Showing 15001 words to 18000 words out of 54681 words

Chapter 6 - Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa novel

05 Oct 2025

40

kaddarar kasancewarki dashi itace akusa Nikuma tawa kaddarar ta kasancewa ta dashi sai yanzu ta wanzu, mijin mu ne kuma kowaccen mu ?arkashinsa take mu darajtashi mukuma masa biyayya kamar yadda aka koyar damu a musulunci." Yanayin ?allon da Meenal tashiga yimata tana jan tsaki haWe da faWin " Dallah ?ar talakawa rufemun baki ke har zaki gayamin son miji? Shekara nawa ina da?on soyayyarsa? Munafuka kawai muzuba mugani ." Aicha ce ta kalli Mutallab da baccin rai yagama sauka afuskarsa ci?in sanyin muryar da batasan tanadashi ba tace " mon amour (masoyina) danAllah kayi hakuri muna tayimaka hayaniya a?anka." Ganin ya mi?o mata hannu yasata sa?in murmushi tana zama kusa dashi zuciyarta cike da zafin kalaman Da meenal tagayamata yo inba agaban mutallab ba ai da ko dambe sai sunyi wallahi amma zata mayar mata sai yafita. " Wallahi bazaka taba cigaba ba indai zalunci kasaka agaba kuma Allah yasakamin tafada tana ficewa daga da?in " sosai kalmominta suka sakashi bacin rai har yana kokarin mikewa Aicha ta riko hannunsa.


#Mutallab Asad
#?an Tagwaye
#Nana Diso
#Billy s fari.
*MUTALLAB ASAD*
Book 2

SHAFI NA TAKWAS
??
? Arewabook:- billysfari
?
? ? Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.

Haka rayuwa taci gaba acikin gidan Mutallab a tsakankanin matan nasa, ya lura rashin iya magana daga jinin Meenal yake dole sai yana kauda kai amma duk da hakan wani lokacin abun nayi masa zafi sosai, baisan dalilin ubangiji na haWa shi da ita ba shiyasa bazai taba sawa kansa cewa sai ya rabu da ita ba saboda munanan halayenta, amma kaso 40 bisa Wari na soyayyar da yakeyi mata ya tafi saboda an jarabci zukata da maison kyautata masu da kuma ?in mai munana masu, sai dai duk da haka yana ?o?arin ganin ya kamanta adalci dai-dai gwargwado tsakaninta da A?cha ta inda zai iya, inda bazai iya ba kuma ya barwa Allah dan bazai kamasa da laifin hakan ba, ta Sangaren A?cha ma wata irin sha?uwa da ?auna haWu da soyayya ke ?aruwa tsakaninsu, tayadda ko fita yayi baya iya buge cikakkun mintuna talatin ba tare daya ji muryarta ba, sosai take daWa shiga ranshi saboda yadda take gudun Saci ransa, uwa uba faranta masa a shimfiWa da takeyi, wannan yasa shima a kullum kwanan duniya yake ?o?arin ya bata farinciki kamar yadda take bashi.

Tsakanin Meenal da A?cha kuwa kishi suke gogawa mai zafi dan yanzu duk ta gayawa A?cha magana sai ta mayar mata dai-dai yadda tayi mata dan tuni girmanta ya jima da faWuwa a idanuwanta, gaban Mutallab ne kawai bata biye mata tana ?yaleta tayita haushinta ita kaWai har tagaji, wannan ya ?arawa A?cha girma da daraja sosai a idanuwansa ta yadda Meenal natasowo da rigimarta akanta zai tsawatar da ita ya nuna mata ranta zai Saci idan har bata kama masa bakinta ba, hakan da yakeyi sai ya zama Meenal na ?ara jin haushinta da ganin Mutallab Win baya mata adalci tunda yakeyi mata faWa agaban A?cha Win dan yajawo mata reni a wajenta take kuma kuka da hakan shine ?arin giuwar da A?cha ta samu da har take iya faWa mata magana.

