Showing 48001 words to 51000 words out of 54681 words

Chapter 17 - Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa novel

05 Oct 2025

49

taya za'a ce ya aikata wannan mummunan abun gareka, ni ban yarda zai iya yin haka ba MAM kayi tunani?" "Haka ne nima kaina ya kwance, amma ina nan dawowa ?asar gobe." "Ok Allah ya dawo dakai lafiya." "Amin ngode sai munyi magana." Kiran Jalil ya shigo wayarsa ya daga daidai lokacin daya shigo bangaren da t?nte take, shima dai akan zancen ne na Idris daya bashi mamaki sukayi har yana ?arara da cewa, "Yaya nifa komai na iya faruwa saboda duk wani abu mara daWi da zai faruwa gareka shi yake kiranka ya sanar dakai, kaga kuwa indai yana da sa hannu a zancen Wauke Afrah to tabbas dole yayi ?o?arin kashe yaron nan saboda kada asirinsa ya toni, kayi tunani." "Jalil na tsorata da lamarin mutane koma dai meye sai na iso."

A Sangaren Idris kuwa rasa yanda zai yi yayi tunda an karSe wayoyin hannunsa, gaba Waya yarda ta ina zai samu mafita ko kuma kuSutar da kansa, hakan yasa ya kalli wani Wan sanda dake kai da kawo abakin cell Win da yake yace, "dan Allah ka taimaka ka ara mani wayarka inyi kira." Kallonsa dan sandan yayi kamar wanda aka rufe ma baki can ya ciro wayarsa ya mi?a mashi yana cewa, "kada ka daWi yin hakan laifi ne idan aka kamu." "Yanzunnan zan baka Nagode." Idris yafaWa yana karSar wayar tare da komawa can gefe yana gwada kiran wayar da yake son yi..

_Washe gari_

Da wani irin matsanancin ciyo A?cha ta tashi sai amai take kalayawa sanadiyar abincin da Dada ta matsamata taci saboda hanyar da zasu kamo duk da ta jirgi ce, wannan yasa hankalinsu gabaWaya tashi basu samu tasowa ba sai kusan ?arfe biyar na marece saboda Mutallab yakira yace a sauya masu jirgi dan bazai iya barin A?cha anan ba da Dada tayi-tayi dashi yabarta har ta?ara samun sau?i amma ya?i, shine suka jira har sai da aka kara mata ruwa ta samu karfin jiki sosai sannan zuwa marece suka baro ?asar, ko da suka iso saukar dare sukayi, hakan yasa Mutallab bai samu ganawa dasu inspector Kabir ba dan jikin na A?cha ya sake rikicewa kafin su iso, da kanshi ya shiga toilet bayan ya gama wayoyinsa ya haWa ruwa masu gumi sosai a barthtub ya dawo ya dauki A?cha dake kwance jiki duk ba ?wari suka shiga ya taimaka mata sukayi wanka suka fito sannan ya kira dr. Cikin daren yazo yasa mata drip, bai samu natsuwa ba sai da yaga bacci ya Wauketa sannan yafito ya nufi sashen t?nte, abinci ta zuba masa yaci lokacin ?arfe goma, yaso yaga yaransa ?a?an Jalil alokacin amma kasancewar dare yayi yasa bai tashesu ba, da Jalil kawai ya samu ganawa bayan yakirasa a waya ya sameshi palournsa yayi masa sannu da zuwa da kuma tambayar jikin A?cha yace masa ta samu sauki sosai sannan suka shiga tattaunawa akan abubuwan da suka faru, Jalil bai baro sashen ba har ?arfe Waya da wani abu, wanda yana komawa sashensa kuma yafara aiki da system Win da yana shigar da bayanan wani business da suka gamo tattaunawa, Mutallab ma duk da gajiya kasa kwantawa yai yayi zaune yana kallon A?cha da gabaWaya ta rame tamkar ba ita ba, tausayinta ne ya kamashi haWe da sake jin girman uwa acikin zuciyarsa, dan badan abinda ke cikin A?cha ba ya tabbata bazata amince ta zauna cikin wannan wahalar ba da ba ci kuma ba sha. Yana wannan tunanin yaji ?arar security Win dake la?e gidansa, can kuma yaji ?arar gateman da aka yiwa wani mugun bugu akai aka shigo cikin gidan. Gabansa ne ya faWi ya le?o ta window daga can saman Wakinsa, wasu mutane ya hango da zasu kai mutum goma rurrufe da idanuwansu sun shigo, atake ya lakabi wayar inspector Kabir ya kirasa ya sheda masa cewa ga Sarayi nan sun shigo masa gida, kafin ya rufe baki ya hango sun taso ?eyar Jalil da Fannah dake faman kuka Wauke da Farrah ?ar ?aramar ?arsu tana kuka itama sun ta?a masu bindiga akai, hankalinsa ne yayi mugun tashi ya kalli A?cha dake faman bacci, ji yayi bazai iya bari wani abu ya sameta ba kamar yadda bazai iya jurar faruwar komai ga Jalil ba, dan haka da sauri yafice daga Wakin ya rufeta ta baya sannan ya nufo cikin palournsa, bindiga yaji an aza masa akai wanda hakan yayi daidai da ?arar jiniyar motocin ?an sanda da suka shigo layin dan koda yakira inspector Kabir suna kan patrol ne, sannan haka ma ?an sandan dake kai da kawo acan farkon layi kasancewar anguwar ta masu kuWi suna jin ?arar security Win gidan Mutallab suka nufo wajen cikin Sa'a kasancewar gare Winabude yake suna zuwa suka ga Sarayin, take suka fara musayar wuta su da mutun biyar Win da aka bari anan farfajiyar gidan tsare da Jalil da matarsa, biyar Win kuma Waya bangaren t?nte ya nufa yafito da ita, Waya ya nufi sashen A?cha, dayan kuma sashen Mutallab yayin da dayan yana can cikin sashen su Jalil yana kwaso wayoyinsu da sauran abubuwan amfaninsu ciki har da system Win da suka samesa yana amfani da ita. Mutallab najin ?arar halbe halbe da jiniyar motocin ?an sanda yayi saurin kaima Sarawon naushi aciki ya du?e ?asa saboda tsananin azabar da yaji Mutallab ya karbe bindige hannunsa yai aresting dinsa da ita yana shurasa har suka fito ya samu ?an sandan sunyi nasarar kashe mutum uku cikin barayin da sukayi musayar wuta biyu kuma sunyi arresting Win su, sauran da suka fito suna ?o?arin guduwa atake ?an sandan da suka ?arasa shigowa sukayi arresting Winsu aka kwashesu akayi police station dasu..







