Showing 39001 words to 42000 words out of 54681 words

Chapter 14 - Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa novel

05 Oct 2025

46

da aka ce baza a bashi Asiya ba Meenal nata yimasa dariya wai yaji yanda take ji lokacin da Mutallab ya?i karSar soyayyarta, gashi shima yanzu ya WanWana sunyi 1-1, Asiya kuwa dama Mommy tafaWa mata kada ta taSa sakawa ranta cewa dole sai ta auri Kamal saboda shi Win ba Sa'ar ta bane, babu kuma tabbacin cewa dole saita auresa tunda suna son juna idan har iyayensu basu amince da aura masu juna ba, dan haka bata bari ta zurfafa ba koda mahaifinta yakirata yace bazata auresa ba cewa tayi Allah yasa hakan shine alkhairi, ta kuma yi ?o?arin datse duk wata ala?a da abubuwan dake kusantata dashi dan nemawa kanta maslaha duk da irin wahalar da take sha, wannan yasa ganin bata daga kiransa, idan yayi mata message bata reply, tadena zuwa gidan Mommy, idan yaje gidansu shi kuma ya aika kiranta bata fitowa ya kwanta ciwo saboda damuwa da tashin hankali ganin zai rasata. Ana cewa iyayenta sun amince daga baya sai ga Kamal ya warke soyayya ta dawo sabuwa tsakaninsu tamkar zasu haWiye juna dan har amsa date Win aurensu nan da wata uku..

***********
A?cha kuwa bayan kwana biyu sun karSi sakamakon gwaje-gwajen da sukayi sun kaima Dr khadija ta duba ta tabbatar masu da cewa duka lafiyarsu kalau babu wanda keda matsala kawai lokaci ne baiyi ba, dan haka sai ta basu shawarwari akan su dan yawaita kusanta musamman a ranakun da ake tsammanin fitowar ?wan haihuwarta (ovulation date) a turance ta hanyar amfani da calendar method, wato tafara ?idaya daga ranar data fara al-ada har zuwa rana ta goma sha bakwai, to a kwanaki bakwan ?arshe wato ranar 11 zuwa ranar ta 17 in son samu ne kullum ya zamana ansamu kusanta tsakaninsu saboda sune kwanakin da akafi tsammanin fitowar ?wan haihuwar mace kuma ana kyautata zaton ciki zai iya shiga, ta kuma rubutawa A?cha folic acid tace kullum ta ri?a shan ?wayar Waya na tsawon wata uku kafin su sake dawowa asibiti, godiya Kamal yai mata sosai sannan sukayi Sallama suka wuce gida suna masu fatan Allah yasa su dace. (kema zaki iya gwada wannan method Win idan kina bu?atar haihuwa, in da rabo sai kiga kin samu, haihuwa Allah ke bayarwa da akwai lafiya da babu, duk wani magani ko tsari da za'a ce ki gwada to kiyi da ya?ini akan cewa Allah zai iya baki ta dalilinsa idan kina da rabon, idan kuma babu rabo sai kiga ba shine silaba wani abunne kadai zai zamo silar ta wata hanyar Adamu.)

Haka A?cha taci gaba da shan maganin da Dr khadija Win ta bata tare da ci gaba da gwada tsarin calendar method har na tsawon watanni uku amma har lokacin shiru, wasu watanni biyu Dr khadija ta sake ?ara masu suka koma gida A?cha cike da damuwa, p.t strip kuwa sun ?arar da yafi kwali daya wanda aduk lokacin da sukayi taga negative hakan na sake sakata cikin damuwa, t?nte ce ta basu addu'o'i tace su rika tashi sunayi duk dare in Sha Allah zasu samu nasu ?a?an suma ganin yadda abun ya dan dami A?cha, dan yarinyar Fannah kullum tana wajenta ko gajiya batayi da reno dan Fannah ta sake samun ciki wata uku kenan yanzu da kwanaki dan tana dawowa arba'in ta samu wani cikin bata sani ba sai kwanaki, tasha kuka sosai lokacin data san tana dauke dashi ganin lokacin babynsu watanta biyar aduniya batayi wayau ba. yanke shawarar zubar da cikin sukayi ita da Jalil amma fir Mutallab ya hanasu saboda ganin yadda yake son ?a?an shi bai dasu su kuma sun samu zasu ce su zubar, ba yadda suka iya dole suka hakura taci gaba da renon cikin A?cha na tayata renon Baby Anam..

