Showing 6001 words to 9000 words out of 54681 words

Chapter 3 - Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa novel

05 Oct 2025

36

bakida wayo ne? Uwarki taxo taki gaisawa da abokiyar zamanki ai sai ace ba?in ciki takeyi narasa irin ?ar kissar nan da kisisina baki da'ita sai wauta da shirme." Meenal dai tana ta zumbura baki haka ta karasa suka tafi. Har sashin takara tace ita wallahi bazata shiga ba" kai wannan yarinya Allah yashiryaki wallahi bari nashiga ni sai da mumy ta karasa tashige baranda sannan ta isa palourn nata yaaAllah mumy ta ambata yadda taji sanyi mai ratsa jiki yashigeta da daddaWan kamshin turaren wuta sallama tayi Afrah da fannah da Aicha suna palour azaune kallo ma duk sukeyi hakan yasaka Aicha mikewa tana faWin " Sannu da zuwa sannu mama tafada cike da girmama." Mamakine yakusa kashe mumy ganin yadda aka Tarbeta cike da girmamawa har kasa Aicha ta gaida sannan ta nufi kitchen ta hado mata lemo ta kawo mata." Su afrah ma suka gaisa anan nr afrah take sanar mata maman meenal ce " Allah sarki mama Aikam nagode sosai Allah yakara girma." " Ameen yaaa Allah Nagode bari naje ko." DanAllah inazuwa tafada tana shiga dakinta turaruka tasamata Aleda ta biyota har waje tana mata godiya har sai dataga wucewarta ta dawo. " Meenal gaskiya kigyara halinki wannan ce kishiyarki kiga yadda tayimun kiga yadda ta tarairayeni." Ai daman munafukace abunda yafi hakama zatayi indai wannan ce mai suffer aljanun." Kinji rashin iya maganar taki ko? To Allah ya kyauta ni sai anjima." To kawai tace mata ta koma.

*******

Yadda afrah tashigo tana kuka yasa kowannen su kallon ta abba ne yace " kada ki sake ki zaunamin anan idan bahaka ba to tabbas zan bata miki ranki." Kuka sosai takeyi dayasa umma rikota tace " ke lafiya zaki daga mana hankali muna zaune kalou sabida Allah." " Zaneni yayi yace " intawo gida. " " tunda haka kikeso sai kizo ki zauna cewar abba." " Haba abba batsaya kaji tabakin yarinya ba karufeta da fada." " Nace bazanji ba duk iskancin da yaran naki sukeyi naga ke kike dorasu aure ne tunda takasa zamansa sai tayi kokari tazo ta zauna agidan." " wallahi Abba bayabani abinci ga dukana da yakeyi bayayimun komai watarana sai bayi wata baizo ba wallahi Abba ina neman Taimako." Shiru yayi baice komai ba umma kuma tacigaba da zage zage da yasa Abba daka mata tsawa yace mata tafita daga da?insa."

***

Wani ?alar missing dinsa takeyi hakan yasata daukar wayarta tashiga yimasa text *Ma ch?ri? ina mutukar jindadin duk sanda kayabeni ina Roka maka Allah yakula mana dakai yahaWe maka kan matanka yakara tsareka akomai naka am in love with kissing you, hugging dinka yanasawa in rasa kaina kazo gareni ma ch?ri? matarka tana mutukar muradinka." Cike da kunya tatashi ta aika masa hakan yasa tamike ta dauki kankana da minannas da kaninfari da zuma ta hada ta markada tashanye.


#Mutallab Asad
#?an Tagwaye
#Nana Diso
#Billy s fari.
*MUTALLAB ASAD*
Book 2

SHAFI NA HU?U
??
? Arewabook:- billysfari
?
? ? Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.