#Mutallab Asad
#?an Tagwaye
#Nana Diso
#Billy s fari.
*MUTALLAB ASAD*
Book 2

SHAFI NA ASHIRIN DA UKU
??
? Arewabook:- billysfari
?
? ? Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.

Ba ?aramin tashin hankali gidan suka shiga ba da fitar ?an sandan duk makota suka shiga shigowa ana jaje dafatan babu wanda wani abu yasama Abba ba acikin daren yazo yana kara godewa Allah da yakare masa yaransa.

Washegari ma ahaka aka cika gidan da ?an jaje itadai Aicha tana part din Mutallab din dan gaba daya bata jin dadi ga wannan aman da bayajin Allura da magani yasata agaba duk da tana kokarin taga taci abinci Amma da zarar taci kuma sai yafita gabadaya daga ci?inta.? Yanzu ma tana kwance wanka tayi tafito wani mini skirt da vest tasaka saboda nauyi yanzu kayan suke mata ajikinta shiyasa Bason sakawa." " Aicha sannu kinji ko dai asubutin zamu koma ne?" " abin kauna anta zuwa asubutin kagafa babu abunda suke dirkamin sai ruwa dada tacemin inyi hakuri laulayi na Wan lokaci ne kuma yau ma nadanji kwarin jikina bakamar jiya ba." " Sannu Allah yarabaku lafiya ni zan fita yanzu masu shigowa jaje tante tace musu bakyanan kawai dan kinga baki iya wannan hayaniyar yanzu ki kwanta ki huta duk abunda kike bukata kya kirani awaya kinji." " Ina zakaje?" "In son naje naga Idriss ne." " Banason zargin kowa amma abin ?auna duk wanda yake maka ayyukan nan wallahi na jikinka ne kaduba jiya daga dawowarmu abinda yafarau dan Allah, Allah dai ya takaita mana, ni wallahi in na tunama gabana faduwa yakeyi Allah yakara tsareka daga sharrin makiyanka mijina ya kula da lamarinka." "Amin Karki zargi kowa matata rayuwar duniyar nan bata taba tafiya batare da tsananin jarabawa ba." " Tohm Abin Kauna Allah yatsare." " Take care love ki daina tunanin nan kinji Allah ?adai ke karewa kuma shi keyin yadda yaso asanda yaso kinji." Daga masa kai tayi tana gyara kwanciyarta dan bacci takeji sosai.