A Sangaren Meenal ganin har ta gama idda Mutallab bai waiwayarta ba asalima yaki saurararta yasa da masoya suka taso mata tafara kula su dan bata so mahaifinta ya haWata da wanda baiyi mata ba, sosai an samu sauyin wasu halayenta da Wabiunta musamman wajen tsafta da iya girki duka ba laifi tana ?o?arin gyarawa, jikinta ma tana kulawa ta dawo asalin Meenal Winta tafarko mai don kwalliya da gayu, wanda sai a yanzu ne take mamakin wai duk me ya hanata yin hakan agidan Mutallab musamman tsabtar jiki da suka fi samun matsala dashi. (Karku manta ko akwai halinta to akwai asiri da Umma tayi da bokanta yace zaiyi tasiri ne akan matar da Mutallab zai aura dan suyi nasarar jefasa cikin ba?in ciki wanda sanadiyar rashin tarbiyar Meenal ya janyo sukayi nasara akanta saboda asiri gaskiya ne, annabin Allah ma ya kama balle kuma mutum.)

Islamiya ma tana zuwa yanzu ba laifi sai dai har yau ba iya kalamai da tausasa zance, haka ma idan abunta ya motsa bata fasa gayawa Mommy magana tunda hakan aka Worata tun farko kuma da hakan ta taso..






#Mutallab Asad
#?an Tagwaye
#Nana Diso
#Billy s Fari
*MUTALLAB ASAD*
Book 2

SHAFI NA GOMA SHA TARA
??
? Arewabook:- billysfari
?
? ? Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.