Yau tunda safe da Mutallab zai fita yace su shirya zuwa la'asar zai kaisu gidan Aryan suna gano matarshi data samu miscarriage, a Wakin A?cha yake dan haka yana dawowa bayan yaci abinci suka fito tare ita tawuce sashen su t?nte ta jirasu su fito shi kuma ya wuce sashen Meenal ya samu taci ado tamkar ba ita ba ta yafa wani Wan ?aramin gyale, kallonta yakeyi tun daga sama har ?asa kafin ya haWe rai yace, "Koma ki canzo mayafinki wannan baiyi ba." Kallon kanta tayi tare da Wago kai tace, "Meye illarsa naga matarka ita mayafin abaya kaWai ne ajikinta kuma tare kuka fito da ita baka hanata ba sai ni."

"Bakiji me kika ce ba? Abaya ce a jikinta data rufe mata ko ina ba tare data bayyanar da surarta ba, ke kuma fa? Dubi yanda kika matse jikinki dan kin maida ni soko da baisan me yakeyi ba na Waukeki nafita dake haka." Ya?are zancen yana nuna jikinta dake saye da riga da sket na lace da suka matseta sosai." Cuno baki tayi kafinta koma cikin dakin tana ?unkuni, wani mayafin ta sake yafowa da kaWan zai Wara wancan Win tana Sata rai ala tilas ya takurata, lumshe idanuwa yayi cike da Sacin rai kafin ya sake Wagowa ya kalleta lokacin data ?araso wajen yace, "Karki Sata mani lokaci Meenal, meye banbancin wannan Win da wancan?" ?an juyawa tayi agabansa tare da cewa, "Ni kam wai meye illar mayafinta inba neman rigima ba." Bai tsaya cewa wani abun ba yaja hannunta ya nufi bedroom Win nata, kayanta dake cikin wadrobe gabaWaya ya samu ta saukesu akan gadon, da alama sai data kure adana wajen nemo kayan da zata saka Win, mayafan dake gun ya shiga Wagawa Waya bayan Waya amma duka shegun ne data saba sakawa, kallonta yai haWe da cewa, "Meenal a ina kika kai duka manyan mayafan da kike dasu?" "Na kyautar."

"Dalili?" Ya faWa cike da mamaki ya gyara tsayuwarsa tare da zuba mata idanuwa, sai data Wan yatsina fuska sannan tace, "Sunfa yimani girma shine na bayar." "O.k amma ai kinsan bana don irin wuWan nan Win da kike sakawa amma shine kika bayar da wuWancan Win dana siya mako kiri?a sakasu, good" ya ?are maganar tare da ficewarsa, wani irin takaici ke taso masa aduk lokacin daya juyo ya kalleta dan tana fita ta wuce kai tsaye gaban motar ta shige duk da tasan cewa ba ranar aikinta bane, A?cha kuwa hakan bai dameta ta buWe baya ta shiga, sai da Mutallab ya tsaya abakin wani shago ya sawo mayafin da zai iya rufewa Meenal jiki kusan kala uku aka saka mashi aleda ya sake cewa a saka mashi wasu irinsu guda uku aka saka mashi aleda sannan ya dawo cikin motar, leda Waya ya mi?awa A?cha dake zaune baya sannan ya mi?a mata Wayar yana faWin, "ki cire wannan mayafin ki Wauki Waya aciki ki saka." Yana tada motar, ledar da Mutallab ya mi?awa A?cha tabi da kallo ba tare da tayi abinda yace mata ba tana faman haWe rai tare da juya ta hannunta, ganin har ya sake hawa kan titin batayi abinda yace ba yasa shi juyowa yana kallonta.

"Nifa bana son wannan ledar waccan nake so daka fara bata." TafaWa tana buWe ledar hannunta Win, "A?cha mi?omun ledar hannunki." Mutallab ya faWa yana mi?a mata hannu ta mi?o mashi ranta na susa ganin gabaWaya ma Meenal Win ta rena masu da wayau, ta hannun Meenal ya karSa ya mi?awa A?cha ta amsa tana cewa, "Allah ya ?ara buWe." HaWe da ajiyeta gefe ita kuma ya mi?a mata ta A?cha Win, bako godiya ta buWe ledar ta ciro mayafan dake ciki, gabaWaya ba wanda zai shiga da kayan jikinta saSanin na cikin ledar data bayar da sai da Mutallab ya zabo mata da wanda zai iya shiga cikin kayan, "WaWan nan baza su shiga ba aciki fa." TafaWa tana yamutsa fuska, banza Mutallab yai mata ita kuma A?cha ta danne dariyar data zo mata tana yimata Allah ya?ara, sai yanzu taji sanyi a ranta dan har ga Allah abun ya bata mata rai, maganin mai ruwan ido kenan A?cha ta sake faWa tana rufe? bakinta. Dole Meenal ba dan tana so ba ta Wauki mayafi blue ta Wora akan yellow Win lace Win dake jikinta, dan yafi sauran mayafan shiga da yake ba?i ne da ganyen haki (hhh lol Meenal=??). A haka suka ?araso gidan Aryan Mutallab ya kirasa a waya dan yana gida su kuma suka wuce ciki.