**********
Meenal kuwa haka tafita daga gidan ba tare da tadamu da maganarsa ba nan tasamu Napep zuwa gida duk da yadda take tsoro hakan bai hana takarasa ba tabawa mai Napep kudinsa tashige gidansu batare da takalli kowanne ma'aikaci ba, ko data shigo mumy na zaune tana cin abinci daga kai tayi ta kalleta tace " Meenal lafiya dai?" Kuka tafashe mata dashi tana zama kusa da'ita nan tashiga gayamata yadda sukayi." Akan dan wannan shine zakiyi fushi haba diyar kirki rayuwar nan sai da siyasa kina kallo Allah yabaki miji nagari mai kaunarki." " Amma kuma yaransa yan iskane Mumy basuda tarbiya " " Kul nakarajin kinfadi haka kiyi hakuri yanzu dole lamarin sai kinsaka siyasa aciki kinji yanzu da suka cinye abincin da bakiyi musu magana ba sai ki tashi ki girka wani idan mahaifin nasu yazo sai gayamasa cikin dabara da siyasa ba da sunan kai kara ba suma yaran kina sakar musu kome zasuyi kada ki taba nuna kin damu yanzu da kika bar gidan ai murna zasuyi ki tashi ki koma kada ma kibari dadynku yadawo yasameki kinji." " Mumy in koma kuma.." " Dole meenal kina dai ganin yanzu ba auren ba mai rikeka tsakani da Allah ya kula dakai ci da sha da suttura shine aka rasa mutumin nan menene bayayi miki? Kuma yaran nasa idan kika duba sun riga sun siye mahaifin nasu da siyasa kinga kuwa kome zakiyi laifinki zai gani dan haka dole kema sai kinsaka kissa duk yadda abu yadameki ki Nuna kamar baki gani ba, tashi muje na kaiki da kaina karki kara wannan shirmen." " Amma mumy Mutallab bayayimun haka kome nayi masa baitaba..." " Kul dinki meenal yanzu kinada wani nauyin akanki." Shiru tayi tana kara bakin ciki da dana sanin zamowa silar kashe aurenta na baya da tayi da Kanta."? Haka kuwa akai dan sai da mumy ta maidata har kofar gidanta ta tura gate tashiga ko data koma yana bangarensa mahaifin nasu dan haka sai data je can tafara bashi hakuri kamar yadda mumy tasakata kamin kuma yace mata tashirya zasuje wajen ubangidansa da barayi suka shigar musa jaje. Batare da musu ba haka tashirya suka wuce, wani irin tashin hankali ne ya mamayeta da taga sun nufo ?ofar gidan Mutallab, wai dama shine uban gidan nasa? Ta tambayi kanta cikin zuciya haWe da cewa, innalillahi wa inna ilaihirrajiun kamar zata saka kuka tace su juya amma tasan bata da damar cewa haka don yasan ko waye mijin nata, dakyar ta iya boye yanayin data shiga da damuwa suka shiga ciki aka yimasu iso ciki amma shi baya nan baya nan sai Tante da Aicha ne suka tarbesu hade da godiyar jaje da sukayi musu, haka yasa ta Wan ji sanyi haWe da samun sassauci aranta tana kallon A?cha data sauya cike da mamakin dan matashin cikin dake jikinta Waya fito, wata nadama da dana sanin abubuwan da tayi masu acikin gidan tasa tafashe da kuka tare da basu hakurin abunda yafaru abaya dan tasan kowannen su bata kyauta masa ba, murmushi sukayi duka suka amsa mata da ba komai tace su bata lambar Afrah da yanzu suka koma London da zama zata kirata itama ta nemi afuwarta sannan sukayi sallama t?nte ta rakota har waje suka gaisa da mijinta da yagama waya da Mutallab yana sanar dashi cewa gashi sun zo yimasa kaje shi da iyalinsa basu isko shi ba yayi masu godiya yana sheda masa cewa ya Wan fita. Bayan sun gaisa Meenal ta shiga suka wuce, gidan yaya kamal ya wuce da ita ta dubo ?arsa mai sunan mahaifiyarsu data rasu suna cemata Mahmah itama da batada lafiya sannan suka wuce gida.