Akwana atashi babu wuya agurin sarki gagara misali A yanayin da kwanaki suke tafiya haka watanni ma suke shudewa zuwa shekaru Mu muke lissafi Amma komai Namu ubangiji madaukaki ya riga ya gama kaddaramana dagon Numfashin naja ina Kara godiya ga Allah abisa Ni'imomin danake ciki Oh ni Aicha yau nice Har nagama service Nafada ina gyara kwanciyata amakeken palon na da yaji sabbin kaya da sabon fasali a gogon da?in Nakallah ina Tunanin Yau ko gobe Ma ch?ri? zai dawo kenan To amma Suprise yakeson yimun kenan tunda dazu mun dade muna waya Amma ya?i gayamun, wani farin ciki nakeji aci?in raina da samun miji mai kula dani sosai da ace Nabiyewa wasu kawayena dasuke zugani akan cewa indage sosai gurin bin malamai dan amallake mun shi batare da ya kara auren wata macce ba da na tabbatar nasaka rayuwata acikin gararin da bazan taba wanyewa lafiya ba. Shiyasa nake yawa gayamusu cewa " ubangijin da yakaddara aurena da mijina yafikowa sannin komai akaina bazan zauna bana addu'a Allah yakaramana kaunar juna ya tsaremu ba Amma bana asarar da kudina agurin dan adam irina wanda na tabbata bazai taba iya tashi shi ?adai ya rokamun Allah bukatuna ba amma ni zan iya zama ni?adai Na rokawa kaina duk abunda nakeso gurin Allah shiyasa ma kwatakwata bana saurarar su aci?in maganganunsu ." Shekarar dana fara makaranta abubuwa dayawa sunfaru daga ciki harda mutuwar jamil wanda ta girgiza mutane dayawa kuma ta haddasa rigima mai girma dan sai bayan mutuwar tasane akejin bashin dayaci kanana da manya wanda asanadiyar hakane sai da abba ya kwanta cuta sosai ganin yadda aban yadamu akan lamarin yasanya Mutallab yabiya kowanne bashin dan'uwan nasa. Ganin har lokacin Allah bai kaddara samun haihuwata ba sai nashiga damuwa sosai tsorona guda dayane kishiya Nabi na rame harma kakan iya fahimtar ina cikin damuwa dan duk lokacin da ma ch?ri? yabani wayarsa to akallah sai naga messages na mata sunfi a kirga Amma abun mamaki bana taba ganinsa yana chatting dasu hakan yasa dai nakasa kwanciyar da hankalina na damu sosai dan gani nakeyi mai wadata irinsa ai karyane ace baya soyayya awaje shiyasa wata rana bayan mungama level 100 yayimun fada akan ban fito da wani abun kirki ba bayan da fari yaga na dage Nan nasaka masa kuka nace nidai danAllah dayake yana bin ?ammata awaje gwara ya auro wacce yakeso. Ranar yayi murmushi ya kalleni baice komai ba " daman nasan kana kule kulen mata dan ina ganin sakonninsu aci?in wayarka ai dole kayimun murmushi ai Nidai ko meenal ce kadawo da'ita da?inka tunda nasan yadda kake kaunar haihuwa ai." " Meenal ai tayi aure yafaWa yana kallona." Adan firgice nace wanne aure kuma." " Am serious yafaWa." Sai naji tausayin kaina kawai dan ganowa nayi idan nice ita ina zan samu wannan gatan sai shedan yashiga rayamun nima idan fa nayi masa wani karamin laifin zai iya aikani gida daga ranar na takure kaina duk da tante tana min faWa sosai akan nadaina saka lamarin haihuwar nan akaina tunda anyi na asubutin anyi na gidan amma shiru. Bankara shiga damuwa ba sai ranar da fannah tazo da yaranta guda hudu wanda ranar naga yadda mutullab yake masu saboda kauna dan yaran dady suke cemasa ma kamar yadda suke gayawa jalil duk da naso abani amira tana jaririya wanda har jalil din ya amsamin amma ganin yadda naga kamar fannah din bataso ba yasanyani jan bakina nayi shiru bankara magana ba bansan dalilinta nahaka ba shiyasa tsakani na da yaran wasa da alkhairi dan yadda mijina ke yimusu hidima ko yaransa karshe kenan dan sai yazamana ko umara zamuje hardasu yake biya amma ni ko da wasa bai taba yimun maganar haihuwata ba a wannan lokacin ne afrah ta haihu itama namiji akasa sunan uban mijinta ansha buduri badankarami ba dan ashekarar suka bar kasar ma suka koma London ita da mijinta da yaronta wanda da ki tayi sai da yan uwan suka sakamata baki, ganin yadda yaga inashiga damuwa wata asabar yadawo daga tafiya ya rukunkumeni yana fadin " DanAllah kidaina dagamin hankalinki mon amour Wallahilazim ko zamu shekara d??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ari baki haihuwa ba ban tuhumarki nasan ubangiji babu ta inda baya jarrabar bawansa mu cika da Addu'a kawai sannan ina rokonki da Allah kidaina damuwa da matan da suke aikamin sako a waya dan ko inaso banaso sai sun aiko koda banda kudi Aicha kyauna da Allah yayimun kadai mata zasu iya bina ballatana kuma inada kudi dan haka kada kikara yaudarar kanki wai yammata basa sona amma inaso kisani bazantaba cin amanar aureba kuma ina rokon Allah yakareni daga duk wata fitina ta mata kwanaki da kikayimun magana nayi murmushi ne saboda rashin sanina da kikayi dan da kinsani bazaki ce wai ina kula kulan yammata ba Allah dai yakara tsareni." Tundaga ranar da mukayi maganar nan nasake sosai sai gashi na maida hankalina akaratu shikuma ashekarun baya zama sosai baga wannan kasar ba baga wancan ba gashi sau uku yake zuwa saudia umarar Azumi wanda dani dashi dasu jalil da yara harda tante da abba ake tafiya sai kuma ta maulidi shima dani ake zuwa aikin hajji ne akaje dani sau biyu nakarshen saboda karatuna ne bansamu zuwa ba. Gyara zaman nayi akan kujerar inajin mugun mutuwar jiki dan dakyar natashi yau daga bacci daga na kwanta sai bacci danayiwa dada complain sai tacemin harda hutu kingama bokon nan ba dole ba hakan yasanya nima nadauka haka dan maganar aiki babu ita tun ina rokonsa har na hakura yanzu.

Matar walid da ita yaranta biyu yanzu itace ma take Wan bani babbar tana wuni gurina harda kwana akwai lokacin dana zolayeta abarmin ita sai naga harda kayanta haka nacigaba da kula da yarinyar Amma sai na lura kamar kakar yaran bataso dan haka sai na mayar da yarinyar kawai bankara zancinba ita kuma bataki kawomin ita ba hakan yasanya nakejin sanyi araina sosai.

