Showing 9001 words to 12000 words out of 56004 words

Chapter 4 - GIDAN AUNTY BOOK 2- END BY MSS LEE

miss lee   

28 Jun 2024

11260

ya faru har kika bar gidan mijinki da ciki , share hawayenta tahee tayi tana sakin ajiyar zuciya , ko ba komai sunyi mata hallaci , sun kubutar da ita daga azabar da take ji a jikinta lokacin da take Niger , a hankali ta soma labarta musu labarinta, tun zuwanta gidan su king, da yadda tayi rayuwa dasu , tabin hankalin da ta samu har zuwa auranta da sanadin barowarta gida  , ba momy da Mimi da suke mata ba , hatta Alhaji isma il da yah moh saida suka goge mata kwalla, momy da Mimi kuwa kuka suke iya  karfinsu, itama tahee du kar da kanta tayi ta cigaba da kukunta, murya a raunane momy ta soma magana  Wannan mata anyi shed aniyar mata , insha Allahu sai taga hukuncinta tun a duniya , cikine kuma insha Allahu sai kin haifoshi kuma sai yayi rayuwa kamar kowa da yar dar Allah kafun ta mayar da kallan ta kan dady  daga yau ta Xama d ata, duk abunda uwa take wayarta zan dunga mata shi da yar dar Allah sannan zan ci gaba da bata kulawa har ta haihu ,itama Mimi cikin kuka ta furta  Nima zan zauna da ita bazan  bata mata ba , komai tare zamu dungayi har ta haifar min baby , murmushi Dady ya saki , dan shima sosai yaji wani irin Kaunar yarinyar ya shiga ransa kamar  yar da ya haifa a cikinsa , yah moh kuwa babu abunda ya furta sabida yadda kansa ke masa ciwo, lokaci zuwa lokaci yana kallan tahee ga ransa yadda yyi mugun baci,basu wani dad e a Wajan ba Mimi ta kama hannun tahee suka bar falon dady, sai faman jan ta da hira take , ita de tahee sai binta da kallo take kawai, duk surutun tahee mimi ta dameta sosai tun bata amsa magana maganarta harta dawo amsawa da  eh ko ah ah , a hankali kuma tana d an amsawa Mimi hirarta, gabaki d aya yinin ranar tahee sai tama tamkar wata sarauniya hatta ruwa idan momy ko mimi suka ga za Tasha da kansu suke bata a baki, tun tana jin wani iri harta d an sake dasu ganin yadda suke kila da ita, da tayi wani motsi momy zatace mata akwai abinda take so, da yamma kuwa da kanta Mimi ta fita driver ya kaita shopping, kome ta gani indai ya burgeta d aukowa take sosai ta suyo abubuwa masu yawan gaske tundaga kan kayan sawa har zuwa turaruka , gabaki d aya kuma siyayyar ba tata bace , siyayyar tahee ce. Data koma gida tahee sosai tayi kuka , tun momy na zuba mata ido har ta dakatar da ita ganin kukan nata bana karewa bane , da daddare ma Mimi bata zauna a palour ba , sama ta koma wajan tahee anan Suka ci abincin da ta kawo musu.


******koda gari ya waye haka momy da Mimi suka ci gaba da kula da tahee , ko sau d aya basu nuna mata basu da alaka da ita ba , sai ma wani irin kulawa da suke bata, hatta Alhaji isma il da shima lokaci zuwa lokaci zai tanbayi momy ko akwia abunda suke so, hatta yah moh da ya dawo gida da wasu kayan ciye ciye ya dawo masu shegen yawa cikin ledoji na tahee , sabida yasan masu ciki da ciye ciye , hakan da yayi ba  karamin faranta ran momy da Alhaji isma il yayi, gabaki d aya sai ya zama kowa tahee yake bawa kulawa, babu Wanda zai ce bata da ala ka dasu, tun tana no kewa har ta soma sakin jikinta dasu ganin yadda suke nuna mata kulawa babu hantara ko nuna banbanci.


=ؕ?=ؕ?=ؕ?=ؕ?

AFTER ONE MONTH

NIGERIA
LAGOS STATE

NAHYAN HOSPITAL.

