Showing 6001 words to 9000 words out of 56004 words

Chapter 3 - GIDAN AUNTY BOOK 2- END BY MSS LEE

miss lee   

28 Jun 2024

11261

, idan kaci amanar Allah , Allah bazai barka ba , ka kula da amanar Allah wannan kamar jarabawace Allah yakeso ya kwadaka , sunkuyar da kai alhaji isma il yayi  insha Allah baba malam , nayi maka alkawari zan d auketa kamar  yar cikina sannan na bata tar biya kamar ni na haifeta  , Allah yayi maka albarsa, yaushene tafiyar? Cewar baba malam ,  Jibi nake san komawa insha Allah  , jinjina masa kai baba Malam yayi  sai a sanar wa iyali  cewar baba Malam,cike da girmamawa ya  amsa da insha Allahu .



=ؖ?=ؖ?GIDAN AUNTY =ؖ?=ؖ?

07041879581
MSS LEE =ؖ?

BOOK 2

Not edited

Page 3 &4=ؖ?

Yinin ranar gabaki d aya kula suke da Tahee tun tana zabura har ta dena sai dai har lokacin babu Wanda tayi wa magana , babu Wanda ya damu da rashin maganarta ta Sabida umarni da baba Malam ya basu, kana kallan Tahee zakagane tana cikin damuwa saidai babu Wanda take cewa komai .
Haka Suka ci gaba da kula da ita harzuwa ranar da Alhaji isma il zea koma , bayan ansiya wa Tahee itama abun anfani, sosai tafito tass da ita duk da bata yiwa kowa magana sai bin fuskar kowa da take da kallo. A cikin jet d in wani amininsa Alhaji isma il zai koma shiyasa tafiyar tasu taxo musu da sau ki, suna zuwa jirginsu ya tashi cikin sararin samaniya zuwa UK.

6 hours 18 minutes ne ya kawo su Uk cikin babban filin Airport d in kidlington date Oxford, duk inda ya saka  kafarsa nan Tahee take sawa , cikin wata katuwar Audi aka zo d aukarsa, bakowa bane yazo d aukarsa face Ya moh, yana ganin Alhaji isma il ya rungumeshi  welcome back dad , shima Alhaji isma il d in rungumesa yayi a jikinsa ,  Thank you my son,  gabaki d aya yah moh bai kula da Tahee dake kusa da Alhaji isma il ba sai da ya bud e masa mota, suna had a ido da tayi yaji zuciyarsa ta buga yana neman nutsuwarsa yarasa , cikin Sauri ya soma karanta adduar da ta zo bakinsa, nuna wa Tahee cikin motar yayi ame makon ta shiga sai ta tsaya kallansa, fahimtar hakan yasashi shiga cikin motar , sai gashi itama ta shiga , ta cikin mirror yah m??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????oh yake kallan abunda ke faruwa , azuciyarsa yana ayyana me yarinyarnan take tare da dady duk da yasan da zuwan ta . Mintuna 15 ne ya kawosu gida , tunda Mimi taji saukar mota ta fito a guje zata fita momy ta hanata, ita kad ai sai faman kunburo baki take , da sallama Yah moh yashigo falon bayanshi kuma Alhaji isma il ne , Mimi na ganinshi ta saki ihu , dagudu ta nufo Alhaji isma il daniyar rungume shi amma kallan da yah moh yayi matane yasata dakatawa a sanyaye ta furta  welcome back dady , nayi missing d inka sosai.. bata  karasa ba idanuwanta suka sauka kan Tahee da ke ra bewa, kallan dady tayi sannan ta kalli Tahee, kafun tayi magana momy ta fito cikin Adon less meshegen tsad a , wuyanta kuma sarkar gold ne tare da ma had inta , ita kadai sai faman walwali take ,ganin sun tsaya ne yasa momy sakin lallausan murmushi  ku shigo daka ciki mana , gabaki d ayansu cikin falon suka shigo Tahee na bayan Alhaji isma il, cike da murmushi momy ta nuna Tahee alamar tabbatarwa  Itace bakuwar tamu? , jinjina mata kai Alhaji isma il yayi , inda Tahee take tanufa, daniyar ta bata , da Sauri Tahee mi ke tana kallanta amma ta kasa yi mata magana , Ri ko hannunta momy tayi cikin tausasawa ta furta  karki damu daughter na ki kwantar da hankali babu abunda zai sameki insha Allah  , Ajiyar zuciya Tahee ta sauke duk da ta ki yin magana sai bun fuskokinsu take da kallo, kallan Mimi da ta zuba musu ido momy tayi  MiMi zoki kaita d akin da aka gyara nakusa da naki , Girgiza mata kai Alhaji isma il yayi , for now akai ta d akin Mimi , sai ta taima ka mata, idan nahuta zamuyi magana  , Toh momy tace , Mimi zatayi magana Yah moh ya kalleta, d an  karamin bakinta ta turo waje tare da ri ke hannun Tahee dake binta da kallo, a hankali suka nufi sama tare , Tana shiga d akin Mimi ta saki hannunta tare da nuna mata  kofar Toilet  ga ban d aki nan, and nan kuma wajan sallah ne ,ga dadduma da sallaya  , tana gama mata bayani tabar d akin. Bin ko ina nad akin tahee tayi da kallo kafun ta tsugunna  kasa tana fashewa da kuka , kukan da yake zuwar mata tundaga  kasan zuciyar ta , kukane take yinshi me rad adi, da Sauri sauri numfashinta ya soma yin sama da  kasa kamar zai d auke , cikin Amincin Allah bakinta ya fara kirawo sunayen Allah , a hankali wata iriyar nutsuwa ya fara ratsata tana sakin ajiyar zuciya, ban d akin da Mimi ta nuna mata ta kalla kafin ta mike ta shigeshi, mintuna kad an ta fito daga toilet d in, inda sallaya take ta nufa tare da kabbara sallah, saida tazo Daidai tahiyar karshe kuka ya kwace mata , lokacin da Mimi take shigowa d akin d auke da tray a hannunta , yadda taji shashshe kar tahee ne yasa ta kallanta, mamaki abun ya bata ganin tana sallah tana kuka, da sauri ta fita daga d akin , ita kuwa tahee batasan tanayi bama , har ta idar da sallarta tana kuka gwanin ban tausayi, a haka wani wahalallan bacci ya d auketa kan sallayar.

