Showing 18001 words to 21000 words out of 56004 words

Chapter 7 - GIDAN AUNTY BOOK 2- END BY MSS LEE

miss lee   

28 Jun 2024

11259

lallashesa akan ya dawo gida , still dukda ya dena fushin amma yace bazai iya zama babu matarsaba idan ba haka ba zai iya samun ciwan zuciya , sosai abeeey ya tausayawa son d in nasa shiyasa be takura masa akan sai ya dawo ba , shima koda ya koma gida kwantar musu da hankali Abeey yayi , amma kusan kullum sai sun kira sa , dukda rashin magana da ya koya hakan baya hana in yana free ya kira ummey ko abeey, wani lokacin kuma ya kira dada da kullum sai tayi masa adduar Allah ya bayyana tahura .

AMMEEY
Cikin kwana bakwai d in da abun bautar su ya bata ba  karamin shiga damuwa da rud ani Ammey tayi ba , ganin har lokacin king be dawo ba , sosai ta shiga matsanan ciyar damuwa , da  kyar ta iya dannewa take kiran sa ko dan tace masa ya dawo amma itama amsarsa kamar ta sauran ce ,  he can t, bazai iya rayuwa babu matar saba  , wannan kalla tasa ba  karamin sosa ran Ammeey yayi ba Amma cikin bariki itama ta nuna damuwarsa tare da baza goyan baya . Sosai ta saka ayi mata binciken a nemo mata tahee cikin SIRRI yadda zata kammala aikinta na  karshe amma duk magana d aya ce ba a gantaba. Tun Ammeey na sa ran dawowar tahee har ta cire gabaki d aya tare da shinfid a sabuwar rayuwa acewarta abunbauta ya Mata  karya may be taheen ta dad e da zama Matacciya shiyasa sosai ta saki ranta, kwarton ta da yake kulle fuska kuwa kusan kullum sai yayi sex da ita, ita kuma ko a jikinta ganin ta salwartar da mutanan da sukeso su zama cikas a rayuwarta, yanxu buri d aya ne yayi saura ta cika, su kwashe gabaki d aya dukiyar Abbey hatta ta king da ummey da suke hari sai kuma bayan Abeey da yafi komai tsaya mata arai da takeso ta kawar.