A hankali d an yatsan king ya soma motsi a hankali , kafun ya fara motsa idanuwansa shima , lokacin gabaki d aya su Abbey suna d akin, mahma ce ta fara lura da yanayinsa, cikin sauri ta matso inda yake tana kiran sunansa, a hankali ya bud e idanuwansa kafun yayi saurin kallesu sabida hasken da ya Haska masa cikin idanu,kara bud e idanuwansa da suka  kara girma yayi, a hankali ya soma bin su Abeey da suka matso Inda yake da kallo,  kara dubawa yayi amma still be gantaba, murya a dushe ya furta  my wife  , duk da rashin lapiyar da yayi babu abunda ya canza daga yanayinsa , fuskarsa ba asake take ba , kuma ba a d aure take ba , yana bin su oummey da kallo ganin yanda ko wannan su yayi shiru,  kasa  kasa ya  kara furta  where is she? And my child ? , yanxu ma babu Wanda ya amsa masa sai ma cikin sauri da abeey ya kallesa , zamuyi magana daka baya bari a fara kiran doctor ya duba ka, be kuma cewa komai har doctor ya shigo cikin d akin kallan sa king yayi fuska ba fara a ya furta  for how long? , cike da girmamawa doctor din ya furta 1 month and 4 days , shiru king yayi yana dafe goshinsa da ya soma sara masa , so yake ya ganta , so yake yasata cikin idanuwansa ko zai ji dady,  karasowa su oummey sukai gaban gadon ,  ya jikinta  jinjina musu kai yayi kafun ya lumshe musu ido, sai da doctor ya dubasa yaga ba matsala tukunna,wasu sababbin kaya king yasa a kawo masa , wani toilet ya nufa kamar ba a cikin hospital din yake ba , su kuma su Abeey suka fito zuwa falon inda king yake sabida abarshi ya shirya, cikin murna abeey ya kira samreen da ke tare da dada ya sanar da ita good news din farkawar king, lokacin a kwance ukhti take amma sai da ta mike tsaye da saurinta, har dada saida ta tsorata,  amma dai anyi yar iskar yarinya, Menene kike mana wannan ihun haka  , murmushi ukhti ta saki lokaci d aya hawaye na sauka daga cikin idanuwanta  dada king ya Tashi  , mikewa dada tayi da saurinta  mu tafi asibitin yanxu  , zasu fita kenan su ilham suka shigo cikin palour , ukhti ce tab kallesu  Yawwa kwanda da kuka shigo, maza kuje ku cewa su mamy zamu je hospital king ya farka  , ihun murna ilham da su sumayya suka saki har dada tana zaginsu, sumayya ta nufi part din mamy lokacin suna zaune su da momy, sosai sukai farin cikin suma , momy har da mikewa ta kalli mamy  ya kamata a had a musu wani abu ko suna bukata  , hakane cewar mamy, firdausi kuwa part din Ammey ta nufa lokacin ta fito daga cikin kitchen hannun ta d auke da wani plate na tangaran, cike da farin ciki firdausi ta fad a mata farkawar king , bata jira jin amsar Ammey ba tabar part d in, a rud e Ammey ta saki plate din hannunta, kan  kafarta  karar azaba ta saki ganin yadda yaji mata mummunar rauni amma duk wannan be dametaba, farkawar king ne yafi komai  kuntata mata , azuciye ta nufi d akinta dukda azabar da  kafarta ke mata.

Lokacin da su dada suka  karasa cikin hospital d in cike da farinciki suke tanbayar inda king yake , abbey ya sanar da ita yana shiryawane, Maya finta dada ta kama ta d an goge kwallar fuskarta  oh ni  yasu , gashi ya farka , Kema Allh ya bayyana ki tahura ta , Allah Yasa kina hannu na gari, nayi musum (missing) d inki wallahi,Allah ya bayyana ki duk inda kike  , bata  karasa zancanta ba Sabida fashewar abu da suka ji, gabaki d aya maida kallansu sukai wajan , ba komai bane ya fad i face kantamemiyar wayar king, idanuwansa gabaki d aya sunyi jajur lokaci  kan kanin, kamar wani zaki ya nufi dada, jijiyoyin kansa gabaki d aya ta mi ke , sam ya manta wacece a gabansa, babban glass din dake kusa dashi ya buga hannunsa da  karfi har saida hannunsa ya fashe glass d in ya tarwatse, babu Wanda be tsorata da yanayin da king yake cike ba , da  karfi ya furta  ina matata? .




=ؖ?=ؖ?GIDAN AUNTY=ؖ?=ؖ?