*************
Duk yadda Jidda take kokari sai data kai bata iya kula da Umma yanzu saboda komai yanzu agurin takeyi duk wanda ya?alleta sai ya zubar mata da hawaye ga wari da takeyi da zarar ka dosota yanzu ma jidda ce tatafi bangaren mahaifinsu a guje tana sanar masa cewa " Umma bata motsi Abba." Haka suka dunguma har anty amarya sukayi asubuti da'ita suna zuwa akace ai ta mutu Nan fa kowannensu yashiga hawaye bakaramin tashin hankali abba yashiga ba Anty amarya kam duk ta firgice tana kara tsoron wannan duniyar mai wuyar sha'ani. Kamin karfe 2 ansanar da kowa jana'iza har yan uwanta na kauye inda kowannensu yaki zuwa sai dai su Mutallab ne sukayi mata sallah Aka ?aita gidanta nagaskiya. Haka akayi zaman makoki Asiya ma sai datazo.

Bayan kwana biyu Mutallab ya ?okarta takarfi da yaji aka fidda Idris duba da yaron yaji sau?i akan zargin da ake yimasa tunda bai mutu ba, yaran da suka shiga wajen fashi gidan Mutallab kuwa aka haWe su da yaron shagonsa akaci gaba da gana masu azaba akan su daWi wanda ya turosu amma sunki fada, hakan yasa inspector Kabir ya sake musu nau'in azabar da tasa yaron shagon Mutallab dake ?o?arin mutuwa faWin "nagaji da Wannan wahalar damu da kukeyi zan fadi wanda ya turomu." YafaWa yana kuka saboda tsananin azabar da sukasha. Inspector kabir ne yace, "Muna sauraronka." "Wallahi duk abubuwan nan da mukeyi Aryan ne yake sakamu duk abubuwa." "What?" Inspector Kabir ya faWa cikin tsananin firgita har yana waduwa zaune, bai ?ara shiga tashin hankali ba da tabbatar da zancen sai da yaron yace abashi wayarsa ya kunna masa recording kala kala da sukayi dashi." " Innalillahi wa'inna illahirrajiun!" YafaWa tuna yadda ake faman faWi tashi da Aryan Win ganin anbinciko masu sa hannu a case Win, tabbas makashinka yana tare dakai idan kuwa haka ne dole yau ba gobe ba su kamosa, take ya haWa ?an sandan da zasu je kamo Aryan ba tare daya tsaya jiran komai ba dan duk wata sheda da suke bukata ta kamasa akan zargin suna da ita a hannu, motoci biyu inspector Kabir ya haWa suka nufi gidan Aryan Win, yana tsaye agaban madubi yafito wanka yana shiryawa inspector Kabir yakira wayarsa, cikin gwanewa da iya makirci ya Waya yana cewa, "inspector Kabir ya aiki?" "Alhamdulillah gani kofar gidanka mun samu wasu bayanai." "Very Good Bari nakira MAM yanzu?" "Ni kafito mufara yin magana tukuna." Inspector Kabir yafada cike da mamakin Aryan da duk wuWannan abubuwan da suka faru basu saka yanar alama Waya da za'a iya gano shi ba, suna tsaye yafito gabansa yai wani irin faWuwa ganin ?an sanda cike a ?ofar gidan, bai kai ga yin magana ba inspector Kabir ya Waya masa ankwa haWe da cewa, "You are under arrest." Wani fizgo kai Aryan yayi da karfi yanayin fuskarsa na sauyawa zuwa ta ainahin mugunsa yace, "under arrest inspector Kabir akan me?" "Idan muka je can zaka ji." Inspector Kabir yafaWa cikin sanyin murya yana saurin ri?osa ganin zai komawa ciki tare da saka masa ankwa aka jefasa mota yana faman fizge-fizge akan wane laifi yayi da zasu kama shi. Haka suka isa police station aka karanto masa bayanin da yaransa suka yi tare da kunna masa recording daya gama tabbatar da cewa nashi ne kuma Shikenan asirinsa ya gama tonuwa, don haka duk tambayoyin da su inspector Kabir suka shiga yimasa bai ce uffan ba har suka gaji suka ?yalesa, wayar Jalil inspector Kabir yakira ya sanar dashi halin da ake ciki yace ya bashi mintuna biyu gasu nan zuwa ba tare da yayi wani mamaki jin cewa Aryan ne dasa hannu akan abubuwan da suka faru, abu Waya ne ya bashi mamaki shine yadda ya tsaya yayi ruwa da tsaki wajen bincike bayan yasan shine ?asurgumin mai laifin da suke nema yayita wahalar dasu.