Shima Dady wanka yayi ya huta kafun yaci abinci , a  ka idar gidan duk lokacin da wani yayi tafiya tare ake zama ayi hira , hakan ce ta kasance a  bangaran dady , tunda ya soma cin abinci yake bin fuskokinsu da kallo , kowa kaga fuskarsa zakaga alamar tanbaya tattare dashi, maida kallansa yayi kan Mimi, kin kai mata abincin ? Eh dady amma da nashiga naga tana sallah tana kuka sai tabani tausayi , cewar mimi, kallanta momy da yah moh sukai alamar  karin bayani , ita ma Mimi kanta ta d aga musu alamar gaskiyar zancenta. Ajiyar zuciya Alhaji isma il ya sauke , kafun ya soma labarta musu abinda ya faru har dalilin na tahowa da ita , tunda ya soma basu labarin Mimi take kuka , shima yah moh sosai idanuwansa suka kad a, hatta momy saida ta share hawaye  wannan bala I har ina ? Yar mitsitsiyar yarinyarnan ma baza a barta ba , koma wanene wannan ya cika babban azzalumi Allah bazai barsaba wallahi , cewar momy, itama Mimi cikin shesh she ka ta soma magana  Dady kabar mana ita anan kaji? Zan dunga kula da ita nima  ,kallanta yah moh yayi ya d auke kansa batare da yace komai ba , kallansa dady yayi,  son baka ce komai ba , Dady duk ynda kace hakan yayi , ya kamata ta zauna anan d in gudun karwani ya lahantata  , cike da gamsuwa dady ya jinjina kansa, gabaki d aya sai suka canza hirar tasu zuwa kan tahee , anan ne dady yake sanar ma momy juna biyun dake jikinta kasan tuwar ta Doctor ce itama .
Duk da Mimi batasan taba , ba  karamin murna tashiga ba , hatta dady sai da yayi mamakin murnar ta, yau bata dad e sosai ba ma ta tafi d akinta , har lokacin bacci Tahee take , babban blanket Mimi ta d au ta lullu be jikin tahee dashi, zata kwanta kenan momy ta shigo d akin, ganin Tahee kwance a kan daddumane momy ta furta  Subhanallah , me nake gani haka ? , da Sauri ta  karasa inda Tahee take , a hankali ta soma tashin ta, cikin firgita Tahee ta farka da har sai da momy ta ri keta  kwantar da hankalinki babu abunda zai sameki kinji bin momy da ido Kawai tahee tayi , nan ma batace mata komai ba , kama hannunta momy tayi ta mikar da ita zuwa saman bed Inda Mimi take ta kwantar da tahee tare da lullu barta , kallan mimi momy tayi  Samuku karatun alqur ani , hakan kuwa mimi tayi ta kure volume din yadda zasu fi ji sosai,  kasa  kasa momy ta furta  ki kula da ita , kafin kafin ta kashe musu light d in ta bar musu mara haske , tunda Mimi ta saka karatun alkuranin nan take Tahee ta soma sauke ajiyar zuciya ita kad ai, a hankali takai hannunta kan cikinta, ganin haka yasa Mimi saurin mikewa , inda tray din dazu yake ta nufa , milk din kan tray din ta suka tare da wasu fruit ta mikawa tahee , karba tahee tayi ta soma cin abincin, sai da ta ci fruit da milk din sosai kafin ta soma ajiyar zuciya , sai a lokacin bakinta ya bud e, daga sama Mimi taji muryar Tahee  Nagode  , kallar nagode din da ta fad a masa yasa Mimi kara sakar mata murmushi cikin murna ta furta  kije ki kuskure bakinki , hakan kuwa tahee tayi sai da ta kuskure bakinta, ta sake wani alwalan kafin ta kwanta a gefen Mimi duk da har yanxu zuciyarta bata gama sakewa ba .