07041879581
MSS LEE =ؖ?

BOOK 2

Page 5&6

Da Sauri Abeey ya nufi king da jini ke zuba a hannunsa, idanuwansa sun  kara rinewa, kallan dada kawai yake da tafi kowa firgita , a zuciye ya  kara furta  ina matata ? , yanxu ma babu Wanda ya iya amsa masa, Abeey na ri ke hannun Ya fusge ko kallansa be yiba , dada ya nufa kamar zai tsakota, ya  kara furta  ina matata? , yanxu kam dada rud ewa tayi ganin yadda ya canza mata kamar ba shiba , itama sai ta  kara rud ewa har tana bugewa sabida yadda tayi baya baya kamar zata fad i abeey yayi saurin tarota, duk da haka king be hakura ba ya  kara nufarta fadan fadan , gabaki d aya idanuwansa sun rufe , zai  karayin wani maganar Abeey ya d auke shi da mari, azuciye ya juya kan abeey,jijiyoyin kansa na  kara Tashi, shi kansa Abeey da yayi marin saida yayi danasanin marin nasa , lokaci d aya yaji shakkar d an nasa, kallo d aya king yayi wa abeey ya nufi kofar fita ko takan wayarsa be biba , gabaki d aya ukhti da ummey  ko karin tsayar dashi suke musamman ydda Jinin hannunsa yake  kara zuba, doctor d in da ya shigone yana ciwan king,  kokarin dakatar dashi doctor yayi, shima king ya d auke fuskarsa da mari, yana fitowa zaki yabi bayansa cikin sauri ganin yadda ransa yake a had e , da gudu ya bud e wa king mota suka bar hospital d in, tunda ya shiga cikin mota idanuwansa suke a rufe har suka  karaso cikin gida, Daidai part d insa zaki yayi packing, kusan 5 minutes idanuwansa suke a lumshe , cikin kakkausar muryasa ya furta  Me ya faru? , sanin ba a  bata masa lokacine yasa zaki labarta masa abunda ya faru, tunda ga accident d in da yayi har zuwa  batan Tahee, da yadda aka bincika ba a sameta ba, har kama sojojin da yayi saida ya sanar masa, lokacin da king ya bud e idanuwansa shi kansa saida ya tsorata da ya nayinsa, gefen wuyansa wata Jijiyace ta fito masa , door d in kofar ya bud e tare da sakko da kafarsa , cikin Sauri sauri ya shiga Cikin building d in nasa kamar yana so ya gasgata abinda yaji da kun nansa  Almost a month ?, itama ya rasata kamar yadda ya rasa shi , tafiya ya soma yi cikin falon da yake da d an duhu, da  karfi yake furta  No hakan bazaiyuba, I don t kiss them , bazan iya ba , my wife , my baby, Innalillahi wa inna ilaihi raji un  , yadda zuciyarsa take bugawa da sauri sauri ne yasashi yin baya , ga wani irin jiii da yaji yana neman kayar dashi, wani show glass da ya turene ya fashe gabaki d aya akasa , muguwar yan kan da yayi sai faman zubar da Jini yake, gabaki d aya Wajan ya baci, saitin zuciyar sa ya dafe, yana rintse idanuwa, bai da mu da yadda Jini ya  bata saba , tsugunnawa kasa yayi tare da runtse idanuwansa , da sauri abbey dake shigowa ya nufi inda yake , idanuwansa sun  kan kance kamar yayi wa king kuka haka yake ji, araunane ya furta  Am so sorry Tahnoon, Allah yayi bazamu ganta yanxu ba , but har yanxu ana kan bincikenta , nasan duk lefi nane da na sani lokacin da zamuje asibitin har da ita, kayi hakuri.. rufe wa abeey baki yayi tare da sakar masa kyakkyawan murmushi, kyakkyawan murmushin dake d auke da abubuwa masu yawa a ciki, yadda idanuwansa sukayi mugun canzawa ne yasa be kalli abeey ba , ya kara sakar masa wani saban murmushi  ba laifin ka bane Abeey, I lost Akhieeee for long time, yana sona sosai, and now I lost my wife again, and also her baby?, No Abbeey, tabbas a wannan karan abunda ya faru had I, I don t need anyone now , duk Wanda na tabbatar da sa hannunsa, I swear Abeey ko wanene bazan  kyalesa ba, the accident, and also  batan matata duk zan bun cika .. rufe masa baki abeey yayi,  ka dena fad an irin haka , bana jin dad i Allah ya ji  kan muhammad, na ro keka da Allah da manzan sa karka yiwa kanka illa, tun lokacin da kayi accident dinnan Ummey bata bacci sosai, bata cin abinci sosai, kasan halin samreen idan ta sawa kanta abu, tana tunanin zata rasaka kaima , na ro keka ka kwantar da hankalin ka ko suma nasu zai kwanta  , murmushi ynxu ma king ya saki be ce wa abeey kuma ba ya nufi stairs , a
Jiyar zuciya Abeey ya sauke kafun ya kira sumayya ta gyara Inda glass d in ya baci, gabaki d aya falon ta had a ta gyara , sai gashi ana shigo da kayan abincin daga part d in Mamy da momy, su firdausi na shigowa dashi bayansu kuma samreen ce itama d auke da wani  karamin tray a hannunta , kallan abeey tayi abun tausayi murya a hankali ta furta  Abeey yana ina ? , yana sama , ki bashi 20 minutes sai kije and please ki tabbata yaci abincin sannan ki masa dressing d in hannunsa, Nima zan dawo nayi baki, jinjina masa kai samreen tayi sai da dau kusan mintuna 30 tukunna sannan ta nufi saman d akinsa, gabaki d aya ya faffasa glass da yawa na d akin, sosai ya har gitsa d akin yana zaune kan sofa idanuwansa a lumshe Jini na ta zuba daga hannunsa , da sauri samreen ta ajje tray d in hannunta, da  kyar take wucewa Sabida in mutum be kulaba zai iya jin ciwo, first aid box ta d auka zata rike hannunsa ya fincike,  kara ri ko hannunsa tayi ya  kara fincikewa, a karo na uku da ta ri ko hannunsa zai fuske itama a zuciye ta daka masa tsawa, kallanta yyi da mamaki gnin hawaye a fuskarta sai kuma cikin sanyin murya ta furta  Dan Allah ka tsaya ba danni ba  , kallanta yayi be ce mata komai ba har ta gama dressing d in ciwansa,tray d in abincin ta d auko shi kuma ya mi ke tsaye zatayi masa magana ya  barar da tray d in abincin, a zuciye cikin d aga murya ya furta  get out of my room" da mamaki samreen ta kallesa hawaye a kan fuskarta,  Ni kake cewa na futar maka a d aki? Yayi kyau , zan fita daga d akin ka bani 10 minutes  , bata jira amsar saba ta fara gyara d akin yana tsaye shima dafe da goshinsa, tana cikin gyarawa kwalla ta caketa da har saida tayi  kara da
Sauri ya nufeta zai ta basa ta dakatar dashi kana ka kuskura ka tabani, kayi abunda ka keso  Tana gama fad ar hakan ta nufi kofa da niyar fita ya ri ko hannunta  Ukhtii why please? Zuciya ta ba dad i, I m feeling lonely, ina jin kad ai ci, ina ji kamar& . , rufe masa baki ukhtii tayi itama hawaye cikin idanuwanta komai yayi zafi maganinsa Allah, karka damu jikina yana bani zata dawo, zaku haifamana baby da yawa , ummey da abeey zasu zama grand parents, dada zata zama grand grand ma , ummey bata ci abinci ba tun jiya na ro keka ka kwantar da hankalinka ko natama zai kwanta kaji? Kanshi ya jinjina mata, itama saida yayi mata dressing d in hannunta kafun ta bar d akin cike da tausayinsa.



