Showing 30001 words to 33000 words out of 54681 words

Chapter 11 - Mutallab Asad Part 2 Complete Hausa novel

05 Oct 2025

42

ne muke dashi da keda karfin tado ?ansanda ba tare da ansamu wata matsala ba, kuma kaga ai alhamdulillah kwalliya ta biya kudin sabulu an amsota kuma kuWinka sun dawo." "Haka ne kuma, Nagode sosai daka kasance mai tsaya mani acikin lamurran akoda yaushe." "Commooon MAM, what a friend's means." Da haka suka ajiye wayar Aryan ya tafa account lamba Winsa ya turawa Farouk." Dariya Mahmoud dake gefe sa yai haWe da cewa, "Gaskiya gayen nan ya ?wareka Aryan, ai dole ya baka kuWi tunda yai maka ?wacen Afrah kana ji kana gani." Murmushi Aryan ya saki yana ajiye wayar agefensa haWe da cewa, "Ba wani ?wace haka Allah ya tsaro Mahmoud cewa tun can ba nine mijinta ba kuma itama ba matata bace, ko da muka rabu da Afrah akwai girmamawa tsakaninta dani shiyasa har yau nima nakeyi mata kallon ?an?ara." "Haka ne." Mahmoud yafaWa yana dariya tare da bashi hannu suka tafe..

***************
Zaune take agaban Dady si faman kuka takeyi ya zuba mata idanuwa, dan shi yanzu gabaWaya al-amarinta yadena bashi mamaki tsoro yake bashi, shiyasa tun jiya da suka zo da ita gida bayan ansallamosu daga asibitin Jabir yai masu kwatance da aka kwantar da ita suka je magana bata haWashi da ita ba, ko washe gari da yazo gaisheshi bai yanka mata ba haka ma da zai fita tayi masa Allah ya kiyaye ko kallonta beyi ba sai yanzu daya dawo daga wajen Mutallab da a wannan karon da kanshi yaje ya sameshi jin lamarin har da saki yayi mashi bayanin duk kalar zaman da yakeyi da ita da cin kashin da takeyi masa. Jiki a sanyaye ya baro wajensa cikin wata irin matsananciyar jin kunyar abinda ?ar tasa tayi, shine ya bu?aci ganinta Mommy na zaune gefe ita kuma ?asa tana kukan munafurci jin daga wajen Mutallab yake cike da tsammanin zai goya mata baya a wannan karon ma, yafi mintuna ashirin yana kallonta ya kasa cewa komai yana tallafe da fuskarsa sai can ya nisa yace, "Kin kyauta Meenal da suka abubuwan da kika yiwa mijinki da ?an uwansa, ban taSa jin kunya irinta yau ba da mijinki ya zauna yana zayyane mani mugayen halayenki, ban taSa nadamar baki gata ba da sangartaki ba sai yau Meenal, tabbas kin cika ?ar halak da kika sanya ni girbar abinda na shuka na hana baiwar Allah nan ta baki irin tarbiyar data dace ga duk wata ?a mace da zata taimaka mata wajen zaman gidan aurenta." Ya?are zancen yana kallon Mommy jikinsa a sanyaye yaci gaba da cewa, "Ashe aikin da kike ?o?arin sata tun tana ?arama dan takoyi girki da iya tsaftace muhallinta gata ce kike yimata amma nake kallon haka a matsayin takura? Ashe faWa da kike yimata nata gyara kanta soyayya ce nake yimaki kallon bakya sonta? Ashe hukuncin da kikeyi mata idan tayi makinmagana cikin rashin Wa'a shine dai-dai da zai sakata ladabtuwa wajen iya tauna kalamai yayin magana amma nake kallon mugunta kike yimata? Kai co! Da nasan wannan rana zata zo da ban hanaki duka haka ba Hajiya Mariya, da akwai yadda zanyi na maida hannun agogo baya wallahi da nayi saboda na tayaki tarbiyar yarinyar nan tare da hukuntata, sai dai kash! Mai gama tariga ta gama, dole na girbe abinda nine na shukashi da hannuwana da sunan soyayya ashe ban sani ba cutar kaina nakeyi tare da lalatawa ?ata rayuwa." Ya?are zancen tare da fashewa da kuka ya Wago hannayensa yana kallo, ajiyar zuciya Mommy ta sauke tare da cewa, "Babu wanda ya isa kaucewa abinda Allah ya kaddaro masa arayuwa sai dai akwai lokutan da ake iya ragewa ?addara kaifi ta hanyar addu'a da kuma tsawatarwa, mu Wauki hakan a matsayin kuskure na rayuwa tare da ?o?arin gyarawa nan gaba, Allah ya sani ina son yaranka gabaWayansu Kamar yadda nake son ?atah Asiya, shiyasa kaga ina matsa masu ga wasu abubuwan da nasan agaba zasu iya cutar dasu musamman ita Meenal Win." Shiru tayi tana tunano abubuwan da suka faru abaya kafin taci gaba da cewa, "Muyi ha?uri mu amshi wannan abun daya faru a matsayin jarabawa tare da Waukar darussan dake cikinta kuma mubar komai ya wuce."