WASHE GARI
Momy da kanta tazo tashin su mimi, lokacin da ta shigo d akin a kan dadduma ta tarar da tahee na sallah, murmushi ta saki dan sosai ta burgeta,  karasa shigowa ciki momy tayi tare da nufar inda mimi take a kwance tana shakar bacci,  Mimi& ,Mimi , cewar momy, d an motsi Mimi tayi kafun ta furta  Uhmmm  , girgiza kai momy tayi kafun ta furta  oya ki tashi lokacin sallah yayi  , motsi mimi ta farayi da idanuwanta kafun ta bud e gabaki d aya akan momy, a hankali ta mike zaune , sai a lokacin idanuwanta suka sauka kan tahee da ke sallah,sai kuma ta mayar da kallanta kan momy da ta mike ta fita ganin har lokacin sallah tahee take , itama mimin ganin lokaci na tafiya ne yasa ta mikewa , bata dad e a toilet ba ta fito , lokacin tahee ta idar da sallanta, itama sallahr ta tayar tahee na gefenta kamar mara lafiya sabida yanda tayi shiru kamar me tunani sai kuma hawaye suka soma sakko mata akan kumatunta, duk da ba sosai Tahee ta girmi Mimi ba amma dukda haka cikin tsokana saida mimi tace mata  Ina kwana Aunty , d an kallanta Tahee tayi kafin ta du kar da kanta kasa , kusa da ita mimi ta matso kafun ta kama hannunta  ki saki jikinki kinji? , Babu Wanda zai  kara ta baki, duk Wanda ya  kara ta baki sai nayi gunduwa gunduwa da namansa  kawai kallanta tahee tayi hawayen da take ri kewa ya fara gangaro mata, zuciyarta ba dad i tun jiya da tabar Nigeria komai da ya faru na  kara yawo a cikin kwakwalwarta, batasan Wana hali mijinta yake ciki ba , Wana hali zai shiga, ya yake ynxu, oummanta , Taheer , gabaki d aya farincikinta ya rushe , abu d aya yayi mata saura yanxu, babynta, babynta da mijinta yake matukar  kaunar gani, babynta da mijinta yake so , so asalinsu, babynta da yake wa kallan d an uwansa da yarasu, Amma gabaki d aya ta rushe musu farin cikinsu da suke ginawa , farin cikin da suke Bu Kata, ta cutar dasu , cuta sosai , an bata Amana amma taci wannan amanar, ta zalincesu ,sannan tana  ko karin  kara salwantar da wani ran , babynta , ace auntyntace ta kashe mata uba, yanxu ma tana  ka karin kashe mata d a, wani tsantsar tsanar Ammey ne ya  kara shigarta, tayi alkawari sai ta koma, sai ta koma ta Nuna wa Ammeey bata isa ta cutar da su ba , idan Allah be nufa ba,hannun da taji akan kumatuntane yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta fad a,kallan Mimi data share mata hawaye tayi, itama Mimi kallan tayi tare da sakar mata murmushi kukan nan ya isa haka Aunt, ya kamata ki watsa ruwa , kafin ki fito zan ajje miki kayan da zaki sa, komai da kike bu kata gashinan agaban mudubi idan kinasan wani abu sai ki tanbayeni kinji , binta da kallo tahee tayi har ta gama maganarta , kafun ta furta  Nagode  da kyar, jinjina mata kai Mimi tayi , ita tafita tahee kuma tashiga toilet d in.