************
*********************
A  bangaran Abeey kuwa babban Amininsa tun na  kuruciya ne yazo duba king, sabida tafiyar da yayi kafun al amarin ne yasa bezo ba , Abbey yana zuwa falourn sa ya tarar da Aminin nasa , kamar yara haka suka rungume juna , ba kowa bane face Alhaji kabeer, gefenshi kuma khaleed ne , shima hugging din Abbey yayi , cike da alhinin abunda ya faru, kallansa Alhaji kabeer yayi ban ji dad in abunda ya faru da son d ina ba ,shiyasa nace dole na zo na duba shi da kaina dan nasan halinka kamar yadda ka ki zuwa d aurin aure na dukda nasan kana da babban dalili, to wannan karan dole a  kara d aura zumunci, suma iyalina insha Allah wata rana zan kawo su, murmushi abeey yyi  baka canza ba har yanxu , ina zahra ta ? Nayi kewar  yata  , gaishe Abeey Khalid yayi, Daidai lokacin da ilham take shigowa falourn bakin ta d auke da sallama , gaishe da Alhaji kabeer tayi , kafun ta gaishe da khaleed da ya tsareta da idanu, a fakaice ta dalla masa harara da yasakashi sakin murmushi, tana fita Alhaji kabeer ya furta  kamar ilham ?  Aushe baka manta sunayensu  cewar abeey  tana zan manta sunayen  yayana tana fita da munti biyar khaleed ya mi ke gabaki d aya kallansa sukayi ,  zan d an sha iska a waje ne , kafin king ya fito jinjina masa kai sukayi a tare , ajiyar zuciya ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login