yake ratsata , tafi munti 10 kwance a wajan gashi ba damar kiran wani, da kyar taja jikinta har ta nufi d akin tafinta sai kuma ta dakata dan tasan cikin sharad in boka duk Wanda yake da ciwo toh tabbas ranar Jininsa za a zu ke cike da wani  karin takaici ta
Nufi d akin kusa dashi, hankalin ta gabaki d aya be kawo kan man gyad an ba , ga baki d aya takaicin ta kaicin dake cin zuciyar ta ya hanata ganin hakan. Tana shiga cikin d akin taji abu kamar abakinta masu kauyi da sauri ta tufosu waje, cikin gigita ta saki  kara ganin hakwaranta biyu sun cire tana  kokarin fara karanta maganganun tsafinta hakwaran suka  bace duka . A gigice ta fara dubawa d akin ko zata gansu Amma gabaki d aya babusu babu alamarsu, da Sauri ta  karasa gaban mudubin d akin cike da tsoro ta bud e bakinta kad an, ha kwaranta biyu data ga babu yasa ta sulale a  kasa sumammiya.

WASHE GARI
Kiran sallahr azuba a kunnan tahee , dama bata da magagin bacci saida ta fara yin wanka tukunna kafin ta yi sallah, gudun kar azo kiranta yasa cikin sauri sauri ta mayar da fuskarta da kwayar idanunta da yake canza mata kamanni, man da zai yasa jikinta duhu ta shash shafa , tsaf ta fito kande  yar aiki abunta, tunawa da muguntar da tayiwa Ammeey ne yasata kwashewa da dad i,  boye abubuwan anfani ta tayi kafun ta fito daga cikin d akin ynxu ma cikin sand a , Asabe bata fito ba shiyasa cikin sauri ta  karasa inda ta zubar da man, tana zuwa taga Jini Jini alamar harda ciwo Ammey taji , cikin Sauri ta d auko abu ta goge wajan tass babu ne cewa azuba wani abu a Wajan , dabara ce ta fad o mata tayi saurin komawa d akin gudun kar a zargeta , kusan mintuna 10 ta fara cin motsin mutum da Sauri ta kwanta . Asabe ce ta bud e d akin ganin har yanxu tahee bacci take kuma a  kasa yasa ta fara tashinta, ban karewa tahee tayi tana bud e kafun ta waro su duka ganin asabe a kanta  ya naganki kwance a  kasa bayn ga katifa  , kallan katifar tahee tayi cikin zuciya ta furta  hauka nake ? A fili kuwa washe ha kwaranta tayi , yo ba ance duk Wanda yake kwana akan irin wannan abu me yaushi aljanin dare na zuwar masa ba , kuma ni inna kwanta a irin wannan abun ai mutuwa zanyi  , dariya asabe ta saka  waya fad a miki haka ? Cike da barkwanci tahee ta furta  malamin Allon mune ya sanar damu kuma yace har ciki a keyi  ta  karasa tana toshe bakinta . Yanxu ma dariya asabe ta saka gudun kar Ammey ta Fito ne yasa ta kallan tahee  kande ya kamata mu fara aikin mu tun ynxu , kar Ammey ta fito  , toh kawai tahee tace mata suka Fito , suka fara shirin abincin safe kasan tuwar daman akwai masu shara da wanke wanke , farfesun kifi asabe tayi da hot chips sai plantain din da tayi , tahee sai kallan yadda take ai tayi a zuciya ita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login