A lokacin da sa?on ya iski wayarshi zuciyarshi ce tashiga bugawa A hankali ahankali kowanne lungu da sakon nata yashiga cike da kulawa yakirata awayar ringing din farko tadaga tana mai saita muryarta cike da ?ar shagwaba tace " Ma ch?ri? (abin kaunata) ya kasuwa am missing you." " Duk wani sashi najikina yana maraba dake Aicha kulawar nan taki bakaramin Nutsuwa take samin aci?in raina ba ina fatan zaki kasance ahaka har karshen rayuwarmu." " Inshaa Allahu Abin kaunata Allah yabani ikon kasancewa yadda kakeso har karshen rayuwarmu yabaka ikon Adalci tsakanin mu da kuma kulawa damu." " Ameen ameen masoyiya yafaWa yana danyin shiru." Itama Wan juyar da idanuwanta tayi kamin tace" Me kakeso yau in girka maka." Murmushi yayi har tanajiyo acikin wayar yace " Ke Nakeso da komai naki dear." Kunyace ta rufeta tace " Tohm angama ranka yadade ayi aiki lafiya Allah yadawo dakai lafiya." Ameen yace mata. Ko dayakashe wayar Meenal yakirawo kusan bugu uku sannan tadauka " Yaya akayi sai kirana kakeyi." " Kina lafiya? " " To bagashi na dauka ba idan banda lafiya ai bazan dauka ba Tsakani da Allah banason takura yaushe kabar gidan ko kamanta yau girkin munafukar matarka kamin kacemun ma ni zan gyara maka bangarenka." Tsaki yaja yana kashe wayar itama tabi wayar da harara tana fadin munafuki kawai sai kace kirana da yakeyi. Tun daga Samanta ta hango Aicha tana shigewa bangaren Mutallab, duk da tasan ranar girkinta ce amma hakan ba ?aramin ?ona mata rai yayi ba don a ganinta iyayi da rawar kan A?cha ya yi yawa, kwafa tayi tare da komawa cikin palourn nata tayi zaune tana tunanin abinda za tayi ta Sakantawa A?cha rai.