"Kiyi ha?uri Hajiya Mariya bisa duk abubuwan dana tayi mako akan yarana, ga Meenal nan ta dawo awajenki tunda mijinta ya saketa, in taso ta natsu tabiki ta gyara rayuwarta ko don nan gaba, idan kuma ta?i ita tasani gata ga duniyar don tafi bagaruwa iya jima, shekaruna ja sukeyi a yanzu banda tabbacin zan sake rayuwa mai tsayi nan gaba balle na iya gyara abinda ke gyaruwa, sai dai ina so ki sani Meenal wanda duk yafara zuwa wajen neman aurenki bayan kin gama idda shi zan aura maki Dan bazan cigaba da kallonki acikin gidana ba kina suna ?irji da matata ba tare da kidaya mana kwana." Yana ?are zancen yami?e yabar palourn yana mai jin zafin rashin kwaSa da kuma tarbiyar daya kasa yiwa ?arsa ya kuma hana ayi mata a shekarun baya gashi nan yanzu wa gari ya waya tsakanin shi da kuma Mommyn dake iya kokarinta alokacin amma baya gani...





#Mutallab Asad
#?an Tagwaye
#Nana Diso
#Billy s fari.
*MUTALLAB ASAD*
Book 2

SHAFI NA GOMA SHA BIYAR
??
? Arewabook:- billysfari
?
? ? Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k ne.

