Showing 36001 words to 39000 words out of 56004 words

Chapter 13 - GIDAN AUNTY BOOK 2- END BY MSS LEE

miss lee   

28 Jun 2024

11265

sai da ta kashe ta yadda iska bazata motsa ba , zoban ta d auko cike da Bismillah tana kunna masa asha guda d aya kawai ya soma ci da wuta , ci sosai kamar Wanda ake fesawa kalanzir, abunda yfi bata mamaki ganin yadda tana kunna ashana tun kafin ta kai wajan zoben ya soma ci da wuta sosai ,  karane ya soma karad e ko ina na cikin kunnuwanta, me kama da ihu ihu na abun tsoro, lokaci d aya  kofar d akin ta soma jijjiga kamar zata cire kanta da kanta , windows d in d akin ma sosai suka soma jijjiga da  karfi, saurin toshe kunnuwanta tahee tayi tana ambatan sunan Allah sosai , ganin duk lokacin da tayi adduar sai zoban nan ya  karaci da wuta, tsawan a wanni biyu , har tsawan lokacin kuma kofar d akin da windows din basu dena jijjigaba ka guru ruwar da take tashi. Lokaci d aya kuma sai komai ya dakata , ihun ya dena tashi,  kofa da windows din ma kamar ba a ta basuba, inda zoban yake ta kalla ganin yadda ya koma  baki  kirin ga wani hayaki da ya soma Tashi daga cikinsa yana  bacewa , lokaci d aya kuma gabaki d aya zuban ya  bace kamar be ta ba wanzuwa ba awajan. Addua Tahee ta somayi tun tanayi a zuci har ta soma yi a fili tana  kara bin ko ina na d akin da kallo, Ta dad e tana addua a bakinta kafun bacci  barawo ya d auketa.

****** Lokacin da tahee take  kona zoban nan da yawa akwai mutanan da basu runtsa ba , musamman mutanan da suke da ala ka da wannan zoban babu Wanda ya runtsa a cikinsu sabida tashin hankali,ko wannansu cike yake da fargabar abunda zai biyo baya , gabaki d ayansu kasa ha kura gari ya waye sukai , karfe 3:00am lokcin da kowa na mahalu ki yana hutawa gabaki d aya banda masu ala ka da zoban da suka bayyana cikin falon su kamar kullum a yola , cike da tashin hankali sai faman kururuwar kiran boyankarsu suke tsawan lokaci, amma babu ita babu alamarta , duk da haka basu ha kura ba suka dunga kiranta cike da tashin hankali, sun dad e sunayi kafin suji saukar tsawa akansu , gabaki d aya suka sunkuyar da kansu alamar girmamawa , bata bayyana ba kamar yadda ta sababa sai amon muryarta mara dad in ji da ya cika ko ina na falon  tabbas kun aikata babban kuskure da kuka bari zoben nan ya  kone , tabbas lokacin tonuwar asirin ko wannan zai fara daga lokacin da zoben ya  bata , yanxu komai ya dawo hannunku Amma kusani gabaki d aya muguntar da kuka dad e kunayi tun daga yanxu ya fara warwarewa , ta dawo , ta dawo , bazata ta ba barin kuba , wannan karan a shirye suke , shirin da bazaku ta ba warwaresaba,na fad a muku a farko dawowarta kamar tonuwar asirin kune , toh lokaci yazo , lokacin tonan asirin ko wannan ku yayi  , sai kuma ta  barke da dariya mara dad in ji da saurare.  D aya daga cikinsu ne cike da fargaba ya soma magana  tuba muke , tuba muke  , sai gabaki d ayansu suma suka d au ka , wata tsawar ta daka musu , tun farkon shigowarku na sanar da ku abinda zai biyo baya Aduk lokacin da kuka  Kona abun aljanu, kutabbata yanxu lokaci yayi sannan cikin zuri arku zasu dunga shan jini  ta sake sakin wata dariyar da ya rud asu gabaki d aya. Cike da fargaba d aya daga cikin su ya soma magana  ya shigabar mu wannan laifin na abar  kauna ce da masoyinta  , yimun shiru , ta fad a kafun ta cigaba  babu ruwana da matsalar ku , kanku a had e yake , duk hukuncin da kuka ga dama kuyi mata babu ruwana , sabida itama yanxu lokacin tonan asirinta ne yazo , lokacin sadaukar da jininkune ya fito , hahahhahahahh, hahahahhahaha jinii, jini,jini , aljanun mu suna bu katar Jininku, ku tabbata kun gyara abunku a tsakanin ku hahahhahaha  , share gumi kawai suke gabaki d aya sun rasa bakin magana  amma wacece wannan shegiyar da take  ko karin  bata mana shirin mu ? , yanxu ma dariya bokanyar tasa kafin ta bud e musu tafukan hannunta, amaimakon suga wacce ta  Kona zoban sai haske ya kashe musu idanuwansu gabaki d aya , har  yar rigan kulle ido suke  bansan taba , bansan wacece ba , sabida duk kogin tsafin mu sun kasa ganin fuskarta, kuma bazaku ta ba sanin ko wacece ba sai ranar da asirin wasunku zai tonu  , tana kai  karshen maganarta ta  bace  bat.
Gabaki d ayan su babu Wanda hankalinsa be Tashi ba , ko wannansu duk da fuskokinsu da yake a kulle hakan bazai hana tsantsan tashin hankalin da suke ciki bayyana ba .