A can Sangaren Mutallab Win gyaran Wakin A?cha keyi cike da zallar farincikin tana tunanin kalaman da mijin nata ya gama faWa mata tana murmusawa aduk lokacin data tuna, tsaye tayi bayan ta kammala taga yadda ko ina yayi ?al sai ?amshi ke tashi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta Wauko remote Win a.c ta daidaita gudunta wanda atake sanyin da ?amshin suka gauraye waje Waya suka bada wani kalar daddaWan ?amshi dake saukar da gajiya tare da saka natsuwar zuciya, ficewa tayi haWe da jan ?ofar ta rufe sannan ta koma part Winta ta faWa kitchen, tsaye tayi tana tunanin yau me zata Worawa masoyin nata, tuna soyayyarsa da tuwo yasa ta yanke shawarar yimasa shi, ruwan zafi ta fara Worawa bayan ta kunna gas, sannan ta gyara kayan miyanta ta markaWa a blender ta ajiye gefe, tuwon semovita ta ri?a masa tare da miyar ugun data sha gyaWa da busasshen kifi sannan ta haWa masa coconut juice, tana gamawa bayan ta haWa komai ta gyara kitchen Win sannan ta wuce bedroom ta faWa toilet tayi wanka da kalolin showergel Winta masu matu?ar ?amshi ta Wauro arwala ta fito ta tsane jikinta da ?aramin towel ta zauna gaban madubi ta shafa mayukkanta dasu khumras da collaccam ta murje duk wani lungu da sa?o na jikinta dasu ta yiwa fuskara light make-up tare da ciro kayan da zata saka a wadrobe, wata haWaWWiyar atamfa ta Wauko da akayi mata Wunkin pitet gown data kame i'lahirin jikinta ta saka, murmushi tayi lokacin data kalli kanta ajikin madubi haWe da ?ar jin kunyar yadda zata isa wajen mijin nata a haka har tana rufe fuskarta da tafin hannuwanta, jin ?arar buWe gate Win gidan ya tabbatar mata da dawowar maigidan nasu, da sauri ta Wauki Wan kwalinta bayan ta ri?e sumar kanta ?asa ta murza Waurin ture yanda za'a iya ganin tulin sumar tata data Waure ta baya, a gurguje ta laka ?an kunnayenta ta sake feshe jikinta da turare sannan tasa flat shoes ta fice daga Wakin da Wan sauri gabaWaya albarkatun jikinta na motsawa, tana fitowa Mutallab na kawowa dan har ya shigo sashen nasu yana faman zuba idanuwa bai ganta ba, cak yakasa Waga ?afa lokacin da idanuwansa suka sauka akan fuskarta tana nufo wajensa Wauke da murmushi, sanyayyar ajiyar zuciya ya suke yana mayar mata da martani tare da buWe hannuwansa alamun tarbarta, a yangace A?cha ta ?araso ta shige jikinsa tana faWin, "Oyoyo m? Ch?ri you are welcome." Tana zagayesa da hannuwanta kamar yadda yayi mata tana Wora kanta a saman faffaWan ?irjinsa, lokaci Waya suka sauke ajiyar zuciya yace, "Thank you Mon Amour irin wannan kwalliya haka kamar zakije gasar sarauniyar kyau ta duniya?" ?ago kanta tayi suna kallon juna ta sakar mashi wani ?ayataccen murmushi daya haifar masa da wata irin kasala tana cewa, "Me nakeyi da gasar sarauniyar kyau ta duniya bayan nasan ni Win sarauniya ce awajen mijina? Muje na taimaka maka ka samu kayi wanka ka huta dan nasan ka gaji." Takai zancen tana kissing bakinsa sannan tana hannunsa suka nufi sama inda sashen nasa yake ba tare data bashi damar cewa komai ba, tamkar yaro haka yabi bayanta yana kallon yanda take juya mazaunanta har suka iso palourn, tura ?ofar yai ya janyota ajikinsa yana jingina da ?ofar tare da Wora hannayensa a saman mazaunan nata ta Wora tafin hannayenta asaman ?irjinsa suna kallon juna, Waga masa gira tayi cikin wata irin tausassar murya tace, "Ya dai Mr. Mutallab?" Yanda jikinsa ya masa ya sashi yin sama da hannayensa zuwa saman bayanta ya sake mannata ajikinsa sosai haWe da cewa, "You look so beautiful Mon Amour." Tare da haWe bakinsu waje Waya yana mata wani irin Nigerian kiss da yasa A?cha taji ?afafuwan ta na neman Waukarta. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun wannan wace irin jaraba ce haka daga shigowarki." Suka jiyo muryar Meenal da tun Wazu da A?cha ta gama gyaran Wakin don neman magana tazo palourn ta zauna bayan ta sauke duka pillow Win kujerun a ?asa ta Wora ?afafuwan ta akan center table dake tsakiyar palourn ta shiga latsar wayarta hankali kwance tafaWa cikin Saci rai, da sauri A?cha ta jaye jikinta a jikin Mutallab cike da jin kunya shi kuma yabi Meenal Win da wani mugun kallo, "Amma dai kaji kunya wallahi ?aramar yarinya na maka karuwanci ka biyeta." Lumshe idanuwa Mutallab yai zuciyarsa nayi masa ?una ba tare daya bi takanta ba yace, "meya kawo ki Wakina?" Kafin ta amsa mashi A?cha tace, "M? Ch?ri bari na haWa maka ruwan wankanka kafin ka shigo." Ta wuce bedroom Winsa kai tsaye ba tare data kalli inda Meenal Win take tsaye ba tana aiko mata da harara, "ba dake nake ba?" Mutallab ya faWa cikin Sacin rai ta turo baki haWe da cewa, "Kana nufin banda ikon shigowa Wakinka ne ko meye?"