Kwance take ada?inta ta bararraje dan jiya bakaramin gajiya tayi ba raba dare tayi suna hira da dada duk kuma labarin gidan take bata wanda wasu maganganun dada ta gyra mata wasu kuma tace dakyau zaman aure hakuri ya gada ai wani kuma tace A'a ba'ayin haka daga karshe dai dada ta huce bangaren tante ta kyaleta duk kuwa magiyar datayi mata data kwana abangaren amma ta Nuna sam ita can zatafi sa?e badai taso haka tabarta ta koma tun daga lokacin bata koma ba sai ta tsaya nafilfilo da rokan Allah akan zaman lafiya da mijinta har ma da zuri'ar da takeso ayanzu tunda ta lura kamar sune cikon farin cikin mijin nata. Tunda yashigo sanyi da farar shadda sabuwa dal yaduba mata idanuwa atake kuma yaji ji?insa ya amsa Alamun feeling dan kayan dake jikin iya gwiwarta suke takardun dake hannunsa ya ?allah kamin yakarasa kusa da'ita yana zura hannuwansa acikin rigarta yashiga shafamatasu kamar a mafarki ta buWe idanuwata caraf tarike hannunta tana turo ba?inta. " Danallah menene haka tafada tana kallonsa " " Matata ce fa inada lokacin tabata ne ko rana yafada yana murmusawa haWe da mamakin rashin warin bakinta aduk lokacin da yashigo gurinta da safe saSanin meenal da wani sa'in idan tayi masa magana yanajin warin sosai wani sa'in har ya dan ?auda kansa, cike da son ya tambayeta amma bayason ya bayyana kai tsaye yace kinci abinci? " A'a kasan ina tashi asuba brush nakeyi sannan nayi alwalah na kwanta wani sa'in ma har nakara wani kamin nakara kwancinya." " Good kinga nima kin koyamun yanzu." Dariya tayi tace " ina na isa har ka tunamin da ma mere idan tatasheka sallar asubahi sai tace " kesaka toka ko gawaye ki dirje wannan bakin naki dan tsamin baki da hamami dole ne bazakuzo kunamin magana ina cutuwa ba." Dariya yayi yace " Allah yayi musu rahama nadai kula mama tanada tsafta sosai." " kai sosaima ai idan kaji rigimarmu da'ita akan tsafta ne itafa ko dan gashinnan yataru a mara ko hammata bata yarda dashi yanzu zakaji tana faWin jiki yayita tashin tsami kuwa tunda dai shi dan adam sai da motsi in kuwa za'ayi motsi dole gumi yafito daga nan kuma yacanza yanayi." Dariya Mutallab yayi yace " Allah sarki mama kice tasha fama akanki." " uhmm ai basai nace maka komai ba." Takardun hannunsa ya mi?o mata dan kallonsa tayi da tuhuma kamin ta maida idanuwanta kai Ai batakarasa gani ba taga ansaka admission ai tuni ta Waneshi tana murna " ma ch?ri? am i dreaming?" Rungumota sosai yayi suna kallon juna yace " You're not dreaming mon amour this is my promise daman najirasu ne sukafara bada admission nayi miki komai yanzu abunda yarage miki fara zuwa. Da mugun mamaki tashiga kissing dinsa tana tsotsar harshensa kamar zata ciresu ganin yana kokarin fita hayyacinsa tajanye bakinta tana faWin " Allah yakara rufamaka asiri duniya da lahira Abunda kakemun Allah yayimaka ninkinsa ma ch?ri? amma wannan makarantar tayi tsada ." " Dabadan kasuwanci na ba to waje zan fiddake kije makarantar datafi kowacce tsada kiyi karatun da kikeso Amma bazan iya nisa dake ba gaskiya kuma nima ayyukana yanzu suna shan kaina dayawa sai kiyi hakuri kiyi manejin wannan ko." Kuka tasaka masa tana kara rungumarsa wanda yakara saka ji?insa saki yanajin wani dadi azuciyarsa shi yana ganin babu wani abu da yayi Amma ita yadda take cikin farinciki sai yasa shima yashiga." Allah yakara daukaka ma ch?ri? yayimaka tukwici da zuri'a tagari yarabaka da duniya da mutanen ci?inta lafiya yajikan mamanmu." " Ameen Ameen Aicha bari naje Asubuti umma tana can tun jiya ban leka ba." " Allah yabata lafiya tafada tana masa addu'ar dawowa lafiya sai da yafito yakula har tayi abun kari batare da ya dameta ba yazuba yaci sannan ya huce. Ai tana wanka ta dana bangaren tante canfa tayita musu ihu tasamu admission dada harda hamdala haka afrah aka hadu ana tayata murna kawayen afrah kowa sai yayi mamakin private university din saboda tsadarta. " yanzu sai asaki rai ko ansamu abunda akeso." " Uhmm dada wannan surprise din bantaSa tunaninsa ba wallahi.