Tarba ta musamman matar Aryan tayi masu da taimakon ?anwarta da aka kawo mata, bayan angaisa A?cha ta koma gefe tana latsar wayarta dan matar Aryan Win irin matan nan ne masu iyayi haWe da nuna kishinsu ?arara akan matan da aka ?ari shiyasa kai tsaye ta nuna Meenal ce tata ta jata sunata fira, A?cha kuma dama batayi mata ba dan haka ta basu iska kora kansu bata bi ba har Mutallab ya shigo shi da Aryan yaiwa matar tasa ya jiki yana faWin, "Madam wato haka kuka batse mani amarya gefe ko? Ai Shikenan zansa abokina ya samo mata ?ar uwa itama." Dariya tayi tana kallonsa haWe da cewa, "To ai ruwa ba sa'an kwando bane Alhaji Mutallab, kaga dole kaga banbanci."

Da haka suka Wan taSa fira sannan sukayi masu sallama Mutallab na ajiye mata kuWin dubiya suka rakasu har bakin mota matar Aryan sai kirari take zubawa Meenal dake gaban mota tana faWin, "Takawarki lafiya uwargida ran gida kuma sirrin cikin gida kuma farincikin maigida." Cike da jin daWi Meenal ta bata hannu suka tafe tana dariya. Sosai Mutallab ya fahimci duk suna yi ne saboda A?cha, motarsa ya ja yatayar suka nufi gida ba tare daya ce ?anzil ba har suka isa, Meenal tafara ficewa cikin motar yana ?an wa?e?enta da habaici sannan aichyta buWe marfin motar itama zata fita. "Mon Amour." Taji ya faWa wanda hakan yasata tsayawa tafasa buWe marfin tana sauraronsa, "Am so sorry for everything, nasan duk abinda sukeyi sun yi ne saboda jiki haushi, so pls krki bari hakan ya Sata maki rai kinji ko." Sai data saki murmushi sannan ya bude ?ofar tafiya, zagayowa tayi ta can Wayan gefensa inda Meenal tafita ta duko kanta ta jikin tagar tana cewa, "Idan dai wannan shine damuwarki ka Wauka ban ji ba kuma ban gani ba, adawo lafiya." Ta ?are zancen tana sakar masa murmushi dan da alamu fita shi zai sake yi, a gajiye ta wuce sashen su t?nte ta gaisheta tana yada zango anan har sai da tayi sallar isha sannan ta wuce sashenta, Mutallab kuwa bayan yayi Sallah shagunansa na Wunkuna ya nufa, bayan ya dawo kuma ya wuce wajen aski daga can Abba yakirashi akan yana son ganinsa, wannan dalilin yasa bai dawo gidan ba har sai wucewar sha biyu a ?a'ida kuma ana gama sallar isha yake dawowa, kasancewar Meenal ce zata karbi girki adaren yasa ta cika tayi fam ganin har lokacin bai dawo ba, a tunaninta yayi hakan ne saboda ita zata amshi girki ba amaryarsa wanda shekaranjiya tana kallonsa ana gama sallar isha ya shigo gidan, da haka bacci ya Wauke ta har ya dawo, sanin dare yayi yasa baiyi tunanin zuwa Wakin A?cha ba sai dai ya tura mata message cewa ya dawo ga abinda ya hanasa dawowa da wuri, ba'a jima ba ta maido mashi da cewa Alhamdulillah ba komai tunda ya dawo lafiya dan haka sai da safe tana ?ara masa da kalmar i love, murmushi ya saki yana wucewa sashen Meenal tare da kunna fitilar palour dake kashe sannan ya kutsa kansa cikin bedrom Winta, da mamaki yake kallonta ganin tayi bacci ba tare data jira dawowarsa ba duk da tasan ita take da girki yau, gefen kanta ya tsaya yana Wan bubbuga pillow Win da take kwance akai yake cewa, "Meenal, Meenal ki tashi mana na dawo." Kamar baza ta amsa shi ba sai kuma cikin muryar bacci, "Da karka dawo ka kwana acan, kuma wallahi kada ka sake tashi na ina bacci, wannan shine adalci naka da kake faWa? Wato tunda ba'a Wauki matar so kake ba shine ka kama kayi zamanka a waje sai yanzu zaka wani shigo Mani kana tashina wai haka ka dawo, to kada ma Allah yasa ka dawo din sai me?" "Ya subhanallahi dama nasan zaki faWi haka Meenal, kiyi ha?uri nake wajen aski ne daga nan kuma sai Abba ya kirani yana son ganina, kin ji abinda ya sa na daWi but am sorry." Wani wasan tsaki ta ja tana gyara kwanciyarta take cewa, "?aryar banza da wofi shi Abban baisan kana da iyali bane.." kafin ta?arasa ya daka mata tsawa cikin Sacin rai yake cewa, "Kada ki kuskura ki daWi maganar banza akan mahaifina ranki ya soma Saci, ke kam bazaki taSa canzawa ba wallahi Allah ya shiryar dake." YafaWa tare da barin Wakin ya nufi sashensa, wata kewar A?cha ce yaji ta taso masa lokacin daya shiga Wakin, ya tabbata da ita keda girki da yanzu tayi welcoming Winsa da kyakkyawar runguma haWe da yimasa sannanu da zuwa taje ta haWa masa ruwan wanka, tsaki yai tuna da Yadda suka rabu da Meenal Win kafin yafara ?o?arin rage kayan jikinsa ya shiga wanka, yana fitowa bai tsaya Sata lokaci ba ko neman wani abu gunta ba duk da ?ar gajeriyar yunwar da yake ji yabi lafiyar gadonsa, ya jima yana juyi akai cike da kewar A?cha kafin ya jawo pillow ya rungume sannan bacci ya Waukesa.