Duba agogon hannuna yasanya nayi saurin mikewa nashiga daki nayi wanka nan kamin nagama shiryawa nadan kishingida sai bacci ya kwashe ni nan gurin.

*****

Gaskiya bantaba ganin irin abokinka ba baban ammar " Murmushi yayi yace " Babu irinsa kaf duniyar nan mum ammar bantaba samun kyauta ba irin ta Mutallab saboda yadda yake kaunata kamar dan uwansa." " Wallahi nagani dubi motar nan fa mai kudi sosai ita yabaka kaduba kaga hidimar sunan ammar da yayi shiyasa nace maka da sunansa akasa." Murmushi yayi yace " MAM ai Wan aljannah ne sunansa kuma next baby shi zansaka ai dolena su ummi ma bakiga yadda yake musu ba." " Kai Ai wallahi sambarka da haihuwarsa shidai kudinsa bai sanyashi tozarci ko wulakanci ba ni mamaki nakeyi da har yanzu bai kara aure ba ni nazata zai mayar da meenal ga shekarun sunja itama tanacan gidan mijinta wallahi Zargin matarsa nakeyi anya tabarshi haka kuwa." " Nima batun haihuwar nan yana damuna amma shifa ko ajikinsa wallahi kuma dakike batun matarsa shi aure yasan wani sirri naku na mata ne?" " kai Tabbijan kana wasa da mata wallahi ballantana ita daman kowa yasan asalunta." " Kada ki dauki zunubi abar maganar Addu'a zamu cigaba da tayasu shine abunda yakamacemu." " To Allah yabashi masu albarka."