haka Abba dake zaune a asubuti shi ?adai dan su anty duk yace musu su koma yanzu dan Mutallab yace masa gashinan shida jalil shiyasa yayi kokarin tsayawa dan shima yagaji da zaman duba da irin manyan asubutin nan ne da basa bu?atar masu kulawa ma da mara lafiya " A'a har ?un karaso?" Barka da safiya Abba suka fada tare suna dirkuwasa." " A'a ku tashi mana yajikin naka ance bakajin daWi?. Dan sosa ?ansa yayi yace " Alhamdulillah." " Ita rayuwar nan hakuri take bukata sai kunyi hakuri dan zama da mata ba abune mai sauki ba kasan ita rayuwar Aure duk inda akace ibadane to sai anyi hakuri sosai akan lamarin dan kasan shedan zagaye yake yaga ya haddasa fitina." " Inshaa Allahu Abba ya mai jikin?" " To tun jiya dai kana gani basu cemana komai ba har yanzun." " To Allah yabata lafiya suka faWa tare a daidai lokacin ne likitan yace " su shigo kowannen su saka kai yayi yashiga gabansu yana wani mugun bugawa da yasanya su faWin Subhanallahi ganin yadda ba?in umma ya?arkace ga idonta arufe ga kuma hannunta kamad an manner mata shi." Gaban mutullab ne yadan buga yace " doctor lafiya kuwa kaga ba?inta fa?" " Shiyasa nace kushigo ai sanadiyar waWuwar datayi tasamu shanyewar jiki sannan idanuwanta ta daina gani munyi duk wani gwaje gwajen da zamuyi Amma gaskiya bamusan matsalar ba sannan hannayenta ma sun daina aiki zadai mugwada dorata akan magani mugani." " Abba zan shirya komai afiddata waje sai .." " Ranka yadade maganar gaskiya zan gayamaka irin wannan laruran ko'ina kakaita asarar kudinka kawai Zakayi banki kuje kuyi tayi mata addu'a ba." Jalil kam hawayene yacika idonsa yafita haka shima abba Nan suka rubuta mata sallama haWe da keen turawa Mutallab da wasu likitoci suka taimaka aka kaita mota basu tsaya ko'ina ba sai gida. Suna isa mai gadin ya buWe musu kofar shiga duk yawancin ba?in ne suka fito haka anty amarya asiya jidda dake gefe guda itama sai dada da shigowarta gidan kenan. Yadda jalil yasakko da keen Abba yafito suka kamawa Mutallab aka sanya umma yashiga turata yadda kowa ya ganta sai da gabansa ya waWi asiya ce tatawo da gudu tana kuka tace " Yaya me yasamu umma? Shima sai yaji kwallah tana kokarin tarar masa " Allah zai bata lafiya kidaina kuka." Bakaramin rikewa sukayi ba gaba dayansu kowa sai sannu yake ambata Anty Amarya ma fashewa tayi da kuka haka jidda da gaba daya itama sai ahankali dan tana hango Abba ta gudu bangaren anty. Haka suka kai umma bangarenta nan mutane suka shiga shigowa suna jajanta mata haWe da neman Allah yabata lafiya.

Mutallab kam yana fita yahuce bangaren Anty Amarya nan yataddata tana kuka yace " Addu'a za'ayi mata ba kuka ba menene kuke bukata anty na yinin bikin naku?" " Mungama komai na kamu su jalil sunyi yinin kuma akwai ai kayan abinci kayan miya ne dai." " Tohm badamuwa za'a kawo yanzu da nama." Godiya tayi masa har zai fita yagano jidda dake gefe guda kuma daman duk yasaurari hirar jalil da abba akan jiddan har ya Nufota batasan yazo ba sai da yazauna akujerar kusa da'ita sai da ya taSata sannan ta dan firgita zata gudu " jidda yafada yana kallonta cike da tausayi dan itama tanada haske duk da dai bata kaisu ba amma tanada haske amma yanzu tayi bakirkirin." " DanAllah karka dakeni nadaina wallahi." " Me isa zakisaka rayuwarkin acikin shaye shaye jidda da hankalinki da karatunki? Meke damunki gayamun me isa baki tafi can gidana ba kika zauna ke kadai anan? " " Yaya danAllah kayi hakuri kunyar afrah nakeji wallahi kaga.." " Is okay banson nakara ganin kinsaka komai bakinki da niyar sabawa Allah kokuma cutawa kanki shaye shaye bashida wani mafita ko amfani atattare damu kinji komai yayi tsanani saukinsa yana tare da Allah ki rabu da batun mijin nan naki tunda yariga yasakeki inshaa Allahu kidage da Addu'a Allah zai baki wanda yafishi kinji tashi muje kiyiwa umma yajiki sai ki bawa Abba hakuri daga nan kitafi gurin su afrah." " To yaya banda kayan sakawa ai kuma ko kaina ta nuna masa ba agyare yake ba." " komai dake nasaka ta dinka ai sunyi dinki dake kitso kuma sai kije ayimiki." Har zatace batada kudin sai tayi shiru da bakinta shikuma ya tasata taje tayiwa umma yajiki aranta bataji komai ba dan tana ganin mahaifiyar tasu itace tajawowa kanta komenene yanzu wanda take wulakantawar sune dai mataimakan nasu baki daya " Umma nasha gayamiki kidaina aikata abunda kikeyi nasha gayamiki watarana zamuzo muji kunya yanzu ni bama kunya ba yadda mukayi musu abu abaya amma basu mantamu suna kulawa damu yanzu ga inda sharri yaje ki lallata mana rayuwa baki dayan mu gataki nan itama ta lallace." Daga nan tayi dakin abba shima tabashi hakuri fada sosai yayi mata kamin yace ko da wasa yakara ji ko gani tasha wani abun to tabbas sai ta bar masa gida. Tana fitowa Mutallab ya dauketa yakaita aka wanke mata kai har kunshi akayi mata daga nan yace tayi gidansa da fari tsoro ne yahanata shiga amma daga baya tashiga daman kuma tace bangaren matarsa ta biyu zataje gaskiya dan bata iya shigarwa su tante kai tsaye haka kuwa akayi danhaka Aicha sosai ta tabeta har tabata abinci dasu afrah suka shigo kuma tashige cikinsu sai daga baya take tausayin kanta dan duk yadda take tunanin wadatar da afrah zatashiga tafi ma amma haka tasaki jikinta akayi komai da'ita kuma duk inda Afrah ta zauna sai tace ga yar uwata nan.