A palour kuwa Momy tsaye a wajan dinning tana shirya breakfast d insu, Mimi na zuwa kawai ta rungumeta a jikinta, tureta momy tayi  Mimi har yanxu baza kuyi hankali bako? Kishiga taitayinki fa , baki kawai mimi ta turo kafun ta furta  Good morning momy , ita momy  morning  , wani ma daidaicin tray Mimi ta d auka ta fara had a kayan breakfast a ciki , ko me ta gani sai ta d inta , kallanta momy tayi alamar  karin bayani, turo baki Mimi tayi  Ni momy batare da ku zan ci abinci ba yau, zan je naci da sabuwar sis d in da nayi, in dady da yah moh sun fito kice ina gaishe su  , tana gama fad ar Hakan tabar wajan, binta da kallo Momy tayi  yau kuma mimi ? Anya Itace kuwa ? Abin ba  karamin mamaki ya bata ba sabida tasan mimi ko cikin mutane batasan shiga amma yau da kanta take furta agaishe da Yah moh , hmmmm, murmushi kawai momy tayi.
Mimi kuwa tana shiga d akin wata abaya ta d auko wa Taheee blue colour me adan flowers pink colour , sosai rigar tayi kyau, bud e kofar toilet d in da akai ne yasa mimi ta d ago kanta, Yauwa Aunt ga kayanki nan, anjima sea naje nayi miki siyayya kinji, yanxu zan dawo  , bata jira amsar tahee ba ta kara barin d akin bayan ta ajje tray d in hannunta, kallan rigar da Mimi ta ajje tayi daga gefe wasu set d in underwear pink colour sababbi kal dasu a cikin Leda , ajiyar zuciya ta sauke , kafin ta saka kayan kamar dan ita aka yisu duk da tana cikin damuwa kayan ba  karamin kyau sukayi mata ba , sosai da sosai kayan sukai mata kyau, kallan fuskarta tayi a gaban mudubi kafun ta ta ba gashin kanta da yake a jike , momy ce ta shigo d akin bakinta d auke da sallama bayanta kuma mimi ce , ganin bataci komai da aka kawo mata bane yasa momy d aukan tray tare da kamo hannun tahee tana zaunar da ita , cikin raha momy ta furta  nifa banaso naga daughter na tana cikin damuwa , ki saki jikinki kamar ni na haifeki, ga Mimi nan ki d auketa kamar kanwar ki kinji , sunkuyar dakanta tahee tayi kafun a hankali ta furta  Ina kwana  , sosia momy taji dadin gaisuwarta amsa mata tayi cikin sakin fuska kafin ta d auko spoon da niyar bawa tahee abinci a baki , kallanta tahee tayi itama momy ta jinjina mata kanta , da kanta momy ta shiga bawa tahee abinci abaki, tana ci hawaye na bin fuskarta , ko saud aya momy bata hanata ba dan tasan shine kadai hanyar da zaisa nauyin dake zuciyar ta ya sauka , sai da ta tabbatar ta koshi sannan momy ta  kyaleta, hand dryer Mimi ta d auko tare da sauran abubuwan gyaran gashi, dakanta ta busarwa tahee kanta, tare da gyara mata uban tulin gashin da ke kanta,kallan Mimi, momy tayi ,  idan kun gama ku samemu a part d in dadyn ki , yana kai karshen zancanta tabar d akin tare da tray din abinci. Saida Mimi ta gyara mata kanta sosai tayi mata packing d inshi kafun ta kama hannun tahee suka fito, sai binta da kallo tahee dake , wani waje suka nufa ,tafiya kad an ya kawosu wani babban falo me shegen kyau da tsa ruwa da yaso yafi Wanda yake a farko, suna shiga mutane uku ne a falon daga Alhaji isma il sai momy da yah moh da yakw gefe, idanuwan tahee na sauka akan yah moh saida gabanta ya fad i addua kawai ta soma yi cikin zuciyar ta , kafin ta zauna inda momy take nuna mata, da kyar tahee ta gaishe da Alhaji isma il tana bin fuskarsa da kallo da mamakin da ita kadai tabarwa kanta sani, cikin fara a ya amsa mata, gaishe da yah moh tayi da yake zaune shima, cikin sakin fuska ya amsa mata kamar Mimi, mintuna biyu falon ya d au shiru kafun Alhaji isma il ya bud e taro da addua , sai da ya tabbatar kowa ya nutsu kafun ya mayar da kallansa kan tahee,  baiwar Allah ko zamu iya sanin sunanki a hankali ta bud e bakinta  sunana taheera muhammad  , jinjina kansa Alhaji isma il yayi alamar gamsuwa kafun ya  kara yi mata wata tanbayar da ya ta bo mata abunda take dannewa a cikin zuciyar ta, hawayen da take kokarin takatarwane sukayi nasarar zubo mata, babu Wanda ya hana ta yin kukan sai ma  kara maimaita maganarsa da Alhaji isma il yayi ko zamu iya sanin wacece ke , me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login