WASHE GARI

Kamar kullum kiran sallar asuba ne ya tasheta, hakanan take jin zuciyar ta a sake kamar ancire mata wani dutse me nauyi a  kirjinta, ga farincikin ganin masoyinta kuma mijinta da tayi , wani irin dad i take ji cikin kasan zuciyar ta musamman idan ta tuna abunda ya faru jiya , komai take yi yau zaka ga fuskarta tana sakin murmushi lokaci zuwa lokaci, ko da bata ga fitowar Ammeey ba hakan kwata kwata be dameta ba , damuwarta d aya ganin har yanxu be shigo part d in Ammeey ba kamar yadda ya saba , tun d azu take kallan hanyar shigowa ko zata gansa amma babu shi babu alamarsa , duk da hakan bata karaya sai da ta  kara kusan 30 Minutes, nan ma still shiru be shigoba, a sanyaye ta juya har ta kar kwanar d akinta taji kamshin turaransa ya ratsa mata hanci , da Sauri ta juyo , shi d inne kuwa , kamar kullum yana sanye cikin  kananan kayan yake  kara masa kyau da kwarjini, gabaki d aya ta maida hankalinta kansa shi kad ai kawai take kallo, shi kansa yaji alamun ana kallansa , a hankali ya d ago da dara daran eyes d insa , zuwa inda taji alamar mutum, yana d agowa idanuwansu ya shiga cikin na juna , gabaki d aya babu Wanda ya janye idanunsa daga shi har ita, kallon kallon kawai suke yiwa junansu, shi mamakin da yake me yasa tun da ya ganta nauyin da ya tokare masa  kirji ya sauka kamar wata aljana ?  , da hannu d aya yayi mata alamar tazo, a sanyaye tahee ta nufi inda yake, tana zuwa ta saukar da inanuwanta , kallan yadda ta sunkuyar da kai tayi kafun a hankali ya furta  Ammey ? , bakinta har rawa yake wajan furta  tun safe bata fito ba , kanshi kawai yayi nodding a hankali kafun ya sauke  kafarsa d aya dayi crossing , lokaci d aya ta bugu da wani glass na ado a wajan , tun kafun ya motsa tahee tayi saurin ta ba kafartasa Tanaso taga inda yaji ciwan kamar zatayi kuka ta ke furta sorry , da mamaki ya ke kallanta kafun ya furta  are you mad ? How dare you ?  ,ya  karasa da d aga hannunsa zai mareta , yadda ta kulle idanuwan hawaye na sauka akan fuskarsa ne ya tuno masa lokacin da tahee ta zuba masa coffee, the same reaction d in da ya gani yanxu , cikin d aga murya yake furta  why ? Why ? Me yasa komai irin nata ? Why ? Ynxu kam tsorone ya kama tahee , batasan me yasa ba , duk lokacin da tagansa sai ta kasa controlling kanta . Muryar Ammeey ce ta katse mata tunaninta tare da ajiyar zuciya , shi kuwa har yanxu idanuwansa na kan tahee da ta kasa kallansa , kallan tahee , Ammey tayi tare da yi mata alamar ta bar wajan, cikin gudu gudu sauri sauri kuwa tabar wajan .
Samun waje Ammey tayi ta zauna a gefensa , duk Wanda ya kalleta zai san ko bata da lapiya ko wacce take cikin damuwa Sabida yadda tayi zuru zuru, kallanta king yayi na tsawan 1 minutes kafin ya furta  Ammey baki da lapiya ? , da sauri ta girgixa masa kai  nashiga cikin damuwa ne ganin yadda gabaki d aya ka canza , kwata kwata baka damu da rayuwar ka ba kamar da hakan yana sani cikin damuwa  , amaimakon ya amsa mata sai kallanta da ya  karayi  the mouth ? , da Sauri ta toshe bakinta, ranta a mugun  bace amma tana  ko karin tannewa , murmushi ta d an sakar masa  karka damu son, burgewa nayi na daki hakwarana , lumshe mata ido yayi a hankali kafun ya furta  karki damu za ayi fixing d insu da wasu, anytime you re ready go and meet doctor maryam zan sa tayi miki cikin sauki  , cike da murya Ammeey ta amsa masa kafin ta  kara kallansa  son kaci abinci kuwa ? Kalli yadda ka  kara Ramewa fa ?