Tundaga sama yatsaya yana kallonta tana kwance ta kunna kida abinta ko ajikinta tana chatting dinta " Ke meenal " Dady yafada yana zuba mata idanuwa. " Naam dady tafada tana kashe wakar tana kashe wayar gaba daya " Wakike jira ya gyaramiki dakin? Kuma da kika kwanta mumy tana kitchen bazakiji kuyi girkin tare ba?" " To dady nifa ban iyaba ." " To wayeke miki nagidan mijin naki?" " Order nakeyi tafada bako kunya." Daka mata tsawa yayi yace " Daga yau ke zakina koyan yadda zakiyimana abinci Wallahilazim ko da wasa wasa kinji nafada kika kara kwanciya tana aiki agidannan to tabbas sai na ballaki mara mutunci kawai sha sha sha kuma kishirya zan sakaki a islamiyya yafada yana barin da?in. Cikinta ne yakada saboda faWan da yayi mata ha?an yasanyata saurin shiga bandaki da gudu tana kasayar da abunda yataso mata daga nan kuma tatafi kitchen tana fadin " To yanzu mumy da kikagayawa dady banzo natayaki ba me zan tayaki tunda ban iyaba?" Mamakin rashin iya lafazin yarinyar tayi sai kuma tace " Bazaki koya bani ba?" Shima Mutallab din zai gaji da fushinsa yazo ya daukeni ne." Mamaki ne yakama mumy dan tabbas takara yarda yanzu meenal tarbiyarta sai a hankali kai wannan jahilci ne ma ."


Bakaramin kyau sukayi ba dan yau daga gurin kwalliya sukayi shigewarsu gurin event dan ita daman aicha tan tsoron ya hanata zuwa daman basu suka dawo ba sai wajejen 12 nadare Aicha sai tashigo motar su mohamud ta dawo wanda saukarta gaban motar muhamod yayi daidai da saukarsa idon Mutallab dayagama jiransa yacika yayi fam dan yace yauma ai bata tambayeshi ba tasan yanzu yayi bacci dan haka sai ta huce bangarensa direct tana shiga ya rufeta da fada " duk motocina sai wani kato yadawo dake Aicha me isa kikeson canzawa ne? Matar aure ce kefa har kije can ki zauna har 12 babu mijinki aciki? Kuma akan wane dalili zai dawo dake me isa baki biyo jalil ba? " kallon wutar bala'in dake cinsa tayi tace " Ayyah ma ch?ri? Jalil baije ba Allah kuma motocin wasu mazan ne nikuma naga ya muhamod shine dan uwana shiyasa nashigo tasa kuma kasan ban iya tuning dare ba danAllah kayi hakuri bazan kuma kaiwa dare ba." "babu inda zaki kuma zuwa." " ma ch?ri? gobe ne fa kamun kayiwa Allah kayo hakuri mijina abun kaunata masoyina tafaWa tana rungumoshi ta baya sai kuma ta jujjuya tace " danAllah banyi kyau ba." kau da kansa yayi yace " bakiyi ba." Shagwaba fuskarta tayi tace " Haba Abun kaunata danAllah am sorry...
*MUTALLAB ASAD*
Book 2

SHAFI NA GOMA SHA SHIDA
??
? Arewabook:- billysfari
?
? ? Paid book ne, N500 via ACCOUNT NUMBER
0020428430
Ishaq Fatima A, Gt bank, sai shaidar biya ta +234 704 040 2435 ko +234 809 845 6130 Ga masu son vip post 1k

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login