Kiran wayar Idris ne ya tada shi bayan komawarsa sallar asuba, cikin bacci ya lulubo wayar yakai a kunne yana cewa, "Hello Idris?" "Na'am ranka shi daWe, kayi saurin kazo ga shagunanka na Winkin nan sun kama da wuta, Idris ya faWa cikin tashin hankali kamar ma yana kuka, wanda hakan yasa Mutallab cewa, "What!" Da ?arfi yana tashi zaune, "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, gani nan zuwa yanzu." Bai tsaya yin komai ba ya zuba jalabiyarsa ya dauki makullin motarsa ya rufo Wakin, sashen Meenal ya shiga a gaggauce ya shiga sheda mata abinda ke faruwa, "Hmm ai ha??in mutum ba ?aWan bane Mutallab, walla??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????hi kaWan kafani indai bazaka dena zaluntata ba acikin gidan nan." Baiyi mamakin jin kalaman nata ba ya juya yafice daga Wakin ransa a Sace ya wuce sashen A?cha, a rufe yaji ?ofar saboda yana sauri sai ya wuce sashensu t?nte, acan ya samu A?cha a kallo Waya ta hango damuwa cikin idanuwansa, gaishesa tayi lokacin da yake fadawa t?nte abinda ke faruwa bayan sun gaisa ya amsa yana cewa, "Bari na karasa wajen t?nte." "Ubangiji Allah ya tsare yafitar kuma ya takaita abun tare da mayar maka da alkhairi". Ya amsa da "Amin A?cha." Sannan ya wuce t?nte nayi masa addu'a ita da Afrah...





#Mutallab Asad
#?an Tagwaye
#Nana Diso
#Billy s fari
*MUTALLAB ASAD*
Book 2

SHAFI NA TARA.
??
? Arewabook:- billysfari
?
? ? Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.