Mutallab na zaune palournsa A?cha na gefensa shi kuma yana aiki da system Win dake gabansa Jalil yai sallama abakin ?ofa ba tare daya shigo ba, sai daya ba A?cha izinin ta shiga ciki ta Wauko mayafinta sannan yace Jalil ya shigo, gaishesa yafara yi kafin yafara yimasa bayanin da inspector Kabir yai masa, wani irin kallo Mutallab yaiwa Jalil na baka da hankali kafin yace, "Sun san ko waye Aryan kuwa awajena? Sun san matsayin da yake dashi da zasu kamasa? Look maza-maza ka kirasu ka sheda masu cewa su sakesa yanzu yanzu ko tashi muje naje da kaina don naga wannan binciken nasu sm bayanda alkibla sai laifi suke Worawa mutanensa." Ya?are zancen yana rufe system Win hannunsa tare da ajiyeta akan Centre table sannan yami?e ya shige ciki ya sauyo kayan jikinsa yana cewa A?cha data shiga kwantawa tayi zai fita amma bazai jima ba yanzunnan zai dawo.

Koda suka isa police station Win har lokacin Aryan na zaune basu cire masa ankwa ba, "What!" Mutallab yafaWa cikin Sacin rai ganin aminin nasa la?e da ankwa a hannu tare da ?arasowa wajen yana cewa, "inspector Kabir wannan wane irin banzar bincike ne haka da zaku rasa wanda zaku kama sai aminina abokina, ko ka manta kowaye ka kama? Aryan ne fa da atare kuketa faWi tashi wajen ganin kun binciko wanda keda sa hannu akan wannan zancen."

"Ranka ya daWe.." "Shut up bana son Jin komai inspector Kabir maza ka kwance sa." Mutallab ya?are zancen a hasale fuskarsa jajir saboda tsananin Saci rai, ba musu inspector Kabir yaje ya kwancewa Aryan ankwar hannunsa ya Wago kai yana kallonsa haWe da murza shatin ankwar data fito ajikin hannunsa, da sauri Mutallab ya ?ara so ya ri?o hannun Aryan din yana dubawa kamar zaiyi kuka haWe da rungumesa yana cewa, "Sorry abokina bansan abun zai kasance haka ba da tuni ba na dakatar da wannan binciken gaba Waya, kayi ha?uri Aryan..." Kafin yarufe baki yaji ya hankadoshi da ?arfi daga jikinsa yana turasa har da kadan ya faWi jalil yai saurin ri?esa su inspector Kabir sukayi kan Aryan Mutallab yai saurin dakatar dasu cike da mamaki yana ?o?arin sake komawa wajensa, "Menene haka Aryan me yafaru abokin." Cikin Saci rai Aryan ke nuna sa da hannu yake cewa, "kada ka sake kirana da abokinka domin duk duniya babu wanda na tsana sama dakai Mutallab, me kake cewa? Ina da matsayi da muhimmanci agunka? To heel with that Mutallab! Kai ba kwan kowa bane awajena face makiyi da akullum wayewar safiyar duniya ba nisa burin daya wuce na cilla rayuwarka cikin kunci da kuma garari, tun muna secondary na tsaneka ganin tare muka taso kuma tare mukeyi komai amma takowace fuska sai ka shiga gabana kafini, tun a waccan lokacin nake shirya yadda zan durkusar da rayuwarka har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login