****************
UNITED KINGDOM
A wata mata shiyar budurwace so classy sanye cikin doguwar rigar material, farace kyakkyawa , hannunta na d auke da siririyar fashion pose red colour , kantamemiyar tsadar wayarta ma pod d in ta ma red colour ,cikin taku irin na wayayyiyar budurwa meji da kanta ta soma sakko wa cikin heels dinta shima red , agogon hannunta take dubawa tun d azu, tana sakkowa daga steps ta soma kwalla kiran sunan  momy kuna ina lokacin na tafi , nasan sister tana can tana jiran mu , wani kyakkyawar baturan yaro ne ya fita daga wata  kofa cikin gudu gudu, yake furta  My love , junior is hear  , kallan inda yaran yake tayi, tubarkalla Masha Allah , wani kyakkyawan yaro ne , sosai yake da kyau fari tass kamar a  bula Jini ya fita , sanye take cikin Red suit na yara da ya  kara yi wa kyakkyawar fuskarsa kyau, gashin kansa kuwa wani irin gyara akayi masa ne shegen kyau da ya kwanto masa har wajan goshinsa, d an mitsitsin bakinsa pink colour sai faman shining yake , da Sauri itama matashiyar budurwar ta  karasa Wajansa, lokaci d aya sukai hugging d in juna , duk da hills d in dake kafarta Hakan be hanata juyasa ba sai faman dariya yake , dimples dinsa na both side na lotsawa, fararan jerarrun hakoransa tass dasu.  Mimi? Da Sauri matar shiyar budurwa ta juya , sai yanxu na ganeta sabida wani irin kyau da tayi gabaki d aya ta canza ta zama so classy, yaron naganin guy din daya kira mimi yayi saurin sauka daga Wajan Mimi ya ruga a guje zuwa wajan guy d in , shima hugging d insa yayi cikin turanci ya furta  Big Dady , sai yanxu fuskar mutumin ta fito, bakowa bane face Yah moh , shima sosai ya canza ya zama wani kyakkyawan guy , sanye yake cikin wasu  kananan kaya shima , sosai kayan sukayi masa kyau . Murmushi ya sakar wa boy d in  you look so wow sweetheart  , kashe masa ido d aya yaran yayi kafun ya ja masa kumatunsa  and also you my Big dady ,suna tsaye momy da dady da Hutu ya kara rutsa jikinsu fitowa , gabaki d aya ko wannansu tashi kalar d aukan wankan , a wannan karan ma kyakkyawan boy d innan wajan su momy da dady ya nufa cikin hausarsa da bata fitowa sosai ya furta  grandparents kun dad e tun dazu muna jiran ku , jan hancinsa momy tayi  toh ai gamu mun fito sai mutafi ko ? Kanshi ya jinjina mata kafun ya kama both hannunta dana Dady suka fito baban harabar gidan , motoci biyu kawai suka d auka d aya yah moh da Mimi , d ayar kuma dady ne da kanshi zaiyi driving din sai momy da junior a gefenta. A hankali cikin tafiyar nutsuwa a mota suka hau kan babban titin da zai kaisu **The inner temple ** lokacin da Suka je mutane sai fuffuto wa suke daka ciki zuwa harabar filin Inda kowa zai had u da family d insa , da yawa daga cikin mutanan sanye suke da suit a jikinsu sai wig and gown na lawyers da ko wanne ya saka, fara dudduba sukai suna jiran Suga ta Inda zata fito tun suna sa ranganinta har Mimi tayi *kokarin kiranta a waya  daga bayansu sukaji wata daddad ar siririyar murya ta furta   momy , gabaki d aya su lokaci guda suka juya zuwa inda muryar ta fito , kyakkyawar matashiyar budurwace ta a jikin karshe fara sol da ita , tsabar farin ta har yellow yellow jikinta yake , sanye take cikin suit ita ba ka sai wig and gown dinta da ta ri ke a left hand dinsa , fashion swag bag dinta ma nakegen hannunta na hagu black colour , sosai hill din data saka yafito da kyawun  kafarta , idanuwanta sanye yake cikin farin glass da kemar medical, siririyar cute lips dinta ya  kara fito tas dashi, duk da suit ne a jikinta hakan be nuna sura ko wani Shati na baiwar da Allah ya bata ba, da Sauri junior ya saki hannunta su momy yaruga wajan matashiyar budurwannan da kudi da jin dadi suka gama zama a jikinta, yana zuwa wajanta yayi saurin hugging d inta,  My love ! I missed you  , kyakkyawan murmushi ta sakar masa da ya  kara mata kyau lokaci guda both dimples dinta suka lo ba,  missed you too cewar matashiyar budurwar tana sakar masa peck a goshi, inda su momy suke ta nufa cikin ta kunya na d aukan hankali , tana zuwa ta rungume momy kafun ta koma kan mimi itama ta rungumeta , cikin jin dadi mimi ta furta  Congratulations sis tahee , you re now a barrister  , wacce aka kira da tahee da kalla da mugun shock , tabbas Itace Amma gabaki d aya ta canza ta zama wata babbar mace meji da aji ga baiwar karatun da Allah ya bata na zama babbar Barrister, itama momy congratulations dinta tayi kafun yah moh da dady kowa yayi congratulations dinta, cikin farin ciki suka fara d aukar hoto gabaki d ayan su , junior ya ta ba tahee kadan , kallan sa tayi da dara daran idanuwanta da suka  kara haske da kyau , alama yayi mata data matso, d an rankwafo tayi batayi auneba taji saukar kiss a goshinta , cikin harshen turanci ya furta  I love you mom .



=ؖ?=ؖ?GIDAN AUNTY =ؖ?=ؖ?