"Look Meenal! Bana son tashin hankali akan me zaki shigo Wakina bayan kinsan ba kece da aiki ba? ai ko shigowa zakiyi kamata yayi kibari sai idan ina nan ina har akwai wani abun, shima sai kin nemi izinin shigowa kafin nan saboda bakisan a wane yanayin zaki iya riskarmu aciki ba." "Saboda gaku jarababbu ko Mutallab." Meenal tafaWa kai tsaye tana kallon cikin idanuwansa kafin taci gaba da cewa, "To wallahi ba'a isa hanani shigowa Wakin mijina ba sai dai ku kudena wannan jarabar taku idan har bakwa son aganeku, munafuncin banza munafuncin wofi." Tana jan tsaki ta fice daga falon zuciyarta nayi mata wani irin tu?u?i ganin da tayiwa A?cha ajikin mutallab tare da banko masu ?ofar da ?arfi, girgiza kai Mutallab yai yana sauke ajiyar zuciya kafin yawuce bedroom, da A?cha yaci karo tana ?o?arin fitowa dan har ta gama haWa mashi ruwan, murmushi ya sakar mata tare da ri?o hannunta yace, "ina kuma zaki je." "Ka samu kayi wanka bari naje na kawo maka abinci." TafaWa tana shafo fuskarsa, "No kifara bani wannan naci tukuna." Ya faWa yana kai hannunsa tayi saurin janyewa tana dariya, "Allah M? Ch?ri kadena." TafaWa aWan shagwaSe tana cuno baki, ba tare da yace wani abu ya shiga shinshinar wuyanta yana kaimata kiss kafin kuma ya shiga yawo da hannunwansa a sassan jikinta yana aika mata da sumbatar ta kowace gaSa, atake A?cha ta shiga karSar sa?on tana juya kai haWe da mayar masa da martani wanda hakan ya sake jefashi wata duniyar ya Wagata cak zuwa kan makeken gadon, cikin ?warewa yake sarrafa kowane sashe na jikinta yana bashi ha??insa itama tana taimaka masa har ya samu natsuwa sannan suka shiga wankan atare, suna fitowa ya kalleta haWe da cewa, "Kin dai hanani naci sai ?walele kike mun ko?" Cikin jin kunya ta rufe fuskarta haWe da cewa, "Ni gaskiya kadena M? Ch?ri bana so." "Aidama nasan bakya sona min Amour shiyasa har yau kika kasa mallaka mani kanki." Ya ?are zancen yana zaunawa bakin gadon tare da janyota ya zaunar saman cinyarsa yana kallonta, "kidena wahalar da zuciyata haka A?cha kibani damar nuna maki irin tarin ?aunar da nakeyi maki ta hanyar zamowarmu abu Waya, ko har yanzu banyi maku ba bakya sona?" Kanta dake ?asa ta Wago haWe da cewa, "wace macce Allah zai mallakawa miji kamarka tace bata so, ko wancan lokacin ganin nakeyi kafi ?arfina shiyasa nafaWi hakan dan kar na yaudari kaina." "Amma yanzu ai kinga banfi ?arfinki ba tunda gani acikin gidana, pls A?cha kibarni na WanWani zumarki kota kashe mani ?ishirwar dake tare dani."