*****

Sautin kukanta dake tashi a babban palon nata wanda manyan yaran mijin suna zaune kowannen su yana kallo batare da sun farga daga ku?an nata ba ko kuma nuna damuwarsu akan haka dayar tace " Nifa Anty mamaki kike ban wai baki daukemu amatsayin ?a?anki ba." Namijin ne yace " Ke kada kikara sakamun wannan matar matsayin uwata tayaya ta'ina?" " Kada kasake kace zakayimun rashin kunya nagayamaka shikenan ni nazama ja?arku? Kullum bautarku kamar jaka banida sukuni banida Nutsuwa duk abunda Nakeyi bakwa gani ahaka ake soyayya dazarar kunganni bangarena banda sirri sai kuce kunzo kallo." Tsaki dayan yaja maccen kuma tayi murmushi dan duk banza yanzu sun sakata kuka ai. " Kada kakarayimun tsaki." " Nayi din..." Baba ne yashigo yana fadin ?ai kai " Ameer? Menene haka matar tawa? Fitsara?." Da dan zafin kai irin na samarin dake tashen balaga yace " yanzu saboda Allah baba bamuda sukuni agidan ubanmu daga munyi abu sai laifi." Kuka maccen tasaka tana faWin " Ni bamusan me mukayiwa anty ba baba bata sonmu kwatakwa bayan mumyn mu kamin taraso tana nuna mana kulawa daga zuwa bangarenta mu tayata hira ta rufemu da fada harda kuka baba danAllah idan laifi mukayi mata kace tayi hakuri maccen tafada." " Kai kai haba hanifa wanne magana kukeyi haka antynku na sanku kunji mamanku kuma ai ?ar aljannace ita kunji Addu'a damu cigaba da yimata kutashi kitafi." Hanifa ce tace " Anty kiyi hakuri sai da safe." Kasa magana Meenal tayi saboda bakin ciki da munafurcin yaran . Amma dai sau nawa zangayamiki ne akan banason ana takurawa yarana shekararmu nawa yanzu saboda Allah yakamata kisan abunda yake batamun rai shine naga ana wulakanta yarana suna kaunarki suna sonki Amma ke kina tozartamun su to bazan lamunta ba dan gidan ubansu ne nanan sunada ikon yin duk wani abunda sukeso nagayamiki banason hayaniya yau Alhaji mutallab asad zai dawo nagayamiki akwai kayan danakeson kwangila agurinsa nasamu zai ganni da safe kitayani Addu'a nagansa dan harka dashi akwai samu." Tana ganinsa yabar sashin nata hakan yasata shiga da?inta tana fashewa da wani rarraunan kuka mutallab kamar taji yace itakam tashiga uku. Tun bayan data samu hurowa agurin mahaifinta sosai shine tashiga taitayinta ashekrar babu nacin da batayi ba dan taga takoma gidan Mutallab amma babu wata hanya ko kofa dan har gidan Abba taje alokacin ne ma tasan umma batada lafiya gashi tazama abun tsoro ga wata rama datayi gashi jidda bata iya kulawa da'ita yarda yakamata har sai da aka daukar mata masu kulawa Dan asiya ance mata tayi aurenta acan wani gari daban tundaga lokacin sai ta sauka daga wasu abubuwan hakan kuma yasanta daga hankalinta ganin Abba yabata damar zama a manemanta ko kuma shi yazaba mata ganin idan har yazaba mata tashiga uku Nan ta haWu da Alhaji Muhammad nasir shima babban dan kasuwa ne yana matukar sonta dan hakan yasanya bayan auren su jamil da asiya alakarsu tayi karfi matarsa ta mutu kusan shekaru hudu kenan yanada manyan yara uku sai sa'anninta guda biyu biyar kenan dan Mumy bakaramin tausaya mata tayi ba hakan dai aka saka rana har akayi biki ko dataje gidan sai yazaman lamari yacanza dan harta abinci bai yarda yar aiki ta damusu ba sai dole uwarsu tasaka hannu dan haka ya hadata da yaran nasa yace ta mai dasu kamar ita ta haifesu dafari rashin m tadinga yi dataga garan sunfita hauka sau ta sakko sai daga nan suka shiga matsa mata sosai gashi su ba fitsaraba namijin ne ma mai dan fitsara acikin kissa da kisisina sukeyimata tun tana boya tayi kuka har yakai yanzu bata iyawa gabansu ma tanayi gashi da wani masifaffan sin yaransa duk da itama yana nuna mata kulawa Dan karyane tafadi abunda tarasa agidan tun daga kulawa harma da cina ko suttura dan mutum ne mai hali da kyautatawa iyalansa dan wasu tafiyan ma da'ita yakeyi dan da ta nuna masa damuwar haihuwa har waje yakaita akace basuda tabbacin samun haihuwa a ranarbyake fadin " To menene zai dameki babyna ga yarana nan ai na bakisu halak malak " aranar kamar tayi zagi saboda takaici sai kuma tace " Hakane Baby nagode." Yauma tana gama aiki suka biyota dan su takura mata dan abaya ta zata kaunace sai daga baya tafahimci makircin sune wayarta datayi ringing ne yasata dawowa daga tunanin datakeyi kuka tafashe dashi kamin takai kun nanta tana faWin " wallahi nagaji mumy zciyata zata fashe yaransa sun hanani zaman lafiya agidana daga masifa sai bala'i sun hanani soyayya da mijina ni wallahi mutallab bayayimun haka komai shiru yakemun amma sai dai yasamun ido shikuma sai faman nadaina takura masa yaransa ina matsa masa mumy yazanyi tafaWa tana fashe mata da kuka sosai." Har cikin zuciyarta taji babu dadu ha?an yasanya tace " Kiyi shiru kinji bakomai daman kowacce rayuwar aure..
*MUTALLAB ASAD*
Book 2

SHAFI NA ASHIRIN
??
? Arewabook:- billysfari
?
? ? Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.



Kowacce rayuwar Auren akwai kalar tata jarabawar Meenal kiyi hakuri kidaina kuka tunda har mijinki yana kaunarki ai Alhamdulillah. " Wallahi mumy akan lamarin yaransa baya nuna kaunar nan haka wancan karan wai kada nakarayiwa yaransa tsawa idan bazan tayashi tarairayar marayunsa ba to kada nasake na ba?anta musu kuma bakiga yadda nake kokari akansu ba budurwar ma fa rannan wai batajin dadi sai nice zangyara mata dakinta." " To ai sai ki gyara meenal ki tuna idan yaranki ne ai zakiso kema atarairayesu ko? DanAllah karki saka damuwarsu kijasu ajika kicigaba da nuna musu kauna zasu kaunaceki a hankali." " Ta'ina momy so sukeyi su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login