07041879581
Mss Lee =ؖ?

BOOK 2
Page 10

Da Sauri na  kara maida hankali na kan junior , daga nesa idan ka kallesa sak zaka ga tsantsan asalin balarabe, sai da ya matso da fuskarsa daidai inda tata yake kafun kamanninsa ya kara fitowa dukda kasan cewarsa yaro , amma sosai zaka hango tsantsan kamannin king, sosai suke kama , kamar tasu hartaso baci , banbancin shi junior har yanxu yaro ne , hatta yadda king yake kallan mutum haka shima junior yake , sosai suka d auki pictures, sun d anjima a Wajan kafun su kama hanyar komawa gidan bayan siyayyar da yah moh ya kaisu. Tahee na shigowa direct dakin ta tanufa sabida ba  karamin gajiya tayi ba , tana shiga wanka tayi kawai ta kwanta , amaimakon tayi bacci sai kawai ta fashe da kuka, Kukane take yinsa tundaga  kasan zuciyar ta , diamond ring d inta da abun hannunta shima diamond da king ya bata take bi da kallo, lokaci d aya kuma ta saki murmushin da dimples dinta suka lo ba  Ammi kin cucenii, kin rabani da farin cikina , why ? , me yasa  , ita kadai take tanbayar kanta,sosai take jin  kuna cikin ranta, yau ta kasance mata ranar farinciki da bakin ciki,sosai take sa ke sa ke cikin ranta , hannun da taji a kuma tunta ana share mata hawaye ta kalla , junior ne fuskarshi shi kamar zaiyi kuka  Ammu me yasa kike kuka ? Girgiza masa kai kawai taheee tayi wasu hawayen na  kara sakko mata , duk lokacin da ta kalli fuskar junior fuskar mijinta take gani, he s eyes , mouth , cute face,he s everything sak irin na king ne , Tohm ki dena kuka kinji  , ynxu ma kanta ta jinjina masa ta kasa magana , rungumeta yayi a jikinsa shima a hankali ya furta  I love you!!!!!! Ammu , a hankali ta furta  Love you more and more my baby . Kusan 3 minutes suna rungume da suna kafun da Sauri junior ya kalleta  Ammu na manta, abinci fa zamuci grandpa yace na kira ki , girgiza masa kai tayi  Allah ya?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? shiryeka son , bari na wanke fuskata sai mutafi , tana kai karshen zancantawta wanke face d inta tare da daukar junior kamar wani baby suka fito down stairs, gabaki d aya kowa da kowa ya hallara tahee da junior kawai ake jira , kallan fuskarta Dady da momy sukai, duk da alamu ya nuna kuka tayi babu Wanda yayi magana , daman ta sabayin kukan , yau da kanta Mimi tayi serving d insu abinci, tunda suka soma ci babu Wanda yayi magana sai junior da lokaci zuwa lokaci yake magana , suna kammalawa kowa ya bawa tahee gift ta zamowarta barrister , a nan d in ma wani saban kuka ta fashe da shi, sun d an jima a Wajan kafun dady ya mike , momy ta bi bayansa , yayi saura tahee da Mimi, daman yah moh shiya fara futa da junior.


*********
***************
**********
***************

FLASH BACK

Tun lokacin da tahee ta dawo Uk wajan Alhaji isma il suka cigaba da kula da ita, tun tana kin sakewa dasu har ta fara sabida yadda ko wannan su yake janta a jiki, A bangaran momy ma sosai take bawa tahee kulawa kamar  yar da ta haifa da cikinta kome zatayi wa mimi shi zatayiwa tahee, sosai suke bata kulawa babu me nuna mata banbanci, kullum momy cikin dubata take kasan tuwarta kwararriyar Doctor . Shima yah moh kullum cikin siyo mata kayan kwad ayi suke shi da dady. Gabaki d aya family sai suke bata kulawa ta musamman. Lokacin da dady yakezo sa tahee a makaranta ta wayarta da baba Malam ya basa yayi anfani ya Fito da soft copy din makaranta dake cikin wayar, duk da yar hanzu be fad a mata wayar na hannunsa ba . Koda sukaje school sabida kokarin ta yasa aka za tayi iya tafiya university, sosai tahee tayi farinciki da hakan, take a Wajan ta cike  bangaran law department, mimi ta cike nursing, haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin ahalin kullum tahee da tunanin a halinta take kwanciya take tashi , fatan ta Allah yasa suna cikin  koshin lapiya. A haka rayuwa tacigaba da tafiya da tahee tana samun kyakkyawar kulawa daga mutanan gidan , mimi ma sosai take janta a jikinta har soyayyar da suke wa juna tayi  karfi, lokacin da tahee ta fara labour gabaki d aya family babu Wanda hankalinsa be tashi ba amma cikin iko na ubangiji ta sum bulo d anta kyakkyawan gaske fari tass dashi kamar ka ta basa Jini ya zuba sabida kyansa, hatta Doctor d in kowa ya gansa sai ya furta  the baby is so beautiful basu wani dad e a asibitin ba aka basu sallama suka koma gida , gabaki d aya familyn momy saida sukazo hatta wata sister d in momy Itace tayiwa tahee wanka sabida yanda suke  kaunarta suma musamman da momy ta basu labarinta . Sosai dady da yah moh suka nuna bajintarsu ranar sunan kamar d ansune ya haihu haka akayi tafi nagani na fad a , baby da maman baby sosai suka tara gift sbd yaro yayi goshi sai san barka . Hatta friends d inta na school wasu duk sunzo mata , ranar suna yaro yaci suna mohammad , Sabida shine sunan da kullum king yakece mata yanaso ya sa wa babynsu, sai suke masa la kabi da junior .kullum momy da mimi ne suke kula da junior , har yaro yayi wayo sabida baiwar saurin fahimta da yake dashi, a haka tahee taci gaba da karatunta har zuwa ynxu da ta kammala karatunta amatsayin barrister.