Shiru yayi mata ba tare da ya amsa mata ba , cike da damuwa ta furta zansa yanxu kande ta kawo maka , ka tabbata kaci idan ba haka ba bazan samu kwanciyar hankali ba , yanxun ma bece mata komai ba sai lumshe mata eyes da yayi  am going Ammey , ki kula  , yana kai  karshen zancansa ya bar part d in , da wani irin shu umin kallo Ammey ta bi bayansa dashi , kafun ta saki wani murmushin da ita kadai ta san ma anarsa, d akinta ta shiga bata jima ba ta fito da wani abu a hannunta , batare da ta nemi temakon kowa ba soma girka masa lafiyayyan abinci , kamshi sai tashi yake , tana kammalawa ta ajje a dinning tare da komawa ta d auko wani abu, warmers din ta bud e tare da bar bad a wani abu d an kad an a ciki,duk abunda take akan idan tahee dake kallanta daga nesa yadda Ammey bazata ganta ba , da Sauri kuma ta koma d aki zuciyarta tana bugawa da Sauri Sauri , kwalla kiranta da taje Ammey nayi ne yasa ta saki ajiyar zuciya, da Sauri ta fito tare da karasowa Indai Ammey take , kamar kullum sai da ta gaisheta cike da bar kwanci, kallanta Ammey tayi sosia kafun ta nuna mata trays din,  part d in da kukaje jiya kuka kai abincin nan xaki kai and ki tabbata yaci abincin , kinjini ko ? Kamar da gaske tahee ta zaro ido tana dafe kirjinta  Ni hajiya ? Kwarankwatsi ballani zaiyi , ki temaka kiyi hakuri  , ajiyar zuciya Ammey ta saki daman abunda take san ji kenan daga bakinta , d an had e rai Ammeey tayi kafun ta nuna mata abincin  maza ki Tashi kikai  , cike da tsora tahee ta kalli Ammey , cikin zuciyar ta kuwa dariyar Ammeey Kawai take , zata sake ro kan Ammey ta daka mata tsawa da Sauri tahee ta mi ke ta nufi dinning , jikin ta sai karkarwa yake ta nufi hanyar part d in nasa , sai da tayi nisa sosai sannan ta tsaya tana daidaita kanta , a hankali ta bude babbar  kofar falon , bakinta d auke da sallama, sanyin ac da kanshin turaran wutane ya daki hancin sa , gefe guda kuma ga  kamshin turaransa da baya fita daga palourn. Babu kowa a cikin falon kai tsaye dinning ta nufa ta ajje tana tuna lokacin da take bashi abinci a baki , gabaki d aya sai ta zubawa falon idanu tana tuna rayuwar su da sukayi a baya , sai data gama  karewa falour kallo, cikin sand a ta nufi bedroom d inta na sama , ko tsoron ya zo ya sameta a wajan batayi , tana shiga nan ma d akin fess yake sai faman tashin  kamshi yake , d akinta yananan kamar yadda yake , babu a bunda ya canza , nan ma bata tsaya ba , ta nufi d akin dressing room dinta , tana bin ko ina na wajan da kallo , sai data gama  kare masa kallo ko tsoran ya shigo ya same ta a haka batayi , tasan yana part d in abeey shiyasa gabaki d aya bata damuba ta kutsa kai cikin toilet d in , bataji alamun motsin mutum ba , sai ji tayi an fusgo hannunta da  karfin gaske , ta bud e baki zata sa ido taji an toshe mata bakin nata da  karfi anjin ginata da jikin toilet d in , zaro idanuwanta tayi a kansa ganinsa sanye da towel kawai , da Sauri kuma ta kulle idanuwanta, azuciye ya furta  bud e idanuwanki da sauri kuwa ta bud e idanuwan, amma bata kallesa ba sai  kasa da ta kalla , akau sashe ya furta d ago ki kalleni, har yanxu ta  ki yadda ta kallesa sai jikinta da ya soma rawa , da  karfi ya furta  ba dake nake magana ba ? , kuka tahee ta saka masa tana d ago da idanuwanta, hawayen da ya gani akan fuskarta ne yasashi kulle idanuwansa  why ? Me ke shirin faruwa dani ? Me yasa nk ganin aljana me irin behavior d inki? Why?  ya furta cikin zuciyar sa , kafun ya matsa baya kad an yana nuna mata hanyar waje ,  idan na  kara ganin me kama da fuskarki, uhmm be  karasa ba ya nuna mata kofar da finger d insa , da Sauri zata kwasa a guje , santsi ya nemi kayar da iya , cikin azama ya ri kota yadda ta fad o jikinsane yasa towel d in kugunsa kwance wa , jikinta da nasa suka hadu waje d aya ,a tsorace tahee ta saki  kara jikinta gabaki d aya ya dena motsi alamar ta suma .