Kallon Afrah t?nte tayi fuskarta Wauke da damuwa take cewa, "Wannan lamari na Mutallab na bani tsoro Afrah, anya babu sa hannun wasu acikin abinda ke faruwa dashi." "Wallahi t?nte abinda tunanina yabani kenan, gashi jiya muka je wajen da Farouk dan acan ya bayar da Wunkunansa na cin biki kowane yashi an zuba kaya masu yawa wallahi, dan har da muka samu ya Jalil acan nake yimasa zancen kayan da aka zuba yace akwai sama ga kala dubu Waya da aka Wunka za'a fitdasu ?asar Gabon yau, kai! innalillahi wa inna ilaihirrajiun." Afara tafaWa tana zaunawa daga tsaye da take akan hannun kujera, A?cha kuwa ajiyar zuciya ta ja ta sauke haWe da cewa, "Dole akwai jarabawa kala-kala a lamarin mumini t?nte, shi zargi abune mara kyau dan haka kada a zargi kowa mu yadda wannan jarabawa ce kuma dan Allah yana sonsa yayi masa ita, mu ro?i Allah ya mayar masa da lunkin abinda aka rasa ya kuma bashi ?arfin imanin daukar wannan ?addara tasa hannu biyu." "Haka ne A?cha abunne akwai ban tsoro, kuma duk yadda kike ganin mutum baya rasa ma?iya indai yana samun Wauka, sai dai kawai a dage da addu'a."

"To Allah yayi mana tsari dasu." Ta amsa da "Amin." Bayan kamar mintuna ashirin A?cha ta koma Wauki ta Wauki wayarta takira Mutallab, lokacin yana tsaye gaban shagunan nasa da sukayi ?urmumus babu abinda aka fitar suna magana da Idris ya ciro wayar jin tana ?ara haWe da Wauka, "Hello M? Ch?ri in Jin da sau?i an samu fitar da wasu abubuwan." "A'a A?cha ba abinda aka fitarwa komai ya ?one sai dai ace alhamdulillah." "Allah ya mayar da alkhairi ya kuma lillinka maka da Winsu." "Amin ya rabbi sai na dawo." Ya faWa yana jin sanyi a zuciyarsa tare da kashe wayar, haka yaci gaba da amsa kiraye-kirayen ?an uwa da abokanan arzi?i da suka ji abinda ya samesa amma banda Meenal dake can tana faWin ha?kinta ne ya fita na cin amana da zalincin da yakeyi mata wasu har gida suke zuwa suna jajanta masa ciki har da Aunty amarya wanda hakan ba kaWan ya farantawa Mutallab ba yayi mata godiya sosai tana yimasa addu'a da kuma sanya mashi albarka, dan yanzu duniya ta gama yimata hankali tana mijinta da ?a?ansa ga jiki tana ?o?arin kyautata ala?arsu ganin irin gudunmawa da taimakon da suka bata ita da yaranta, don tuni Walid shine general MD na Sangaren wajen Wunkinsa, yanzu haka yana kwance ba lafiya sanadiyar rashin hankalin daya shiga na ?onewar wurinsu, A?cha Mutallab ya zaune dake zaune gefensa yace, "Wannan itace Aunty amarya Waya matar mahaifinmu, nasan ba lallene ki ganeta ba tunda sau Waya muka je gidan kuma cikin dare." "Eh amma na ganeta saboda Afrah nace mani ta tafi wajenta." "Ok to Shikenan." Sai da suka Wan taSa fira sannan Aunty amarya tayi masu sallama ta wuce suka gaisa da t?nte sannan ta shiga sashen Jalil da Fannah ke faman jan tsufa don cikinta ya shiga wata na bakwai ta dubota suka gaisa tana addu'ar Allah ya sauketa lafiya Afrah ta rakota har zuwa bakin gate, juyowa tayi tana cewa Afrah, "Nikam Afrah kin fara gyaran jikinki kuwa? Lokaci na daWa matsowa fa tunda yanzu sauranmu wata Waya ko kuwa?" Cike da jin kunya Afrah tace, "Eh Aunty t?nte tafara haWa mani wani maganin sanyi da ake haWawa da sassa?en mangwaro da mazar?waila tana haWa mani da madara ina sha, "eh dama shi yadace kifara yi yadda kayan gyaran jikin zasu amsheki idan kin sha, kinsan wannan sanyin na infection da kuke cewa idan ba'a fara magance shi ba ko ansha kayan Wa'a basu cika aiki a jiki ba, zan sa Khalil ya kawo maki ganyen garahuni dana sa Hajiya ta samo mani sai ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login