('('('('('('

BACK TO STORY

Karfe 9:30 na dare dady yabu  kaci ganawa da kowa da kowa na cikin family d in, gabaki d aya taruwa sukai cikin babban falon dady, lokacin junior na jikin momy yana bacci , taro dady ya bud e da addua bayan salatin annabi da sukayi, shiru dady yayi yana juya maganar da zaiyi , itama momy shiru kawai tayi batace komai ba , gyaran murya dady yayi kafun ya soma magana ,  Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah , ina  kara gode wa Allah da ya bani ikon ganin ranar nan, ha ki ka nayi farincikin kammaluwar karatunku, ina  kara gode wa Allah, sannan ko wannan ku gift d insa da na basa yana wajan momy a Wajan ta zaku karba , abi na biyu kuma maganata akankine tahee, lokaci d aya zuciyar tahee ta buga jin ya ambaci sunanta, amma bata ce komai ba sai  kasa da ta  karayi da kanta.Ba sai na maimaita abunda suka faru shekaru bayaba, amma yanxu lokaci yayi da za a wuce wannan ga bar, lokaci yayi da tabon mutanan da suke cikin kuncin ya goge, ko ba a fad a ba nasan kinsani junior ya fara wayo, yana bu katar sanin mahaifinsa, yana bu katar salin ahlinsa, ke matar aurece na tabbata Indai mijinki na raye to tabbas yana cikin kuncin rayuwa, mahaifiyarki tana cikin bakin cikin rayuwa haka ma d an uwanki, lokaci yayi da zamu koma Nigeria gabaki d ayan mu. Ba tahee data d ago kanta ba hatta yah moh a mugun firgice ya kalli dady kansa na sara masa , cikin zuciyar sa ya maimaita  Nigeria ? , kamar dady yasan me yake fad a ya  kara maimaitawa  eh Nigeria, Nan da 2 weeks duk Wanda yasan yana da abunyi yayi kafun nan da 2 weeks dan tafiya ba fashi  , idanuwan ya moh har sun fara yin ja, itama tahee da wani irin shock take maimaita Nigeria cikin zuciyarta. Wata waya ya ciro daga cikin aljihunsa tare da wani  karamin hoto da ya fad i batare da sanin saba , wayar ya mi kowa tahee  Nasan bazaki manta da wannan wayar ba ko? Sabida tare da ita aka sameta cikin aljihunta , ita tahee kuwa gabaki d aya bata san me yake cewa ba , hankalinta yana kan hotan da ya fad i a kasa , hakanan zuciyar ta take san ganin hotan, saida dady ya  kara kiran sunan ta kafun ta saka hannu zata kar ba wayan ya su buce mata a hannu sabida bud ewar da hotan yayi ita kuma wayar ta gangara inda yah moh yake, da Sauri tahee ta d auki hotan zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri , gabaki d aya sai suka maida hankalinsu kanta, kallan Alhaji isma il tahee tayi kafun ta mayar da hankalinta kan hotan, shima a Daidai lokacin da yah moh ya d auki wayar tahee da ta fad i, cikin wani irin zabura tahee ta furta  Oumma? , da sauri Alhaji isma il ya mi ke tsaye yana  ko karin yin magana wayar tahee tayi haske, cikin wani irin shock yah moh ya mi ke take a wajan ya soma ganin jiri jiri na d ibarsa , babu abunda yake maimaitawa sai  Innalillahi wa inna ilaihi raji un , nuna wayar tahee kawai yake yana ja da baya ga juwar da take  ko karin kayar dashi , mimi har ta soma kuka babu abunda take fad i sai yaya moh , meke damunka . Ga baki d aya sai abubuwan yaso d aurewa dady kai musamman Wayar tahee da yah moh yake nunawa, kamar daka sama ya furta  King da  karfi, take a wajan kuma ya sulale  kasa . Da sauri dady da su momy suka nufa inda yake, tahee kuwa kasa  karasawa inda yake sai fuskarsa da ta tsurawa ido, kusan 2 minutes tana kallan fuskarsa kafin cikin shock ta mayar da kallanta kan junior dake bacci, sosai tashiga rud ani kanta itama ya soma juyawa take a Wajan itama ta sulale. Tashin hankalin da ba a sa masa date, sai suka rasa kan wa zasu tahee data suma ko yah Moh daya suma , babu abunda dady yake furtawa sai 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login