Be san me yasa ba , sai kawai ya tsinci kansa da sakin murmushi, murmushin da ya dad e beyi irin saba , da hannu d aya ya d auketa ya fito daga toilet d in , akan sofa ya ajjeta ya shirya mintuna kad an ya dawo d auke da bottle water d in gabaki d aya ruwan ya juye mata a jiki a firgice ta farka zata kurma ihu ya daka mata tsawa  shut up  ,yana kai  karshen zancen sa ya juya bayar dakin, tunanin abunda ya faru d azu tayi kafun ta d auki hannunta d aya ta mari fuskarta  why ? Me yasa bana jin magana  , tunanin yadda zata fita ta soma ganin bata da wata hanyar fita , abincin data kawo masa ne ya fad o mata arai , yanxu idan yaci abinci fa ?  , dukda yadda jikinta yake a ji ke Hakan be hana ta saka gudu ba , da Sauri Sauri take taka steps, lokacin da ta sakko har ya gama zuba food d in da zaiji, ganin yana shirin d aukar spooon ne yasa tayi Sauri kwalla kara da karfi  No karkaci  , be gama fahimta me take ba kawai sai ganin tahee yayi ta ture tray d in gabaki d aya hatta abincin da ya zuwa sai data  barar dashi , rai a  bace ya d ago da eyes d inta, batai aune ba sai saukar marin shi taji a bothside kumatunta, da Sauri ta dafe wajan tana binsa da kallo ganin yadda ransa ya  baci,  kara d aga hannu yayi zai mareta sai kuma ya fasa a kausashe ya soma magana  idan na sake ganin ki cikin part d in nan zakiga abunda zai faru,leave now  , ya daka mata tsawa , ita kanta ta tsorata zata gudu ya tsayar da ita  washe kwashe miki Wannan trash d in  , jijjiga masa kai tayi ta nufi haryan kitchen , duk da yayi mamakin yadda akai tasan hanyar kitchen d in bece komai ba sbida yadda ransa yake a  bace , be san dalili ba amma yaji zuciyarsa tana masa ba dad i, kayan kashe shara tahee ta kwaso tashare Wajan ta goge kamar babu abunda ya zube , komai a nutse take yinsa gabaki d aya akan idanuwansa yana kula da movement d inta hawayen ta da suke fitowa ne ya fi komai tsaya masa arai , ko data gama bata kalli indayake ba tayi hanyar fita ,  hey ! , yace mata , jiyowa tayi har yanxu hawayen be dena sauka ma , yadda ta saukar dakai sosai zata baka tausayi , zai yi magana sai kuma ya fasa  get lose  , da Sauri ta juya tana goge hawayen fuskar tata , ta  kasan ido yake kallanta har ta fice , hannunsa ya d ora akan saitin zuciyarsa , yadda take hawayene ya soma ya dawo masa akai , at the same time yana tuno hawayen tahee d insa , he don t know why he feel bad , kamar ya kira ta , but he will never do so, mamakin kansa yake yadda idan tayi abu take d aga mata  kafa , abunda ya faru a toilet ne ya fad o masa arai da lokacin da ta taho da gudu ta 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login