"You're are free to do so M? ch?re but not now." Ta faWa tana rufe fuskarta ya zaro idanuwa haWe da cewa, "Sai yaushe kenan ni Mutallab naga takaina." Dariya ta saki tana mi?ewa daga saman cinyar tasa ta nufi ?ofar fita Wakin tana cewa, "Ko yaushe amma banda yanzun." Tayi mashi Gwale sannan tafice da sauri tabar Wakin gabaWaya, sashenta ta koma ta Wauko lafiyayyen abincin data shirya masa ta jere akan dining table, tana cikin gyara kulolin yafito waya a kunnensa yana magana da Aryan, tsaye tayi har ya ?araso wajen ta ja mashi kujera ya zauna itama ta nemi ta kusa dashi ta zauna tana jiran ya ?are, kallonta yai yamata alama data zuba masa ta buWe kular ta fara saka mashi tuwon sanan ta zuba miyar ta tsiyaya masa ruwa a cup ta ajiye gefe, "Wow har yawuna sun tsinke." Ya faWa lokacin daya gama wayar ya haWe hannayensa waje Waya yana murzawa irin he's eager Win nan ya Wauki ruwan dake gefe ya Wan kurSa sannan ya soma cin tuwon yana lumshe idanuwa saboda yadda yayi mashi daWi ita kuma tana yimasa dariya, sai daya canye ta sake ?ara masa ya canye shima saboda Allah yayi masa don tuwo ko wane irine ta tsiyaya masa coconut juice Win daya sha madara ta bashi yasha, Wago kansa yai yana kallonta haWe da cewa, "Na gode Mon Amour abincin yai daWi sosai Allah yayi maki Albarka." Ta amsa da "amin" sannan ya mi?e ya koma palour ita kuma ta shiga tattare wajen ta kwashe kwanon tagyara sannan tadawo suka zauna suna kallo tana yimasa fira, bai bashi yafita ba sai da aka kira sallar magrib don dama bayan la'asar ne ya dawo gidan, arwala yayi ya sauya kayan jikinsa sannan suka fito tare ya nufi sashen Meenal ita kuma ta nufi sashen su t?nte, tana ciki ya shigo ransa aSace da alama Meenal ta Sata masa rai, gaishe da su t?nte yai sannan ta rakasa ya Wauki motarsa ya fice zuwa Masallaci dan daga can zai biya wajen Abba da Dadyn Meenal ya gaishesu dan tunda yadawo bai samu zuwa ba, ita kuma anan sashen t?nte ta tsaya tayi sallah suka Wan taSa fira sannan ta wuce sashenta ta sake gyara kanta kafin ya dawo dan ita da kanta tana jin tana bu?atar mijin nata a yanzu, sai dai data tuna me zai faru da ita kuma sai taji gabanta na faWuwa, da wannan tunanin ta gama shiryawa tsaf cikin kayan baccinta masu matu?ar Waukar hankali bayan tayi sallah isha tana jiran dawowarsa.
Mutallab kuwa daya dawo sashen su t?nte yafara wucewa ya kaimasu abinda ya siyo masu a leda kafin sukayi sai da safe ya wuce sashen Meenal, kusan karo sukayi da ita tana regen sashen A?cha Win ko zataga dawowarsa, ganin kallon da yakeyi mata ya sata haWe rai tare da cewa, "Me akayi ne wai kazo kayi mani tsaye, idan ba shigowa zakayi ba ka koma inda kafito." Ajiyar zuciya ya sauke yana Wan bin palourn nata da kallo yau ba laifi ta Wan gyara ba kamar kullum ba ya mi?a mata Wayar ledar dake hannunsa yana cewa, "Badai wani abu ko?" Ta amsa ta buWe ledar tana cewa, "Muga Wayar dan bazan yarda ba sai nafara zaSa." Ba tare daya bi takanta ba yace, "Ba wannan na tambayeki ba nace akwai wani abu ko natafi Shikenan sai da safe." "Zaka faWi haka tunda kasan baka yimani adalci ba nata yafi yawa, ni dai duk aka zalinceni.." bata ?arasa ba ya daka mata tsawa haWe da cewa, "Wai meyasa Meenal sam bakya da hankali, na dawo baki yimani sannu da zuwa ba, na siyo abu na kawo maku bakiyi godiya ba sannan ina tambayarki in akwai wani abun kina ?o?arin kafada mani maganar banza, ina dai kome zanyi kuWi na ne ba naki ba ko?" "Eh amma idan ma zaka sayi abu wani yafi yawa ai nawa ya dace ace yafi yawa tunda nice babba ba ita ba, Shikenan kuma sai kace bazanyi magana ba." "Mtssss..." Yaja tsaki ranasa aSace yana cewa, "Kijira idan nata Win yafi yawa sai kiyi ?orafi." Ya?are zancen tare da ficewa daga Wakin yana mamakin wace irin rayuwace haka Meenal keda ita, jifa da ledar Meenal tayi zuciyarta nayi mata wani irin sululi haWe da jin Wacin wai yau mijinta ne zai kwana da wata acikin Wakinsa a gidanta, wani irin kishi taji ya taso mata wanda atake hawaye suka fara saukar mata a fuska tana jin wata irin tsabar A?cha Win marar misaltuwa a zuciyarta...





#Mutallab Asad
#?an Tagwaye
#Nana Diso
#Billy s fari
*MUTALLAB ASAD*
Book 2

SHAFI NA BIYAR.
??
? Arewabook:- billysfari
?
? ? Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.


Jiki a sanyaye Mutallab ya turo kofar Wakin A?cha ya shiga, daddaWan ?amshin turaren wutar data saka daya marabci hancinsa ya sashi sauke ajiyar zuciya haWe da tafiya da kaso hamsin bisa Wari na damuwarsa, tasowa tayi saye da hijabi har ?asa dake jikinta ta tarbesa tana cewa, "oyoyo m? ch?ri sannu da zuwa." Ta bashi kyakkyawar runguma tana karSar ledar dake hannunsa, murmushi ya saki haWe da ri?ota yana cewa, "Yawwa Babyn m? ch?ri inata sauri kar nadawo na samu kinyi bacci duk da nayi tsammanin iskoki a sashen su t?nte, ya zaman gida?" "So boring saboda baka cikinsa." "Allah Mon Amour?" Ta Waya masa kai tana ?arasawa daga ciki tare da Wora ledojin akan center table shi kuma ya nemi kujera ya zauna yana jin wata irin kasala tattare dashi, "Me zaka ci?" "Gashi nan a leda ki dauko ki zuba mana, ina fatan dai bakiyi wahalar girka mana komai ba ko?" "Eh dayake Wazu da yawa nayi abincin shiyasa ban Wora wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login